3
by @asmybaliyu
Abdul-Rahman Aliyu jalingo ya rika muka mai da dama tun daga minister,senator ,har deputy governor yyi karshe yabar siyasa ya fada kasuwanci ,yana da matar aure daya da ya'yah ukku Maheer ,Aiman sai Auta Yasmin Maheer yana karatun (Medicine) a kasar Gemerny sai aiman dake karatun masters dinsa anan cikin .(B.U.K) fannin kasuwanci yake karanta sai auta yasmin wanda yanxu ta gama karatun secondry,gaba daya iyalin abdul-rahman jalingo sun taso cikin gata tun tasowarsu mahaifinsu ke siyasa ,dan haka basu san kalmar bbu ba a rayuwarsu iyayensu sun sangartasu da kudi ta koina ,haka gaba daya jinin fulani ne,sai ma Aiman da baya kama dasu maheer ko kadan,bai dauko hasken fatarsu ba,bakar fatar mahaifiyarsu ya dauko,yayinda su Yasmin suka dauko farar fatan mahaifinsu dan mahaifinsu fari ne sosai tamkar balarabe."
Wlhi farhaa abun da kikeyi bakya kyautawa ko kadan ,be serious aiman ba irin mutanen da ake daukar maganar su da wasa bane,,ki daga wayar kiji mexai fada,Haba farhaa karkiyi min wannan horon ya fada cikin sanyi murya shuru tayi plz kice wani abu ina son jin muryarki."a fada min meye laifina da ake hukuntani haka?"ya fada yana sauke numfashi,nan ma shuru tayi jin yyi shuru yasa ta kashe wayar,
A hankali ya kalli khalil jikinsa yyi sanyi sosai yake fadin"ta kashe min waya maxa."
Shaye da toka khalil ke fadin nifa na fara jin haushin wannan farhaa dan taga kana sonta dayawa shiyasa take juyaka,,kafita har karta."baxan iyaba ne bakasan yana keji ba,
Kai farhaa irin wannan shanyawa haka ,ko albarkaci na abokina baxai ciba,kin dagawa abokina hankali kin hanasa barci ,kin hanasa cin abinci ,
Kun manta kuna da xuhra lokaci daya khalil da aiman suka kalli juna haka suka saki murmushi sun gano laifinsu,
Xuhra bata gaban aiman macce daya aiman keyiwa wannan son kuma gata agabanmu,ki manta da xance xuhra .Ba xato taji aiman ya kamo hannunta ya dora kan kirjinsa yana kallonta da kyawawan idanunsa,tana jin yarda xuciyarsa ke bugawa......ganin haka khalil ya koma mota yana komawa mota ta fisge hannunta,ahankali ya shiga murmushi yana sosa kansa murmushin da bata taba ganin yyi sa ba,haka yyi kyau sosai dan lokacin yana sanye da farin yadi kyal wanda har ana hango farar vest din dake jikinsa yadin ba karamin kyau yyi masa ba,,anan ya cigaba da bata lbrn Xuhra yana fada mata a uk.Suka hadu yar katsina ce,sai da yaga ta sauko ya mata sallama.
****
Aiman !"
Mahaifinsa ya kirasa cikin natsuwa jin yyi xuciyarsa a hankali tana tsinkewa ahankali yake fadin"na'am daddy.
Ka shirya xuwa jibi visa dinka xata fito xaka koma uk da karatunka,nariga nasa anyi maka komai ,,amma daddy meye amfanin karatunta da nake anan?"ya fada cikin tashin hankali ,wani kallo yaga mahaifinsa nayi masa yayi saurin sadda kansa kasa.Kana sane da nasan duk iya shegen da kake aekatawa a waje dakuma cikin makarantar ku ,kai gaka dan masu kudi."Amma daddy wa yake kawo maka waya'nnan maganganun."yyi maganar shaye da toka,
Kayi min shuru ka rufe man baki mutunen banxa,naga ma magana ka shirya kayanka kabar kasar nan ,tashi kabani wajen mutunen banxa...!"xaiyi magana daddy ya wani daka masa tsawa,ko gabansa baya gani haka ya nufi part dinsa tamkar wanda yasha kwaya."
A ranar ko wajen mum dinsa bai shiga ba ,itama tasan kwanan xancen shiyasa ta sharesa ,,haka ya kashe wayoyinsa duka farhaa nata kira bata samu.Ganin har kusan tara da rabi na dare bai shigo ba mum tabi bayansa da kayan abinci,,tareda yar aikinta tana ajey masa yar aikin tayi gaba mum ta xauna gefen gado ,ta jaye bargon da ya rufe dashi ya bude idonsa da suka kada sukayi ja lokaci daya ,ya kalli mum dinsa cikin fushi yake Fadin."meyasa daddy yake min haka mum tamkar bashi ya haifeni ba ,ammai dani karamin yaro .Na fada masa bana da raayin xuwa uk karatu dan me sai naje ,,yabarni nayi raayin kaina mana,yana maganar ne cikin fushi wanda jikinsa har kadawaq yake.Sai dai kayi hkuri kasan daddy baxai canja ba,,shekara biyu ne fa kawae ka dawo wancan lokacin ya akayi da maheer shida ma yafika tsanar kasashen waje yanxu komai bai xama tarihi ba."mum plz ya fada yana shigewa toilet ,
Kansa ya sakarwa ruwa ko xai samu saukin abunda yakeji taya xai tafi yabar farhaa,wlhi an cucesa angama da rayuwarsa dama ana dawo da baya,da bai fara son farhaa ba....Haka mum ta karasa xamanta bai fito daga toilet din ba tariga da tasan yyi fushi .......
Mexai hana katura magabatan ka agidansu farhaa a tsaida maganar aurenku ko baiko ne ayi maku shekara biyu fa ba wasa ba ,nasan mahaifanta baxasu jiraka ba,kai ma kasan halin daddy wlhi baxai yarda ba."nidai canja wata shawara banda wannan pls.....
A firgice ta mike tsaye hawaye na bin fuskarta tashin hankali karara ya hango akan fuskarta ,khalil ya cigaba da fadin farhaa aiman bai so haka ba.Mahaifinsa ne mai tsattsaurin ra'ayi ,dan allah ki kwantar da hankalinki mudai fatan mu ki rike mana alkwari."xaki jiramu ki cigaba da karatu?"ya fada yana kallon yanayinta.......