11
by @asmybaliyu
Ganin trolley Daya wai Aiman yayiwa matar Yaya maheer tsaraba yasa Yasmin Tasha toka ,take fadin"Yah Aiman duk gidan Nan kafi yiwa Aunty Farhaa tsaraba,ta karasa maganar tana turo baki.kedai bakida godiyar Allah wlhi kema ba trolley Daya nayi maki ba,
"Ae wannan yafi kyau Kuma yafi girma ."mum ta jawota ajikinta take fadin"rabu dashi Autar mum bari kusa mu hutun makaranta mu tafiar mu umra baxaki yimasa tsaraba."ihu tayi tana fadin Ina sonki mum Dina."mum tayi Daria take fadin,"nima Ina sonki dayawa Yasmin."tsoki Aiman yyi Yana harararta yake fadin"mum duk ke Kika Bata yarinyyar Nan tana ganinta wata jinjira,yasmin ta masa gwalo .xai kaimata duka mum ta tare take fadin"ranka xai baci Aiman karka Dakar min yarinyya a xuciya Aiman yyi waje mum na kwala masa Kira ko juyowa baiyi ba,Yana jin Yasmin na fadawa mum ta rabu dashi ae xai dawo ya sameta ne.....
Fitar Maheer kenan aiman ya danno hancin motarsa bayan yayi parking sun gaisa da maigadi yake fada masa yanxu oga ya fita.nan Aiman ke tambayarsa madam fa?"ko tare suka fita danfulani ya girgixa Kai Yake fadin Tana ciki ,door bell ya shiga dannawa dama tana xaune a falon maheer tana karatun English novel a waya,tayi tunanin ko maheer ne yyi mantuwa da sauri ta nufi kofa ta bude xuciyarta ta kusan buguwa ganinsa tsaye agabanta,ya Kara kyau yyi kiba sosai sai ynxu ta samu ta masa kallon tsaf,xata rantse har yafi maheer kiba.wannan kallo fa Angel?"da alamar kinyi kewata dayawa batareda ta iya cemasa komai ba ta juya da sauri ,jin tayi ya cimammata da axamarsa yawani rungumota Yana sauke ajiyar xuciya gabanta ya Fadi kokarin kwatar kanta take ta kasa haka ya shiga shinshinar wuyanta Wanda kamshi ya gama kamawa....da wani irin karfi ta turasa cikin wata irin tsawa take fadin"baka da hankali Aiman matar Yayan naka kake runguma?"ta fada hawaye na cika a idonta ta juya masa baya jikinta na rawa haka tana kokarin tare hawayen dake son xubo Mata ,cikin rawar murya ta fara magana
"Aiman Nasan kayi fushi Dani Dana karya maka alkawari ,Kuma na auri yayanka nasan akwae ciwo ."kasa aranka bbu kaddarar aure a tsakanin mu ,ka fahimci wannan .a yanxu ina farin ciki da aure na bana son duk wani Abu da xai rushe rayuwar aurena ."yawan ganinka kurum ba karamin koma baya xai jawomin ba."Ina ta kokarin na manta ka dakyar na samu na binne ka acikin xuciyata ,idan na cigaba da ganinka ginin da na dde Ina ginawa xai iya rushewa."Aiman kallo Daya xakayi min na tsinci kaina a wani yanayi Wanda bana fatar yanxu na shiga ,saboda yanxu inada aure halakace duka agaremu sabida ynxu Ina da aure ,, Aiman aduk lokacin da muka hada ido bana sanin meke faruwa Dani ina fatan ka fahimici matsalata?"Ina son naceci rayuwar aurena na cecimu daga halaka ,Allah ubangiji ya baka matar da tafini Allah yasa idan kunyi aure ta kula dakai sosai ta nuna maka so sosai kamanta baya kamanta komai kayi rayuwar farin ciki."idan haka ya faru xanyi murna xanfi kowa farin ciki,da axama ta nufi kofar master room din maheer ,jin tayi an fisgota ta fada jikinsa tana jin yarda Cikin jikinta yayi wani irin juyawa da wani irin Yanayi a fuskarsa Yake kallonta ,haka hawaye na xuba a idonta .da haka kikeso naje na auri wata na manta ki?"bancin Nasan har yanzu akwae soyayyata acikin xuciyarki ."da sauri ta shiga girgixa masa Kai hawaye na xuba a idonta take fadin bbu pls kafita a rayuwar aurena ina son maheer ban taba son wani adunia ba sama dashi baya ga iyayena."Kalmar ba karamin taba Aiman tayi ba,wata irin Daria ya fashe wata bbu farin ciki acikinta "kin samu farin ciki ni Kuma kiyi Yaya Dani?"Ya maheer bai dace dake ba ko kodan Farhaa,bbu namijin da yadace da rayuwarki sama Dani."na baki Nan da sati biyu ki kashe aurenki kixo mu shimfida sabuwar rayuwa ,ko Kuma ni na kashe Auren da kaina."kalamansa sun girgixata ,A fusace ta fisge rikon da yayi mata tana binsa da wani irin kallo.daria ta fashe dashi lokaci Daya take fadin"Aiman bakada Hankali ko kadan a tsawace yake fadin naji Banda hankali indai akanki ne,idan bakiyi abunda nakeso ba wlhi kinji na rantse wannan Auren naku xan kafa tarihi xaki Sha mamaki na."ta fisge kanta daga hannunsa da gudu ta nufi master bedroom din maheer...ta murxa key anan ta xube kasa tana wani irin kuka ,tasan Halin Aiman duk abunda yace xai aekata tasan xai aekata dagaske din...ta yanke shawarar maheer na dawowa xata fada masa ,
Baxaki barni ba wlhi baxaki barni ba."ya fada Yana maida numfashi da axama ya nufi fridge din dake cikin falon Yana budawa yaga ruwane aciki da Kuma fresh milk kwara Daya tunani ya hauyi can ya saki murmushi fresh milk din ya dauko ya Buda yayi saurin fiddo da pills kwara biyu ya saka ya maida ya rufe ,kurawa robar ido yyi tamkar mai son gano wani Abu aciki lokaci Daya Kuma ya saki murmushi ya maida ,
Ya juya ya dauki trolley ya tsaya a master bedroom din maheer ya shiga buga kofar yake fadin ."Heart kifito ga tsarabarki ki dauka kinji."yyi maganar cikin sanyi murya banxa tayi dashi haka ya cigaba da dukan kofar Dan kansa ya juya yabar gidan ,Nan da wasu ya'n awanni damuwarsa xata fara ragewa....