MAHEER

9

by @asmybaliyu


Hango aiman yyi yana saukowa daga matattakalar jirgi cikin maron yadi dinkin kaftan,yyi kiba sai sajen da ya axa wanda ya kewaye kyakkyawan fuskarsa ,Rungume juna sukayi cike da farin ciki...Yaya mahaeer ina su mum ."Maheer ya buga kafadarsa yake fadin."ka kyale mum tana fushi dakai dan xaka sauka a gidana.,,A mota sai hira suke burinsa kawae ya gama da gdan yayansa ya wuce gidansu farhaa meyasa wayanta kashe?"tunda wayarsa ta fadi ,bai kara samun lambar farhaa ba,hakama aunty mariam .idan ya kira wayoyinsu duka kashe ...Haka yaxama tamkar mahaukaci khalil kuma sun bar kano shida familynsa,shekaru biyu din nan a daddafe yayi su kullum mafarkinsa na kan farhaa,ko ynxu a mota maheer ke masa yana tsokanarsa yana fadin ya axa kiba har da tumbi."sai dai aiman yyi daria kurum suna kawowa gdan maheer ,aiman ya kalli yayansa yake fadin ."Yaya gdn nan naka yana da kyau....

Cikin barci taji ana hura mata kunnenta ,ta bude idonta dake cike da barci take fadin har ya iso kenan.?"ya gyada kai yake fadin yana falo,bara na shiga toilet na dauko dogon hijab na kallesa nace bara naje na basa ruwan sha."wannan turaren baxata taba mantawa da shiba a rayuwarta da shi kansa mai turaren ,shi kuma aiman idonsa na kan kofa ya kosa yaga matar yayansa,da yaki yadda ko pics dinta ya turo masa ta whatssapp .Yasan yayansa yasan tsarinsa shiyasa bai kara tambayarsa pic dinta ba,tayi sallama da siririyar muryarta wannan muryar da mai muryar baxai taba mantawa dasu ba,ko shekara nawa xaiyi bai ji muryar ba,ya dago kansa sukayi ido biyu .Kowanen su sai da ya shiga (SHOCK!")aiman saboda tsananin kidimewa sai gaya a tsaye hawaye na bin fuskarsa ,shikenan Ya rasa RUHUNSA sanyi idaniyarsa juyawa kawae yyi ya fita daga falon xubewa tayi akan kujera da sauri da sauri take maida numfashi ,allah yasa mafarki take aiman !aiman !"aiman shine kanin maheer ta shiga ukku."hawaye tamkar an kunna famfo da haka maheer ya sameta ,ya dagota a gigice yake fadin"lfy meya sameki.duk ya rude ,kaina ke ciwo."ina aiman din tayi karfin halin fadin ya fita amsa wya.Muje kisha maganinki ya fada yana dagata duka ajikinsa.....

duka suka hadu a wajen cin abinci sai dai maheer ne yyi serving din kowa ,duk lokacin da suka hada ido da aiman sai ta dauke kai,dukansu bbu mai magana .Maheer ya lura da farhaa ta kasa cin komai ,maheer ya dagota cak.!"ya axata kan kafafunsa yake fadin"xamuyi fada farhaa buda baki na baki bakya son cin abinci so kike bbyna ya kwashi yunwa,,ya fada yana kai spoon din abinci abakinta bbu musu ta buda bakin,xuciyarsa yaji tana kokarin tsinkewa saboda wani irin kishi da bakin ciki ,ture plate din abincin yyi idonsa ya kada sosai ya mike tsaye da wani irin yanayi a fuskarsa yake fadin"Yaya bani key din motarka xan wuce gida,

"Abinci fa?"komai bakaci ba , na koshi ina son naje naga mum."kabari muje tare no kabarsa,ka kula da matanka."Maheer ya cigaba da ba farhaa abinci yana fadin dauki ga yacan kan center table,xan shigo anjima aiman ya kalleni cikin ido da ido yake fadin ."ngd amaryar yayanmu abincin ki yyi ddi sai kinxo karbar tsaraba ya fada yana ficewa daga falon da wani irin yanayi a fuskarsa ....Mum dad sunyi farin cikin ganin yaron nasu,amma shi aiman hankalinsa baya ma kansu ,part dinsa ya shige ya sakarwa kansa ruwa xuciyarsa na wani irin halbawa......

Har sun shiga mota xasuje gidansu yaga ta fara hawaye meya sameki farhaa?"ya fada yana tsaida motar ya jawota yana lallashi yana share mata hawayen amma kamar karo mata su yake,pls ki fadamin ya fada cike da damuwa a fuskarsa ta kwantar dakai ajikinsa ta fashe da kuka.Bbu abunda ya sameni maheer kawai ina son nayi kuka ne ina jin yin kuka shiyasa nayi ,ya dago fuskarta yana share hawayen yake fadin kinga kuwa kukan nan sam baya yiwa fuskarki kyau.!"ya dago kanta yace kalleni nan ta dago idonta da sukayi ja ta kallesa ,kinga kin bata fuskarki kin rina kyawawan idanunki ,sam kuka baiyima fuskarki kyau pls ki daina....."banda abunki fatima wakejin yin kuka ko son yayi kuka haka kwae kuma sai yayi kukan ,banta ji ba sai akanki dole kukanki da dalili."shiru tayi batace mai komai ba ,ita kanta tasan bata kyautawa aiman ba ,batayi masa adalci ba.Yaya xatayi idan kaddara ta tsara masu hakan?"har suka isa gidan su maheer bata gama dawowa dai-dai ba....