1
by @asmybaliyu
Kasancewar lokacin damina ne shiyasa garin yau ko kadan bbu rana ,hadari ya hadu sosai gaf ake da sauko da ruwan sama.sauri kawai take a gefen hanya wanda dai-dai kun ababen hawa ne ke wucewa ,kuma da sauri wanda ko napep daya bata hango ba,lokaci daya taji jikinta yyi sanyi tasan wannan lecture din ita da samunta sai wani ikon allah,kafin ta gama tunani ruwan sama ya sauko da karfin gaske ,Ya salam...!"ta fada a hankali gefen hanya ta koma bbu wajen da xata tsaya ,idan tace ta koma gda wahala xata sha tayi nisa sosai da gida.daga nesa ya hangota a hankali yake fadawa bala driver ya rage gudu,su tsaya su taimaka mata da alamar makaranta xata tafi.. "cikin bin umurninsa bala yayi parking gefenta,ganin mota gaf daita yasa ta kara matsawa.A Hankali bala ya fita motar ya cimmata da lema a hannunsa,yana hangosu daga nesa amma baisan me suke fada ba,cikin minti biyu sai gasu gaban motar ,bala ne ya bude mata gaban motar ."Amma baba da alamar xan jika maka sit."tayi maganar tana kallonsa,bbu komai ya fada mata..ina ne makarantar naku..?
yyi maganar batareda ya kalleta ba hankalinsa na kan tukin da yake,"anan cikin (B.U.K.)har bakin get ya sauketa har xata bude marfin motar tamkar daga sama taji ana fadin."Ban san me sunan malamar ba.?"ta shaafa sosai ta mirror take hangosa ruwan tarwaɗa ne ,muna haɗa ido nayi saurin ɗauke kai .na fita daga motar na russuna ina fadawa baba nagode allah ya kara girma.."da haka na tunkari get din shiga makarantar......
Suna xaune a gefen itaciyya mota taxo ta tsaya gaf dasu ,itada friends dinta kowane rikeda (text book) Yana dubawa ,cikinsu babu wanda ya maida hankali kan motar,mamallakin motar ya fito kananan kayane ajikinsa ,blue din shirt ce da bakin wandon jeans.sunyi matukar dacewa da fatar jikinsa dogone ruwan tarwaɗa wanda turawa ke kira da (chaculate)Yana da manyyan idanu da dogon hanci,ya'mmata sai ɗaga masa hannu sukeyi ,kai Aiman din nan ya hadu cewar aysha "bilki tace akwae wulakanci amma kuma yana da taimako sosai,,
Gaba dayansu suka mike tsaye batareda sun maida hankalin su kanshi ba,Jameela ce a gaba tana amsa waya jin tayi ansa kafa an hambareta sauran kadan ta kai kasa ,kawayenta sukayi saurin tarota baiso hakan ba ko kadan sau yake tasha kasa,So yake ko sau daya ya koyawa yarinyyar nan hankali cike da balai da masifa jamila ta nufesa ,Caraf farhaa ta rike mata hannu dan allah malama ki sakeni."wlhi yau sai nayi maganin wannan gayen uban wa ya fada masa mu ya'yan matsiyata ne ?"muma ae iyayen mu suna da kudi,mln baka gani ka kusa taɗeni?"yadan kalleta cike da isa yana danna waya yake fadin ."Auh magana kikeyi.."Ranta taji yana kara baci ,ka turani kuma ka kasa bani hakuri "ta karasa maganar cike da masifa da balai ,wani banxan kallo ya shiga watsa mata ,kalleni da kyau namaki kama da sa'ar ubanki ne.?"Ya fada fuska bbu walwala ,cikin ihu da tsawa Jamila ke fadin baida ubana ba wlhi sai dai ubanka."ta fada cike da balai da masifa hannu ya daga xai xabga mata shegen mari caraf aka rike hannun,cikin fushi ya kalli wanda ya rike masa hannun.ransa yaji yana kara baci ,hannunsa ya shiga ja suka bar wajen,,meye amfanin haka dan allah jamila ko kadan ba girmanki bane fada da namiji akan hanya,wani kallo ta shiga watsawa farhaa gaba tayi tabar sauran kawayen nata wanda suka bita da ido ,farhaa ta sauke ajiar xuciya take fadin"kun san halin jamila badai saurin hasala ba,ku kyaleta xata sauko ne,,muje (cafeteria )a hanyar su ta xuwa farha ke fadawa su bilki yau shi ya rage mata hanya,ban taba ganinsa makarantar nan ba sai yau."ke fuska biyu garesa baya da mutunci amma bakiga yarda ya'mmatan makarantar nan ke sonsa ba."Shuru farhaa tayi ta cigaba da sauraren hirar dasu bilki keyi kan aiman har suka karasa cikin(Cafeteria)....
****
Mahaifina malam usman mutun ne mai rufin asiri dan kasuwa ne,ya mallaki matar aure daya wadda muke kira da umma."da ƴa'ya hudu Yaya Sadiq shine na farko sai anty mariam ,fatima(Farhaa)sai auta kamal Ya sadiq yana hada masters dinsa a jami'ar (A.B.U.)Anty mariam tayi n.c.e fannin (primary edication)tana gafda yin aure,farhaa na jamiar (B u.k) anan kano tana karantar (Low)sai auta kamal yana primary 3.....
***
da gudu ta fada kanta tana mata oyo yo."ɗagani farhaa nauyin tsiyane dake wallahi,dani da yah faisal wayafi nauyi?"ta kaimin duka na jaye ina daria xan rikaki ne wlhi.."wai dan allah yaushe kika dawo ko kiyi min waya."ke kyaleni da tambaya su hajar na gaisheki .
"bara na watsa ruwa naxo musa labule kin san dai abunda nafiso ,allah yasa kin sayamin da xani nasan wani abu kika bani"nan ta cire kayan jikinta ta fada banɗaki ......