WASA DA RAI

002

by @milhaart

Ba jimawa ta fito jikinta sanye da wata koɗaɗɗiyar atamfa ruwan toka sannan kanta sanye yake da hijab shima ruwan toka har ya fara komawa fari fari, da sallama ta ƙarasa inda yake ,bayan sun gaisa suka zauna nan suka shiga lambun masoya, suna hirar su hankali kwance cike da so da ƙauna.


 *Shin wace ce Zainab?*

Zainab ƴa ce ga alhaji Adam da matar sa Hajiya Saratu, mai kuɗine shi sosai a garin Adamawa(Mubi) , a lokacin faɗan boko haram ya rasa kowa da komai nashi,matarsa da ƴarsa tilo suka tsira Hakan yasa sukayi hijira suka dawo jahar gombe ,ta dalilin wani Abokin kasuwancin ya bashi wani gida wanda ɗaki biyune ,sai kitchen da ban ɗaki, a lokacin zainab na da shekara biyar a duniya ,anan ya fara sayar da kayan miya a kofar gida ba laifi yana samu, wanda duk a ciki suke ci suke sha kuma ya sanya Zainab a makaranta.



   Matar sa saratu haifaffiyar ƴar garin Damaturu ce marainiya ce, a yawon sa na kasuwanci ya haɗu da ita ƙanin mahaifinta ya bashi auren ta, daga nan ya ɗauko matar sa suka dawo cikin garin maiduguri suna zaman auren su lafiya lafiya.



   Sai bayan da ya rasa komai ta fito mishi da asalin true color ɗinta ,duk irin wahalar da yake sha bata gani kullum cikin kushe abubuwan da yake yi take , Zainab na da shekara 13 Hajiya saratu ta haifi ɗanta wanda yaci suna Ibrahim, tun bayan haihuwar sa komai ya lalace jarin ya karye sanadiyar tilasta masa da takeyi akan sayan Abubuwan da ba dole ba a haka jarin ya ƙarye ya zauna baya komai sai buga bugan da yake yi, daƙyar da maƙyarƙyasa Zainab ta kammala secondary school tun daga nan karatun ya tsaya.





   Audu ɗane ga abokin mahifin Zainab, shine yake taimaka musu da ɗan abinda ba a rasa ba tun zainab na ƙarama har ta girma ya nuna kwaɗayin sa akan ta na yana son auren ta ,ba bata lokaci baba ya bashi aurenta wanda a yanzu bai wuce watanni 4 ba bikin su, wannan kenan.



      *cigaban labari*

Zainab ce kwance a ɗakin ta wanda ba komai cikin sa sai wata tsohuwar taburma gefe guda kuma kayan sawan tane ɗaure acikin wata zani, hannun ta kuma rike yake da wayar kirar andriod tana karanta littafin *Dangin Ubana* na marubuciyar nan Fadeelah Yakubu wacce aka fi sani da Milhat, idanunta fal yake da hawaye tana tausayin halin da Haisam ke ciki sai taji ai ita alhamdulillah tunda Iyayenta su duka biyu suna tare da ita ba kamar haisam ba, da baida kowa daga Allah sai mahaifiyar sa.



    Mama ce da ɗago yamutsasen labulen ɗakin nata ,daga tsaye tace "Me kikeyi ne a ɗakin nan tun safe baki fito ba?"

  "Karatu nake mama"

 "Aikin kenan, ana ta karanta shirme ni ina mamakin audu ma wallahi kawai ya ɗauki wayar sa ya baki kwanaki nawa wayar nan tayi hannun ki mtsww"

  "Uhmn mama akwai abinda zan miki ne?"

 "Kaji min ƴa to kawai don na leko shine akace dole sai zaki min wani abu ko?"

  " ba haka nake nufi ba mama, kiyi hakuri"




 "Kyaji dashi " lekawa tayi ta duba inda baba yake zaune taga ya tashi, saɗaf saɗaf ta shigo ɗakin tana faɗin "Yau kusan sati uku fa kenan abincin mu ya kusa karewa ki faɗawa audu akan kari" tana maganar cikin raɗa.


  Zainab tace "Amma mama baba fa ya hana,yace in........"

"Rufe min baki shasha kawai,to me zamuci idan abincin ya ƙare ko ubanki zamu sa a tukunyar ne mu dafa?" shiru tayi bata ce mata komai ba.


   "Zaki tashi ne ki wuce ko sai jikin ki ya gaya miki?" ba dan ta so ba ta mike ta sanya hijab ɗinta ta fice daga cikin gidan, sai dai wannan karon ba shagon ta nufa ba wani gida dake kusa dasu ta Shiga da sallama har ƙasa da durkusa ta gaida dattijuwar matar da ke zaune a karkashin bishiyar mangoro tana gyara shinkafa ,bayan ta amsa gaisuwar tatar sai tace "Mama Nusaiba fa?"

"Tana ciki, tana wannan shegen wayar da bata karewa dan Allah ki rika bata shawara"

Murmushi tayi haɗe da faɗin "Toh mama insha Allahu"

  Mikewa tayi ta shige ɗakin da ya kasance na nusaiba, nusaiba ƙawarta ce tun na yaranta ita ma ƴar talakawace amma sai dai ita tana da yayu maza har biyu wanda sune suke ciyar da su da duk wani bukata nasu.



    ilaikuwa yarda tace tana kwance tana ta Video call jin sallamar Zainab ne ya sanya ta katse ƙiran haɗe da ijiye wayar ta zauna tana faɗin "Kinsan Allah kina raina anjima nake shirin zuwa duba ki"

  "Ai dama nasan haka zakice , kin kini yanzu kin ma manta dani"

  "Ban manta dake ba wallahi zee tawa ke ɗince sai a hankali da zarar an fara magana sai ki rika cewa Allah yace annabi yace ki duba ki ga yadda na canza.." hannu tasa ta ɗauki wayar ta haɗe da faɗin "Kinga wayar nan ina zaune aka kawo min ita har gida Iphone 7+ ce ,kin makale wa mai shago ko ƴar Tecno mai tochi ya ƙasa saya miki matsiyaci kawai"


    "Kinga duk abinda zakice akaina kice amma karki ƙara zagin sa" ta mike da niyar tafiya tayi saurin riketa "matsala ta dake saurin fushi, amma wayar hannun ki fa ta wace ce?"

"Tashi ce"

  "Affff itel ce fa, hmm to na daiyi shiru kan kice na zagan miki masoyi, amma da zaki bi ta tawa wallahi da rayuwar ki ta canza ke hatta iyaye ki ma sai sun huta"

  "Kamarya kenan fa? Ban gane ba?"

  Mikewa tayi ta tura kofar ɗakin nata kana ta dawo ta zauna a bakin gadon tace "Tsakani da Allah baki ga yadda ɗakina ya canza ba?"

  Kallon ɗakin zainab tayi tabbas ɗakin ya zanza yasha gyara, zainab tace "Na gani Yaya Ali ne ya gyara miki ko?"

  "Mtsww me na sama yaci bare ya bawa na kasa? Ni na gyara kayana da kaina"

  Waro ido zainab tayi tace "Da kanki wai kina nufin ,gado da katifa da su waldrope ɗin nan duk kece kika canza da kanki?"


   "Kwarai bari ma ki gani"

Buɗe waldrope ɗin tayi tace "kinga kayan nan duk mallakinane"

   Itama gun waldrope ɗin tayi baki a buɗe take kallon kayan "Uhmn zaki iya samun fiye da haka idan kina so"


   "Ina so mana amma me kikeyi haka?"

  "Jikina"

Wani irin kallo Zee ta yiwa Nusaiba, kallon nan fahimta ba

Murmushi Nusaiba tayi tace "Jikina shi ke kawo min kuɗi"

juyi take ta ɗaura da faɗin "saurayina Faisal babu inda bama zuwa tare na sake mishi jikina yayi yadda yake so dani idan ya gama ya cika min jakata da kuɗi ga kuɗi ga morewa"



   Waro ido zainab tace "Kina nufin wai zina kuke yi kuma yake biyan ki? Karuwanci kenan fa Nusaiba"

  "More rayuwa dai wani karuwanci, kin san Allah idan kika fara harkan nan zaki fahimci abinda nake faɗa miki, duk wasu bukatun ki za'a miki su bayan nan kuma a kawar miki da sha'awa"

  "Wa iyazubillah , Nusaiba haka kika zama? Yaushe kika zama haka? Inna lillahi wa inna ilaijirraji'un"

  "Mtsww ke malama ya haka taimakon ki fa zanyi amma tunda bakya so shikenan" wani katuwar leda ta miko mata haɗe da faɗin "gashi wannan naki ne"

 "Na mene ne wannan?"

"Kaya ne na saya miki, set biyar ba yawa kema ya kamata ki faso gari"




"Allah ya min tsari bazan sa kayan haram ba, ni kinga tafiya ta zan kaiwa Audu wayar sa,Allah ya ganar dake"

Dariya tayi kana tace "Ki daiyi shawara zan ajiye miki wannan, dama donke na saya" ta nuna mata ledar buɗe kofar tayi ta fice bayan tayiwa mama sallama, ta nufi shagon audu ta tarar ma baya nan , ta bada wayar aka ajiye masa ta juya ta koma gida tana mamakin yanda akayi nusaiba tasauya.




   Tana shiga cikin gidan nasu mama tare da faɗin "yaya kin same shi?"

"A a baya nan"

"Toh ina kika je tun ɗazu?"

  "Gidan su Nusaiba" tana kai nan ta shige ɗakin ta , a bayyane mama tace "Ko me ke daminta oho"

_______________

Milhart

Ƴar Terawa

Please share and comment