page 18
_Typing🤳🏼_
*_....🌪️ZULFAH🌪️...._*
_UMMU MAHER_
*@MRS GREEN🍏*
_GAWURTATTU 3_
Book 2 page 18
*_follow Zulfah on Arewa books_*
https://arewabooks.com/book?id=64ff0277d73b80a18ea59540
*_VIA GROUP ZULFAH FANS_*
***
gSsodCRZGcEjERSEsBY
_*AMMA ARAB!AMMA ARAB!
!AMMA ARAB!!!*_
_kai daga jin sunan kasan sunan ya
amsa sunansa,AMMA ARAB ta kawo
muku wani supplement na gyaran
jiki mai sanya daɗi da ƙamshi AMMA
ARAB gidan ƙamshi_
*MUSUK*
*MADARAR TURARE*
*KAJIJI*
*ROT*
*SANDAL*
*HUMFUR*
*SANDAL FLASK*
*SANDAL WUD*
*AALUT*
*GAF-GAF*
*JANNAMI*
*ƘWALAKCA*
*MAHAHABSUFYAN*
*WANNAN SHINE GRP ƊINA
NA WHATSAPP,KI ANTAYO SABODA KADA AYI BABU KE*
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
***
HnDN6KUJYnkBDT7S
*ADDRESS👇🏻👇🏻👇🏻*
Zaria road kwankwasiyya sabon gari ɗangwauro house number 224
Kano
OR CALL MY CONTACT
***
*AƘWAI WANI SUPPLEMENTA NA GYARAN JIKI DA TAZO MUKU DASHI KE DA KANKI IDAN KIKA YI ZAKISAN EH LALLAI ZAKI GIGITA ME GIDA,KINSAN MAZA SAI DA ƘAMSHI DUK MATAR DA BATA SAYI WANNAN SUPPLEMENT ƊIN BA TO AN BARTA A BAYA*
*AƘWAI BABBAN MAGANI NA INFECTION,WANDA ZAI DAWO MIKI DA MARTABARKI NA ƳA MACE,ZAI CIKO MIKI DA NI'IMARKI KI KOMA ƳAR GATAN MEGIDA*
*AƘWAI BABBAR KAMBASA,TA TURARA KAYA HAJIYA KI BUƊE BAKIN ALJIHU KI JIƘO DA ƘAMSHI,KINA ZAMA AN SAN KIN ISA MACE HAJIYA DON AMMA ARAB TA SHARA SOSAI WAJEN KAWO MUKU KAYAN GYARA NA MATA*
*AƘWAI SABULAN GYARAN JIKI SUNE KAMAR*
*MULATO SOAP*
*FACE CREAM*
*FACE SOAP*
*MULATO WHITENING LOTION*
*HAIR GROW OIL*
*HAIR GROW CREAM*
*KAR-KAR OIL*
*MINT LEAVE OIL*
*ANTI PIMPUS SOAP*
*AƘWAI SABULUN NANKARWA*
sannan ina harkar👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
*ABIN BUKI*
*ABINCIN OFFICE*
*SNACK*
KAMARSU👇🏻👇🏻
*WAINAR MASA*
*SINASIR*
*MEAT PIE*
*CINCIN ƊAN LAUSHI*
*CUP CAKE*
DA DAI SAURANSU.
AMMA ARAB GIDAN GYARAN AURE😄👏🏻
_ZULFAH 1_
______A hankali ya karɓi wayar yana ƙaremin kallo sannan ya ce"Zulfah kin manta damu ko?number ɗinki ma idan na kira bata shiga?,ashe ni ne bakison yin waya dani?".
banza nayi masa kuma ban kashe wayar ba,haushi kawai yake bani nayi nadamar kiran Hjy Innah don da ban kira taba da ban kalli fuskarsa ba,ganin ya buɗe baki zai ƙara magana na kashe wayata ba tare dana ƙara saurararsa ba.
_BAYAN ƘWANA 2_
da sauri na tashi daga barcin daya ƙwasheni lokaci ɗaya,wani mafarki nayi da mahaifiyata tana gargaɗeni dana koma Nigeria hankalina ya tashi sosai,aranar na fara shiri mukayi sallama da illelia sai kuka takeyi wai yanzu bana son zaman nan nafison zaman Nigeria.
*****
Hjy Innah tana ganina ta fara kuka tana ce wa"Allah sarki ashe mahaifinki ya shaida miki maganar bukin naki da Bilalu ko?". da sauri na kalleta ina ɓata fuska tare da hawaye na ce"wai ni me yasa ina dawowa Nigeria nake fara haɗuwa da musibu kala kala ne?daga wannan sai wannan?ni nace inason auren Bilal ɗinne?to ni wallahi bana sonsa kuma idan aka auraminshi duk abinda ya faru ku kuka da kanku".ina faɗar hakan na wuce ɗakina kai tsaye,ina shiga na faɗa kan gado na fashe da wani irin kuka mai mugun ɗaci,da na sanin dawowata nake saboda daman nasan hakan zai iya faruwa dani.
Bilal yayi murmushi wanda yafi kuka ciwo,don duk abinda na faɗa yaji ya zauna yana kallon Hjy Innah wacce ke kallonsa cikin idanun tausayi,ta riƙe hannunsa sannan ta ce"zauna jikana inason kayi haƙuri,Zulfah yarinya ce ƙarama saboda haka bata ma san wata soyayya ba,kai ne dai zaka koya mata saboda haka a hankali zaka dinga binta wannan ranar auren naku da aka saka baza a canja ta ba tana nan akan wata biyu masu zuwa insha Allah".
sai alokacin yaji zuciyarsa ta ɗan sassauta bugun da take masa,ya kalli ɗakin da Zulfah take ƙofar a buɗe yana son shiga don ya rarrasheta amman kuma yana tsoron abinda zai iya biyo baya,don haka ya koma ya zauna sai kuwa yaji Hjy innah ta ce"bita mana ko tsoronta kake ji ne?kar dai fa tarihi ya maimaita kansa don hakama ubanta ya yi da gyatumarta,yayi ta tsoronta kamar uwarsa don haka kada ka zama sako tumaki ɓallo jakai".
ɗan murmushi yayi,don yana da tarihin mahaifiyar Xulfah tsaf don mahaifiyarsa ta karanta masa komai nata,har da cewa ita ba zata bari ɗanta ya auri ƴar gidan Rabi'atu ba,saboda tasanta da iya salo na yaudarar miji shiyasa alokacin zamaninta tayi baƙin jini sosai.
ya ɗan sosai kansa sannan ya tashi jikinsa duk asanyaye don yana tsoron abinda zai biyo baya,Hajiya Innah ta ce"haba haba fisabilillahi wannan wani irin abune?namiji da tsoron mace?ni nasan wallahi wata'ala idan akayi auren nan shikkenan sai abinda Zulfah ta kimtsa maka,kamar yadda gyatumarta ke yiwa gyatuminta".
Murmushi yayi sannan ya ƙarasa ɗakin da murmushinsa mai ƙawata kyakkyawae face ɗinsa.
motsi naji a bayana da sauri na waiga da idanuwa na waɗanda suka kaɗa sukayi jawur.
Zan fara fidda yayyafin masifa kawai sai naga ya hayo gadon ya rufemin bakina gam,sannan ya fara magana yana kallon ƙwayar idona wacce take shining tamkar na shafa mai,abindq ke ƙara sanyasa wani yanayi kenan indai har yayi tozali da Zulfah,shiyasa bai cika son kallon Zulfah ba abinda ke sa da yawan maza basa kallon idonta saboda ƙwarjininsu.
ya lumshe ido ya buɗe ya ƙara jaddada godiyarsa ga ubangiji sannan ya ce"Zulfah bana son kukanki don Allah ki daina,ya zanyi ne?Allah ya jarabceni da sonki duk da nasan bakya sona amman ki rufamin asiri ki aureni ko zuciyata zata sararamin,wallahi Zulfah idan har na rasaki tabbas na rasa rayuwata domin kuwa nasan bazan rayu babu ke ba."
da mugun sauri na cigesa don jin zuciyata nake tamkar zata fashe,yaji zafin cizon sosai son har sai da yayi ƴar ƙara don ba ƙaramin cizo na garƙama masa ba,na tashi daga kan gadon ina kuka na nunasa da yatsa na ce"Bilal kake ko wa?ka buɗe kunnenka da kyau ka jini?indai har kaga na aureka to ni Zulfah bana numfashi domin kuwa ban dace da auren mutum mara zuciya irinka ba,da za ka yiwa kanka adalci da ka koma inda ake sonka amman ba ni Zulfah b............."
Wani irin zafaffan mari naji an saukar min a dukkanin kuncina guda biyu,da sauri na juya don ganin waye da wannan aikin?fuskar da ba'a taɓa yi mata ko da marin wasa ba?sai gashi yau an yimin marin daya nemi gigita ɗan ƙaramin tunani na?.
Wacece wannan wacce ta mari Zulfah?????.
da sauri na juyo don ganin wacce ta mare ni,sai wa?Hajiya Innah nagani tsaye akaina tana wuci ta nuna ni da yatsanta cikin fushi ta fara magana.
"wacece ke har haka?da kikq ɗauki kanki da zafi?don kinga yana sonki sai ki nemi ki halakasa?ke wacce irin mara hankalice?kinsan halinda ya faɗa sabadin tafiyarki?kinsan ciwon zuciyane ya kamasa saboda rashin ganinki?abinda ya tunzura zuciyata kenan na umarci ƴaƴa ƴan albarka akan dole asa ranar aurenku,ayi kowa ma ya huta in banda haka me zaisa asa ranarku ahaka?duk haƙurin da yake dake bazaki ƙaunace shi yadda ya ƙaunace ki ba?idan wanine kikaga yana wa Bilalu haka ke ba mai hanawa ba ce?ashe ke ce babbar mai buga ganga idan kika ga ana neman ran ɗan uwanki?to ki buɗe kunnuwanki ki jini da kyau,aurenku babu fashi sai dai akai gawarki kamar yadda kika ce".
Tana faɗar hakan ta fita da saurin gaske,na bita da ido kawai don nayi suman tsaye don ban taɓa ganin ran Hjy Innah ya ɓaci har haka ba?yanzu akan Bilal ne aka mare ta?marin da har ta koma ga ubangijin ta ba zata manta hakan ba?lallai kuwa ya zamar mata dolen tilas ta koyawa Bilal hankali,kuma ya zamar mata dole ta nemi mafita yanzu ba sai anjima ba zata bi dad ɗinta har office ɗinsa don bazata yarda a mayar da ignorance ba.
da sauri ya nufoni yana lallasheni nayi saurin ɗaga masa hannu,cikin kuka ra hargowa na fara magana cikin zallar fushi"me zaka ce min?har akanka aka taɓamin lafiya?saboda kai ko?to ka rubuta ka ajje sai na rama marina akanka alokacin da baka taɓa tunani ba,don ayanzu idan har nayi maka bazanji sanyin zuciyata ba".
Ina faɗar hakan na fito da saurin gaske ina kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.Hajiya Innah ta bini da kallo don tana zaune cikin ɓacin rai,bata ce dani komai ba ta bini da ido kawai tausayina fal cikin zuciyarta,don babu yadda za tayi ne shiyasa har ta yiwa jikarta mafi soyuwa aranta wannan hukuncin,ya zamar mata dole yin hakan ne don tasan halina da taurin kan tsiya,shi kuma gogan ba zai iya takamin burki ba saboda yana tsorona sai dai ya bini sasaka ayadda naso.
ko kallon gabana bana yi,burina kawai in isa inda nake son isa ɗin sannan na sanya azuciyata yau bazan ƙwana agidan ba,idan ma don na dawo gidan ne aka samu damar yimin abinda aka aikatamin ɗin to bazan dawo ba,don ayanzu haka gidaje na acikin garin Abuja sunfi guda biyar kuma duk mallakinane.
buɗe mota kawai nayi aka fara tuƙani,zuciyata na yimin wani irin suya tamkar zata faso ƙirjina ta fito aranar nayi nadamar yin hakan tafi cikin ƙwando.
Bilal yana tsaye na hau mota,amman ban ma san yana wajen ba don biyo ni yayi har compound ɗin gidanmu.
tafiya yake amman bai san inda yake sanya ƙafarsa ba,hankalinsa da nutsuwarsa suna ga Zulfah ne,shi dai da zai iya yaƙi da zuciyarsa da ya haƙura da son Zulfah,amman babu yadda zaiyi auren Zulfah ya zamar masa tilas don shi idan har ya haƙura zuciyarsa ba zata taɓa yi masa adalci wajen barin Zulfah ba.
bai san ya kawo kansa babban falon ɓangarensu ba,sai da ya jiyo muryar mahaifiyarsa sama sama,don kaf gidan babu wanda yasan Zulfah ta dawo daga shi sai masu gadi da kuma hjy innah.
"Bilal me yake damunka?ba dai ciwonka ne ya tashi ba?don Allah ka rufamin asiri ka tashi kada ka mutu Bilal kai kaɗaine ɗana namiji mafi soyuwa araina".kuka take sosai tana faɗar hakan,Murashsha ma na ɓangaren lokacin don itama tunda taji an saka ranar Zulfah da Bilal ɗinta,ta fara ciwo sosai don har sai da hawan jini itama ya kamata,son maso wani kenan ƙoshin wahala.ita tana son Bilal shi kuma baya sonta Xulfah yake so don haka ta tabbatarwa kanta tunda har Zulfah yakeso ta tabbarwa kanta ba zai taɓa sonta ba don Zulfah ta yi mata rata sosai,don Zulfah kallabi tsakanin rawuna ce.
da sauri su Murashsha da ƙannensa sukayo kansa suna kuka,sai dao da ƙer aka samu ya buɗe idonsa sai me kuma?sunan Zulfah kawai yake kira.
"Zulfah"!
"Zulfah"!!
don Allah kada ki ce bazaki iya aure na ba,indai har kika ƙini to tabbas ina cikin matsalar rayuwa mutuwa zanyiiiiiiiiiii."
Kalmar ƙarshe daya faɗa kenan sai suka jishi ɗibbbbbbb✍🏻😫😭😭😭😭😭😭😭😭
_INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN_
Anan zan tsaya fans,sai gobe kuma ko an jima don sauran suna kan computer ayi haƙuri na yau kaɗanne...........
*MRA GREEN CE*
***