Dijamah Yar fulani

Chapter 7

by @mamanteddy

بسم الله الر حمن الر حيم


Kasa tafiya dijamah tayi,inda take tsaye tana ware²n son shiga cikin wannan companyn na *~ALIYU HAIDAR COMPANY NIGERIAN LIMITED...~*

Fiye da munti talatin tana tsaye,inda wa'innan securities din kallon ta basu sakeyi ba...illah ma cigaba da harkokin su da sukeyi...


'Bangaren Aliyu haidar kuwa,bayan yagama meetting da ba'kin nashi ne,wanda turawa ne,dakuma manyan gomnati sukaxo akan suna son abasu shares na wannan company, wato suna son asusa hannun jarin su....


Bai amince da bukatun su,sai dai yace masu" suje nan da mako guda su dawo...akan xaiyi tunanin akan lamarin...sosai sukaji da'din laramcin da Aliyu haidar yayi masu...inda basu '6ata dogon lokaci ba,suka bar company nin....


Bayan tafiyan su ne,yatara ma'aikatan masana'an tan,inda yasa P.A nasa yakuma masu bayanin abun da xa'a kuma gyarawa a cikin company n.


Sosai ma'aikatan suke godiya da 'kara tunatar dasu...don kowa yasan halin sir Aliyu haidar... Abu 'kan'kani xakayi yace" ya a sallameka,asamo masa wani makofin ka...irin wannan halin nasa ne yasa suke masifan tsoron masa gargada acikin wannam company nasa...


Bayan yagama abun da xaiyi ne,ya nufi parking space na company n,inda ya 'dauki motansa,'kirar accura....2021.


Nufan tanfatsetsen gate din company n yayi don yafita daga cikin ta,inda nan idonsa ya sauka akan dijamah, wanda suke kici²n hanata shigowa cikin company n...

Bangaren dijamah kuwa ganin wa'innan securities sun hanata shiga,kawai sai ta fakaice idon su tayo cikin wannan company... Inda cikin hanxari wannan securityn ya kai hannu ha'di da jawo mayafin jikin ta,gani ya fixge mayafin nata ne yasa shi dakatawa,don a ganin sa xata dakata da shiga cikin wannan ma'aikata,amma sai yaga ko ajikinta,kara kutsa kai take ciki abun ta...dayan securityn ne cikin xafin rai,dakuma ganin batada galihu ya kaimata mari.


Wanda dai² a idon Aliyu haidar...


Cikin hanxari da yafito daga cikin motan nashi,inda da nufan wannan securityn ya dauke shi da mari...ji kake tass,jin saukar marin yasa da sauri dijamah dake tsugunne tana kuka saurin mikewa ha'di da firgita...dajin wannan irin marin nasa...da yakuma kai masa wani marin ne yasa dijamah cikin sauri tarike hannun sa cikin gur6atacciyar hausan ta,ta hau cewa" don Allah kayi hakuri ka rabu da shi,na yafe masa...ka kyalesa...


P.A Dake bayan sa ne yayi saurin dakatar da Aliyun shima,inda cikin hanxari yace mawa securityn ya tafi sai anne mashi,nan take wannan securityn ya hau xubar da hawaye ha'di da bamawa Aliyu hakuri, inda yake cewa" shi sam bai san wannan bafullatan 'yar uwansa bace...kallon sa Aliyu haidar baiyi ba,inda nan take yajuya ga dijamah ha'di da bata mayafin ta,kallon ta baiyi ba,yajuya xai bar wurin...cikin xaxxakan muryan ta ne ta hau cemasa" dan Allah hamma na shigo cikin wannan wurin...


Kallon ta ya juyo yayi,inda lokaci guda yaji tausayin yarinyan ya tsirka masa azuciya,sakin mata lallausar murmushi yayi, inda a hankali ya bu'de bakin sa wanda kamar baison maganan yace" kina son shigowa ne...?


Daga masa kai tayi alaman ehhhh....


Nan yace" okay shigo tohhh...


Cike da murna dijamah tayo bayan su,inda P.A ya fada duniyan tunani,yau sir Aliyu ne da murmushi.. Har da amincewa wannan 'kas'kan tacciyar bafullatan nan tashi go cikin company....?


Hmm lallai taci fara yau...don da'alama yana halin mutun ci kenan.


Juyowa yayi ha'di da dakatar da P.A inda yace masa,yajuya don yafasa fita, cike da mamaki P.A yace" okay sir...


Yana fadan haka yajuya ha'di da nufahn wani '6arayi na cikin company n.


Bayan tafiyan P.A ne Aliyu ya juyo ha'di da kallon dijamah, wanda take ta waige² tana kallon wurare tana murmushi...

Kafeta yayi da ido,inda yake tunanin daga wani daji ta fito ne...


Kan daga bisani yace" 'yar fillo ya sunan ki...?


Sai asannan ta kallesa,inda a hankali tace" dijamah...


Murmushi yayi kuma ha'di da cewa"wow...nyc name...Khadija... Right.

Kallon sa tayi ha'di dacewa" mai kace ne...! Banji mai kace ba..ni.

Dariya tabashi,don't haka bai bata amsar tambayan ta ba,illah cewa da yayi...okay mai kk so a cikin wannan company...?

Shiru tayi tana kallon sa,don tun datake bata ta6a ganin mutun mai kyensa ba,a hankali tace" kai wannan kyakykyawa ne,dariya yayi inda yace mata" allah ko deejah...kodai kina ciki ne..?


Abunka da hausa bai isheta ba,nan tace" wai nan ina ne...umma tace mun masana'anta ne,shine nakesom ganin ko'inah na cikin ta..

Murmushi Aliyu haidar yayi,inda ya kalleta ha'di da lumshe segxy eyes din shi,wanda yake kara jan hankalin 'yam mata dasu...


Sannan yace" ehhh muje na nuna maki wasu wurare...batare da tunani komai ba,yanufi cikin masana'anta n hadi da nuna mata wasu wuraren inda yasha surutu har yagaji,komai taganj tambaya...


A haka sukafi minti talatin,inda daga bisani yanufi office dinsa da itah,don ya lura ta gaji,kuma tana bukatan abunci...


Da shigansu yanufi fridge..inda ya dauko lemu guda biyu..yanufi wani dan hop...inda kace wurin shakatawane,amma wirine kaman dirning.. Inda ya ajiye lemun ha'di da sawa a kawo masa abun da xai dan ta6a..


Ganin yanufi fridge din ne yasa dijamah tambayan sa,wannan mene ne..?


Wanda yabata amsa da fridge ne,hadi da mata bayanin amfaninsa..sosai yau yake cikin farin ciki,wanda shikansa yake mamakin nishadin dayake ji a yau,wanda kaman suna tare da Basmah...


Da aka kawo masa abun da xasu cine,yanufi dan wannan wurin da itah,inda aka ajiye masa kajin da aka kawo masu.


Batare da tunanin komai ba,ya ajiye mata nata a plata,inda ya ajiyw mata,fork da knife...

Bai kalleta ba ya fara cin nashi,inda dijamah ta tsuramai ido,don ta kasa cin nata,ita sam bata iyah cin abun ci da wannan abun ba...


Kaman ance yakalleta,nan yaga tana nan xaune,ita bata ciba,kuma batace masa komai ba..a hankali yace deejah ya baki ci ba...?


A hankali tace" ni ban iyah ci da wannan abun ba.


Dariya ne ya subuce masa,wanda sai da yy har yagaji sannan yace" tohh bari kiga yanda ake ci da shi...


Nan ya dau spoon ha'di da fara koya mata yanda xatayi,...haka ta hauyi inda data yanka naman yasa mata tafi ala dole ta iyah yanxu..ita kuma sai murna take...


Shikuwa tausayin dijamah mane fal,a ranshi,kawai yaji yana tausaya mata,da yanayin rayuwan nata...


Su Anwar ne da Abbas suka shigo office din nasa,ha'di da kiran sunan sa da dolars...


Maganan sune ya datse sakamakon idon dasukayi da dijamah, wanda tay

i masu shige da aljana...lolz....😂😂