005
by @milhaart
Wayarsa ce ta fara ringing yayi saurin ɗagwa banji me akace masa ba yace "Okay am coming turo min yaron nan da mota" ya ijiye wayar, ya ɗauki kayan da ya cire ya mayar kasantuwar basu zo da kaya ko ɗaya ba, sai da ya gama sanya kayan yace "Ni zan fita, sai da yamma zan dawo idan kina bukatar wani abu call me"
Kai kawai ta girgiza masa alamun to, har ya kai kofa ya dawo ya rike fuskarta da hannu biyu baiyi wata wata ba ya haɗa bakin shi da nata wuri guda, sun daɗe a haka har na tsawon minti biyu nan da nan ta fara karban saƙon da yake aika mata, ganin zai iya bata lokaci yayi saurin janye bakin sa yana maida Numfashi Idanun nan sun canza kala daga farare zuwa jaa, murmushi yayi "Get ready for me tonight" yayi magan cikin raɗa a saitin kunnen ta ya kashe mata ido yayi ficewar sa.
Zee kuwa ji tayi duk ta rasa sukuninta wani nauyayen ajiyar Zuciya ta sauke tana lashe baki (Su zee diamond an fara hawa network) murmushi tayi ta cigaba da cin abincin ta hankali kwance.
Alhaji yusuf na fita company wanda ya kasance nasa ne, nan ya tarar da ana jiran sa ba mata Lokaci suka fara meeting , basu suka gama ba sai ƙarfe 6 na yamma ko wannen su ya yi tafiyar sa. Gidan sa dake GRA ya nufa gidane na gani na faɗa ya haɗu iya haɗuwa tun daga waje zaka gane cewar kuɗi sunyi kuka anan, gate man ne ya wangale masa tamfasheshen gate ɗin, yara na wasa a play ground suna hango motar sa suka ruga da gudu suna "Daddy oyoyo" shafa kansu ya rika yi ɗayan bayan ɗaya fuskarsa ɗauke da kayataccen murmushi , ɗaukar ƴar karamar cikin su, umarni ya bawa driver akan ya kwaso kayan dake cikin booth , yayi yana gaba suna biye dashi suka shige parlor.
Driver yana dire kayan ya juya ya fita.
Wata mata na hango jikinta sanye yake da leshi mai tsadan gaske an mata ɗin Bubu, fara ce kal kamar jinin jikinta zasu fito hutu da jin daɗi sun ratsa jikinta sosai (Jiki duk madara😂 ) da ɗan saurinta ta karasa inda suke tana mamakin ganin nasa sabida a iya lissafinta next week ya kamata ya zo "Sannu da zuwa Alhaji" murmushi yana mata wani irin kallon da masoyi yake wa masoyiyar sa "Yauwa Wifey na same ku lafiya?"
"Lafiya alhaji ban san zaka zo ba, kayi wanka bari na shiga kitchen na girka maka abu mai ɗan sauki"
"A a barshi kar ki damu abu na zo ɗauka zan koma yanzu sai next week zan dawo , akwai wasu baƙi da mukayi ne daga india so dole sai da ni za'ayi meeting ɗin amma please haɗa min ruwan wanka duk ji nake kamar amin duka"
"Ayya sannu bari na haɗa" ta haura sama inda nan ne ɗakin sa yake.
Zama yayi a tsakiyan yaran yana bawa kowa tsarabar sa , yara ne guda biyar ,3 maza 2 mata, babban zai kai 14yrs,na biyu 12yrs, na uku 8yrs na huɗu 5yrs sai ƙaramar 3yrs don maganar tama bai gama fita sosai ba sai gwaranci take ta masa shi kuma yana ta biye mata, Alhaji Yusuf Tukur Taura kenan irin mutanen nan ne da suke son iyalin su amma kuma hakan bai hanashi neman matan banza ba a waje ba duk da cewar shiɗin matan sa biyu ne, uwar gidan sa na garin gombe yaran ta 4 ,biyu mata biyu maza Biyu,sun manyanta sosai babban ɗansa Shuraim yakai 30yrs wanda ya gama university yanzu haka shi yake kula da business ɗin baban nasa dake Ghana , Sai Hafiz 27yrs shi ke kula da company ɗinsa dake gombe , Sadiya 25yrs Nurse ce a Specialist sai Khadija da take finan year a yanzu wannan kenan.
Cigaba
Ba ta wani juma ba ta fito haɗe da "Faɗin Husby na haɗa" mikewa yayi sai da yazo gab da ita yace "Allah yayi albarka Imra'atussaliha"
Murmushi tayi ta amsa da "Amiin zaujil Bait,Ya labarin su Aunty Lubna da yara?"
"Lafiya lau tace ma na gaida ki" yana kaiwa nan ya shige abinsa bai ma tsaya jin amsar da zata bashi ba, sauri sauri yayi wankan don a lokacin an fara kiraye kirayen sallar magriba, duk hankalin sa yayi kan Zee diamond ɗinsa ya barta ita kaɗai tun safe , sallar ma a ɗaki yayi a gurguje, shiri yayi cikin dakakkiyar shaddar sa fara kal sai sheki yake, ƙasa ya sauko ganin bata nan ya haura ɗakin ta ya tarar da ita zaune akan sallaya da alama ta idar da sallah tana azkar, bai shiga ɗakin ba ya ɗan leka "Ni na tafi" ganin tana kokarin mikewa ya yayi saurin dakatar da ita "A a yi zaman ki hajiya ta,ayi mana addu'a bauchi zan wuce yanzu flight ɗina zai tashi by 8,ina isa zan ƙira ki ina yaran nan suke ban gansu ba?"
"Su Isma'il sun tafi masallaci, Ayra kuma suna ɗakin su"
"Okay sai anjima"
"Allah ubangiji ya tsare hanya, a sauka lafiya."
"Amin ya Allah ƴar albarkana" murmushi kawai tayi shi kuma yayi ficewar sa. Da kanshi ya ja motar don tun a hanya ya sanar da driver ya tafi ya sallame shi. Sai da ya biya yayi musu take away na abinci dasu snacks haɗe da tsire ya wuce masukin su.
Zainab
Tunda ya fita barcin ta kawai take hankali kwance ga sanyi AC na kaɗawa ta shige duvet abinta bata da sauran damuwa a duniya ,dama matsalar baba ne kuma ya fara samun lafiya, sai da akayi azahar ta farka tayi kana ta cigaba da barcin a haka har akayi la'asar kana ta shige ban ɗaki tayi wanka haɗe da ɗaura alwala bayan ta fito ne ta shimfiɗa sallaya sallar asr ta farayi kana tayi magrib, anan kan sallayar ya shigo ya tarar da ita idanun ta a lumshe alamar haryanzu barcin bai gama sakin ta ba "Am sorry zee diamond tawa ayyukan office ɗin ne dayawa" kallon sa take tana kallon kayan jikin sa kamar dai da kaya brown ya fita in ba dai idanun ta ne suka mata ƙarya ba.
Ganin kallon da take masa ne yasa ya gane kallon ko na mece ce "Daga gidana nake"
"Dama kana gida anan ne?"
"Eh anan amaryata take while uwar gida na cha gombe, kar ki damu kan mu koma zan nuna miki gidan nawa" da toh kawai ta amsa masa.
Mamaki take yana da mata har biyu kuma yake neman matan banza "Oh ni zainab yanzu shikenan nima za'a sani a layin matan da ake ƙira da masu bin maza (Karuwai)" ta ayyana hakan a ranta hawayena gangarowa tayi saurin sa bayan hannun ta ta share, ganin hakan yayi saurin riko hannun ta "Kar ki damu Zee diamond a yanzu ni naki ne, meyasa zaki yi min asarar hawayen ki akan wannan? Bayan kina gani duk na kyale su don na kasance a tare da ke" wani abu taji ya tokare mata wuya ji tayi kamar ta shake masa wuya to idan ma kishin zatayi sai tayi a kansa? Allah ya sawwaka tayi kishi a kan wannan mutumin kamar kwaɗo. Dire ledojin hannun sa,bayan sunci abincin suka fita izuwa shopping, kaya ya loda mata, kananun kaya dasu abayas haɗe da zannuwa, haɗe da sleepling dresses masu kyau.
(Abin na su azimun ne)
Audu
"Wato Audullahi ban isa da kai bako? Ince maka ga abinda nake so dakai amma ka koma bayana kana munafurci, sabida ka raina ni?" ta karashe maganar a sigar tambaya rai a ɗan bace.
Ɗan ɗagowa yayi ya kalle ta "Mama me kuma akace nayi?" ya yi tambayar haɗe da dukar da kai ƙasa
"Wato me akace kayi ma ko?"
"Wallahi umma ban san maganar me kike ba kiyi hakuri"
"Maganar fili.... Sai da nace maka kar ka sayar da filin nan amma ka zaga kaje ka sayar don ban isa da kai ba ko?"
"Innalillahi waya faɗa miki, ni wallahi ban sayar da filin ba yana nan idan baki yarda ba yanzu zan shiga na ɗauko miki takardun ki gani,wallahi ba sayar ba" ya ƙarasa cike da mamakin a ina taji wannan katon ƙaryar.
"Toh ai ji nayi wai anyi wa mahaifin yarinyar nan aiki, nayi mamaki gaskiya to a ina suka samo kuɗin tunda nasan basu da hanyar da zasu samu wannan himilin kuɗin"
"Wato ma tasan baza su samu kuɗin ba" Ya ayyana hakan a ransa amma a zahiri yace "Ni ma ban sani ba umma zuwa nayi na tarar basa specialist sai aka sanar dani anyi referring ɗinsa zuwa FTH kuma an biya kuɗin aikin"
"Ikon Allah" ta rike ha'ba "kuɗin nan kace min ya kai dubu 400 Ko?"
"Eh hakane umma" ya amsa a takaice.
"Toh Allah ya kyauta ko a ina suka samo oho, kaga Audullahi tun wuri ka sake tunani ka nemi matar aure yarinyar nan dai ba matar aure bace kuma......."
"Audullahi bai da mata sai zainab ko bayan raina kuwa, na rasa dalilin tsanar nan ta me ,me yarinyar nan ta miki kika tsaneta har haka a iya sanina babu wani takun tsaka tsakanin ki da ita ko da ni sai kyautatawa" baba ya chabi zancen haɗe da shigowa ya zauna daga gefenta.
"Affff muka kyautata musu dai , sama da shekaru goma kai kake ɗawainiya da su babu yadda ban yi da Kai ba akan bana son mu'amalar ka dasu da kai amma kafi karfina, Abdullahi dai ɗana ne ni na tsuguna na haifi kayana ba wani kato ko katuwa ta haifar min shi ba, Don haka yadda nake so da abinda nake so zai min" ta karashe tana hararar Baban ƙasa ƙasa, tsaf ya gani.
"Ni ne ƙaton kenan ko?" ya nuna kansa. Kawar dakai tayi gefe haɗe da faɗin "Ni dai bance ba haka kawai sun shanye Ka ɗan nawa ma baza su bar min shi ba yoooo akan me , baza ta sabuba wallahi, yaron nan kana gani akan idanun ka duk wahalar da aka sha ya samu admission a unimaid amma sabida tsinanniyar yarinyar nan yaki tafiya wai in ya tafi wa zai kula da ita sai kace wani ubanta." ta karashe kamar zatayi kuka sabida taji zafin abun matuka sannan ya fama mata tsohuwar ciwon da ta daɗe tana jinyar sa.
"Halima daɗin dake bakya mantuwa wannan maganar ta riga ta wuce , hakan na nufin ba hanyar cin abincin sa bane a likitancin tunda gashi yana kasuwancin sa me kuma ya saura?"
"Business admin ya karanta a GSU , a unimaid kuma Medicine ya samu da yanzu ɗana Likitane wallahi bazan taba yafe musu ba" ta kama bakin ɗankwalinta ta share idanun ta da yake ta zubar da ruwa.
Kallon sa baba yayi "Ta shi kayi tafiyar ka" tsum tsum ya mike jiki ba kuzari yana jin babu daɗi amma shi baiyi dana sanin yin hakan ba duba ga irin soyayyar dake tsakanin shi da ita "Mama ta fiye dawo da maganar da ta wuce wallahi" ya fice zuwa shagon sa dake kofar gidan su.
*WAIWAYE*
Abdullahi ɗane ga Malam usman mele da matar sa halima da ƴaƴan su 4, 3 mata 1 na miji wanda ya kasance shine babban ɗansu wato Abdullahi , Abdullahi yarone mai kwazo bai da buri irin yaga ya girma ya zama likita , yana da kokari sosai , hakan yasa mahaifin sa ganin ya taimaka masa ta ko wani hanya ya samu ingantacciyar karatu, duk da ya kasance bai da ƙarfi principal ne Na makarantar Malam Inna goverment school.
Ingantacciyar rayuwa ya bawa iyalan sa, bayan ya gama secondary school yayi applying jamb.
Sakamakon yayi kyau sabida 268 ya samu wanda first choice ɗinsa Unimaid(University of maiduguri) ne hakan yasa ya samu admission kasantuwar 250 ake bukata. A ranar da ya duba ya samu admission ba ƙaramin murna yayi ba sabida burin sa na gab da ciki.
Shirye shiryen tafiya ya fara, ana gobe zai tafi ya shirya ya je gidan su zainab, a lokacin zainab na da shekara 13 a duniya ,kuka ta rika yi jin zai tafi Maiduguri rokon sa ta rika akan ƙarya tafi ya barta, Abdullahi na matukar son zainab tun dawowar su garin yake jinta a ransa sai kuma wata shakuwa ta shiga Tsakanin su, duk da a lokacin Zainab Yarinya ce bata fahimci me so ba bata ma san mene ne shi ba.
Dakyar da makyar ƙyasa ya rarrashe ta sannan ya mata alkawarin bazai tafi ba, baya ya koma gida washe gari da ta kasance ya ranar zai tafi yayi ƙaryar rashin lafiya kamar da wasa Abdullahi yace shi ya fasa zuwa sai ya fake da tafiyar ce ta sashi rashin lafiyar kuma idan ya tafi bazai iya karatun ba asaran kuɗin za'a yi , tashin hankali da ba'a sa mishi rana iyayen sa sunyi mamaki matuka duba ga yadda yake son karatun amma haka kawai yace baza shi ba kuka yake sosai , tambayar duniya amma yace shi kawai ya fasa har duka sai da umma ta masa amma ya ce shi ba inda zashi babu yadda sukayi doke suka hakura.
A lokacin da zainab taji labarin ya fasa tafiyar ba karamin farin ciki tayi ba harda ƴar tsallenta ta rungume shi yayi saurin tureta ya bata rai , yayi hakanne don baya so ta saba da taba jikin shi duba ga yanzu ta fara tasawa "Ba na hanaki ba? Na faɗa miki yanzu ke ba yarinya bace haka kikeyi da maza idan kika je school ko?"
Saurin girgiza kai tayi tana matsar kwalla tace "A a walllahi ya Audu banayi, kuma na maka alkawarin bazan sake ba" ta cigaba da matsar kwallar ta.
"Zainab don na faɗa miki gaskiya shine kike min kuka to shikenan , ni tafiya ta ma zanyi kuma a yau ɗin nan zan tafi maiduguri" ya juya da niyar tafiya ,tayi saurin rike masa riga ganin irin kallon da yake mata tayi saurin sake shi kai a ƙasa tace "Dan Allah kayi hakuri bazan sake ba wallahi" ta ɗago idanunta tana kallon sa murmushi yayi "Idan kika sake fa?"
"Ka zane ni" ta faɗa kai a ƙasa girgiza kai kawai yayi yace "Shiga gida zanje Massallaci"
"Baza ka tafi ka barni ba ko?"
"Eh bazan tafi ba ,amma idan kika kuma zan tafi, sannan share wannan" yana nuna mata fuskarta ,tayi saurin share hawayen nata , sai da yaga shigar ta kana ya juya ya tafi yana jin yana kara nitsewa a soyayyar ta.
(Ni ko nace Anya Malam audu bakayi kuskuren yin hakan ba kuwa).
*BAYAN SHEKARA ƊAYA*
Jamb Abdullahi ya kuma yi amma wannan karon 200 ya samu takaici da bakin ciki ta rasa yadda zatayi wa ranta don a kullum cikin ƴan uwa da abokan arziki faɗi take wai ɗanta zai zama likita, hakan yasa yayi change of course zuwa business admin, sannan karon GSU yayi applying Gombe state university kuma yayi hakan ne sabida makarantar a unguwar su yake, ba bata lokaci yayi register ya gama komai ya fara zuwa lectures.
*AFTER 4 YEARS*
Zainab da kannen Abdullahi na hango zaune suna hirar su ta ƴan mata a gidan su Abdullahi nan suka fara musun wacce yayan nasu yafi so a cikin su "Ya Abdullahi yafi sona" faɗin Fatima , maryam tace "Ƙarya kike yafi sona" salma tace "Uhmn ku daina bata yawun bakin ku yafi sona tunda duk cikin ku ni kaɗaice yake cewa Angel"
"Duk kuyi shiru malamai yafi sona" wata uwar harara suka mata, maryam wacce tafi su rashin kunya da tsiwa tace "Ke kuma wa ya kasa sa ke da zaki ɗauka?"
Fatima tace "Kalen dangi mana sai Zainab akwai rainin wayo wallahi"
"Oho dai ko ma me kuce nasan dai yafi sona , tunda ai sabida ni yaki zuwa maiduguri , kunga kenan yafi so na" kallon kallon suka farayiwa juna suna mamakin abinda tace ɗin.
Karaf kuwa a kunnen Umma da fitowar ta kenan daga ɗaki da sauri ta nufo inda suke haɗe da faɗin "Me kike ce Zainab?"
"Umma wai su salma ne sukace Ya Audu yafi son su a kaina shine na faɗa musu yafi so na don ni ya fasa zuwa makaranta a maiduguri" Hannun ta ɗaura a kwankwaso ta gyara tsayuwar ta "Tabɗi jam" tana wani irin huci ,wata katuwar ashariya ta lailayo
"ke don kutumar ubanki ki fice min daga gida ko naci ubanki."
Yadda tayi maganar a tsawace ba iya zainab ba har su salma saida suka shiga taitayin su, Allah sarki Zainab baiwar Allah sum sum ta fice daga gidan.
Umma ta shige ɗaki tana jira dawowar Audu daga makaranta, ilai kuwa ba a rufe mintuna 20 ba sai ga shigowar sa , sannun da dawowa ƙannen sa suka masa ya amsa musu dakyar da alama akwai gajiya a tattare dashi, parlor ya nufa bai kai ga shiga parlor ba ta kwashe shi da maruka masu kyau har sau biyu har sai da yayi tangal tangal ya faɗi a kasa, nan ta hau kanshi sai duka take kai masa da belt ɗin dake hannun ta, Abdullahi kuwa hakuri yake bata don shi bai san laifin da yayi mata ba sannan bai gudu ba yana nan zaune yana kare fuskan shi, kannen sa na daga gefe sun rakube suna matsar kwallar tausayin yayan su, haɗe da jin haushin zainab don duk abinda ya faru itace sila, duka take kai masa ta ko ina ba ji ba gani, malam usman da shigowarsa kenan yayi saurin nufar inda take ya kwace belt ɗin yana tambayar ta laifin me yayi mata take dukan ƙaton saurayi haka.
"Malam ka barni na kashe yaron nan kan ya kashe ni da bakin ci, ashe yaron nan mara mutuncine , baida hankali wawa sakarai shasha wanda bai san inda yake masa ciwo ba, ban taba sanin cewar girman banza yayi ba sai yau" ta kai masa wani marin.
"Wallahi Halima kika sake marin sa sai na saba miki, tunda baki ji kunyar dukan sa a gaban ƙannen sa ba nima kuma bazanji kunyar tsinka miki mari a gaban su ba" ya faɗa a hasale.
"Tambaya zaka yi kaji me yayi ba ka hauni da faɗa ba" ta faɗa tana gunguni
"Sau nawa kike so na tambaya? Ki sanar dani abinda ya miki tun kan ranki ya baci" ganin fa ran sa ya baci yasa ta fara faɗin "Malam ashe yaron nan kin zuwa Unimaid da yayi sabida figaggiyar yarinyar nan ne? Kai amma Allah ya isa wallahi bazan taba yafe musu ba ,sun shanye min kai bai ishe su ba sun haɗa min da yaro kullum cikin bauta musu kuke nikam na shiga uku na lalace" ta ɗaura hannu aka tana kuka mai sauti.
"Magana kike wanda na kasa fahimtar sa ,ki min dalla-dalla ban son jan rai kin sani."
Ɗan tsagaitawa tayi da kukan da take tace "Gashi nan, makarantar da aka kashe kuɗi akansa yaki zuwa ashe akan zainab yaki zuwa"
Baba Ya kaɗu da jin hakan tabbas Inko hakane Abdullahi yayi wauta kallon sa yayi don ya tabbatar da abinda tace ɗin saurin dukar da kanshi yayi a ƙasa babu alamar tsoro ko fargaba a tattare dashi saima kawar da kansa yayi idanun nan nasa sunyi jajir.
"Abdullahi maganar da ta faɗa hakane?"
Kara yin ƙasa yayi da kansa yana jin kunyar haɗa ido da mahaifin sa.
"Ga makaryaciya ko? Baka yarda da magana ta ba sai tashi ai kana ganin yanda yayi da ido wiki-wiki kamar munafuki zaka gane cewar gaskiya ce"
"Kinga ya ishe ki hakanan ki bari ya bani amsa da bakin sa, me yasa ka aikata hakan?" ya maida akalar tambayar sa ga Abdullahi. Jin shiru bai bashi amsa ba hakan ya hassila shi "Idan baka bani amsar tambayar da na maka ba wallahi ni da kaina zan hukunta ka hukunci mai muni kuwa kasan kuma zan aikata" ya karashe a kausashe.
"Dan Allah baba kuyi hakuri wallahi tausayin ta nake ji kuka ta rika yi,tana roko na kar na tafi ni kuma Tausayin ta nake ji shiyasa na fasa" ya dukar da kai ƙasa
"Toh ai shikenan ka kyauta" yana kai nan ya yi hanyar ɗakin sa.
"Shikenan? Shikenan fa kace malam shikenan kana nufin maganar ta wuce kenan?"
Ɗan waigowa yayi "To me zan iya yi a kai? haka Allah yaso kuma ma ai yanzu yana final uwa ko ba shikenan ba tunda abinda ya zabarwa kansa kenan" yayi shigewar sa ɗaki.
Fushi sosai sukayi dashi , kullum cikin neman yafiya da hakuri yake a gun Iyayensa sun ɗauki lokaci mai tsawo basu manta wannan ɗanyan aikin da ya aikata ba , duba ga cewar Haka Allah ya tsara suka rungumi kaddara suka yafe masa ,amma Umma tun daga ranar ta daura ƙaran tsana wa zainab ta hana ta zuwa gidan ta sannan ta hana su salma mu'amala da ita duk da su ɗin ma hakan suke so gani suke itace silar komai, tsanar ba a iya kan zainab ya tsaya ba har kan iyayen ta, Umma gani take kamar sun shigo cikin rayuwar sune don su cuzguna musu.
Bayan ya gama karatun sa ,yayi NYSC Baba Ya buɗe masa babban shago wanda kaf cikin unguwar babu mai girman shagon sa kuma alhamdulillah yana ciniki sosai, a wannan gabar ya bukaci baba ya nema masa auren zainab yayi farin ciki sosai sabida ya daɗe yana son wannan haɗin amma ya zabi ya bar ko wannen su da zabin ransa, kuma a yanzu tana da shekaru 17 a duniya, a ranar da ya sanar da mahaifin zainab baiyi ƙasa a gwiwa ba ya bashi auren ta akan idan ya gama ginin sa sai ayi auren kamun nan zainab ta ƙara girma sosai, da labarin ya riski Umma haukane batayi ba don a ranar ta wuni tana masifa da bala'i duk suka watse suka bar gidan, Baba majalisar su ya wuce ,Audu Kuma shagon sa yayin da su Salma suka wuce islamiya sai da ta karaci masifar ta ita kaɗai yamma lisss suka dawo.
A rana daya aka saura auren Salma da Fatima, Salma na aure a Abuja tana auren wani shahararren ɗan kasuwa, Fatima kuma tana aure anan cikin garin Gombe, sai maryam wacce haryanzu bata ƙarasa Candy ba tana ajin ƙarshe wannan kenan.
*CIGABAN LABARI*
"Halima ya kamata ki manta komai duk abinda kiga ya faru to rubutaccen al'amari ne dama tun chan Allah bai ƙaddara abincin sa a likitanci bane ki kwantar da hankalin ki dan Allah."
"Malam kenan a dake ni a hanani kuka? Wallahi bazaiyu ba taya ma zan bari ɗana ya auri mayyar yarinyar nan? Kana dai ganin tun ba a je ko ina ba ta malleke min ɗa sai abinda tace yake yi har ya isa tsallake maganar mu da burin da ya taso tun yana yaro baza ta sabu ba wallahi."
Mikewa yayi "Toh shikenan tunda kin zama mijin na zama matan ki hana shi auren nata mu gani ,wallahi idan kinga an fasa auren nan sai dai in mutuwa nayi ko kuma yarinyar ce tace bata so don ko shi Abdullahi bai isa yace ya fasa ba don baku isa ku mai dani karamin mutum ba" yayi ficewar sa.
"Lallai akwai ƙaramar tashin alkiyama a gidan nan, kaaai na rantse da girman Allah babu wanda ya isa yasa ɗana ya auri alakakai." sai ji tayi yace "To kishirya zawarci na tabbata kin gaji da zaman gidan nan"
"Haba malam Da girmana zawarci har jikoki nake dashi to ya kake so su salma suyi idan suka ji wannan abun kunyar? Ni zaka saka akan wannan ƴar......."
"Kul kul ki haɗiye idan na kuma ji kin aibata yarinyar nan sai na saba miki shasha kawai" baba ya katseta ,yayi gaba abinsa ya fice daga gidan ma gaba ɗaya.
Umma durkushewa tayi ta ɗaura hannu a ka tana faɗin "Na shiga Uku yau na ga ta kaina, Allah ya isa wallahi bazan taba yafe musu ba sama da shekaru talatin mijina bai taba min tsawa ba amma yau ta da dalilin ki har zagina yayi, ni ce shasha?" ta kuma kurma ihu ,surutai tayi ta yi har ta gaji don kanta ta bari.
Jalal
Na gani a zaune ya ɗaura fararen kafafun sa a kan ɗan madaidaicin table ɗin dake tsakiyar kujerun da aka jera a garden na masaurata yana shakar daddaɗan iskar dake kaɗawa a hankali, idanun sa a lumshe kamar mai barci amma a zahiri ba barcin yake ba, duk da cewar yaji tafiyar mutum yana nufo shi amma hakan bai sa ya buɗe idanun sa ba sai ma kara gyara zaman sa yayi "Barka da hutawa my prince" ta furta tana masa wani irin murmushi wanda take bayyana zallar so da ƙaunar sa da take.
Hafsat tace dashi ƴa ga Mairo kanwa ga sarauniya Sa'adah (Mahaifiyar yarima jalal).
Banza yayi da ita kamar baya gun, jin yayi shiru ne yasa ta ɗauka barci yake a hankali ta zo dab dashi ta tsaya tana ƙare wa kyakkyawar fuskar shi kallo wanda zara zaran gashin idanun sa ke kwance,hakan nan gashin giran sa a kwance kamar na mace sai kuma bakin sajen sa ya ƙara wa fuskar tasa kyau da kwar jini sai sheki yake sabida gyaran da yake samu.
A hankali ta kai hannun ta da niyar ɗaura shi a kan sajen sa "Don't you dare" a razane ta maida hannun ta don ta tsorata sosai tayi baya da sauri, fuskar nan ta kamar jar kosan da bata gama soyuwa ba,fara ce amma farin bleaching ,ga kan nan yasha attachment ,bakin nan ya sha jaan jambaki , idanun nan yasha eye shadow kalan kayan ta , sannan tasha eye lashes irin dogin nan , hakan ne yasa kananun idanunta suka buya, tana kallon sa da fuskar tausayi don ta sani yau kam ta tabo tsuliyar dodo.
A hankali ya ware idanun sa kamar wanda suke masa ciwo,sauke kafafun sa yayi ya sanya a takalmin sa na sau ciki kana ya mike.
Nuna ta yayi da manuniyar sa "How many times? How many times have i told you not to mingle in my life? Ki daina shiga harkata you disgust me, i just hate you with passion ke ko kunya ma bakya ji?" ya karashe maganar da sigar tambaya.
"And I love you" durkusawa tayi ta haɗa hannayen ta wuri guda alamun roko tace "Ya jalal dan Allah ka so ni wallahi ina sonka bazan iya daina son ka ba ,da ace zan iya da na daɗe da cire ka raina ,Bazan taba gajiyawa ba ko da kuwa naman jikina zaka rika yankawa kana ajiyewa a gefe"
Kallo yayi mata na baki da hankali yayi tsaki ya juya ya fara tafiya da gudu ta rufa masa baya ba tare da bata lokaci ba ta rungume shi ta baya "Dan Allah jalal ka soni ko da kuwa bazai kai yadda ni nake son ka ba am dieing and craving for your love." janye jikin sa yayi daga nata haɗe da shafa mata maruka har gudu biyu a kuncin ta na dama hagu, nuna ta yayi da ƴar yatsa "Ashe dama haka kike ballagaza a hakan ne kike so na aure ki? Ni banga abin so a tattare da ke ba bare naje zanyi wa Ummi biyayya , ga ki mummuna , ballagaza sai wari kike wallahi ganin ki kaɗai tayar min da zuciya yake......" yayi fuska kamar mai shirin yin amai sai ya kalli jikin sa ya yatsar da yawu "F**k yanzu zaki sa na kuma yin wani wanka, don't you ever try this nonsense with me." yayi tafiyar sa ,tayi tsaye tana kallon sa hannayen ta duka biyu a kuncin ta, ba ta daina kallon sa ba har ya bace wa ganin ta, sauke hannayen ta tayi ta harɗe a kirjin ta,wata irin shu'umar murmushi tayi mai kama da dariya "We shall see jalal, we shall see."
*CIKIN FADA*
"Amma rankashidaɗe na daɗe ina mamakin yadda za'a ce mutum ya bata a cikin masarautar nan, idan ban manta ba wannan shine na biyar da bayi suka bace a cikin masarauta that means muma we are not safe, sannan ina tsoro da fargabar kar maganar nan ta fita wajen masarauta idan kuwa hakan ta faru sunan masarautar nan zata baci Allah" faɗin sarauniya Sa'adah.
"Ni kai na ina mamakin hakan Ummin yara mutum ai yafi karfin ace ya bata haka kawai sai kace kuɗi? A nemi mutum a rasa ni kaina na fara jin tsoro wallahi?" jidda (Aunty amarya) kenan amarya agun mai martaba kuma uwa ga Yarima Taheer.
Mai martaba dake zaune tsakiyan matan sa sarauniya Sa'adah na yanka masa fruits ta mika masa lemo ya karba, yayin da Sarauniya jiddarh na masa fifita, ɗan numfasawa yayi damuwa ya bayyana karara a fuskar sa shi kansa da abin yake kwana yake tashi tun yana ɗaukan abin kamar wasa amma ya soma fin tunanin sa ɗan gyara murya yayi kana yace "Ni kaina na daɗe ina nazari akan lamarin nan amma kar ku damu insha Allah zamu gano bakin zaren."
A tare suka amsa da "Allahu yasa" ya amsa da amin nan suka cigaba da hirar su cike da kwanciyar hankali cike da nishaɗi. Kamar ba kishiyoyi ba.
*Shin wane ne sarki Muhammad Abduljalal?*
Muhammad Abduljalal ɗane ga sarki Abduljalal wanda suka gaji sarauta tun daga kakannin kakanni, Muhammad shine baban ɗansa na miji wanda ya kasance duk kannen sa matane hakan ne yasa bayan rasuwar mahaifin sa ya gaje shi, muhammad saurayine mai jini a jika Kyakkyawa ne son kowa wanda kana ganin sa zaka gane fulani ne na usul, a ranar da aka naɗa shi a matsayin sarki aka ɗaura auren sa da Sa'adah ƴar umman sa ce, dama ya daɗe yana son ta amma bai bayyana hakan ba sabida bai yi rayuwar sa a nigeria ba a turkey yayi karatun sa saida mahaifin sa ya kwanta ciwon ajali ya bukaci dawo kusa dashi Bayan rasuwar mahaifin nasa aka naɗa sa sarki.
Zama suke mai cike da so da ƙaunar juna kasantuwar sa'adah yarinya ce mai nitsuwa da girmama iyayen ta, bayan shekara ɗaya da auren nasu Allah ya azurta su da haifan ɗa na miji wanda yaro yaci sunan kakan sa Abduljalal, tun bayan haihuwar sa bata kuma samun wani cikin ba har ya kai shekaru biyar.
Ziyara sarki ya kai zuwa masarautar bauchi nan yayi gamodakatar da ɗiyar sarki mai suna hauwa'u wacce ake ƙira da Gimbiya Jiddarh,baiyi ƙasa a gwiwa ba ya nuna kwaɗayinsa akan ta haka ba karamin daɗi yayiwa mahaifin jiddarh ba duba ga Sarki Muhammad mutumin arziki ne babu wanda zaiki haɗa zuri'a dashi duba da nagartar sa da kuma asalin sa, bayan dawowar sa gida ya sanar da sa'adah tayi kuka sosai amma bata nuna masa ba, bayan ƴan watanni a ka kawo Jiddarh a matsayin amaryar sarki.
Jiddarh nada saukin kai ga son mutane hakanne yasa suke shiri sosai da Sa'adah wadda ta kasance kamar yaya a gareta zama suke na gaskiya da amana sai ɗan abinda baza a rasa ba na daga cikin ajizancin ɗan adam.
Jiddarh na cika wata goma a gidan sarki ta haifi santalelen ɗanta wanda yaci sunan mahaifinta Taheer , yaro yaga gata daga gun Mahaifinsa da kuma Sarauniya sa'adah itace take masa komai tamkar ɗanta yayin da komai na jalal Jiddarh ce idan ba faɗa maka akayi ba zaka ɗauka Jalal ɗan jiddarh ne kuma ka ɗauka Taheer ɗan sa'adah ne, Taheer na da cika shekara 2 Sarauniya Sa'adah ta haifi kyawawan ƴaƴanta Ƴan biyu na miji ɗaya mace ɗaya wanda suke kama sak da Yayan su Abduljalal sai dai shi ya fi su haske sabida hasken mahafin su ya ɗauko su kuma bakin fatar sa'adarh suka ɗauko mai kyau da sheki, wanda aka sa musu suna Amina da Aminu amma ana kiran su da Afreen da Afraa tun daga nan bata kuma samun wani cikin ba amma kuma Jiddarh bayan Taheer ta haifi ƴaƴa 5 bayan shi, Fadeelah ,fadeel, Shamsuddeen ,shamsiyya sai ƴar auta Khadija wacce suke ƙiran ta da Nana.
Abduljalal ya taso a sagalce kasantuwar soyayyar da sarki yake masa da kuma Sarauniya jiddarh sam basa ganin laifinsa , duk abinda yake so shi akeyi hatta abinci sai an tambaye shi abinda yake so akeyi, Mahaifiyar sa(sa'adah) sam bata goyon bayan hakan amma sun fi karfinta wani abun idan sukayi sai dai ta zuba musu ido idan kuma taga abin na neman yayi yawa tayk magana hakan kuma bazai sa su canza ra'ayin su ba , amma duk da hakan Abduljalal shine ɗa mafi soyuwa acikin ranta sai dai alkunyar da takeyi irin na fulani da sukeyiwa ƴaƴan su na fari.
Takaitaccen labarin Gidan Sarki muhammad kenan.
Zainab
Sai da sukayi kwanaki 8 a abuja babu abinda sukeyi sai aikata alfasha sai dai su fita suje restaurant ,shopping wurin shakatawa da dare idan suka dawo yayi ta kwakular ta son ran sa, tun bata so har ta saba wanda idan ma bai taba ita zata taba shi.
To ya kuka ji salon labarin namu? Muje zuwa haryanzu wasan bai fara ba.
Please share & comment Fisabillah