TSANANI

54

by @mmnashfaq

107/108





***





Tace "doctor maiye abun sha'awa a rayuwa ta? Kaman ta waye ni? kaman ta munanan aiyukan dana aikata a rayuwa ta? sannan kai saurayi ne ni kuma bazaura, duk da nasan baza ka girme niba amma a fanni aure na maka girma, dan Allah karkayi amfani da wa'innan kalman wajen kwantar mun da hankali"


Ya k'ura Mata Ido na wasu sekonni kafin yace "ban damu da waye keba mai kika aikata kin mun girma, abunda na sani kawai ina sonki kuma bazan iya rayuwa babu keba, dan Allah ki aure ni koda baki soni ba, nasan soyayya ta ma kawai ta ishe mu, Zainab ba wanda yafi k'arfin jarabawan rayuwa ya fad'a masa, kema ba laifin ki bane, kuma Umar bai barki haka kawai ba, da ya barki da nutsuwar ki da baki amince da k'udurin sa ba, ki manta da rayuwar ki na baya ki fuskanci wanda zakiyi nan gaba" ai batasan lokacin data rungume saba, dan sai yanzu itama ta yarda da abunda zuciyar ta yake fad'a Mata kullun akan doctor, kuka ta saka amma ta kasa ce masa komai, d'ago ta yayi yace "Zainab halamu ya nuna so kike nima ki saka mun ciwon zuciya" komawa tayi ta kwanta tana murmushi a wannan halin y'an uwan ta suka shigo suka same ta, ba k'aramun dad'i sukaji ba ganin ta cikin walwala sukayi ta ma doctor Mansur godiya, Abbas na shigowa ya rungume sa yace "mungode sosai doctor gaskiya ka cancanci kyauta a gare mu domin kai kad'e kake iya ceto rayuwar Momma mu idan ya tafi gangara, doctor Mansur ya shafa kansa yana jin son yaran a zuciyar sa, yasan shima da yayi aure da wuri daya aifi kaman su"


Amna tana futa Ammar ya kafeta da Ido itama kasa d'auke idonta tayi a kansa, kwata kwata sun manta da Daddy Abbah da Baban bauchi suna wajen, Ammar tsugunawa yayi a gaban ta yace "har yanzu ina kan baka na dan Allah ki bani dama na turo iyaye na" ya fad'a maganan yana had'a hanun sa waje d'aya" Abba ya tafa masa yace na fuskanci so kake kamun kwace da k'arfi, kunya ne ya kama Amna ta juya zata koma ciki da gudu Daddy ya dakatar da ita yace "zo ai bamu gama magana ba" k'arasowa tayi tana rufe fuskan ta, Daddy yace ni abunda yake gabana yanzu karatun ki, gashi kinzo k'arshe kuma bazanyi gangancin barin ki kikoma school d'in nan ba, inaga abunda za'ayi zansa amiki exam d'in kawai, hakan ya miki?


Cikin girmamawa tace "bani da bakin dazan gode maka Daddy saidai na maka addu'an gamawa da duniya lafiya, Allah ya k'ara maka lafiya da nisan kwana" Abbah suma suka mishi godiya yace "ai yiwa kaine duk wanda ya taimake wani shima Allah zai taimake sa, ya kalli Amna yace burina yanzu ki futar da mijin aure a miki aure ki huta kema, yanzu ki fad'a mana wa kike so?


Kanta yana k'asa tace Daddy inaso kafin nayi aure na koma rigan mu, dan bani da burin daya wuce nakawo cigaba a rigan, ilimi ya yalwan ta, su futa a k'angin jahilci"


Daddy yace "wannan duk mai sauk'i ne, zan baki gudumawar million biyar kije kifara gudanar da k'udurin ki, idan baikai kiba zan cika miki daga baya"


Kuka ne ya kub'uce Mata tace "nagode sosai Daddy Allah ya dubi bayan ka ya saka maka da mafificin alkairin sa"


Yace "Amin amin yanzu so nake Saifuddeen yana dawowa ayi maganan auran ku, dan zaman ki a gida ya isa haka.


A tare suka d'ago Ido suna kallon Daddy gaban su yana bugawa da k'arfi, Ammar ya k'ura Mata Ido yana jiran yaji abunda zata fad'a, Amna tace "Daddy Saifuddeen kuma? Gaskiya bazan aure saba dan Momma na ma bata son shi sunfi son Ammar nima shi nakeso" yadda tayi maganan saiya bata kunya ta kwasa da gudu tabar wajen" Ammar bayan ta yabi yana sauk'e ajiyan zuciya kaman wanda yayi gudu shima, Daddy yayi hamdala a zuciyar sa, dan shima wa d'ansa yake sha'awan ta, ya kalli Abbah yace duk da haka zan buk'aci ganin Saifuddeen d'in muji ta bakin sa"


Ammar ji yayi kaman an sauk'e masa wani kaya mai nauyi a zuciyar sa, yasan Daddy ma yayi maganan Saifu ne kawai badan yana son saba"


Godiya sosai Abbah ya musu kafin suka tafi, tana zuwa ta rungume Zainab tace "Momma nayi abun kunya a waje"


Kafin Zainab tayi magana Malama Aisha tace "abun kunya kuma y'ata?


Amna ta dawo kusa da ita ta kama hanun ta tace "Ummi y'arki tayi abun kunya" labarin yadda komai ya faru ta basu, suka kwashe da dariya doctor Mansur yace ba abun kunya kikayi ba, kin fad'a abunda yake ranki ne, kuma nima ina sha'awan ki dashi, kinga sai a had'a auran mu kawai"


Tace "laa doctor kayi kusan aure ne?


Ya kalli Zainab data rufe idon ta ganin zai kunyata ta a gaban ya'yan ta yayi murmushi yace "eh na kusa dan nasamu wanda zuciya ta takeso, ba kowa bane illa Momma ku"


Duk wanda suke wajen sukace Alhamdulillah shikenan Momma kin samu magani har d'akin ki" Abbah ya shigo yaga suna ta murna ya tambaye su suka fad'a masa, murmushi yayi irin tasu na manya yanajin farin ciki a ransa, yasan yanzu Zainab d'insa ta samu miji, sallaman ta akayi ta koma gida, komawan su gida yayi daidai da zuwan iyayen doctor Mansur, karb'a na musamman aka musu, tunda k'anin sa ya d'aura Ido akan Malama Aisha yace yaga Mata, Abbah yace masa to yanzu dai bazamu ce maka eh ko a'a ba, dan ta tab'a aure kuma mijin ta ba sakin takadda ya mata ba, yayi furuci ne daya ke nuni da saki, amma yanzu zamu kirasa muji ta bakin sa" Abdallah yace "dan Allah Daddy ku kirasa yau yazo muji abunda zai fad'a, idan kuma bai zoba zansa hukuma su d'auko mun shi, Abbah hak'uri ya bashi akan duk yadda ake ciki zai jisu, zai sake magana doctor Mansur ya dakatar dashi yace baya son gaggawa, murmushi Abdallah yayi yace "Yayah da yake ka samu naka ba ai dole kace baka san gaggawa" bayan sunci abinci sun huta suka tafi, Abbah yacewa Yaya Kabiru ya kira masa Baba, wayan sa ya ciro ya kira number Baba, Baba yana kwance tunanin Amna ya addabe zuciyar sa, yaga kiran wayan Kabiru kaman bazai d'auka ba, ganin idan bai d'auka ba bazasu daina kiran ba ya d'auka cikin masifa da nuna gundura yace "wai kiran mai kake mun ne?


Yaya Kabiru ya danne zuciyar sa yace "dama muna so muji makoman auran Aisha ne a wajen ka?


Tsaki Baba yayi yace "da ina buk'atan y'arku ai Dana nemeta, tun ranan data kori wanda zuciya ta takeso na yanke duka igiyan auran da yake tsakani nina da ita, dan haka karku sake mun maganan wata Aisha" kitttt ya kashe wayan sa, kasancewan muryan wayan a bud'e yake yasa duk sukaji abunda yace.


Amna zare ido tayi tace "Ummi wallahi harna manta kina da miji, dama Baba yana nan akan wannan bak'in manufan sa?


Malama Aisha tace "yanzu kam ai saiya k'arata dan yayi biyu babu, dan nima yanzu naga mijin aure"


Abba yace "yanzu hankalin mu yafi kwanciya tunda ba auran ki a kansa Allah yasa hakan shine mafi alkhairi.


Abdallah suna isa ya kira number Abbah bayan sun gaisa yace Abbah dan Allah kabani izini gobe naje kotu na karb'a Mata takaddan sakin ta"


Abbah yayi murmushi yace "karka damu Abdallah mun kirasa ya sheda mana tun lokacin data tafi ba igiyan auran sa akanta"


Ba k'aramun murna Abdallah yayi ba yace gobe yana hanya insha Allahu, dan bazai iya zama ba tare dayazo ya gina soyayyan sa a zuciyar Aisha ba"


Abbah shidai murmushi kawai yayi ta masa sukayi sallama ya kashe wayan yana dad'a godiya wa ubangijin mu.


Bayan sati uku Ammar ya dawo da kud'in da Daddy ya bayar na gudumawar Amna, dama kafin ya iso ya sanar dasu su shirya, yana zuwa ya tadda su cikin shiri, Zainab da yanzu soyayyan doctor Mansur ya dawo da ita hayyacin ta, ta murmure ta dawo Zainab d'inta na ainifi maiji da ado da kwalisa, idan ka gansu da Amna saika kasa banbance waye Zainab waye Amna zab'an kamannin su, mota biyu sukayi na zuwa Tilde, suna isa rigan Larro suka wuce direct, gidan Baffa Sule suka fara biya wa suka samu baya nan, aka shiga jeji aka nemo musu shi, yana ganin su Amna ya washe baki yana nuna tsantsan farin cikin sa yacewa mai d'akin sa "baki gane Amna da Abbas ba ko?


Tace "ina suke? Amna ta taso ta rungume ta suka fara murnan ganin juna, kafin kace mai labarin zuwan Amna ya baza ko ina a rigan, kafin wani lokaci gidan ya cika fal da mutane, kowa yana murnan ganin Amna da Abbas, su Zainab sai suka dawo y'an kallo ganin yadda Amna ta juye baffulatanan ta sak saika rantse batajin hausa, Goggo D'ahare Maree Lantana da Larai sukazo wajen suna ta rab'e rab'e, Amna bata lura da su ba saida taji an rungume ta tabaya ta juyo sukayi Ido hud'u da Adda Larai Amna cikin farin ciki tace "Adda Larai ashe zan sake ganin ki? Suka sake rungume juna suna farin cikin sake had'uwan su, tambayan juna sukeyi bayan rabo da yare, Amna tace "ina su Goggo, nuna Mata inda suke tayi, saida ta razana lokacin da Idon ta ya sauk'a akan su, gani tayi sun rame sunyi bak'i, ga tsufa ya bayyana a jikin su, ta taka har gaban su ta tsuguna ta gaishe da Goggo kafin ta kalli Adda Lantana tace "yaushe a gari Adda Lantana?


Lantana da takeji kaman ta nutse a wajen tsaban kunya tace "mijina ya jima da sakina Amna, ta tsuguna tana kuka tace dan Allah ku yafe mun Amna dan munga rayuwa kuma munsan hakkin kune yaketa bibiya mu, su D'ahare ma suka nemi gafaran ta, Amna tace ban rik'e ku da komai ba dama, na yafe muku sai dai Allah ya yafe mu baki d'aya, taja hanun Goggo sukaje gaban Zainab tace "Goggo ga Ma'aifiyar mu nan wanda k'addara ya rabamu da ita"


Baffa Sule yace "tabbas k'addara ne ya rabasu da ma'aifiyar su, ma'aifin su kuma yana Abuja, b'arayi ne suka sace su suka kawo su nan, Baffa Salihu kuma ya tsince su ya taimaki rayuwar su ya rik'e su da gaskiya da amana, da yake Allah ba azzalumin bawan sa bane, sanadiyar musguna musu da kukayi tayi yasa suka gudu a gidan, suna futa Allah ya had'a su da iyayen su.


Kowa a wajen ya taya su murna sosai tare da addu'an Allah ya saka musu, ita kuma Goggo taga sakayya daidai da abunda ta aikata, dan ga ya'yan ta zaune a gida ba aure, su D'ahare harda y'aya uku uku ma, Larai ce kawai mai aure a cikin su.


Goggo ta tsuguna cikin kuka ta nemi gafaran su, Zainab ta d'agota ta share Mata hawaye tace "karki damu haka Allah ya tsara rayuwar su, kuma kamata yayi nagode miki da barin su da kikayi suka zauna a gidan ki, sai kuma muyi addu'an Allah ya gafartawa Baffan su, Abbas kam nunawa yayi kaman bai tab'a ganin su ba, Goggo tana so taje ta nemi gafaran sa tanajin tsoro, dan tunda yace Mata shi soja ne wancan karan tsoran sa ya d'arsu a zuciyar su, bayan komai ya lafa Amna ta gabatar da abunda ya kawo ta rigan kuma sunyi na'am tare da nuna farin cikin su sosai, Baffa Sule ya nuna musu wajen da za ayi ginin makarantun.


Amna da Abbas suka sulale suka nufi bakin ruwa, kallon ruwan sukeyi cike da sha'awa da kewan Baffan su kafin suka nemi waje suka zauna suka rungume juna suna kuka, a haka Zainab sukazo suka same su, hak'uri akayi ta basu, kafin suka tashi suka shiga gidan su na da, d'akin Baffa suka shiga suka samu komai yana nan a yadda suka barshi, anan ma sunci kuka saboda tunawa da Baffan su da sukayi, suka had'u aka mishi addu'a, kafin Amna tace a rushe gidan ayi sabon gini, saida sukaga an fara aikin kafin suka bar komai a hanun Baffa Sule, Ammar ya bashi waya da layin Airtel yace zasu dunga kiran sa suji yadda ake ciki, suna futa Amna tace "dan Allah muje gidan Baba ya gammu muga yadda zaiyi"


Basu k'iba suka d'auki hanyan gidan suna futowa a mota suka ganshi yana k'ok'arin shiga gida, Amna ta d'aga murya tace "barka da yamma Baba"


Yana jin muryan ta ya juyo da sauri yana washe baki yace "nasan dama zaki dawo gareni domin kema kina sona, zalincin Aisha ne yasa ta kore ki"


Malama Aisha ta futo tace haka ne saidai bansan waye azzalumin ba tsakanin ni dakai, Ido ya ware yace dama kuna tare? Amna wuce mu tafi ke kuma na rantse miki idan kika shiga gidana saina karya miki k'afa"


Zainab tace "ai dama ba shiga tazoyi ba, tazo ta sanar dakai Amna y'ar Yayar tace uwa d'aya uba d'aya, kuma nasan kana da labarin Yayar ta Zainab da take aure a Abuja, to nice Zainab d'in, kuma nice ma'aifiyar Amna da Abbas, ta juyo ta kalli Amna da Malama Aisha tace ku kuma ku shiga mota mu tafi"



Baba binsu yayi da Ido har suka bace masa da gani, nadama ne mara musaltuwa ya shigesa yace "ko ba'a fad'a mun ba kamanni ta da Amna ya nuna mun kece ma'aifiyar ta, yanzu shikenan nayi biyu babu ba Aisha ba Amna, yau wani irin bak'in ranace a gare ni, zazzab'i mai zafi ne yaji ya rufe sa a tsaye a wajen, ya shiga gida ya kwanta, y'an uwansa sukazo suka kaishi asibiti, haka yayita jinyan zuciyar sa daga k'arshe ya dangana, ya fara tunanin wanda zai auri Aisha suyi auran kisan wuta ta dawo masa, dan bazai yarda ta auri wanin saba.


Amna sun isa Birnin kudu lafiya a daran Ammar ya d'auki hanyan Bauchi.



Saifuddeen tunda ya tafi ya rasa nutsuwa a zuciyar sa, kullun idan ya kwanta bayi da mafarkin daya wuce na Amna, wani abokin sa da suke school d'aya da Amna ya kira a yaji ko su Amna sun fara final exam, yace masa ai sun gama tun last week, yana jin haka ya fara shirin dawowa Nigeria, yau jirgin su ya sauk'a a garin Abuja, bai jima da sauk'a ba jirgin sa na zuwa bauchi ya tashi suna sauk'a iyayan sa suka zo suka d'auke sa, tun a mota ya sheda musu yazo yin aure ne, ba k'aramun murna sukayi ba jin d'ansu zaiyi aure, suna zuwa gida yaci abincin yayi wanka ya zauna yana basu labarin Amna tare da nuna musu photos d'inta, sun yaba da kyauta, suna cikin hira yaga an haska photos d'in Zainab a NTA news ana sanar da an sameta yanzu haka tana gidan iyayen, dukan su sun zaci Amna ce, jiki na b'ari ya kira Ammar danjin abunda yake faruwa a bakin sa, Ammar bai b'oye masa komai ba ya mishi bayanin Amna ta koma gidan su kuma ma'aifin ta rik'ekk'en d'an mafiya ne, hankali tashe yace kana nufin Baban Amna maye ne?


Ammar yace...........





***





Mmn Ashfaq