TSANANI

53

by @mmnashfaq

105/106






***






Taga an hasko photon Zainab, dafe k'irji tayi tace "Momma na maiya faru ake neman ki? Matsawa tayi jikin tv dan taji abunda ake fad'a dakyau, duk wanda yake falon nutsuwa yayi danjin abunda za'a fad'a, sanarwa aka farayi da cewa "ana cikiyan wannan baiwan Allah ne data b'ata shekara biyu da suka gaba ta, ta futa gida cikin tashin hankali har yau ba'a sameta ba, sannana anama duk wanda ya ganta koya sanar da inda take albishir d'in za'a bashi million goma kyauta, Allah yasa a dace, sanarwa daga mijin ta Umar Gambo" kafin aka jero numbers d'in da za'a kira, jiki na b'ari Amna ta kira Zainab, tana d'agawa tasa kuka tace "Momma azzalumin mutumin nan ya bada cikiyan ki dan Allah ki kula mun da kanki, karki bari yasa a sace ki dan Allah.


Murmushi Zainab tayi tace karki damu insha Allahu bazai tab'a samu naba, yaushe zaku fara final exam d'inku?


Amna da har yanzu bata dawo daidai ba tace "sauran wata d'aya" addu'a Zainab ta Mata kafin sukayi sallama, suna ajiye wayan kiran Ammar ya shigo wayan ta jin muryan ta yasa ya gane itama taga abunda ya gani, yace "Amna kaman photon ki naga ansa kuma naji har anbada mak'udan kud'i ga wanda ya sameki, dama kin tab'a aure ne? Dan naji yace mijin ki Umar"


Tace "bani ake nema ba, Momma na suke nema kuma Umar d'in shine ma'aifin mu, Zainab kuma itace Momma na"


Ajiyan zuciya ya sauk'e kafin yace "ki kwantar da hankalin ki insha Allahu bazai tab'a nasara akanta ba, nima zan shirya sanarwan an sameta kuma tana gidan iyayen ta, amma sai kingama exam zan sanar da nawa" godiya Amna ta mishi sukayi sallama, washe gari Amna tana shiga school taga anata nuna ta, wasu harsun fara kiran waya suna sheda sunganta gasu tare da itama ma, jin haka yasa Amna taje security office da yake school d'in, ta kira number Ammar ta sanar dashi halin da ake ciki, yace tab'a security da yake kusa da ita wayan, suna karb'a ya fad'a musu waye shi da kuma ma'aifin sa kafin ya musu barazanan da karsu bar kowa yazo kusa da ita, yana kashe wayan ya kira Daddy sa ya sheda masa halin da ake ciki yace yaje wajen ta yanzu zai turo y'an sanda su futa da ita, a take ya d'auki hanyan school d'in.


Amna suna gama wayan ta kira Zainab tana kuka ta fad'a Mata abunda yake faruwa, Zainab hankalin ta ba k'aramun tashi yayi ba, a take ciwon ta ya tashi Abbah shigowan sa kenan yaga nunfashi ta yana sama sama, y'an uwanta maza ya kira akan suzo a kaita asibiti, Abbas dawowan sa daga school kenan ya samu Momman sa a wannan halin cikin tashin hankali yake tambayan abunda ya faru, sukace suma a haka suka ganta.


Yace "dole akwai abunda aka fad'a Mata ya d'aga Mata hankali" wayan ta ya d'auka yaga last call d'inta, sunan Amna ya gani yace mai ya faru da Adda Amna na dayasa hankalin Momma tashi, kiran ya sake bi Amna tana d'agawa cikin kuka tace "Momma sai kiran waya sukeyi" Abbas yace suwaye suke kiran wayan? Tanajin muryan Abbas ta fashe da kuka tace "Abbas azzalumin mutumin nan zaisa akaini wajen sa yanzu"


Abbas cikin tashin hankali yace wani mutumin? Daurewa tayi ta mishi bayanin komai, ajiyan zuciya ya sauk'e yace "yaushe kika fara tsoro ban sani ba? Meyasa kike abu kaman ba baffulatanan riga ba, Adda Amna karki manta Baffa bai raini zuciyar mu da tsoro ba, ki futo ki taho gida duk wanda ya tunk'are ki kinsan makasa ki murd'e sa ya mutu, idan sukaga haka zasu rabu dake, kefa cikekkiyar baffulatana ne, karki bari Hausawa suyi nasara akanki" k'arfafa Mata gwuiwa yayi tayi har taji tsoro da fargaba yabar zuciyar ta, tace "karka damu Abbas koda yayi nasaran d'auka na namaka alk'awarin saina dawo ajalin sa yau d'in nan basai gobe ba kaman yadda yayi zaton yayi namu, ya zamo dole yasan muna raye, kuma yau zan sanar dashi Momma tana raye kuma tana gidan ma'aifin ta tare da iyalan ta dayayi zaton ya kashe, ka kula mun da Momma ina nan dawowa gare ku nan bada jimawa ba" kashe wayan tayi ta tashi zata futo fili ta inda za'aji dad'in kamata, amma security suka hanata futa fur, ranta ba k'aramun b'aci yayi ba ta d'aga hanu ta tsinkawa sucurity mari, ga mamakin ta sai taga ya sunkuyar dakai baice Mata komai ba, jiniya taji ta buge hanun security ta futa, dan a zaton ta har anzo dauk'an ta ne, tana futa taga Ammar ya taho wajen ta cikin tashin hankali yana tambayan ta ba abunda ya faru da ita? Tace "yanzu dai ba abunda ya faru, saidai bansan zuwa anjima ba" kafin ya bata masa Daddy da Yayan Abbah da Daddy ya biya ya d'auko sa suka k'araso wajen, Daddy yana zuwa ya Mata umurni data shiga motan security, tana shiga suka d'auki hanyan Birnin Kudu direct.



Abbah jin abunda Abbas yake fad'a yasa suka tsaya da futa da Zainab da suke shirin yi suka tambaye sa abunda ya faru, bayanin komai ya musu, Abbah yace "kar kuyi wannan kuskuren, kabari ta dawo gida tukunna sai musan abunda zamuyi dan maganin wannan abunda ya tunk'aro mu" waya ya ciro ya kira k'anin sa na bauchi, tun kafin ya fad'a masa k'anin sa yace masa nasan abunda yake faruwa yanzu haka ma muna hanyan Birnin Kudu"


Hamdala Abbah yayi kafin suka d'auki hanyan asibiti, likitoti sunyi iya bakin k'ok'arin su amma Zainab bata farfad'o ba, dole yasa suka buk'aci a kira musu ainihin doctor ta, doctor Mansur yana office yana aiki yaga kiran Zainab ya shigo wayan sa murmushi yayi yace "y'ar halak kaman kinsan tunanin ki nakeyi a zuciya ta, d'agawa yayi bakin sa d'auke da sallama yana lumshe Ido, jin abunda Abbas yake fad'a masa yasa ya bud'e idon sa da sauri ya tashi, yace gani nan zuwa yanzun nan" ko gida bai jeba ya wuce airport, ya koyi sa'a ya samu jirgi zai tashi, fasinja d'aya yayi jinkiri, aka maye gurbi dashi, yana sauk'a a Kano yayi shatan mota zuwa Birnin Kudu, kwatancen asibitin akama driver yakai shi, yana shiga ya fara bata taimakon gaggawa, bakin sa ya had'e da nata yana hura Mata iska, bai jima yanayi ba ta farfad'o, ya Mata allurai tare da d'aura Mata ruwa, likitotin sunyi mamakin ganin simple abu ya Mata ta farfad'o sab'anin su da suka jima a kanta, futowa yayi yana goge zufa kafin ya tambaye su abunda ya faru, Abbas ne ya mishi bayanin komai, Ido doctor Mansur ya zaro yace yanzu ina Amnan? Basu rufe baki ba sukaji shigowan su Amna, tana shigowa taje ta rungume Malama Aisha tana cewa meya samu Momma na? Hak'uri doctor Mansur yayita bata kafin yace "ki nutsu kije ki zauna kusa da ita, inaso idan ta farka ta fara Ido biyu da dake.


A school kuwa student sun dage sai kiran number Umar sukeyi bai d'auka ba, Umar yana ta baci saida ya farka yaga kira barkatai a wayan sa daga different numbers kafin yabi kiran wani kiran ya sake shigowa ya d'aga, sheda masa akayi anga Zainab a ATBU bauchi, dirowa yayi daga kan gado yace "karku barta ta gudu yanzu zan turo a d'auka mun ita" Umar kiran wani d'an k'ungiyan su da yake Bauchi yayi yace masa anga Matar sa a bauchi dan Allah yasa aje a d'auko ta, yace masa ba damuwa yanzun nan za'a d'auko ta, ana zuwa aka samu bata nan, hankalin Umar ba k'aramun tashi yayi ba na rashin ganin ta da ba'ayi ba, ya kira wanda ya kirasa ya sheda masa anganta yace meyasa kayi saken data gudu?


Yace "ranka shi dad'e ina tabbatar maka dazan samo maka ita dan batasan ana neman taba, kabani daga yau zuwa gobe har gidan da take da zama zan binciko maka" Umar yace ya turo account number sa ya yura masa 2 million, idan kuma yayi k'ok'ari aka ganta zai k'arasa masa sauran 8m d'in"


Jiki na b'ari yaron ya tura masa ba'a jima ba saiga alert d'in 2m farin ciki kaman zaiyi hauka.


Umar yanzu ya mayar da hankali sa Bauchi danjin labarin Zainab.


Zainab ta kwashi awanni kafin ta farka, tana bud'e Ido taga Amna a gefen ta, Amna naganin ta bud'e Ido ta rungume ta tace "Momma maisaya kike mana wasa da rayuwar ki, ko so kike k'unci ya sake shigowa rayuwar mu, mun shiga k'unci da TSANANI na rashin uwa yanzu kuma muna murnan samun ki kuma kina so ki mayar damu marayu, meyasa Momma ko har yanzu baki yar mu ya'yan ki bane?


Zainab rungume ta tayi tace "har abada bazaku sake shiga wannan rayuwan ba, Amna nafi kowa sonku a duniyan nan, kuma ko Makaho ya tab'a fuskan ki ya tab'a nawa zai tabbatar da ke y'ata ce, Amna rashin kune aifar mun da ciwon zuciya a baya, mai kike tunanin zai faru dani idan aka rabani daku a karo na biyu? Toshe Mata baki tayi tace "ba wanda ya isa ya sake rabamu sai Allah, kisa a ranki zakiyi rayuwar farin ciki rayuwa mai yanzci keda ya'yan ki, Umar shiba Allah bane dan haka ba abunda ya isa ya mana, daga farko nima naji tsoro, amma da Abbas ya k'arfafa mun gwuiwa sai naji akoda yaushe zan iya tunk'aran sa, ki dage wajen mana addu'a kawai Momma, kuma kimun alk'awarin bazaki sake bari Umar ya tayar miki da ciwon ki ba"


Zainab ta share hawayen ta tace "na miki alk'awari insha Allahu bazan sake ciwo akan Umar ba, saidai idan Allah ne ya aiko mun dashi" doctor Mansur ne ya tafa musu dan yaji duk abunda suke fad'a yace "nima haka nake fata, inaso Zainab ki k'arfafa zuciyar ki kicire tsoron Umar a ranki dan ba abunda ya isa ya miki, daga yau kin daina b'oye kanki kenan, ya zamo dole yasan keda ya'yan ki kuna raye, dan mungama tsara komai nida Ammar, ya kalli Amna yace jekuyi sallama dasu Ammar zasu tafi"


Tana futa ya matso kusa da Zainab ya kama hanun ta yana murzawa a hankali yace "saura kad'an nima kisa mun ciwon zuciya, da kinsan yadda nakeji a zuciya ta idan ciwon ki ya tashi da bazaki sake bari ciwon yazo ko kusa dake ba, Zainab bazan b'oye miki ba tun farkon ganina dake Allah ya jarabe zuciya ta da sonki, a lokacin bansan sonki nakeyi ba saina d'auka tausayi ne kawai, har kika zauna a gidana a tausayi nabar abun, bansan ina miki son dani kaina bana ma kaina ba sai ranan da na kawo ki garin nan kikayi kusan mutuwa a mota na, ranan ji nake nima zan iya mutuwa idan kika mutu, tunda na koma Abuja na rasa kwanciyan hankali da nutsuwa a tare dani, har iyaye na suka fahinci halin da nake ciki, suka tambaye ni nafad'a musu komai dangane da rayuwar ki, zakiji mamaki idan kikaga yadda suka goya mun baya akan na aure ki, yanzu ma haka suna hanya dana fad'a musu baki da lafiya, Zainab ga k'ok'on barana ki taimake ni kisa mun sadakan zuciyar ki a ciki"


Zainab jin abun takeyi kaman a mafarki ta tashi ta zauna tace.......





***




Mmn Ashfaq