TSANANI

52

by @mmnashfaq

103/104






***





Shugaban su yace "ba kowa bane suka maka wannan aiki sai d'aya daga cikin y'an uwan yara ukun daka lalata musu rayuwa, shiyasa mukayi k'ok'arin nuna maka illan koran yaran nan da kayi amma a lokacin ka nuna mana taurin kai dan ka k'ara aure ka samu abunda kakeso baka buk'atan su, daka bari k'ungiya ta gama moran kwayoyin halittan su daga k'arshe muka kashe su da haka bai faru dakai ba, tun lokacin da yaran nan suka koma gida suke jinya domin ba k'aramun rarike su kayi ba, d'aya daga cikin su ta mutu a wajen jinya, biyun kuma sun rayuwa dakyar, hakan yasa yan uwan wanda ta mutu sukaje gidan su sauran yaran suka nemi address d'inka domin yarinyan ta sanar dasu komai daya faru tsakanin ku kafin ta mutu, sun jima suna targeting d'inka, sai yau suka samu dama duk da Matan ka sukaso suyi raping amma basu sameta ba sai suka huce akan y'arka, sukace suma sun rama abunda kama y'an uwan sune kaji inda zafi"


Ya bud'e baki zaiyi magana aka dakatar dashi sukace yaje ya nemo musu Zainab domin itace a gaban su yanzu, dan idan bai kawo taba komai zai iya faruwa dashi.


Yana dawowa d'akin tsafi yaga kira ya shigo wayan sa ya d'auka, sheda masa akayi maigadi ya gudu yabar asibin, ranshi ba k'aramun b'aci yayi ba, dan yaso a kamasa yasan duk yadda akayi da had'in bakin sa hakan ya faru da y'ar sa, gashi baisan daga wani gari yazo ba, zuwa yayi d'akin driver ya tambaye sa koya san garin su maigadi, ga mamakin sa shima driver baya nan ba kayan sa ko d'aya a d'akin, shima bisaga halamu guduwa yayi, haka ya koma d'aki zuciyar sa ba dad'i, yana zuwa ya tadda Hanifa a tsaye cikin shirin ta na futa, ya k'arasa kusa da ita da sauri yace "ina kuma zakije? Cikin kuka tace "inaso naje naga halin da y'ata take ciki ne? Yace wata y'ar kin data mutu tun ranan da aka Mata fad'e" bata k'arasa jin abunda yake cewa ba ta fad'i ta suma a wajen, ruwa ya d'auko ya yayyafa Mata ta farfad'o, kuka ta saka masa tace yanzu shikenan Arfat ta mutu? Sun kashe mun y'ata yanzu ina gawan ta yake?


Sai lokacin ya tuna da ko gawanta baikai ba, tashi yayi ya shiga d'akin daya ajiye ta, ya ganta a inda ya barta, bata rib'e ba kuma bata sandare ba saboda abunda ya zuba Mata daga bakin sa dauk'an ta yayi yaje toilet ya Mata wanka harda soso da sabulu kafin ya d'auko rigan farin shaddan sa ya saka Mata, shi d'aya ya kaita mak'abarta ya binne ta batare daya Mata sallah ba, yana dawowa gida ya samu y'an uwan Hanifa a cike a gidan, ta'aziya suka masa ya wuce d'akin sa, har ranan suna, suna gidan basu tafi ba, baiyi wani taron suna ba, amma ya kawo kaji da saniya, wanda suke gidan sukayi watan dan sa, lokaci yana ta tafiya har y'an biyu suka sheka suka fara gudu ko ina k'ungiya bata sake mishi maganan Zainab ba, kuma bata d'auki y'arsa ko d'aya ba, duk da yana iya k'ok'arin sa na ganin ya samo Zainab d'in amma abun yaci tura, ga mutuwar Arfat yak'i b'ace masa a zuciyar sa, dan ji yayi dama shi suka kashe suka bar masa ita, b'angaran Hanifa kam zuwa yanzu ta hak'ura da mutuwar Arfat ta rungume y'an biyu tana nuna musu soyayya sosai, saidai rashin maigadi a gidan ya mungun d'aga mata hankali, shiyasa yau da Umar ya shigo ta tunk'are sa da maganan.


Kallon ta yayi yace "Hanifa yanzu har kina sha'awan maigadi a gidan nan bayan duk abunda ya faru damu na mutuwan Arfat"


Tace "Arfat kwanan tane ya k'are amma bamai gadi bane ya kashe ta, saidai jikina yana bani sun had'a baki da Zainab ne ta turo wasu suka ma y'ar mu fad'e harta mutu, amma yanzu kaga duk wanda ka kawo zaiyi mana aiki maikya domin ba sanayya tsakanin sa da Zainab"


Umar shuru yayi yana nazarin abunda ta fad'a, yasan tabbas Zainab zata iya zuwa ta had'a baki da kowa ma dan ganin taga bayan sa musamman da tasan bata da d'a yanzu, furzar da iska mai zafi yayi a bakin sa yace duk inda kike Zainab zan nemo ki na d'auki fansan abunda kika ma y'ata, tabbas wannan karon bazan barki ba, waya yayi yasa a turo masa sojoji biyu suna masa gadi a gidan sa, kafin ya tashi ya shiga d'akin Zainab albums d'inta ya d'auko ya ciro photon ta guda biyar ya kai duk kafofin watsa labarai akasa cikiyan ta, da alk'awarin duk wanda ya ganta za'a bashi mak'udan kud'i mai mungun yawa"



Inna Turai tunda ta koma gida ta mance da wata Zainab ta bud'e kasuwancin ta, daga farko kasuwa ya bud'e Mata tana ciniki sosai abunka da k'auye, k'auyen ma k'aramun k'auye, ganin yadda ta dawo da kud'i sosai sai aka fara k'in siyan kayan hanun ta ko wani magidanci ya hana iyalan sa shiga gidan ta, tana futowa zataga ana gudun ta, idan ta nufi inda taron mutane suke tun kafin ta k'araso zataga an watse wasu har kifawa sukeyi, abun ya fara d'aure Mata kai, gidan ta ya dawo bamai shiga, daidai da ya'yan ta da suke cikin gidan sun futa a gidan sun kama haya, yau tana zaune tayi nisa a tunani taji sauk'an jifa a jikin ta da sauri ta tashi ta futa, dandazon Mata tagani a waje da wani yaro a kwance baya nunfashi tace "bayin Allah lafiya? Meya samu yaron?


Ashar suka dura Mata kafin d'aya daga cikin su tace "ban tab'a zaton ke ba dattijuwan arziki bane sai yau, duk irin gudun ki da mukeyi hakan bai miki ba shine saida kika kama min d'ana, wallahi koki sake shi komu kashe ki yanzu anan"


Kuka Inna Turai ta saka tace "y'ar nan ni kike kira mayya da girma na?


Tace "inba mayya ba to meye ke, kuma a ina kika samu mak'udan kud'in da kike kashe wa inba ta maita ba, mufa bamu son dogon jayayya domin aradun Allah idan baki sake mun kuruwan d'a ba zamu iya kashe ki anan mu kashe banza"


Inna Turai cikin kuka tace "wallahi niba mayya bace, kuma sheda ne dan duk zuri'an mu ba maye" rufeta da duka sukayi kafin suka Mata tsirara. Akace ta tsallake yaron da yake kwance, yaro da dama dogon suma yayi saboda fad'owan da yayi daga bishiya, zallakawan Inna Turai yayi daidai da farkawan sa, suna ganin yaron ya tashi suka dad'a tabbatar da mayyace ita, duka suka tufeta dash saida suka tabbatar bata iya futar da nunfashi maikyau tsaban duka kafin suka barta suka tafi.


Dillaliya ce kawai ta tsaya ta taimaka Mata suka shiga cikin gidan, ta gasa Mata jikin ta sosai, kafin ta Mata shinfud'a a tsakar gida ta kwantar da ita tace "keko Turai da girman ki maiya kaiki karb'an maita a birni?


Inna Turai tace "Dillaliya niba mayya bace wallahi, nida ko tafin hanuna bana gani ta ina zanyi maita? Labarin yadda ta samu kud'i ta bata, da irin butulcin data ma Zainab.


Dillaliya jin tana da mak'udan kud'i yasa ta gyara zama tace "kema kinyi kuskure nuna kina da kud'i a karkara Inna Turai, yanzu abunda zamuyi ina da wani d'an uwa a cikin Birnin Kano sunan shi kantin kwari, yanzu ki kawo kud'in na kai mishi yana juya miki kina karb'a da kad'an kad'an, kinga ba wanda zaisan kina da kud'i ma, sannan kuma zaki zauna da kowa lafiya.


Inna Turai fad'a Mata inda kud'in yake tayi, Dillaliya jiki har b'ari yakeyi wajen d'aukowa, ka nannad'e kud'in tayi a cikin fatarin ta, ta futa dashi ba tare data sake bi takan Inna Turai ba ta fuce a gidan, Inna Turai kullun tana saka Ido taji ta inda zata b'ullo amma shuru har shekara ya gota, kuma zuwa yanzu daidai da abincin da zataci gagaran ta yakeyi, yau taje k'ofan maigari tace dan Allah ya tara Mata mutanen garin akwai abunda takeso ta fad'a musu.


Yasa aka tara masa mutane k'auyen tas, kafin ya Mata gargad'i da karta kama kuruwan kowa a wajen, bayan kowa ya gama hallara, Inna Turai ta fara musu bayanin yadda akayi ta samu kud'i, da duk kalan cin amanan da tayi a birni wa uwar d'akin ta, ta k'are da cewa wallahi ni ba mayya bace nasan hakkin Zainab ne yake bibiya na, dan Allah ku duba girma na ku daina zagi na da duka"


Wajen ne ya kaure da kuskus kowa yana Allah wadar da hali irin na ta, daidai da ya'yan ta basuji tausayin ta ba, saida mai gari yasa su dole suna ciyar da ita, tun ranan aka daina ce Mata mayya, saidai duk garin ba maiyi da ita, ya'yan ta ma sai tayi wata uku bata gansu ba, saidai kullun zasu saka Mata abinci can k'asan kwano suba almajirai su kai Mata, dan sun hana yaran su zuwa wajen ta, rayuwa gaba d'aya ya juya Mata, bamaiyi da ita a garin, gashi bata da ko sisi ballan tana tabiya kud'in motan da zataje garin su Zainab ta nemi gafaran ta, ta dawo abun tausayi duk wanda yasan ta da ya ganta yanzu bazai ganeta ba, zuwa yanzu ta koma ga Allah kullun cikin sallah da neman gafaran ubangiji take.




Amna tana zaune a falo suna kallon labaran NTA taga an hasko........






***






Mmn Ashfaq