001 Katse ta Mama ta sake yi ta hana Khadija magana, wurga mata wata uwar hararar tsana tayi sannan tace. "Wallahi Khadija na tsaneki bani sonki a yanzun bani kaunar ganinki, ke har wani uzuri zan maki Khadija? Bayan cikin shegene a jikinkinki duk tarbiyar da na baki, abu daya nike
*A SANADIN SOYAYYAR MINTI*
*REPOST*
Na
*Jameey yar'mutan kankia ce❣️*
***
*Gajeran labari*
*RANAKUN POSTING FRIDAY, SATURDAY AND SUNDAY*
001
Wata macece wanda bata wuce shekara 60 ba zaune a madaidacin parlourn gidansu ba abunda take sai aikin kuka dan abun duniya ya taro yayi mata yawa, wata yarinya ce ta fito daga cikin wani daki ta zauna kasa kusa da kafar matar itama kukan take, dan ta rasa mai zata ce ma mahaifiyar tata kallonta tayi sannan tace."Mama Dan Allah kiyi hakuri ki yafeman wallahi ba zan sake ba, nayi maki wannan alkwarin, wallahi sherin she... Tas! Mama ta wanke ta da mari tana nuna ta da yatsa cikin tsananin fushi ta fara cewa. "Allah ya tsine maki albarka insha Allah ba zaki gama da duniya lafiya ba Khadija, tunda har kika sa na zubda hawaye saboda dake kika jaman zagi a cikin unguwa, Allah ya i... Da sauri Khadija ta rike kafafun Mamanta tana girgiza mata kai tana hawaye masu ciwo dan kukan ma ya gagareta dan tana cikin tashin hankali ba kadan ba, yanda Mamanta take tsine mata tana mata fatan masifa ta fada mata bayan kuma itace uwa a gareta mahaifiya cikin tashin hankali tace. "Mama dan Allah ki barni haka karda abun yayi man yawa kin tsine man sannan kuma zakiyi man Allah ya isa? nasan ko baki ce man Allah ya isa ba ni tawa rayuwar tazo karshe tunda har ta dalilina kika zubda hawaye,dan Allah Mama ki yafeman wallahi ba zan sake ba, kiyiman Uzuri Ma... Katse ta Mama ta sake yi ta hana Khadija magana, wurga mata wata uwar hararar tsana tayi sannan tace. "Wallahi Khadija na tsaneki bani sonki a yanzun bani kaunar ganinki, ke har wani uzuri zan maki Khadija? Bayan cikin shegene a jikinkinki duk tarbiyar da na baki, abu daya nike so ki sani bani bake har abada, karki sake kirana da sunan Mamarki na yafeki daga cikin ƴa'ƴana, ki kirani da suna HAFSAT dan yanzun ni ba mahaifiyar ki bace, Allah ya tseni maki albarka."
Allah Sarki kuka na sake rushewa dashi dan duniya tayi man kunci ban san ya zanyi da rayuwa ta ba, sannan kuma na tsorata da yanayin da mahaifiya ta take ciki, tashi nayi na koma dakina na cigaba da kukana, wanda tunda jiya mukaje asibiti likita ya sheda mana ina ɗauke da karamin ciki dan wata ɗaya nake aikin kuka, ba kukan komai nike ba Ila kukan dana sani da biye ma son zuciyata da nayi, yunwa naji ta taso man Kuma bani sha'awar cin komai sai dan'wanke da manja da yaji wanda yaji tabarnuwa da kayan kamshi na yaji, tashi nayi na fito parlour tadda Mama nayi zaune tana share hawaye matsawa nayi kusa da ita nace. "Mama yunwa nike ji Kuma dan'wake nike son nace." Ji nayi Mama ta wanke ni da mari cikin zafin rai tace. "Wallahi baki da kwanon abinci a gidan nan, kije wajen wanda yayi maki cikin ki gaya mashi abunda kike son ci, sannan Kuma karki sake kirana da sunan mama na gaya maki tsinanniya lalataiciya dake."
Kasa motsi nayi, ba abunda nike sai hawaye dan ni yanzun na kasa kuka ma, ji nike daman nike kukan da Mama take da naji saukin abunda nike ji a raina, hakuri na sake bata sannan na tashi na koma dakina inajin yanda yunwa take azabzabata na rasa yanda zanyi gashi bani son cin komai idan ba dan'wake ba, haka na wuni a daki a ranar ban sake fitowa waje ba, balle har Mama ta ganni ta sake tsineman, tun karfe 1 nike zaune inajin yunwa har hudun marece yayi, tunowa nayi inada wasu kudi da Nura ya bani tunin daɗewa,cikin sauri na tashi na dauko kudin na zura hijab dina dan zuwa nema ma ciki abunda zan sama shi, ina fitowa na tadda Mama da Yaya Aisha sun hada kai suna kuka, Yaya Aisha Yayata ce wanda muke uwa daya uba daya, da yake nice Auta a gidanmu yanda na gansu ne hankali ya tashi dan nasan kukan da suke ba wuce na cikin nan ne, tsaye nayi ina kallonsu nima ina zubda hawaye, kallona sukayi lokaci guda suna man wani irin kallo wannan kallo ba komai bane illa kallon tsana dan Ina ganin tsantsan tsanata a cikin kwayar idonsu, ta sowa Yaya Aisha tayi ta nufoni gadan gadan ni Kuma ina ja da baya haka muka kamayi har muka kai karshen bango, kulle idona nayi dan nasan ba dadi zatayi man ba, kamani tayi ta fara wanka man mari tana zagina, nan suka rufeni da bugu ita da Mama, tun ina yi basu hakuri har nazo da na kasa sai dai ido, tun ina gane idan nike har ta kai da bani gane mai akeyi, haka suka kama buguna suka barni kwance sheɗashaɗa cikin jini rai hannu ga Allah, ba su damu da wani hali nike ciki ba, tun la'asar sukayi man haka suka yashar dani suka cigaba da hidimar gabansu, Yayane ya shigo Jamilu shine babba a gidanmu kuma yana da matarshi,yana shigowa ya taddani cikin wanann halin kallon Mama yayi sannan yace."Mama mai yasamu Auta na ganta kwance cikin jini kuma hankalinku kwance harda ke Aisha.?" Cikin fushi yayi tambayar dan yasan abunda ke faruwa dani likitin da yaga mana ina da ciki shi ya kirashi waya ya gaya mashi halin da ake ciki da yake abokinshi ne, kallon shi Mama tayi sannan tace. "Jamilu Khadija cikin shege tayi gaya maka ne banyi ba, dan na fiddata daga cikin jerin ƴa'ƴana, baku ba Khadija kuma kabarta ta mutu, idan yaso nima akasheni ba damuwa ta bane."
Kallonta yayi ya fara cewa. "Haba Mama ya kamata ki yarda da kaddara mai kyau da marar kyau shine cikon imani, kisani wannan cikin yana cikin zanar kaddarar Auta dole sai tayi wannan cikin wallahi kaddararta ne, banyi tunanin ganin haka daga gareki ba Mama, kuma ke Ai... Wanke shi Mama tayi da mari tana cewa. "Har ni zaka gaya man kaddara Jamilu, inace nice na haifeka ba kaine ka haifi kanka ba, tun kafin ka zama mutun nasan zanar kaddara, balle kace man wata kaddara wallahi Jamilu badan nakai zuciya nesa ba kaima da na tsine maka wallahi mutun banza, ka fita ido na kulle daman ance da ka haifi namiji kwara mace dan ita mace itace tasan kishin uwarta daman ance ciwon ƴ'a mace na ƴ'a mace ne."Tunda Mama ta mari Yaya Jamilu bai sake cewa komai ba, sai ma zuwa da yayi zai dauke ni ya kaine asibiti domin ceto raina cikin fushi Mama tace."Wallahi mudun ka kuskura ka taɓa Khadija to sai na tsine maka albarka, mutumin banza wanda baya kishin uwarshi."
Cikin kuka Yaya Jamilu ya matsa kusa da Mama yana cewa. "Dan Allah Mama ki man rai kar ki biye ma zuciya kizo daga baya kina da na sani karki manta Autarki ce fa kwance cikin wannan halin, kuma hannunka baya ruɓewa ka yanke ka yada."Shiru Mama tayi tana share hawaye, tsaki tayi ta bar mashi parlourn dan mudun ta tsaya cikin parlourn tsab zata tsine ma Jamilu, haka itama Aisha tabi bayan Mama, kallona Yaya Jamilu yayi sannan ya ida isowa wajena ya daukeni cikin sauri ya fita dani ya sani cikin motor dinshi sannan muka dauki hanyar asibiti, sosai yake ba motarshi wuta ikon Allah ne kawai ya kaimu dan gudu yake ba na wasa ba, muna zuwa ya ruga ya kira nurse suka turoni bisa keken mararsa lafiya, haka aka turani rai hannu ga Allah, direct emergency room aka wuce dani, tsayawa Yaya Jamilu yayi baki emergency din yanata safa da marwa. Niko tunda aka shiga dani likito suka dufuha kaina dan ceto raina da abunda ke cikin cikina dan jini nike zubdawa bana wasa ba, sun kusa awa uku suna abu guda sannan suka samu suka tsada jinin, allurai sukayi man sannan suka kaine dakin hutu, fitowa likitan yayi yace ma Yaya Jamilu. "Alhaji Jamilu ina son ganinka a office dina." cikin damuwa Yaya Jamilu yace mashi. "Allah yayi mata cikawa ko.!?" Kallon shi kawai likita yayi sannan yace."komai dai mainene meet me in my office." gwaɗa mashi kai kawai Yaya yayi sannan suka tafi office dinshi, duba da yanayin da yake ciki yasa likita ya bashi ruwa mai sanyi yasha sannan ya fara magana yana cewa. "Alhaji sai dai ayi hakuri, dan muso mu ceto cikin da ke jikinta, amman Allah ya kaddara sai ya zube sakamon faduwar datayi har cikin ya bugu, sannan magana ta biyu sai anyi mata wankin ciki kuma mahaifarta bata kwari bai zama dole ta sake daukar wani cikin ba inba wani ikon Allah ba, hakuri zakayi haka Allah ya kaddara sannan zaka sa hannu domin zuwa gobe idan Allah ya kaimu ayi mata wanke cikin idan Allah ya kaimu."
Cikin tashin hankali Yaya yace. "Innalillahi wa'inna'alaihijirun, abokina kai dai kasan komai Auta bata taba aure ba, kaddara ce ta hau kanta wanda ba mai tsalake ma kaddara idan Allah ya kawota, ba wani abu da za'ayi mata wanda ba sai anyi mata wannan wankin cikin ba, dan da matsala ace za'ayi ma budurwa wanki ciki ka duba dan Allah."Kallon shi Doctor yayi cikin tausayi dan yasan abokinshi yana cikin damuwa balle yasan yanda suke son autar tasu, cewa yayi. "Wallahi Abokina babu wata hanya idan ba wannan ba, da ace anyi hakuri an raini cikin ta haifeshi da lafiya lau dan kaddara ce kuwa, wannan yana cikin kudin kaddarar Khadija, amman garin ya hakan ta faru har Mama ta bari ta faɗi har haka.?" Cikin takaici da bakin ciki Yaya Jamilu yace. "Ai daman abunda Mama take so kenan, cikin nan ya zube taddawa nayi ita da Aisha sun mata dan'banzar duka, dakyal na samu ta barni na kawota asibiti, amman ka bani lokaci naje na gaya ma Mama halin da ake ciki komai kenan sai ka jini."Kasa cewa komai Dr Dikko yayi, dan baiyi tsanmanin jin haka daga wajen Mama ba cewa yayi. "To shikenan ka dawo lafiya, sannan ka dawo da wanda zata kulla da ita mutun daya, kasan dokar asibitin nan ba'a kwana amman tunda gidane mutun daya zai kwana, fatanmu Allah ya bata lafiya." "Amin ya Allah." cewar Yaya Jamilu sannan ya fita, sai da ya fara biyawa gidanshi ya gayama matarshi halin da ake ciki sannan yace ta shirya ma Dija babbar diyarshi wanda muke sa'a daya da ita yace ta tafi dan kula dani shi kuma zaije gida suyi magana da Mama, haka aka aiko man da Dija shi kuma ya wuce gida wajen Mama.
Koda ya shiga sallama yayi ya tadda parlourn ba kowa wuce wa yayi ciki nan ya tadda yaiyaina mata guda hudu duk sunzo dan an gaya masu abunda ke faruwa, sai hakuri suke ba Mama dan Yaya Aisha tunda taga halin da Yaya Jamilu ya fidda ni tayi da nasanin bugana da tayi, dan kuwa Mama bataji komai ba Yaya Fatima ce tace. "Mama ya kamata ki sama ranki hakuri, mu dauki kaddara wanann abu jarartace ya kama mun zamo masu cikon imani, ke kuma Aisha kin bani mamaki wallahi bai kama ki biye ma Mama ku bigi Auta ba, ya kamata ace kin ba Mama hakuri ba ki tayata wannan mumanan aika aika ba." cikin jimami Yaya Amina tace. "Ni ko wani hali Auta take ciki amman dan Allah Mama kiyi hakuri." ita dai Yaya Khausar bata ce komai ba, dan abun duniya yayi mata yawa so take taji muna wani asibiti domin taga lafiya ta, shigowar Yaya yasa duk suka miƙe suna tambayar shi halin da nike ciki, samun waje yayi ya zauna ya nemo jarumta ya sama kanshi, sannan ya gaya masu halin da ake, ai take suka fara koke koke, dan Yaya Aisha tafi su dan kuka take tana nadamar buguna da tayi abun Mamaki ba abunda Mama tace inba kallonsu da take ba, hawaye ne kawai suke zuba bisa idonta, kallonta Yaya sannna yace. "Mama baki ce komai ba kinji halin da ake ciki Auta tana buƙatar taimako."Tashi Mama tayi zata bar dakin, Yaya Fatima ta riko ta tana cewa. "Mama dan Allah ya kamata ki yafema Khadija, ki anshi kaddarar da tazo mana tana bukatar taimako."Zaunawa Mama tayi sannan tace. "Bintu mai zance? Aje ayi Allah yasa a gama lafiya." Tana gama fadin haka ta tashi ai take Mama ta wanke jiki ta fadi kasa tana amain jini, da gudu sukayi kanta suna kiran suna ta...Daukarta Yaya yayi suka wuce asibiti, gado aka bata sannan aka sama mata drip dan temper dinta ce ta hau sannan Yaya ya cike takadar da za'ayi man aiki, sai wajen mangariba Mama ta farko haka ta matsa aka sallamaita ni kuma aka barni da Dija, duk da nima na farko amman ba sosai nike yin magana ba.
Washe gari da safe Doctor ya shigo ya duba jikina, hana bani komai yayi yace 10am za'a shiga dani ayi man wankin ciki, sanann ya tafi wajen 9 na safe Yaiyauna duk sun zo sun cika asibitin suna duba lafiya, goma nayi aka zo tafiya dani za'a yi man aiki haka na bar yan'uwana suna kuka, dan ban san wani hali nike ba nidai naga suna kuka...Wajen Mama kuwa tunda ta koma gida take kuka, dan tanajin ciwon abunda ya faru dani sosai, dan ma anbar mata Yaya Amina a gida ita ta kama kwantar mata da hankali tana gaya mata maganganu masu dadi wanda zai sa taji sanyi a zuciyar ta..Kallon Yaya Amina tayi sannan tace. "Amina bakisan abunda nike ji ba shiyasa, amman na yafema Khadija Allah yasa ta dauki darasin duniya, daman ita duniya haka take tafi bagaruwa jifa, na yafe mata Allah yasa iyakar kaddararta kenan kinga ta biye ma san zuciya ta lalata rayuwar ta a banza."Haka aka kirasu waya aka gaya mata anshiga dani dan yi man aiki, tayi man fatan fitowa lafiya.
*Akwai Data available masoya akwai ko wane network kuma cikin rahusa 270 1GB ko wane network,banda 9Mobile shi 300 1GB*
*Zaki biya kudin data idan kina bukata ta wannan account din 8160508316 Jamila Bello Abubakar Opay bank,*** for call or whatsapp*
Share please ✓