WASA DA RAI

001

by @milhaart

WASA DA RAI

Oct/Fitattu5 2023


   ©️ Milhart

_Da sunan Allah mai rahma mai jin kai, Tsira da amincin Allah su tabbata ga shugaban mu annabi muhammadu S.A.W , Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah ubangijin talikai mai kowa mai komai mai rayawa da kashewa da ya bani dama da ikon sake ɗaura alkalami na akan sabon labari na mai taken *WASA DA RAI* ,ba wayona ko dabarata bane ikon sane shine ya nufa, ina rokon Allah yadda ya bani damar farawa lafiya ya bani ikon gamawa lafiya ameen._

Godiya ta musamman ga masoyiyata *SHAMSIYYA MANGA* ina Ƙaunar ki Rabin Rai,ina kuma miki fatan alhairi.

_*Gargaɗi* littafin WASA DA RAI mallakina ne haka ma haƙƙin mallakar sa don haka ban yarda a canza min labari na ba ta ko wace irin siga ba._

P________1


Shimfiɗa

"Da ga ƙarshe dai mun haɗu AJ da ma na faɗa maka ko wane ne wannan mai *WASA DA RAN* al'umma ni Abdul'Alim sai na kawo ƙarshen sa , duk da cewar ka ɗan caza min kai" ya ƙarashe yana kallon AJ dake durkushe hannayen sa a ɗaure a baya, bakin sa na zub da jini,daga gefe da gefen sa kuma yaran sane wanda suke masa aiki, haka zalika a bayan sa sun kai su 20 ko wannen an ɗaure su.



  Daga chan gefe kuma wasu matane wanda a ƙalla zasu kai talatin da alama sun jigata sosai , wasu na zaune wasu kuma kwance don wahala, yunwa da kuma ishin ruwa wasu a sume masu ɗan ƙarfi a cikin sune suke ta murna da godiya ga Allah ,suna hamdallah da ya kubutar dasu daga hannun azzaluman mutanen da basu ɗauki ran ɗan Adam a bakin komai ba,sojoji ne akansu suna basu taimakon gaggawa.




   Liutenant dake zaune kan wani dutse ya kuma kallon AJ yace "Yau ina cika bakin naka? Yau ina tsafin naka? Yau baza ka 'bace bane?" yana wani irin murmushi.

  "Hmm Abdul'Alim tabbas ka ci sunan ka The servant of all knowing, Tabbas ka shammace ni , ka far min a lokacin da ban tsammata ba amma ka sani hakan ba yana nufin kayi nasara akaina bane, nayi wa kaina alkawarin cewar ni ne ajalin ka kuma sai na kashe ka, mafi munin kisa" ya karashe maganar cikin karaji cike dajin haushin sa, tabbas yayi kuskure da bai kashe Abdul'Alim a Lokaci da ya samu dama ba gashi yanzu komai ya dagule masa.



   Murmushin nan nashi Abdul'Alim yayi kallon yaran sa yayi "Ku sasu a mota mu wuce"yayi maganar da tsigar bada umarni.

  Yayi hanyar motar sa wata mata ya gani cikin matan nan a zaune ita bata farin Ciki haka kuma ba kuka take ba, kamar zai wuce sai ya dawo ya sugunna a gaban ta yace "Baiwar Allah" ɗan ɗagowa tayi ta kalle shi "meyasa kowa na farin ciki amma banda ke? Ko akwai inda yake miki ciwone" ya tambaya cike da tausayin matar.

  Murmushi tayi wanda ya kasa gane ko na menene "Baka gane ni ba ko Abdul?"

 Cike da mamaki yake kallon ta ya akayi ta san sunan sa?

  Ganin irin kallon da yake mata ne yasa ta ce "Ba zanyi farin ciki ba, kuma bazan taba murna ba muddun wanchan yana raye"

Bin hannun ta yayi da kallo yaga AJ take nunawa bai kawo komai a ransa ba ya alakanta tsanar da ta masa da kila tasha wahala ne sosai a hannun sa.



   "Kar ki damu insha Allah gomnati zata ɗauki mumunan mataki akansa"

A razane ta mike shima mikewa yayi yana kallon ta "Abdul kasha faɗa min cewar ni kamar uwa ce a gare ka ina mai baka umarnin da ka hallaka shi"

Shiru yayi yana kallon ikon Allah Tabbas ya so ya gane fuskar ta amma dauɗa da datti sun hana ya gano ita ɗin wace ce sannan ya so ya gane muryar amma a ina ya taba jin sa?


  "Uhmn Abdul ina baka umarni da ka kashe AJ ina so kayi gunduwa gunduwa dashi a gabana ba tare da ka kashe shi ba, yanda ya maidani tamkar wata baiwarsa ina matsayin Mahaifiyar sa ina so ka yanka min shi part by part Kayi min gunduwa gunduwa da namar jikin sa"

 Waro ido Abdul'alim yayi jin da yayi tace mahaifiyar sa, bama shikaɗai kowa na gun sai da ya kuma kallon ta ya kalli AJ ba kamar matan nan da suka san irin azaba da yayi ta gana musu ashe ita ɗin mahaifiyar sa ce?

Cike da kiɗima da mamaki Alim yace "dama wannan Ummi ce da suka daɗe suna nema? ashe AJ ne ya sace ta yake gana mata azaba? Ya jero wa kanka tambayoyin a zuciyarsa da babu mai bashi amsar su sai AJ,waigowa yayi yana kallon AJ da ke kallon su babu tsoro a tare dashi ko dana sani.


  Abdul'Alim ji yayi kamar ya shake wuyar sa ya huta da irin wannan abun takaici uwa fa, uwa mahaifiya AJ yayi wa haka? Sai yau ya sake tabbatar da rashin Imani irin na AJ duk yadda yake ɗauka ashe ya wuce nan, kallon ta yayi yace "Ummi dama kece?"

 "Nice Abdul'Alim" hannayen sa duka biyu ya zura a wandon kakin sa ya juya mata baya yana kallon AJ yace

"Ummi ki faɗi duk abinda kike so ayi miki dashi,yanzun nan zan bada umarnin a aiwatar."


  "Ai na faɗa maka ,yanka min shi nake so kayi, ina so ka fara cire min yatsuntsa da ya daɗe yana taba jiki na dasu ,ku rika ajiye min naman sa a gabana ina gani"

 Kallon ɗaya yayi wa yaran sojojin suna tsaye suna jiran umarnin sa "John" ya ƙira sunan sa, da sauri ya karaso gaban sa haɗe da sara masa "Yes Sir"

 "Do as she says"

"Okay sir"

 

Murmushi john yayi shifa dama idan wurin mugunta ne yana gaba, farin cikin sa shine yaga ya kama ƴan iskan gari yana hora su bare kuma wannan tsinennen ko a addinin su da al'adar su suna girmama uwa duk lalacin ta sai shine zai wulakanta tashi uwar? zaro wani wuka a aljihun sa, dogo ne sai sheki take yana walwali kana ganin ta kaga sabuwar wuka da alama ma ba a taba amfani da ita ba, gata da kaifi wanda ko namar Giwa ce sawa ɗaya zai yanka ta, har inda AJ ke zaune ya nufa yasa wukar Hannun sa ya yanke igiyar da aka ɗaure shi dashi , sauran sojojin ne suka rirrike masa shi murmushi yayi idanun sa na zub da kwalla ya tabbata yauce ranar da zai bakwanci lahira "Ku sake ni ba sai kun rike ni ba" suka ji ya faɗa da ido Abdul'Alim ya musu nuni da su sake shi ɗin.


 John da babu ɗigon imani a tattare da ya riko hannun damar AJ, manuniyarsa ya sa wuƙa akai ji kake chaat ta faɗi a ƙasa runtse idanu AJ yayi yana jin zafin har cikin kwakwalwar sa.



 Takowa ummi tayi ta suguna a gaban sa babu ɗigon tausayin ɗan natan ta tufar da yawo akan yatsar sa da aka yanke haɗe da faɗin "Allah ya tsine maka Albarka"

*ASALIN LABARI*

"Zainab kinga halin uban nan naki ko? wai ace mutum kullum shi cikin babu yake ki duba kiga ubanki tunda ya sa ƙafa ya fita tun safe bai dawo gidan nan ba, malalaci kawai"

  Wacce aka ƙira da zainab ta zuba uban tagumi , tana kallon mahifiyar tata, tace "Haba Mama ,kema fa kin san baba yana kokari abin ne yafi ƙarfin sa, dan Allah ki daina mumunan furuci akan sa bana jin daɗi"    "Kyace haka ai ke gaki mai uba, da zaran an fara magana sai ki bata rai toh wallahi bazanyi shiru ba, Ibrahim ya tafi makaranta babu abinda yaci banda ruwan da ya ɗirka wa cikin sa, kuma nasan Yanzu ya kusa dawowa tun da ai ƙarfe biyar ake tashin su a islamiya"

  Mikewa tayi ta nufi katangar gidan da duk rabin sa a rushe, an toshe da tsummakara,sauran kuma an katange su da kara, hijab ɗinta ta zaro maroon ne tsabar koɗewa har fari fari tayi ,tsakiyar kan hijab ɗin kuwa har ta fara yagewa kamar ansa mata ruwan batir.


  

    Sanya hijabin tayi, ta nufi hanyar fita, mama tace "Ina kuma zaki?"

"Zan fitane ko zan samo wani abu bana so Ibrahim ya dawo ya tarar ba komai"


    

    Washe baki tayi haɗe da "Toh toh ki hanzarta dan Allah kar ki dawo hannu na dukan cinya yauwa a dawo lafiya" girgiza kai Zainab tayi tana mamakin hali irin na mahaifiyarta.

 


    Bayan ta fita a wani dakalin dake kofar su ta zauna, tana tunanin ina zata je ,ina ta nufa wa zai taimaka mata? Zumbur ta mike ta furta "Ya Audu" tafiya take da sauri sauri ,bata yi tafiya mai nisa ba ta isa wani ɗan madaidaicin shagon, kaya ne a cike a ciki da alama yana ciniki sosai don ganan mutane kowa na sayan abin da yake bukata , ganin mutane dayawa a shagon yasa bata karisa ba, tsayawa tayi daga nesa har tsawon mintuna goma tana tsaye a gun.



     Ɗago kansa da zaiyi ya hango ta a tsaye , sai yaji tausayinta ya sani tunda har tazo to akwai matsala , yaron shagon sa ya umarta da ya kula da shagon ya fice izuwa inda take.

  "Zainab lafiya kika tsaya daga nan?"

 Yana mata wani irin kallo wanda kana gani kasan kallon soyayya yace kai a ƙasa tace "Ina wuni?"

  Fuska a sake ya amsa da "lafiya lau ,ya gida ya su mama?"

 "Lafiya lau"

  "Madallah tun yaushe kika zo nan? Ai da ki aiko min da yaro zan zo na same ki har gida ai ba sai kinzo ba"

  "Uhmn dama dama...." sai tayi shiru ta kasa karisa maganar da ke bakinta.


    "Haba zainab ya kamata ace fa mun wuce nan zuwa yanzu ya kamata ace kin san matsayin ki a wurina,na sha faɗa miki mun zama ɗaya ki daina jin kunya ko shakkar sanar dani komai kinji?"

   Matsar kwalla ta fara yi ,cikin muryar kuka tace "Wallahi tun shekaran jiya rabon mu da abinci, ruwa kawai muke ta sha, abincin da ka kawo ya ƙare haka ma jarin da ka bani mun cinye"


    "Amma baki kyauta min ba, har kukayi kwanakin nan baki sanar dani ba gaskiya kin bata min rai"

 "Kayi hakuri dan Allah wallahi bana son ɗaura maka ɗawainiya ne shiyasa"

   "Ai kaji ai ,yanzu ki koma gida zan turo da yaro dai na kuka kinji"

   Hannu tasa ta share hawayenta tace "Nagode sosai Allah ya saka da alhairi"

  "Na sha faɗa miki babu godiya a tsakanina dake,matsayin kanwa kike a gareni kuma matar da zan aura insha Allah so duk wani abu da na miki ko zan miki yiwa kaine, yanzu ki wuce gida anjima zan zo idan akayi sallar isha, kimin wannan kwalliyar da kike min wacce take sace min zuciya" ya kareshe maganar cikin sanyin muryar da yake sace mata zuciya dashi.




   Rufe fuskar ta tayi da tafukan hannun ta, tayi saurin barin wurin, bai bar kallonta ba har saida ta bacewa ganin sa.

    


   Da sallama ta shiga gidan nasu mama dake kwance a ɗaki jin muryar ta yasa tayi saurin fitowa tana washe baki, ganin ta ba komai a hannun ta ta bata raai haɗe da faɗin "Ya dai?ya na ganki haka?" ta karashe maganar cikin sigar tuhuma.



   "Mama na....."

"Dallah malama ki min shiru shasha kawai, dake da ubanki duk baku da amafani a gidan nan, shi ya fita ya dawo hannu na dukan cinya, kema kuma haka to wai ko nice kuke so na fita na nemo muka abinda zaku ci?"


   Jin abinda tace ne yasa ta lura da baba da yake kwance a kan wata koɗaɗɗiyar tabarma wanda rabinta a cinye take , kallon mama kawai yake bai ce mata komai ba, inda yake ta nufa,durkusawa tayi tana faɗin "Baba sannu da dawowa"

"Haka zaku ƙare munafukan banza kawai" tace cike da tsiwa.


 "Yauwa mamana, ina kika je ne na dawo bakya nan?"

   "Naje shagon........"

Kan ta karisa maganar da take wani yaro ya kwaɗa sallama , mama ce ta amsa da "Waye?" madadin ta amsa sallamar.

  

   "Nine"

"Kai waye kaji min ɗan iskan yaro" ta faɗi a hatsale.

"Audu ne ya turi ni"

   "Shigo shigo mana kaji min ja'irin yaro ,shigo nace" ta mike jin an ambaci sunan audu

  Yaron shagon sa ya turo wanda ko wani lokaci shi ke kawo mata aika ya shigo tare da wani yaro sa'arsa, katon din taliya da Indomie ce, da wata bakar ledar , shi kuma ɗayan man gyaɗa da manja ,da gishiri da maggi ya ya riko a hannun sa.



    Mama baki har kunne garin sauri har tuntunbe tayi ta buge ƙafarta amma bata tsaya ta duba raunin da ta ji ba ,ta cigaba da tafiya tana faɗin "Madallah madallah ga ɗan albarka kai audullahi ,babu abinda zance wa yaron nan Wallahi uwar ka ta iya haihuwa" nan suka shiga dire kayayyakin , suna gama direwa suka fice abinsu.



    Baba yace "Mamana na hane ki da zuwa roko amma kin ki ji ko? Yaushe kika fara bijirewa maganata?"

  Kai a ƙasa tace "Kayi hakuri baba Wallahi nima ba yin kaina bane,gani nayi yau kwanaki uku kenan bamu ɗaura tukunya a gidan nan ba, baba ni ban damu da kaina ba Ibrahim nake tunawa yaro ne bai san babu ba"

  Ajiyar zuciya ya sauke yayi shiru yana tuna abubuwa da dama sai yace "Allah shi kyauta amma dan Allah alfarma ɗaya nake nema a gare ki ,ki duk rintsi ki rike mutunci da darajar ki ta ƴa mace kar ki bari halin rashi da muke ciki yasa ki bi son zuciyar ki, sannan dan Allah ki daina rokon Audu bana jin daɗi duk da cewar na bashi ke" 

  "Insha Allah baba zan kiyaye"

  Charaaf kuwa mama ta cha'be zancen "Ai dole kace haka, kana bakin ciki da taimakon mu da ake , yooo in ba shi ba wazai bamu , baka da aiki kullum sai yawo da koɗaɗdiyar riga sai kace wani........."

   "Haba Mama" zainab ta dakatar da ita "Rufe min baki shasha kawai ki tsaya kina biyewa ubanki zai kai kine ya baro, ki taso ki dafa mana Ɗan wake naga ya sako fulawa a ciki"

   Jiki a sanyaye ta mike ta zare hijab ɗin dake jikinta,ta rataya shi a kan igiyar shanyar dake tsakar gidan nasu ta nufi inda murhu yake ta fara kokarin haɗa wuta.




     "Kuma ki tabbata kinyi shi da kyau kar ki cika kanwa yauwa" faɗin mama tana kaiwa nan ta shige ɗaki.



   Bata kai ga gama girkin ba Ibrahim ya dawo amma ganin an hura wuta ya sanya yayi ta murna, abunka da yaro.


  Bayan sun gama cin abincin ne kuma baba da Ibrahim suka fita sallar magriba basu dawo ba har sai da akayi sallar isha.

  A kofar gidan suka tarar da Audu a tsaye wanda shima isowarsa kenan,har ƙasa ya durkusa ya gaida baba ,fuska ba yabo ba fallasa ya amsa kana ya masa godiya ya shige gidan haɗe da faɗin "bari Ibrahim ya kirawo maka ita"

  Kai a kasa ya amsa da"Toh baba na gode"


*🆕RELEASE🔰*


   ```FT5```

       2️⃣0️⃣2️⃣3️⃣



💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼 *hohoho Allah ya kawo mu qarshen shekara tazo😍, masu iya magana suka ce mai laya kiyayi mai zamani🤸🏼‍♀️, wani kaya sai amale🏇🏼, in kaji ana a marmatsa to giwa ce ta iso🥳,haka in kaji kira ba banza ba🤩...Ina ku ke masoya, ma'abota karatun littafan hausa, kuma masoya littafanmu🥰, Hajiyoyi kun karanta waɗannan littafan ba?, LULLUƁIN BIRI, MUGUN NUFI, CAPTAIN FAWZAN, MATAR UBA, SUNE SILA....To ya ku ka ji salon dukka labaran?😍, sun ƙayatar ba?, sun tafi da ruhika ba😅?, to fa ai su ɗin duk ba komai ba ne, somun taɓi ne cikin shirin da muka yi na nishaɗatar da ku a sabbin labarai masu jan hankali🥰ku shirya kawai ku biyo mu cikin tafiyar TEAM FITATTU BIYAR, salon labaran da suke daban da saura, labarai masu tarin darasi, ma'ana da kuma tsuma zuciyar me karantawa da sauraro😍...LITTAFAI BIYAR A ALƘALUMA BIYAR CIKIN MAFARKI ƊAYA😍...Hajjiyoyi da Alhazawa da kuɗi ƙalilan za ku mallaki littafan da baza kuyi danasani da nadamar siya da karantawa ba💃🏼, akwai tarin ilimi aciki🫶🏼, akwai nishaɗi😹, wa'azantarwa🌝ga uwa uba ƙayatacciyar soyayya mai saka jiki kyarma saboda tsantsar shauqi😍...*



*LITTAFAN SUNE KAMAN HAKA👇🏻*


1- *ƘAYAR RUWA na Halimahz*

2- *FARGAR JAJI na Aisha Abdullahi Yabo*

3- *WASA DA RAI na Fadeela Yakubu Milhat*

4- *LOKACI NE na Fatima Oum Mumtaz*

5- *KWANTAN ƁAUNA na Nana Haleema*


_LITTAFI ƊAYA:- ₦500_

_LITTAFI BIYU:- ₦800_

_LITTAFI UKU:- ₦900_

_LITTAFI HUDU:- ₦1000_

_LITTAFI BIYAR:- ₦1200_

_VIP 2k._


Za ku biya kuɗi ta wannan account...

*6314170140*

*FIDELITY BANK*

*SA'ADIYYA ZAKARIYYA HARUNA*


sai ku tura da shaidar biya tare da sunan littafin da kuke biɗa a wannan number....*Oum Mumtaz(***)*


katin waya zaku tura hoton MTN da sunan littafin ta wannan number...*Milhat(***)*



*ƳAN NIGER KU TURA DA KUƊINKU TA Mkoudi 89356025 airtel, SANNAN KU TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBA...Aisha Yabo(***).*


_LITTAFI ƊAYA:- 350f_

_LITTAFI BIYU:- 600f_

_LITTAFI UKU:- 650f_

_LITTAFI HUƊU:- 750f_

_LITTAFI BIYAR:- 850f_



```ƳAN KASUWAN DA ZA'A TALLATA MAKU HAJOJINKU DOMIN KASUWANCINKU YA ZAGA IN DA BAKU YI ZATO BA, TALLAN YA KASU KASHI-KASHI:-```


*_TALLA A KOWANNE PAGE NA BOOK 500, 5pages2k, Complete Book 10k._*

*_•TALLA A VEDIO NA YOUTUBE 1500_*

*_•TICTOK 1500_*

*_•INSTGRAM 1500_*

*_•FACEBOOK 1500_*

*_•WHATSAPP STATUS; 24hrs500, 48hrs1k, 72hrs1500, 168hrs3500._*


```ku tura da kuɗin ta account numbern da ke sama sannan ku tura da shaidar biya haɗe da details na abin da kuke so a muku talla akai ta wannan lambar...NanaHaleema(***.)```


*Youtubers da suke son mallakar littafanmu domin ɗorawa a channel sai kuyi magana a wannan lamba...Halimahz(***).*



MUNA MARHABAN DA KOWA CIKIN MUTUNTAWA, A ISO LAFIYA🤩


*Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga duk wanda ya siya littafin Fitattu Biyar...son so fisabilillah😍*


_________________________

Milhart Ce

Yar Terawa

Please share ,and comment