page 14
_Typing🤳🏼_
*_....🌪️ZULFAH🌪️...._*
_UMMU MAHER_
*@MRS GREEN🍏*
_GAWURTATTU 3_
Book 2 page 14
*_follow Zulfah on Arewa books_*
https://arewabooks.com/book?id=64ff0277d73b80a18ea59540
*_VIA GROUP ZULFAH FANS_*
***
TgSsodCRZGcEjERSEsBY
_*AMMA ARAB!AMMA ARAB!!
AMMA ARAB!!!*_
_kai daga jin sunan kasan sunan
ya amsa sunansa,AMMA
ARAB ta kawo muku wani
supplement na gyaran jiki mai
sanya daɗi da ƙamshi AMMA
ARAB gidan ƙamshi_
*MUSUK*
*MADARAR TURARE*
*KAJIJI*
*ROT*
*SANDAL*
*HUMFUR*
*SANDAL FLASK*
*SANDAL WUD*
*AALUT*
*GAF-GAF*
*JANNAMI*
*ƘWALAKCA*
*MAHAHABSUFYAN*
*WANNAN SHINE GRP
ƊINA NA WHATSAPP,KI
ANTAYO SABODA KADA AYI BABU KE*
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
***
/BrUXmBHnDN6KUJYnkBDT7S
*ADDRESS👇🏻👇🏻👇🏻*
Zaria road kwankwasiyya sabon gari ɗangwauro house number 224
Kano
OR CALL MY CONTACT
***
*AƘWAI WANI SUPPLEMENTA NA GYARAN JIKI DA TAZO MUKU DASHI KE DA KANKI IDAN KIKA YI ZAKISAN EH LALLAI ZAKI GIGITA ME GIDA,KINSAN MAZA SAI DA ƘAMSHI DUK MATAR DA BATA SAYI WANNAN SUPPLEMENT ƊIN BA TO AN BARTA A BAYA*
*AƘWAI BABBAN MAGANI NA INFECTION,WANDA ZAI DAWO MIKI DA MARTABARKI NA ƳA MACE,ZAI CIKO MIKI DA NI'IMARKI KI KOMA ƳAR GATAN MEGIDA*
*AƘWAI BABBAR KAMBASA,TA TURARA KAYA HAJIYA KI BUƊE BAKIN ALJIHU KI JIƘO DA ƘAMSHI,KINA ZAMA AN SAN KIN ISA MACE HAJIYA DON AMMA ARAB TA SHARA SOSAI WAJEN KAWO MUKU KAYAN GYARA NA MATA*
*AƘWAI SABULAN GYARAN JIKI SUNE KAMAR*
*MULATO SOAP*
*FACE CREAM*
*FACE SOAP*
*MULATO WHITENING LOTION*
*HAIR GROW OIL*
*HAIR GROW CREAM*
*KAR-KAR OIL*
*MINT LEAVE OIL*
*ANTI PIMPUS SOAP*
*AƘWAI SABULUN NANKARWA*
sannan ina harkar👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
*ABIN BUKI*
*ABINCIN OFFICE*
*SNACK*
KAMARSU👇🏻👇🏻
*WAINAR MASA*
*SINASIR*
*MEAT PIE*
*CINCIN ƊAN LAUSHI*
*CUP CAKE*
DA DAI SAURANSU
AMMA ARAB GIDAN GYARAN AURE.😄👏🏻
*_ZULFAH 2_*
________cike da mamaki na ƙarasa,jikina duk a saɓile saboda ganin wanda na gani ɗin shima kallona yake sosai yana sanye cikin kakinsa waɗanda sukayi bala'in yi mishi kyau,ya sanya glass mai ruwan zaiba sai walƙiya yake kana ganin kanka aciki,asalin kyaunda na Fulani ya ƙara bayyana sosai na shagala ina kallonsa,shima yana kallona sosai kamar yadda nima nake kallonsa.
jikina yana rawa na fara gaishe sa,saboda yadda ƙwarjininsa ya cika wajen a hankali ya amsa da ɗan murmushi akan kyakkyawar fuskarsa ya ce"Zulfah dama munzo ne mu tafi dake".gabana ne yayi wani irin mummunan bugawa,idanuwa na suka kawo ruwa suka fara zuba shar shar,cefanen dana yo wa mahaifiyata ya faɗi ƙasa sai kifi da kuma maltina,saboda yau na samu kuɗi jimillar kuɗinda na samu har dubu ɗaya da ɗari baƙwai,saboda haka jikina yana rawa na siyowa mahaifiyata kifi da maltina don tana masifat cin daɗi,kuma ayadda na fuskanta ada can ba ƴar ƙananan mutane bace,kuma tana da wani tambari a hannunta kamar irin nawa,sai dai ita Sudan aka saka ajiki maimakon nawa da aka saka sunana.
muryata tana rawa na ce"don Allah yallaɓai kayi haƙuri ku barni haka,wallahi ni iya gaskiyata na faɗa muku,kuma wallahi......."da sauri ya katseni yana ɗan shafa gemunsa alamar shi abin ma bai damesa ba ya ce"ni dai nace ki tashi mu tafi,kuma kada ki sake ki shiga gidanku kina jina"?.da sauri na ɗaga kai na don ban san me zai biyo baya ba.
amman abinda yafi komai bani mamaki,bai wuce yadda ya kafe akan sai na shiga gaban mota ba,na zaro ido zanyi kafiya kawai sai naji anyi sama dani,ba'a direni a ko ina ba sai acikin gaban motar nayi tsuru da idanuwa na tamkar na mujiya na kama hawaye na rashin gata,idan da ina da gata da ba'a yimin abinda akayimin ba kawai daga ganina sai ace dama ni ake jira?saboda an maisheni wata banza mara galihu?.
tattausan hannunsa naji akan pink lips ɗina,nayi saurin waro idanuwa ina kallonsa sai kuwa ya ce"shiiiiiiiiiit kada in ƙara jin bakinki".tsoro da ƙwarjininsa suka sanya ni yin shiru har muka fara tafiya,muna cikin tafiyar sai naga sauran ƴan sandan motarsu ta canja hanya,da sauri na waiwayo na kallesa idanuwa na suna zubarda ruwa cikin tsoro da fargaba na ce"yallaɓai ya naga haka kum .........."? bai ce min ƙala ba ya cigaba da tuƙinsa cikin ƙwarewa yana kallona sosai, wani babban gida nagani agabana sai naji wani irin faɗuwar gaba tuni na fara salati,na juya naga ya haɗe fuskarsa tamau babu damar yi masa musu,gabana sai lugude yake shikkenan yau zai siyar dani?shikkenan yau zan rabu da Ummana,bansan lokacin da na fashe da wani irin kuka ba ko kallona baiyi ba har naji ya kashe motar har lokacin kuma ban daina kukan ba,tsayar da motar da yayi yasa kai na ya faɗo gaban motar na fashe da kuka ina ce wa"wayyo Allah na Umma shikkenan rayuwata ta ƙare".
Da sauri ya ɗagoni sai gashi mun haɗa idanu dashi yadda kasan daman saboda hakan ya ɗagoni,tuni muka fara kallon ƙuda dashi yayi min ƙuri nima na mayar masa da kallonsa,lallai yabo da godiya sun tabbata ga Allah mahalicci,lallai Allah ya iya halittar mutane masu baiwa da dama kyau da tsaruwa kam M/D yana dashi,duk da jikin da yake dashi bai hanashi kyau ba yana da jiki amman ba sosai ba amman za a iya sakashi acikin masu ƙiba,gashi da tsayi sosai ga kuma jiki maɓallin rigarsa na gaba ya cire,yayinda kallona ya kai wajen da sauri na runtse idona saboda tsoro,ni ban taɓa ganin gashi ajiki haka ba?sai kace gashin kai?na rufe idanuwa na gam gam.
tsinto maganar nayi yana cewa"gawayi kike shafawa a fuskarki ko"?.ya faɗi maganar yana shafa fuskata da ɗan yatsansa,wani irin tsalle nayi na wuntsila gefe sannan na ƙara rufe fuskata,bai ƙara cewa komai ba ya fito daga motar ya rufe sannan yazo ya buɗemin inda nake,da sauri naja na tsaya wai ni bazan fito ba ai kuwa sai naga kawai ya ɗaukeni tamkar ƴar tsana yayi gaba dani,ina wutsil wutsil ina kuka amman bai sanya ya ajjeni ba bai kuma ji ƙyanƙyamin jikina ba,don ma ina wanka amma sai inyi sati banyi wanka ba,saboda ba kullum zan samu sabulun ba.
¢¢¢¢¢¢
*_ZULFAH 1_*
_____ina sane naƙi buɗe ɗakina don bana son wata damuwa sam,don abinda na yiwa Bilal ɗazu nasan zasu zo su nemi damu na,saboda haka nayi zamana a ɗakina ko abinci ban fito ci ba,itama Hjy Innah bata neme ni ranar ba don ina jiyo muryarta tana cewa,ƴar banza kyaji dashi ciwon ajali a ƙafa bazan nemeki ba,tunda ke baki da kunya da sanin na gaba dake.tana ta maganganunta nayi mata banza don tsohuwar ta fara damuna,saboda haka na fara haɗa tafiya a ɓoye don na gaji da Nigeria baki ɗaya,ga zafi ga kuma damun mutum don rayuwar America dana yi ban san wani zafi ba,idan ma zaka fita dole ne sai ka sanya siweta.
a hankali na gama shirina tsaf cikin wasu riga da wando,wandon irin farado ɗinnane rigar kuma irin me buɗewar nan ce,na sanya belt ɗin kayan,wandon golden yellow rigar kuma ja na sanya hular rigar me fesin kaf,itama kalar ja na ɗaure gashina ya zubo har gadon baya na sanya janbaki ba tare dana sa hoda ko ɗaya ba,dama ni hoda bata cikin hubby na saboda haka kaf kayan ƙwalliyata babi hoda sai janbaki da sauran kayan ƙwalliya.
Wow faɗin yadda nayi kyau ma ɓata bakine,na ambula fresh one turare mai matuƙar ƙamshi da sanyaya zuciya,troly ɗina na ja ce amman ita ta turu sosai na sanya cingum a bakina ina takawa ɗai ɗai,ga uban high hill ɗin dana saka shima me ruwan ja da igigoginsa masu mugun tsayi.
ina fitowa Hajiya Innah ta tsuramin idanuwa tamkar zata ɗaukeni,na juyar da fuskata inajan troly ɗina ba tare dana ce mata komai ba.
da sauri ta tashi tana ce wa"ƴar Innah ina zakije kuma harda wannan uwar aƙwatin?".bance mata komai ba na cigaba da tafiyata,da gudu ta biyoni tana yimin magana amman na share ta don banga wanda zai hanani tafiya ba,don na gaji da rayuwar tenshon da surutu,yawan magana baya cikin halina amman daga dawowata sun koya min magana, saboda haka yanzu na gaji gwara inje inda kowa yake da haƙƙinsa ake bawa kowa abinda yake so,daman gidana ina da me aiki wata baturiya me suna illelio mata mai kirku tun ina ƙarama muke tare da ita,duk zuwa tare muke zuwa da ita amman wannan karon itama taje garinsu dake America,saboda haka na taho ni kaɗai.
Hajiya Innah tuni ta fara hawaye tana ce wa"wallahi duk inda zakije sai dai mu tafi tare,don wallahi bazan zauna anan ana yimin kallon hadarin kaji ba,shegun matan ƴaƴa sunci sun ƙoshi kowacce tayi naman wuya sai kallon ga wuri ga waina suke min,saboda haka alƙur'an tare zamu tafi".sai ta cigaba da kukanta tamkar jiniyar ƴan sanda wi'wi'wiiiiiiiiii.
dole naja na tsaya saboda ta riƙemin bayan riga na juyo cikin jin haushin salon son hanani tafiya da take so tayi na ce"haba Innah ki barni na tafi mana?so kike in zauna wannan me kalar mayun yana taɓamin jiki?to ko zaman U.S danayi babu ɗan iskan daya taɓamin jiki,saboda na san me nake yi saboda haka na barki dashi ke ya dinga taɓa jikinki yana jin abinda yake so ɗin".
da sauri taja baya tana cewa"Oh ni wannan ƴa ni kuwa jiki busai busai me za'a taɓa aji?haba Zulfah ni yanzu ni kike zagi"?.ɗan murmushi nayi wanda nayi ƙwana biyu banyi ba na ce"to naji ni dai na tafi ko dady bai san na tafi ba,idan ya dawo kya bashi sallahu".
Ina faɗar hakan nayi parking space,tun kafin in ƙaraso sabon direba na yazo ya tsaya gabana,tare da wangalemin murfin motar na shiga ya tura kayana cikin but ɗin motar,ina hango Hajiya Inna na harar sabon direban nawa tana cewa"munafuki algungumi ashe kasan za tayi tafiya ko?to wallahi ba gilin gilin ba tayi mai,zakazo ka sameni har uwar ɗakin taka Allah yasa kada ta samu jirgin dolenta ai ta dawo,tunda filin jirgin bana kakanki Alfa's bane".
Ni dai na toshe kunnuwana da earpiece don bana son hayaniya,sai da mukayi nisa sannan na fara jin wata irin kewar Hajiya Innah na saki ɗan murmushi lokacin da na tuno da faɗanda tayi tayi akan tafiyar da zanyi wai har da cewa Allah yasa kada in samu jirgi............
¢¢¢¢¢¢¢
_BILAL_
Bilal ya kalli mahaifiyarsa jin wani furuci da tayi ya ce",haba Umma ni aganina tunda inason Zulfah kamata yayi ki bani goyon baya tunda ƴar uwata ce,amman bai kamata ki tubure akan bazan aureta ba babu wanda yasan gawar fari,kuma anan gaba Zulfah zata zama surukark.....................✍🏻
"kai!
Kada ka ƙara kiran wannan matsiyaciyar yarinyar da sunan surukata,wannan yarinyar daba ƴar sunnah ba........"tun kafin ta ƙarasa Bilal ya juyo da mugun tsoro cikin firgici fa kuma tsoro........✍🏻
_MRS GREEN CE_
domin chart dani kai tsaye ***
*_GAWURTATTUN UKU🔥🔥🔥2023 SEPTRMBER._*
_1-ƘWAI A BAKA...!!!🥚_
👇🏽
*(Ummu Affan)*
_2-NA FAƊO DAGA BENE NA ZARCE RIJIYA...!!!🫗_
👇🏽
*Badi'at Mrs bukhari*
_ZULFAH_🍏
👇🏽
*Ummu maher(mrs green)*
_Littafi ɗaya;400_
_Littafi biyu;800_
_Littafi uku;1000_
Ga masu son tura kuɗinsu ta acc sai su tura a wannan acc ɗin👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank
Sai ka tura da shaidar biyanka ta wannan no ɗin👇🏽👇🏽👇🏽
***
Masu tura kati kuma sai su turo screenshot na katinsu Mtn ta wannan no ɗin👇🏽
***
Ƴan Niger zasu turo katin Moov ko Airtel ta wannan number.
***
*GA MASU SON A TALLATA MUSU HAJARSU A DUKKANIN SHAFINMU na facebook,whattpad,telegram,youtube,group da status,zamu tallata muku ne akan farashi me rahusa*
10K ne kacal.
Sai ku tuntuɓe a numbobinmu kamar haka👇🏽👇🏽👇🏽
***
***
***
Domin tallata muku hajojinku a cikin littafinmu na sati ɗaya ya kama👇🏽👇🏽👇🏽
2K
sati biyu
3k
idan kuma kanason har mu gama book muna ɗora maka ya kama
10k kacal.
Mun gode da zaɓar gawurtattu uku ako da yaushe.🙏🏼