12
by @asmybaliyu
Bata san tafiar Aiman ba,itama anan ta bingire sai barci cike da mugun mafarkin Aiman din,gashinan ya biyota da wuka xai kasheta....agigice ta farka xufa sai xubar Mata Yake ta koina , addu'a ta fara jerowa haka gabanta ya cigaba da faduwa.dakyar ta mike tsaye toilet ta nufa ta wanke fuskarta da bakinta ta kalli agogon bangon dakin Sha biyu harda minti goma Sha biyar na Rana,wani irin juyawa cikinta keyi yunwa takeji sosai......Kai tsaye kitchen ta nufa Dan ta samu abun motsa baki ,samota ta fitar cikin fridge cikin minti goma ta soya kwaya biyar ,ta xubo ama dai-dai cin plate fridge ta bude ta dauko ruwa Daya ,Nan idonta ya sauka kan mutumin nata wato fresh milk mayarda ruwan tayi ta dauki fresh milk falo ta koma ta kunna t.v.cikin tashar(NOVELA MAGIC)Wanda suke haskaka firm din (Halita)daukar waya tayi tamkar ta Kira aunty Maryam ta fada Mata Aiman kanin maheer ne,sai Kuma wata xuciyar ta fada Mata ta fara Kiran maheer.sai da ta kusan katsewa sa'anan aka daga
Hi babe!"ya fada sounding so swt wara ido tayi kafin ta Ciro wayar a kunnenta ta duba Wanda ta Kira lambar maheer ta Kira,to ya akayi aiman ya daga?"xaiyi magana ta katse Kiran duka ,wani kunci Yana mamaye xuciyarta ahankali Bata San lokacin da Aiman ya xama mugun mutum ba."Fresh milk rabi kawai Tasha taji wani irin tashin xuciya da gudu ta nufi toilet tana xuba wani irin amai........tamkar xata fitar da duka hanjin cikinta gaba Daya ta fita hayacinta ta gama galabaita ,dakyar ta dawo falo Kara Kiran wayar maheer tayi jin tayi mararta na wani irin juyawa tamkar xata fito waje,tana jin lokacin da maheer ke magana .Amma axaba ta hanata amsa sa,
Cikin minti biyu jini ya fara bin kafafunta addu'a kawae take karantowa gaba Daya ta fita hayacinta......
Shikuma maheer fitowarsa kenan daga (theater Room)ya cimma Aiman a office dinsa ,anan Yake fada masa Farhaa ta Kira ya amshi wayar ya Kira sai dai Taki magana Kara dialling call din yyi akaro na biyu wannan karon Bata daga ba,maheer ya kalli Aiman Wanda hankalinsa duka Yana kansa,na Kira Taki picking call dina inaji ajikina bbu lfy Aiman bara nasa kayana muje gidan,
Shaye da toka da turo baki Aiman ke fadin kana son wannan Farhaa din dayawa."murmushi kurum maheer yyiwa kanin nasa kayansa kawae ya canja suka tafi ,a mota ma sai fada Yake yiwa Aiman yaki sauri.aiman gaba Daya haushin yayan nasa yake ji ,karshe maheer ya karbi tukin.......kowane second bugun xuciyar maheer fita yake ,door bell ya shiga dannawa shuru yaji mota ya koma ya dauko key yayi amfani dashi......xuciyarsa yaji tana neman tsinkewa da wani irin mugun gudu ya cimmata jini ya gama Bata koina a falon,
Ya dagota Yana Kiran sunan ta agigice ko motsi batayi ,ya kalli Aiman Wanda kamar an dasa sa a wurin Yana hango mahaukaciyar soyayyar da dan uwansa Yake yiwa Farhaa dinsa ,a kidime shima Aiman ya karaso xuciyarsa na harbawa ganin yarda take fitar da jini baya son ya rasata wlhi,
Muje Asibiti Yaya!"Aiman ya fada a rude ,Aiman din ya dagata xuwa mota kafin maheer yabi bayansa...wani irin gudu Aiman yake yi Wanda ya daga hankalin maheer din,cikin tsawa maheer ke fadin ka natsu Aiman kayi tuki da kyau."ko kulasa baiyi ba burinsa Yakai farhaaa Asibiti baxai iya hakurin rasata ba..
Dakyar Dr.Jaleel ya samu ya tsayarda jinin Nan Kuma suka fara kokarin ceto rayuwarta,maheer Yana tsaye kamar gunki Yana ganin yarda ake Danna kirjin Farhaa,sai lokacin wasu irin hawaye masu xafin gaske sukayi nasarar xubowa akan fuskarsa , addu'a Yake Allah ya tashi kafadun Farhaa dinsa idan bbu ta baxai iya Rayuwa ba.An samu dai-dai tuwar numfashinta sa'anan aka gwada jinin maheer xaiyi dai-dai da nata aka diba, aka Kara Mata sabida ta xubar da jini da yawaa,maheer Yana dakin hutu ya kasa runtsawa har allurar barci akayi masa still idonsa biyu...Aiman na xaune agefensa knocking yaji bakin kofa yasan mum ce ta karaso da sauri yaje ya bude Mata ,mum agigice ta karasa gaban gadon maheer din.Riko hannunsa tayi tana masa magana cikin rarrashi.....ta kalli Aiman take fadin "ina Farhaa din?"hop jikinta da sauki,cikin sanyi murya Aiman ya fada Mata da sauki (miscrage )ne ta samu
Yana kula da mum ko kadan Bata ji ddi ba, aransa Yake fadin"am sorry mum nayi hakan ne Dan farin ciki na,
Fita waje yyi Yana sauke ajiyar xuciya ,ya samu ya gama da plan (A) sauran plan (B) dinsa sai kusan magrib Farhaa ta farka lokacin maheer na gefenta da Kuma Aunty Maryam ,hawaye na cika idonta take fadin"ya xube ko maheer?"
Maheer ya jawota ajikinsa Yana Dan buga bayanta ,
Aunty Maryam ta Dan ja tsaki cikin jin haushinta take fadin "ka daina lallashinta pls maheer Dan taga ana rarrashinta shiyasa take wannan sangartar. Allahn da ya baki shi ya xabi ya rabaki da shi."idan Kika sa hakuri xai baki wani,rada maheer ya shiga yimata a kunne kina son wani baby?"ki samu sauki mu koma gida a samu wani....."ya fada Yana shafa cikin nata ,shi maheer bbu ruwansa ko kunyar aunty mrym baya ji,dakyar Tasha tea.umma da Abbanta suma sunxo sun dubata ,kwanan ta biyu maheer shike kwana daita ta Dan samu sauki sa'anan suka sallameta Kai tsaye gidan su maheer suka sauka ,Wanda umurnin mum ne abari sai ta Kara samun sauki.......kowa na gidan su maheer yana Mata sannu Banda Aiman Wanda da ya ganta xai wani hade Rai.satin ta Daya ta koma gidanta ,
Tana kwance kan jikin Maheer taji Yana waya da Aiman Yana masa fada,
"Haka kurum saboda aboki ka kwashi jiki kaje har (kogi state)idan daddy yaji kashe ka xaiyi bbu ruwana wlhi!"maheer ya fada sounding so very serious,Ina jin dariar Aiman din ta cikin waya,
Naji maheer na fadin kwana biyu kawae xakayi ka dawo kana jina?..sa'anan ya kashe wayar Yana shafa gashin kaina Yake fadin Aiman na gaisheki wai Yana kogi state."Ni dai shuru na masa,
Nayi gyaran murya nake fadin maheer !"na Kira sunan sa cikin wani irin Yanayi ,dama akwae maganar da nakeso muyi dakai."Ya subbaci bakinta Yake fadin uhm!"Ina jinki ya cigaba da aika Mata da xafafan kisses Wanda suka hanata magana ,cike da shagwaba take fadin plz maheer magana fa xamuyi ,ba yanxu ba my bby wife." ya fada Yana cire rigar barcinta ,kukan shagwaba kawai ta saka masa ganin yaki bari tayi magana.....
Kogi state.....
Cross ya kamata mutafi ynxu na matsu burina ya cika."Anya Aiman kana iya wannan aekin?"shaye da toka Aiman ke fadin mexai Hana inhar xan samu abunda nakeso ,daria cross yayi Ina fatan account Dinka akwae kudi dayawa."ya fada cikin harshen turanci ,
Idan bani da kudi ya xaayi inxo Nan Don ubanka!"Kai kasan koni waye!"salute dinsa cross yayi Nan Aiman yayi masa transfer din 100k agigice cross ke kallonsa ,ka kaini wajen wanna bokan idan Naga aekinsa yyi yarda nakeso xan baka kyautar 1million ,cikin ihun murna cross ya daga Aiman sama Yana xagaye dakin dashi .
Muje na sauka hotel na samu abunda naci na watsa ruwaa sa'anan mutafi ,
Tare suka fita cross ya Goyasa akan babur ya kaisa hotel ya biya kudin kwana biyu ,Nan cross ya jirasa ya watsa ruwaa .yayo masu oder din takeaway,ba wani cin Abinci yayi ba ,burinsa ya gansa gaban wannan (hatsabibin bokan)Aiman har ya gaji da tafia cikin dajin sai masifa yake yiwa cross tunda yake a Rayuwarsa bai taba tafia irin wannan ba ,gaba Daya ya gama galabaita sai xagin cross Yake ta uwa ta uba da harshen turanci.....