Dijamah Yar fulani

Chapter 4

by @mamanteddy





   *🏔️DIJAMAH 'YAR FULANI....🏔️*


*EPISODE 7&8*


"Umma ne tacigaba da cewa" bakowa ne mahaifin ki ba,illah jounalist Muhammad maccido...kuma 'dan asalin garin gombe ne....

A sanadiyan aikin sa ta jarida ne,allah ya ha'damu da shi,mutum mai yawan kyauta,tausayin talakawa kullum tsakanin shi da talakawa sai dai son barka...

Sanadin xuwan sa garinmu shine,yana son sanin wasu daga cikin al'adinmu na buxaye...


Don haka koda yasamu wasu daga cikin 'yan uwan mu na maliy,sai suka ce akawosa wurina.


Acewansu nice mae si

Surutu,kuma xan fa'da mai har abun da bai tambayeni ba...don ni kaina nasan alokacin nan,ni 'yar fa'di ba'a tambaye ki bane...


Haka aka taho da maccido inda nake sayarda Abuncina...a dandali.


A ranan shi kanshi sai da yagaji da surutu na ko da ake fa'da mashi...don ban barshi ya tafi ba,sai da na sayar da abunci na tasss tukunnah.


Don shima nasan inna dawo xan kara 'dora ta la'asar ne...


Tun daga wannan rana kullum mahaifin ki,wanda mukai mai lakani da suna maccido sae yazo wurina a dandali...inda nikuma nayi ta koromai jawabin rayuwan mu ta buxaye...dakuma yanda ba 'dauki karatun boko da wani mahimmanci ba...sosae Yakejinn da'din yanda nake bashi labarin mu...inda nikuma bawai saboda wani abu bane nake fa'da mashi,illah saboda ganin ana haskoni a cikin television...a haka sha'kuwa ta fara shiga tsakanina da muhammad maccido...


Inda daga baya soyayya ta shiga tsakanin mu da shi...

Sosai muke son juna,inda ni dai kawai son shi nake.amma nasan ba aurena muhammad xaiyi ba,duda irin son dayake nunamun...

Ammma sam ban kawo wai muhammad maccido da gaske yakeyi xai aureni ba...dakuma 

Saboda nasan halin 'yan nijeria,insunxo kasarmu haka xakaga suyita cewa"suna san yara,amma duk yaudara ce.

Don daxaran sun tafi 'kasar su,shikenan sun manta da sun ta6a son wata buxuwa...tohhh da wannan yasa ban samawa raina auren muhammad maccido ba...musamman shima,wanda ko a 'kasan nasu ansan da xaman sa.


Ana gobe xai koma 'kasan su nijeriya ne,duk nadamu don nasan shikenan rabuwan mu taxo tsakanina da shi,amma damamaki sai naji yana cewa"inya koma gida,nan da sati xai turo iyayen sa akan maganan auren mu...


Hmm wannan rana nayi matu'kar farin ciki,wanda rabon da inyi irinta ni kaina na manta...


A haka mukai sallama da shi,inda da nadawo gida ne abun duniya ya dameni,don nasan da wuya su baba na su amince...


Musamman dana tuna da yaya ta,munawwarba yanda ta auri wani sojah a najeriya... wanda turosu akayi nan kasan mu,amma tun da akayi mata auren nan da shi,bamajin ko labarin ta...

Kuma ba bawai mara hali ta aura ba,don Lokacin da tayi aure da mukaje 'yan kauye muka xama...amma tun da tayi aure so daya ta ta6a xuwa garinmu,wanda alokacin dana ganta ni kaina ban gane taba saboda yanda ta chanja,ta dawo kaman baturiya abin ka da farar fata...daka ganta kasan bata cikin wahala...amma halinta bana 'dafan iyaye ba ne sam.

Tun da taxo sau dayan nan bata ',kara dawowa ba har wannan lokaci,wanda koda ta haifi 'dan ta na farko,sai dai mukaji labari,don bata fada ma kowa ba...

Rayuwanta yakoma irin ta turawa xiryan,don tsakanin ta da kowa sai dai ido...idon ma baya ganin ta.


Kuma munawwarah tun asalin ta bata damu da karatun mahammadiya ba,amma na boko kuwa itace sahun gaba,dun haka da tasamu gidan miji ta cigaba da karatun ta,duda ban mae takaranta ba.


Wannan dalilin yasani kasa mawa su guggo magana...

A haka har lokacin da muhammad maccido yafa'damun xai turo iyayen sa yayi,wanda aranan da yace"bai karya alkawari ba...yako turo iyayen sa.dattijon arxiki.


Don sam basununa kyama a garemu ba...

Sunan baba na baisan da maganan ba ne,amma sam bai nuna masu bai sani ba.. Kuma haka ya kar6esu cikin mutuncin mu na 'yan maliy...


Koda yaji maganan su,da abun dake tafe dasu,bakaramun farin ciki baba yayi ba.

Sai dai da suka nimi a tsaida magana ne yace"masu yanaso sunyi hakuri yaji ta bakin yarinyan tukkunnah...


Batare da damuwa ba,sukayi ma baba na sallama,akan cewa xasu dawo bayan mako guda.


Inda bayan tafiyan su ne,baba yasameni akan nasan da maganan muhammad maccido???


Ba tare da wani abu ba nace" masa ehhh...tunda baba yaji haka yasan na amince da muhammad maccido kenan.


Don haka guggo da baba sukasamun albarka sosai,kuma nayi matukar mamaki akan amincewan nasu...don ban kawo ba.


A kwana a tashi satin da'aka tsayar ta dawowan iyayen muhammad maccido yayi,kuma a wannan rana suka dawo...wanda ba'a 6ata lokaci ba suka tsayar da auren mu bayan watanni biyu masu xuwa...


Tun daga wannan rana soyayyar maccido yasamu wuri ya'kara xama a cikin xuciyata...wanda haka muka 'kara sabawa da kuma son juna fiye dana baya...


Guggo har mamakin da yanda kullum maccido yake xuwa hanyar kasarmu take,inda haka yakuma kwantar mata da hankali sosai...xullumin da takeyi akan auran namu ya ragu.


Don ayanzu tasan maccido ba'karamun kauna ta yakeyi ba...gakuma yanda yanda ya 'dauki guggo da baba...abun sai dai sam barka...


A kwana a tashi ba wuya gai rai,kuma mai nisan kwana...don auren mu yanxu tini ya matso... Don yanzu auren mu saura kwana uku kenan

..


Guggo tana ta zuba ido ko xataga xuwan munawwarah,amma shiru babu itah babu labarinta...wanda a haka har ranan 'daurin auren mu yaxo....ranan da baxan ta6a manta shi a rayuwata ba...a wannan rana ne,dubban mutane kuma manya tsakanin nijeriya da agadas suka shaida daurin aurena da maccido... Inda kowa kagani a wurin fatan Alkhairy yake....


Bayan kuma 'daurin aure ne,dangin maccido suka xo akan yanxu a lokacin xasu wuce dani xuwa nijeriya...


Nayi kuka sosai da naga a ranan shikenan na rabu da baba na da guggo... Inda guggo ke tamin nasihohi masu ratsa zuciya...

A haka muka biyo jirgi har cikin garin gombe,inda da saukanmu garin dangina suka ce baxa'a wuce dani gidana ba sai anfara kaini wajen surukata,wato mahaifiyan muhammad maccido... Kuma itace kaka a wurun ki...




____________________________


Koda muka isa gidan su muhammad ba'karamun mamakin gidan mukayi ba...don a wannan lokaci in akacemana gidan shugaban 'kasane tabbas ba xamu musaba...dan gidane nagani kuma na fa'da,girman sa kuwa nayi maki yanda xaki gane tafi rugar har'do baki 'daya....


Gaba 'dayan mu muka xama 'yan 'kauye,kauyen ma irin wanda suka fito daga daji,badaga cikin mutane ba...


A haka wasu ma'aikatan gidan suka yimana iso har cikin tankasheshen falon hajiya babba...inda anxuba kayan alatu kaman ba'asan ku'din suba,don dukiyan da'aka xuba a falon bakin bama xai iyah fa'da ba.don masalta maku sai yasa na 6ata shafuffuka ban gama ba...


Wasu daga cikin dangin nasa kuwa ban da ya mutsi babu abun da suke bin mu dashi,yanda kasan basuga mutane ba.wasu ko daga cikin su nan take suka kar6emu hannu bibiyo...inda sukayi mana sannu da isowa.kuma anan take suka umarci ma'aikatan hajiyan,wato masu hidimtamata akan suka wo mana kayan motsa baki...


Sannan wata dattijuwa ta shiga don tasanar da hajiya babba isowar mu gareta...


Haka ma'aikatan ko suka dinga kawo mana kayan ciye² wanda sai da suka cika gabanmu tam sannan suka fara kawo mana gaisuwa cike da girmamawa.


Cikin wannan ma'akatan gidan kuwa harda uwani...wanda muka ha'du da itah a lumo...


Toh kunsan abunka ga 'yan maliey babu dukiya ammma kuma akwai girman kai,dajan ajin kansu.don haka babu wanda ta kalla abun da aka kawo mana...


Niko maman teddy nece tohhh🤔'yan maliey kenen babu dukiya sai girman kai😇🤪


Hmm du haka muke,amma ban ga kaman hassenart bamalli ba,marubuciyan RUYUWAR AFRIDAH hmm itace tabiyo su xiryan bata yarda da raini ba😅🤪,amma tana dason wanda yasan darajarta😇,kuma badai isah da ixxah ba🤨😎,niko nace"mallawan maliey kenen....tun fil'axim akan haka aka sanku....😍😅

Hmmm yohhh niko nace"tohh ni maman teddy ko yanake oho🤔


Kune dai kukasanni,don haka basai nayi sharhi ba🤗


Kar dai ku manta maman teddyn kuce....😅😍


Haka su ummah shattu suka dunga xama,amma hajiya babba bata da alaman fitowa...don su basu san wainan da ake toyawa ba,don hajiya babba nacan ana fama daitah akan tafito wajenmu,amma sam ta'ki futowa,acewanta ita sam baxata ha'da xuri'a da bugaje ba.


Ganin haka yasa wannan dattijuwan fitowa daga 6arayin hajiya,inda take shaida mana cewa"hajiya babba batajin da'di,kuma kuma ta samu bacci ne...nan ta karke maganan dacewa"amma nan da gobe dakanmu xamu xo mukawota wurin hajiyan...


Godiya su innata sukayi,inda haka muka mi'ke ha'di da nufowa gidana...


Sosai muka yaba da tsarin gidan,dakuma girman sa,don ba'karamun mamaki mukayi daganin irin wannan gida ba.

Ni kaina ban kawo cewa"maccido nada wannan mahaukacin dukiya ba...


Tun daga wannan rana,muke xaune cikin lafiya nida mahaifinki...sosai yake nuna mun so da kulawa,inda ya samun ma'akata masu yawan da xasu ringa'ka mun hidima...

A cikin su kuwa harda uwani,wanda ya daukota daga gidan hajiya babba.


Sosai muke zaman lafiya da ma'aikatan gidana...don ni macace mai yawan surutu da barkwanci...don haka suke tsananin kaunata...


________________________________


Sati na biyu da aure,maccido yace mun xai kaini na gaida hajiya,kuma acan xan mata wuni,in yadawo wurin aikin sa sai ya dauko ni mudawo gida tare....


Cike da farin ciki na shirya,inda nace mawa uwani ta shirya itama muje tare,don naji da a hannun hajiyan take...


A haka muka shirya duka ha'di da nufan gidan hajiya babba...


A wannan rana ne na fahimci yanda hajiya babba ta dauke ni a zuciyanta,don wannan rana naga wulakancin da ban ta'6a gani ba...


Ciki da fara'a muka shiga falon hajiya babba, inda na sameta xaune kan 2 seater,dayan '6angarenta kuma wata mata ce,wayyayyiyar gaske,irin wa'annan matan da sukaci boko har suka gaji,wanda suke neman maza ido rufe...


Ko arzikin amsa sallaman bamusamu ba,inda cikin sayin jiki na duka har kasa na gaishe da hajiya babba.... Amma kallona batayi ba,illah ma cike da tsawa da masifah ta hau cewa"kehhh.....matsa ki bani wuri...kina tunanun xan kar6eki a matsayin suruka!!! Tohh lallai kinyi kuskure....jubiki da allah,gayyar yunwa...tohhh ni nan dakika gani,inkin malleke shi,tohh ni nafi karfin ki makirah....


Nan tanisa ha'di da kallon maccido wanda gaba 'daya maganan hajiya babba bai masa da'di ba...


Kai kuma saunawa xan fa'da maka baxan yarda wannan busasshiyar taxama suruka ta ba..amma ka kiji...tohh kutashi kubarmun gida...ranan daka amince da auren binta ne xaka iyah shigomun cikin gida....

Ku tashi kufita nace....hajiya babba tace" cike da tsawa...yayin da doc.binta ke gyafe tana sakin murmushi,itah ala dole tayi kamu da uwar miji....


Kallon ta nayi,inda lokaci guda idona ya ciko da kwallah,uwani ko ganin halin dana shiga yasata,saurin girgixamun kai alamun kar nayi kuka akan maganan hajiya babba...

Nan maccido yafara ba hajiya hakuri akan tayi hakuri,kallon shi batayi ba,illah fixgixga batare da tace mashi komae ba...


Bai kuma bin ta kanta hajiya babba ba,yajuyo ha'di da mana sallama sannan ya nufi wurin aikin sa....


A wannan rana nasha wulakanci a wurun hajiya babba, amma sam ban nuna na damu ba,inda rashin nuna damuwata yakara bakanta ran doc.binta...

Haka rayuwa ta cigaba...inda shekarata daya a gudan maccido na haifoki,kuma har alokacin hajiya babba bata daina nuna mun kiyayya ba.amma sam ban duba wannan,tunda maccido yana nuna munso matuka....a wannan shekara kuma sai danaje wurin su baba na,inda kan na haifeki sai da naje sau biyu...wanda har alokacin munawwarah bata xoba...kuma taji labarin nayi aure....a nijeriya kusa dasu....amma bashi yasa ta nemeni ba...


Ba karamun murna Abbanki yayi ba dana haifeki,inda nan take yasa maki suna NANA KHADIJA...wato sunan hajiya babba... Hajiya kuwa bakaramun bakin ciki tayi ba,dajin hauhuwa ta...


Kwanan ki uku a duniya ne,ina xaune a kan gado na,a bedroom...inda nake goye dake abayana....


Kattawan maxa ne suka shigomun bedroom ba ko salllama,fuskan su duka a rufe da wani bakin kyalle....ihun su uwani nakeji,inda nan take na hau salati...amma kafin na farga tuni wani daga cikin su ya shakamun wani powder a fuska...


Wanda tundaga nan ban kuma sanin halin da nake ciki ba,sai farfadowa nayi naga ganni a rugar har'do....