Dijamah Yar fulani

Chapter 6

by @mamanteddy



بسم الله الر حمن الر حيم


Kallon ta justice madina tayi" inda a hankali ta kai hannun ta ha'di da shafa kan 'yan nata,wanda Ashekaru batafi 11 yrs ba,nan tace mata" eyyah my baby,ya Aliyun naki shima xai dawo very soon kinji...? Don haka plz ki kwantar da hankalin ki,nasan duk don baki saba da kasannan bane,shiyasa kike kin ta,but inkika yi 'yan kwanaki nasan xakiji son nijeria sosai my dear...

Justice madina ta 'karke maganan ha'di da bin 'yan nata da kallo,kuma dason amince wanta...


Shiru meenash tayi,batare da tace mawa mom 'din nata komai ba.

Don itah tana nan akan bakan ta nakin amincewan xaman ta nijeria....


'Bangaren dijamah kuwa,sai dai muce alhmdllh,don ansamu nasaran farfa'do wanta...inda umma tayi matukar farin cikin haka...


Wannan kuwa tsofaffin sun jajirce matuka,inda ummah ke ta masu godiya...


Bayan dijamah taci abunci ne,yawindo..ta kalla umma ha'di da tambayan daga inda suke...?


Ada umma taso rufema wa yawindo komai da yashafesu,amma ganin karamcin da sukayi masu yasa umma baiyana mawa yawindo da mai gidan nata komai....inda ba'karamun tausaya mawa ummah da dijamah sukayi ba.don yawindo harda kuka,abunka da rigima ta tsofaffi😂


Tun daga wannan rana,yawindo da mijin ta,wanda dijamah kekiransa da baba suka basu umma bukka.inda lokaci guda rugan nan kowa yasan dijamah... Don tuni tayi sababbin kawaye a wannan rugan surbanjo...inda yawindo ta dauki dijamah kaman jika,don har wasan jika da kaka takeyi mata...haka ma baba,don su basu ta6a haihuwa ba,tun da sukayi aure,inda yanzu har tsufah ta riskesu....

Wannan kenan...


_____________________________


A kwana a tashi babu wuya gamai rai...cike da mamaki nake bin dijamah da kallo,don a yanxu taxama cikakkiyar mace" wanda kyawun 'yamma tanci ya bayyana mata sosai,don yanxu xatakai shekaru 15 a duniya...gaba daya ta saje takoma bafullatan usul,inda take 'dauke da kwaryan nono,wanda da'alama xata fita ruga ne,taje cikin kasuwan cikin garin Adamawa...


Bayanta ummu ne,itama dauke da kwaryayen nono...dasauran fulanin rugan nasu,wanda dukan su sauri sukeyi don su isa kasuwa da wuri...


Kafin su isah kasuwan cikin garin ne,idon dijamah yasauka akan wani sabon company,wanda da'alama ba'a da'de da bu'deta ba,cikin harshen fulatanci tace ma ummah" ummah wannan kuma mene ne,gida ne...?


Murmushi ummah tayi hadi dace mata"a'a dijamah masana'anta ne...inda ake sarrafah abubuwa.da kirkire kirkire...


Cike da hauka da wauta dijamah tace" yehhhh ummah kafin a tashi kasuwa xanje na ga cikin sa,aradu 'kamshi naji daga can wurin,ummah kila wurin madafi ne ko...?


Umma ne tayi saurin kallon dijamah ha'di dacewa" a'a dijamah karkije kinga mu ba'ki ne...kuma nace maki ba wurin madafi bane,masana'anta ne...


Tun daga nan dijamah batakuma cewa" komai ba,inda a ranta ta kwallafah son xuwa cikin wannan company,don acewanta wurin saida abunci ne,dasuke gani a wurin kasuwa...

Niko maman teddy nace" tohhh dijamah kodai kwadayi xa'aje ayi ne...🤣




Kwance yake wanda daga shi sai gajeren wando ajikin sa da singilite...fari be Tass kuma kyakykyawa na ajin karshe,dogo ne amma ba can ba,irin wa'innan mazan ne da'ake kira da segxy guys...

Fuskan sa kewaye da siririn saje...dagani basai ance maka ba,xakasan irin wannan butters din ne...

Wanda mata ke deting da rushing din sa,wanda su mata kebin su,basu ne ke son su ba...cika yake yana batsewa,fuskan sa 'daure tamau,wanda da ganin sa kasan irin maxan nan ne wanda basa son raini...sam...

Gyefe guda kuma wata budurwa ce...rike da hannun shi tana masa magiya,wanda da alama sun gama masha'an su ne,don Aliyu haidar shaharrarrene wajen keta ma 'yam mata hadi,amma ga wanda yasani,don a duniya kowa ganin mutumin kirki ake mai,don shi akwai yawan kyauta,sadaka,taimakon marasa karfi,don haka ne,kowa yasan shi,inda Abokanshi kemai kirari da dollars...


Shi mutum ne wanda inyayi sex dake baya kuma 'karayi dake,sai dai wata...irin wa'innan maxan ne harijai...masu yawan bukata,kuma shi sam baya da ra'ayin aure,don yace har yanxu baiga irin matan datayi mai ba...


Da sam ba haka yake ba,bai mu'amala da matan banxa,sanadin fara wannan dabi'a tasa sanadin wata da ake kira da Basmah,wanda ita tafara sa Aliyu haidar a wannan hanya,don ita tafara neman bukata a gareshi,don dama itah watsattsiya ce...tun daga nan abun ka ga mai yawan nema,shikenan suka fara wannan mu'amala,inda ita ala dole son shi take,kuma so da aure,wanda shi ko sau 'daya bai ta6a tunanin ta a matsayin matan auren sa....inda ita basma 'yar kawan mahaifiyan sa ce,aminiyan ta sosai wato justice madina.kuma Aliyu ne dan justice madina na farko,inda daga baya ta haifi meenash,wanda sukenan 'ya'yan da Allah yabasu...


Wannan shine ta'kai taccen labarin Aliyu haidar..


Budurwan dake gyefen sane mai suna sobrina takai hannun ta gana Aliyu tana murxawa cike da salonta na jawo hankalin sa gareta...inda shikuma gogan kallon ta baiyi ba,illah ma cewa dayayi cikin masifah,sobreen out....!!!


"Cike da rashin xuciya irin ta karuwan mata ta kara matsawa kusa dashi,wanda ko kaya babu a jikin ta,kai bakin ta kai xata ha'de da nasa,inda ya kauda kai ha'di da hanka'de ta gyafe...ganin yaki saura ranta yasata fara cewa" plz im sorry my baby...im so sorry....kallonta bai yi ba,illah daukan laptop din sa da yayi,wanda yake kan bedside drowern dake gyefen sa...


Cike da dacin rai sobreen ta fara xubar da hawaye,don ita sam bata gansu da Aliyu haidar ba,tana matsanan cin bukatan sa alokacin...don haka nan cike da kuka take cemasa" plz Aliyu i will give my self...


Kallon ta baiyi ba,illah mikewa da yayi yanufi privacy don ya tsaftace jikin sa...


Bayan yayo wanka ne,yafito sanye cikin rigar wanka,hannun sa kuma 'dauke da karamun towel ,wanda yake goge sumar kansa da shi...


Ganin sobreen ta saka kayanta,wanda da'alama tafiya xatayi,yasa shi jawo bedside drower ha'di da wurga mata ku'din da yakai kimani #200k.


A hankali ta kai hannun ta,ta dauka,inda ta kuma matsawa kusa dashi,ha'di da manna mai kiss a tattausan lips din sa,sannan ta fito daga bedroom din nasa...


Shiko Aliyu haidar bayan kammalawansa ne yafito daga bedroom din,inda yake sanye cikin shigarsa ta suit wanda yakuma bayyana haiban sa da kwarjinin sa...wata 'yar aikin part din nasa ne,tayi saurin xubewa ha'di da gaishe sa,kallon baiyi ba,illah nufan dirning area,inda aka jeramasa abun cucuwa,wanda kalolin su bama xasu kirgu ba...


Xama yayi akan 'daya daga cikin kujerun dirning dun,inda ya ajiye brief case 'din sa,akan wani kujeran....


Nan cikin hanxari cookern taxo ha'di dafara serving nasa...


Bawani cin abuncin yayi ba,don sauri yake ya isah,companyn sa,wanda yake da bakin da xasu xo wurin sa....

A hankali ya maida kallonsa ga wrist watch din dake manne a tsitsiyan hannun sa,inda yaga kusan 10am...karamun tsaki yayi,ganin lokacin dayace ma'aikata su hadu a mitting room yayi,gashi ya makara,kuma bayason African time...


Mikewa yayi cikin hanxari ha'di da nufan company n nasa...


Dijamah kuwa dataga ta kammala saida nono,kuma wasun su basu saida ba,kawai sai ta yanke shawarar xuwa wannan company.


Inda batare da kowa yasani ba,ta dauki 'yar mayafin ta,wanda dashi da babu duka 'daya...ta nufi wannan company n dataga an rubuta...


*ALIYU HAIDAR COMPANY LIMITED....*


Nufahn inda taga motoci na fitowa tayi,wanda cike da tsawa wani security yayi mata magana da cewa" keehhhh mai xaki shiga kiyi anan...


Kallon shi tayi,wanda sunan yayi mata tsawa ne,amma ko 'darr bataji ba,nan kanta tsaye tace" naxo inga irin wurin ne...


Cike da kyankyanin ta don karnin nono takeyi ba kadan ba,wanda nan securityn yace"kehhh wuce kiban wuri babu inda xaki shiga...


Yana gama fa'damata yasa koma wajen tsayuwansa,inda 'dayan securityn dasuke tare yake binta da kallon,aranshi kuwa cewa yake ko mai yakawo wannan bafullatan dajin nan ohooo....


Kallon ta sukeyi,ha'di da bin saken jikin ta na fulani da kallo...wanda yasha nono ga datti da yayi har ya gaji.