9
by @nanadiso10
9
LATYFAH IMAM
Nana diso
Ko data isa gidan alhaji mai lema babu mai gadin da ya hanata shiga, " barkanku da yamma ta faɗa tanata kuka. Amsa mata sukayi tare da bude mata maƙeƙin gate dinsu tashiga tunda takarasa hucewa farfajiyar gidan da motoci akallah 5 suke harabar bata iya gane ƙan gidan ba sai data hango wasu masu aiki take tambayarsu bangaren matansa takeson zuwa, mai wankin sai ya nuna mata bangaren ammy tunda ita aketa zuwa yiwa jaje da gaisuwa ko data isa zubewa tayi a palour ganin ammy zaune idonta yayi jajir sai laila dake gefe " hajiya kiyimana aikin gafara wallahi bamuda sani akan abunda tsinanniyar yarinyar nan tayi muku, ni daman tun farko ban yarda da wannan auren ba ganin yarinyar ba kalar gidan nan bace ba, to saboda Allah ina kyakyawar yaron nan ina mummunar yarinya da inada tabbacin asircemuku alhaji tayi. " ke wacece? Laila ta tambaya." " Afitar da'ita laila banason jin komai abakinta." " Hajiya kiyimana rai kitaimaka danAllah abarmu agidan nifa matar babanta ce...Bata karasa ba ammy ta wanke mata fuska da mari sannan tasaka aka fita tubda tadawo hankalinta yatashi na gidan da zasuje ga kayansu da katifunsu a waje. Dataga dai basuda yadda zasuyi nan ta nufi gidan dillalin unguwar don samun karamin gidan haya aikuwa tayi sa'a tasaku aƙan zasu dinga biyansa dubu 70 ashekara, ko da suka saka almajirai suka kwashe musu kayansu suka tayasu sawa aisha kallon uwar tata tayi tace " Yanzu umma nan zamu zauna saboda Allah?" " munada inda yafi nan ne? Dole ki zage wannan sana'ar kwallaiyar taki dakikeyi kidinga kawo ko dubu talatin ne nikuma zanje nasaro wani abun mufara siyarwa shi kuma abbas sai yadinga siyar da rake yayanku shima ai zai bada wani abun muhadu murufawa ƙanmu asiri wannan mutanen basuda mutunci." " Allah ya'isa wallahi ubangiji yasa aratayeta ma kowa ya huta muna cikin sitturar mu gashinan tajawo mana." " kedai bari Aisha ai wallahi babu tsinanniya sama da latyfah haihuwarta bata tsinana komai ba kuma kada kuyi mamakin iyami tasaka kisan. Dariya sosai Aisha tasaka tace daman mana sunga kudi ba'a saba dashi ba dole su sata ai." To amma naji ance kishiya zaiyi mata?" " haba umma haba yaya Aisha komai lallacewar hannunka baka yankeshi ba abbas yafaɗa yanzu duk dawainiyar da latyfah tayimana shine abunda zamu saka mata." " Allah yasa suyimata kisan Gillah nafaɗa din." Tashi yayi yafita daga gidan yana faɗin Allah ya kyauta.
DanAllah kidaina kukan nan iyami, babaah tafaɗa Allah yana bayan mai gaskiya inshaa Allahu kuma zatayi halinta. " baba larai ta'ina gaskiyan zatayi halinta? Gawar yaron ma an saceta ko da ɗannan yana raye wallahi zai iya barin latyfah agidan yari saboda tsanar dayayi mata." Malam idi ne yashigo yace " Addu'ar dai zamu cigaba dayimata Allah ai baya bacci." " Yanzu malam idi ko gida za'a samarmin na haya danAllah." " Haba iyami wanne irin gidan haya kuma ai dan halak baya manta alkhairi, kin dawo nan kenan sa da zama sai ku zauna tare da baba." Iyami na kuka tashiga yimasa godiya mahaifiyarsa ce tace babu godiya ai tsakanin su. "Yanzu iyami abunda yakamata muyi shine a binciki lauya dole muma mu nemi lauya." " Malam idi yanzu ta'ina zamu samu lauya? Ta'ina? Bayan kasan harka da masu kudin nan ba'acin riba." " inshaa Allahu zamuyi nasara yanzu dai zanje nasamu lauya naji yadda za'ayi kuma ƙinsan dole ne daya daga ciƙinmu ya nemi magana da'ita latyfah din dan muji takameme abunda yafaru." " To yanzu ta'ina zamu fara?" " akwai wani abokina agidan prison din zanyi magana dashi zuwa gobe sai muji yadda za'ayi ubangiji dai yafiddamu." " Ameen yaaAllah."
***
Yau kusan sati kenan suna faman aiki da zirya atsakanin su dan basa zama kwata kwata duk cuku cukun yadda kayan abiey zasu shiga yaƙeyi gaskiya yayarda abiey jarumi ne, haka yake zirya ƙadai gurin signing da bayani.
Ƙarfe biyar daidai yaƙalli agogon hannunsa, yarinyar dake aiki akusa dashi ya ƙallah mashaaAllah yafaɗa yana ƙallon yadda kirjinta yaciƙo acikin rigarta,tsigar jiƙinsa yaji ta mimmike sai kuma yacigaba da rubutun da yaƙeyi, kamin yatashi yafita harabar ciƙin ma'aikatar ya dauƙi motarsa sannan yafita. Ko daya isa gida har mai aikin dake gidan ta bude masa yazo ya huce ta palour amma Nana tayi tagumi. " Nana." Yafaɗa da kakkausar murya cikin sanyi tace " yayanmu?" " Tunanin menene haka ko bakida lafiya?. " Yayanmu banasamun latyfah hankalina yakaa kwanta wa." " Me abiey yace miki dangane da kawaye? Why can't you focus akan abunda yakawoki,." But yaya ko..." " Please stop nana jiki kwanta yafaɗa yana barin gurin. Ko da yashiga daƙinsa wanka yayi sannan ya fito da wasu samfuran atamfofi yashiga zabar design yadaɗe azaune kamin kuma ya miƙe ya dauki lemon da yashigo dashi yasha dan shi dai bayason shayi idan yazame masa dole shine zaisa yafi gane dumaman tuwansa kokuma wani abu mai nauyi shiyasa yake tafiyarsa African restaurant dake garin yaci amala yaci tuwo, karar wayarsa yasashi waiwayar bayan nashi, sunan da yafito ajiƙin wayar ne yasakashi jan tsaki yana dauƙe ƙansa yanaji aka cigaba da kira kusan sau 5 kamin kuma a daina kira. Rufe idonsa yayi yana hango yadda yake kissing din amina, ganin tunanin sai sanyashi acikin halaka yasanyashi ambatar Astagfirullah yamiƙe.
GIDAN YARI
Masifu da bala'un dake gidan yari baƙi ko bayani bazai taba faɗuwa ba, Bantaba tunani ko nazarin wannan rayuwar akeyi aciƙin gidan yari ba, wasu suna tunanin kawai mutum yana zuwa wani ƙebabban guri ne idan lokacin da akasaka masa yaciƙa sai yadawo, yau gani ni LATYFAH IMAM na tsinci ƙaina acikin wannan halin, kaddarata ta sauya komai nawa ya sauya hatta da ƙamanina daga ƙirji nq faɗa sosai da rama a ciƙin ƴan satuƙan nan sai idanuwana suka kara fitowa, ga kurajen fuskata ta suka zama taɓo sai maiƙo dake fita a fuskata,kafata tayi faso, baƙina kuwa warin da yake tattare dashi da datti ne ƙaina ban iya misaltawa, ranar da aka kawoni har kauda ƙaina nakeyi idan wasu na magana acikin daƙin amma yanzu nashiga sahunsu warin ma banaji, daman ance sai da kwanciyar hankali ai ake iya jin warin ma amma yanzu banaji, ciƙin rayuwar mu bayan samun lafiyar jiƙi bana tunanin akwai abunda yaƙai samun ince kaje inda kakeso sannan kaci abinda kakeso, aduk inda kake a yanzu haka, ka godewa Allah ka tuna akwai wasu mutane dake awani guri adaure da basuda ƴanci zuwa ko'ina sai inda aka kauwame musu, basuda ƴancin cin abunda sukeso sai abunda aka basu, basu da ƴancin kwanciya a inda suke so sai inda aka nuna musu, masifu ne ƙala kala tun daga ƙan ruwan sha, abinci da gurin kwanciya ga uwa uba bangaren horo da ladabtarwa.
Sautin kukane kawai ke tashi aciƙin ruɓabban bandaƙin danayiwa kaina alkawarin banshiga, amma da masifar kashi ta ciyoni sai gashi nice yanzu tsugunne ina fitar da abunda ke a cikina, nadaina jin warin bandaƙin nadainajin kyankyamin bandaƙin, bakaramin daɗi naji ba da nasamu nafitar da abunda ke acikina bayan kashin dake a kasan bandaƙin, da mugun zarni dake tashi abandaƙin, takalmin da akabani ya tsinke haƙan yabani damar samun leda na daureshi ƙamar yadda naga wasu daga ciƙinmu sunayi. Yadda nayi datti naƙe tashin wari sai kayi tunanin bantaba wanka ba kokuma bantaba goga turare ba, to ina ake batun wanka agurin nan ciki ma bai koshi ba, kwanciyar hanƙali ba'a maganar smau domin wanda ke shashin nan bayan huƙuncin dauri da suke dashi harda horo mai tsanani wanda inadaga ciƙin wannan mutunen. Fitowata ƙenan ina gyara zaman taƙarmina da yatsinke naji ance *lok'acin abinci* haƙan yasakani fara gudu sosai, shigar kaya kafana shine yasani kara runtse idanuna amma kuma ban tsaya da gudun da nakeyi ba, har Allah yasa na i'sa ga mutanen dake turere niya, kwanon silba ne ɗan karami na ƙarbar abinci, girman kwanan ko ɗan shekara daya kazubawa binci zai nemi ƙari amma agurin mu wannan babbar ni'ima ce, shiga nayi nafara bangaje bangaje har na isa layi ina zazzare idanuwa, tabbas na canza dan naga acikin rayuwar gidan nan idan ka nuna kai mai sanyi ne to tabbas cutarka akeyi, farkon zuwana sai na daukesu a matsayin mahauƙata masu gudu domin ƙarbo abinci ashe nice mahaukaciyar dan fada da ihu shine babban abunda zai taimaka maka ta wani bangaren, ashe kibama tanada rana dan wata suwaiba dake daƙinmu ce tazo ta turani daga layi, hakan yasakani tankadata ina zazzare idanuwa nashiga layi, maganar nutsuwa bafa ayi turereniya ce har taƙaika da ƙarbar abincin, hannuna nasaka zan ƙarbi abincin naji sauƙar bulala abayana da tasakani na gantsare hawaye nabin fuskata, yadda matar nan mai kama da samudawa ta ƙifarmin da abincin kasa yasani binsa da kallo sannan tajani akan zanje nayi wanki, " Kece akace a tsanantawa horo, kin kashe mijinki." Bance uffan ba dan zuwa yanzu yaci ace na saba da kalar zalunci da horon danake samu, wankin danagani yasani kara zare idona yana kawo ruwa yadda ta zubamin bulala yasani saurin gantsarewa ina durkusawa nafara daukar sabulun da Oman nashiga hadawa, " zanje nadawo minti 50 na baki." Ta faɗa tana barin gurin, banyi wata wata ba nayi saurin cire kayana na saka wani kayan prison din danagani acikin kayan wankin nawa nafara wankewa dan nima yanzu na'iya dabara da wayon danaga anayi, fara wanke nawa nayi na shanya bisa wani dutse sannan nashiga jibgar wankin da bantsaya ba sai danagana shima da kuka na dago duba da bayana daya dage, cikin ikon Allah har na gama na baza bata dawo ba kayan nawa dai basu bushe ba haka na sakasu sai gata tadawo tana hanƙadani ta cillani ciƙin daƙin da muke kwana ta rufe kofar da kwaɗo, atake naji fitsari ya kamani dan haka sai nayi gefe na tsugunna nayi acikin wata roba danaga sauran ƴan daƙin sunayi daman na debo ruwa tun da safe nazo nayi tsarki nayi alwala agefen kofarmu, natafi can lungun dakin dana tabbatar babu najasa nashiga sallah.
*********
Kawu bala me yashigo yana sallama yaƙasance irin mazan nan masu sautin murya dan haka suna jin yanayin sallamarsa suka fara fitowa " Anga gawar Abdulkarim a asubuti tun jiya yanzu nasaka ayi masa wanka zamu shigo dashi nan gidan sai ayi masa sallah." Ƙarar da Amiey tayi tafadi yasaka su kawu bala nufar ƙanta mumy har tana tuntube saboda tashin hanƙali.
Innalilahi wainna illahirrajiun a duk halin da kake ciki ka godewa Allah kakara godewa Allah.