LATYFAH IMAM

18

by @nanadiso10

18


LATYFAH IMAM


Nana diso



Idanuwa na Na dago na zuba masa su, atake suka canza kala! Cikin girmamawa da iyayena suƙa koyamin Nace " Allahn daya halicce ka shine wanda ya halicceni! Nayi mamakin furucin da ƙayimun domin bantaba tsammanin ɗan gidan Alhaji mai lema zai kasance mara tarbiya ba! Kana tunanin inasonka ne? Kokuma ina son dukiyar mahaifinka? Ko daya mahaifinka abunda yayimana mu da iyayenmu bazamu iya biyansa ba! Kamar yadda kake ganin an tilasaka to nima haka aka tilasani! In har zakaje ka bijerewa mahaifinka akan afasa auren da nima ka taimakamin dan bansan ɗan da baba yakeyiwa kuka yakai haka gurin watsar da tarbiyarsa ba! Kunsan da yadago manyan idanuwansa me yayi min? Marina yayi marin da Na manta rabun da ayimun na manta rabon da ataɓa lafiyar jiƙina, bai tsaya anan ba sai ya ciro bandir sin ƴan naira dari ya watsomin yana faɗin " who are you da zaki gayamin irin wannan kalmar? Who is your father? Wacece uwarki? Ƴar Ladanin masallacin k'okuma mai awara ? Doyi kikeyi wari kikeyi? Ni Abdulkarim mai lema nafi ƙarfin tarayya dake ƴar gidan talakawa! Yaja motarsa yayi tafiyarsa! Me zanyi? Kuka ko ihu? Ai ƙam zuciyata kasa rike kuƙan tayi kuma naƙi dauƙan kudin nayi cikin gida ashe karamin ƙanina abbas yana ƙallon komai! Sai ya tattaro kud'in yashigo gidan! Kuka nasaka ina rusa ihu, iyami dake girki tafito tana tambayata ko lafiya? Haka umma ma tashigo tana fadin ai idan da kwadayi da wulakanci yarinya sai muni amma saboda rashin son gaskiya da tsoron Allah kin dage sai kin auri mai kudi! To ai da alhaji mai leman kika aura ba ɗansa ba!" " Iya baƙinki kamin na cimiki mutunci." Iyami tafaɗa tana nuna umma. Umma tafita tana dariya ! Mutunci daman kunada sauran mutunci tasa dariya harda shewa!. Bakin cikin lafazinta yasa nasakawa kukana ƙarfi ina kallon kakara kuma uwata ubana ƴar uwata! " Iyami." " Basai ƙin gayamin komai ba naji duk lafazin yaron, ai nayi tunanin zaki iya? Ashe bazaki iyaba kika amince? Inake ina yaron nan mai kama da turawa saboda Allah? Inake ina yaron da turawa suka raina? Tun farkon maganar nan sai da nasanarmiki akan kice baki amince ba kika nunamin kada muzama butulu, abunda bakisani ba latyfah imam rayuwar aure ta huce duk yadda kike tunani, morewa aure ki aure wanda yake sonki yafi naki ba laifi idan duk kunason kanku amma idan namiji ya aureki bayasonki ai zan iya kiramiki da abunda zaiyi miki sai yafi ta'addanci! Kinada kyau kuma ke kyakyawace kada ki barinwani yadinga sakaki awani tunani ke kikace zaki iya dan haka sai kicigaba da haƙuri." Bance mata komai ba duk da ina sauraron duk abunda take cewa sai dai nacigaba da kukana muna zaune abbas yashigo shima idonsa yayi jajir, kamar yadda nagayamuku abbas ɗan ummane amma yana mutuƙar sona. Mikomin kudin yayi yace " Yaya kiyi hakuri Allah bazai bari wani bawansa ya wulakntaki ba." Kallon kudin hannun nasa nayi inajin wani baƙin ciki acikin raina! Ganin bazan karba ba yasakashi ajiyewa yafita.


Aciƙin satin aka kawo lefena, ashe bakaramin rigima akeyi ba agidan alhaji mai lema dan Rikicin da Ammy takeyi sai yasaka alhaji mai lema buɗe baƙinsa yace indai takara magana akan lamarin auren nan to tabbas a baƙin aurenta, hakan yasata kauda kanta akaina amma duk wani alkabair tana jifana dashi! Kawo lefe unguwar mu Sai yazamana yajawo cecekuce acikin mutane anata faɗin ankawomin lefe zanje na saida kaina saboda kudi! A satin nana ta dawo daga tafiyar datayi! Suka zauna da iyami suka tsara yadda zasu gabatar da bikin nikuma ina gefe abun duniya ya isheni duk yadda natsara aurena da irin soyayyar da zamuci da mijina yau ta ruguje! Innalilahi wainna illahirrajiun aduk lokacin dana tino da abdul abunda nake ambata kenan! Nana ce ta tsayamin akomai na bikin nawa, abikin ma dangin mahaifiyata haka sukace basuda hali kunsan ummyn nana itace tayimun gado set da kujeru da tv da fridge kai naga kauna ranar kuka nayi saboda farinciki dan komai tsiya anfidda ni ƙunya, ranar da aka ƙaini bayan kowa ya watse ƙunsan Abdulkarim bai kwana gidan ba. Inada kwana uku agidan sai ga kaninsa aliyu da laila ƙunga irin zagin da sukayimun apalour daman tunda naji yadda suka shigo yasa nasakawa kofar bedroom dina key har suka karaci zaginsu amma ban fito ba suka gaji suka tafi. Ranar ma kwana nayi ina kuka! Ranar da abdul ya dawo ranar satina daya agidansa cikin girmamawa nace masa barka da zuwa ina mikewa! Kumsan menene abunda yafito daga baƙinsa! " tasarmin agujerar nan dan ba kujerar talakawa bace ba ba'a saba hawa agida ba..and wannan ne naƙarshe da zan kara zuwa palour na naganki zauni da mummunar fuskarki a palour na to tabbas sai na ƙona fuskarki, hawayen fuskata na share nayi shigewata daƙi shikuma yana jan tsaki, tunda nashiga daƙin sai yazamana damuwa tanason illatani wani zubin da rana nana zatabiyo musha hira, idan kuma tanada aiki a offices bata biyowa! Rana tsaka alhaji mai lema yace in fara zuwa aiki hakan yasa nadinga yimasa addu'a ina gode masa, amma sai yacemin ai abunda nayi masa komaima ayanzu zai iyayimun dan ni zaiyiwa godiya da na zauna da abdul, kuma duk wani abu idan yayimun in tabbatar na sanar masa nadai amsa da to ina kashe wayar bayan munyi sallama!.


LATYFAH IMAM ranar da nafara zuwa aiki shima na fuskanci wulakanci daga mutane da dama aciki kuma harda wasu ma'aikatan dan sai kaji ance elephant ashe abdul ne idan zai aika akirani idan zan karbi wata takardar yake cemin haka! Abun mamaki sai muka haɗe da nana duk da ita tarigani fara aikin amma matsayin da aka kaini hatta Abdulkarim din sai da yayi mamaki! Dan daga shi sai ni abangaren!.


Ranar lahadi yakama babu aiki haƙan yasakani kunna TV dan maganar gaskiya gidan mu ba'a taɓa kunna gen ba nepa ce dai munada ita TV kuwa bamuda ita adaƙinmu! Hakan yasaka duk inda naga TV sai na tsaya nayi kallo indai takaice muku ina mutuƙar son kallo! TV dita da ummy tabani sai aka saka awani daƙi da babu komai ba'a jona ba tunda masu jiran suka kula kusan gidan ancikeshi! Na nutsar da zuciyata ina kallo a tashar mbc bollywood zazzafan film sukeyi mai zafi, na soyayya na mai da hanƙalina gaba daya ina kallo sai ji nayi kawai ankashe TV din an shigayimun faɗa! " Ubanki yasamin TV din kokuma uwarki? Nagaji nagaji dake kifita rayuwa! Natsaneki bazantaba son baƙar macce ba! Mummuna mai katoton baƙi." Raina yayi mutukar ɓaci na kalleshi nashiga mayar masa da martini Nima, " Dan iska irinka wanda baya tsoron Allah da tsoron saɓon Allah shine wanda zanzo? Kokuma lalataccen da bayabin iyayensa? Kokuma farin da babu farin zuciya?Na tsaneka fiye da yadda kake tsammani Abdulkarim mai lema idan ka isa sawwakamin in rabo da wannan auren kaddarar!." Bankarasa bude baƙina ba naji ya ƙifa min mari ya hambaŕeni ya buga kaina abango jinayi kamar nayi fitsara dan azaba kuka sosai yaci ƙarfina!. " ko wanene ubanki baki isa ki zageni ba! Monkey kawai mai siffar dabbobi, tumbi kamar i jaƙar taɓo! Yafaɗa yana na barin gidan!. Kuka sosai nafashe dashi ina baƙin cikin zagarmin imam da akayi dabaijiba bai gani ba! Wata igiya nagani a wajen gidan na dakko zan rataya kaina, ashe Nana ta iso ina shigowa palour ta kwace igiyar ta cillar ta hauni da masifar da bata taɓa yimun ba. Nima banyi shiru ba nahau magana ina faɗin to ni nayi ƙaina nana? Kibarni na mutu in huta da baƙin cikin mutane kibarni in mutu in huta danAllah! Ta rungumeni taba bani haƙuri sosai gami da yimun nasiha masu ratsa jiki!


Maganar kashe mijina kuma bansan komai akaiba nadawo daga aiki kenan na tarar dashi... Nan takarasa musu labarin tana goge hawaye tare da ɗan jiza baƙin jin yadda mararta ta murda.


CIGABAN LABARI.


LATYFAH IMAM kowanne bawa da kalar tasa ƙaddarar ki godewa Allah dataki ni yaran mijina biyu na kashe wallahi da hannuna wata ƴar budurwar yarinya tafaɗa kinganni nan babu abunda bazanyi ba akan kishi! Kuma badan komai na kashe su ba sai dan yarana su samu gado su ƙadai! Daya matar datayi magana na ƙallah " To Naki ai da sauki tunda bake kikayi kisan ba Nifa ɗan makociyata na jefa a rijiya muna faɗa Allah yasa kamin aɗakoshi ya mutu!. Wata ta gefe tace " Ni ai mijin nawa na zubawa abu acikin lemo yamutu saboda kishiyar da zaiyimun! Zafaffen hawayene yashiga gudu a fuskata! Allah karabamu da mummunar kaddara banda wasu acikinsu dake bani labarin bashine yaƙawosu! Me ake da gidan yari? YA Allah ko makiyina ƙarda kajarraba nafaɗa ina miƙewa jin anzo buɗe mana kofa! Yau mun Samu aiki mai sauki dan wankin kayane mukayi duk da ina ɗan jin jiki yanzu baƙamar da ba! Ga yunwar dake jigila dani ga ƙuma zazzabin da baya barina! Wayene yacika fuskata ina gano irin yadda aka zalunci ne wato shi talaka bashida mataimaki sai Allah acikin wannan gidan akwai wanda dubu biyar takawosu saboda sun kasa biya wasu kuma an manta da case dinsu ma! Kuka mai sauti nakara fashewa dashi ina karajin tsoron Allah acikin raina, yanzu Alhaji mai lema yaje da hakkina ina? Yaje dashi ina? Nafaɗa ina sakin wani kukan wannan shine tukuicin alkhairi da bayiwa zuri'arsa, kafata na kallah yadda ta kumbura tayi fururu ga kuma tsatsagewa datayi, Latyfah imam tundaga nisa naji manyan gidan nakirana da gudu natawo ina tsoron kada nayi laifi su tabamin lafiyar jikina tunda yiwa mutum bulala ba abuni mai wahala agurinsu ba. " Har kasa na durkusa gaban namijin da yazama shugaba a wannan yankin namu da ake cewa darakta, kallona yayi da cikin nawa mukayi gaba sai aka sakamin ankwa ahannuna aka shigar dani mota mukatafi ashe wai yau ake zaman kotu! Tunda Nashigo har na tsaya agurin mai lefe ban iya nadaga ƙaina na kalli kowa ba! Iyami dake kallona tana kuka kasa kasa nasan tausayina takeji, Muryar laila naji tana faɗin ai gashinan tun yanzu ƙingani.


Ayau ashirin da bakwai ga watan January kotu ta dawo domin sauraron karar wacce ta kashe mijinta, Domin yanke hukunci na karshe!


Alkali ne yace " Ina lauyan wacce ake kara da wanda suke kara?"


Ya mai girma mai shari'a nine lauyan wacce ake kara! Barrister salisu.


Ya mai girma mai shari'a nine lauyan wanda suke kara! Barrister josh.


Lauyan wanda yake kara ko kamada abun cewa? Girmamawa yace " Tabbas inadashi ya mai girma mai shari'a."


Malama latyfah kowa yasan bakyason mijinki kuna ƴartsama tsakaninku harma mai gadin gidanku yasha zuwa yarabaku faɗa sau tari da yawama yana kamaki da makami a hannunki kamar wuka kina ikrarin zaki caka masa!."


LATYFAH IMAM ce ta zubawa lauyan idanu tanajin yadda zuciyarta ke zafin na irin karya da aka haɗa tace " Ni bantaɓa daukar makami ba! Kuma bantaba dambe da mijina ba kumama bani na kasheshi ba."


Sosai yashiga yimata tambayoyi tana amsawa!


Da wannan nakeso kutu tayi adalci azartarwa wacce ake kara da hukuncin daurin rai da rai a gidan yari.


Ya mai girma mai shari'a latyfah imam tanada juna biyu! Babu ta inda kotu zata iya zartar mata da hukunci har sai ta sauka! Duba da abunda ke cikinta bashida laifin komai face ma hukuntata zaisa ayi barna da tazajawo matsala!. Ya mai girma mai shari'a cikin jiƙinta bashida alaka da abunda wacce ake tuhuma ta aikata! Muna neman kotu tayi mata sassauci har sai ta haihu sai azartar mata da huƙunci.


Ya mai girma mai shari'a inada korafi!


Korafi baiƙarbu ba!


Barrister salisu yacigaba da magana " Dan haka muke neman kotu ta bamu belinta zuwa bayan haihuwarta."


Alkali ne ya gyara murya yace " Kotu bata