MAHEER

13

by @asmybaliyu



Wurin fili ne sai wata Yar karamar (bukkah)dake tsakiyyar filin tun kafin a isa Aiman ya fara jin xuciyar sa na wani irin tsinkewa...tsayawa yyi cak!"da mmki cross ke kallonsa cikin harshen turanci yake tambayarsa meya faru"cikin sanyi murya yake fadin mukoma kawae Cross na fasa."

Cikin xaro ido cross ke fadin ."mun iso fadar sarki bamu isa mu juya ba,,Aiman xaiyi magana sukaji wata irin tsawa haka suka ji wurin ya soma juya masu .daganan basu sake sanin ya akayi ba,farkawar da sukayi suka gansu cikin wani irin daki mai duhu Wanda ko tafin hannunsa basa iya gani,cikin mintuna biyu Kuma sai ga haske ya bayyana.wani irin mutum suka gani a gabansu mai wani irin tsawo Wanda tunda Aiman yaxo dunia bai taba ganin mutum mai tsawo da kauri kamarsa ba,gaya da wasu irin mayyan idanuwa masu ban tsoro ,wani irin fashewa da Daria sarki yayi Wanda yasa dakin ya shiga girgixa........"meyasa xaku koma?"ka daina sonta kenan"ya maida alakar tambayarsa kan Aiman ,a hankali Aiman ke fadin"Ina sonta Mana ,inhar xaka taimaka min na sameta xan baka duk abunda kakeso sarki."

Wani irin Daria sarki ya fashe daita ,ya murxa hannunsa saiga katon mirror ya bayyana a hannunsa dauke da hoton Farhaa da Kuma maheer ,kana son matar yayanka dayawa."A hankali Aiman ya shiga daga Kai tamkar kadangare ,

Murxa hannunsa sarki ya Kara yi a karo na biyu mirror din ya bace bat a hannunsa.

"Mekake so ayi da Auren su ?"wani irin murmushi Aiman ya yayi kafin yace ina so ya saketa na aureta sarki."ya fada sounding so very happy."a hankali sarki ya rufe idonsa ya shiga surutu yafi minti biyar a haka kafin ya bude idonsa agigice yake kallon Aiman Wanda shima hankalinsa duka Yana kansa,

"Yayanka baxai iya sakinta ba,haka kaima baxaka iya aurenta ba."cike da tashin hankali Aiman ke fadin"meyasa sarki."

Akwai kariya sosai ajikin yarinyyar Wanda tun tana karama take dauke dashi ,Abu na biyu yayanka Yana da ibada sosai haka Kuma Yana son yarinyyar Nan fiye da son da kakeyi Mata."wani irin bakin ciki Aiman yaji akasan ransa Taya xaa ce maheer Yafi shi son Farhaa.?"Hanya Daya ce xaka samu wannan yarinyyar."sarki ya fada Yana yiwa Aiman wani irin murmushi,

Wace hanya kenan?"

Aiman ya tambaya batareda ya kalli sarki ba,Yana ji ajikinsa bbu nasarar samun Farhaa.xata xama taka yarda kakeso a Kuma duk lokacin da kaga dama ,haka xaka juya yayanka daita yarinyyar Wanda bai isa ya rika koda hannunta ba.muddin kana a wuri."gaba Daya kan Aiman ya daure baya fahimtar mai sarki ke nufi ,sai cross ne ya shiga yimasa bayani cikin harshen turanci......Wani irin kallo yake yiwa cross kana nufin na rika xina daita Bata hanyar aure ba gaskiyya nooo!"ya fada cikin fushi da alamar ya manta a inda Yake,karya kake Yaro baa yiwa sarki musu,haka idan akaxo wurin sarki baa komawa sai da biyan bukata .'"idan Kuma kaki ,yarinyyar Nan xata mutu!"agigice Aiman ke kallonsa sarki ya shiga gyada masa Kai Yana wani irin murmushi.........na baka minti biyar kayi shawara anan ya bace masu bat.!"

Agigice ya juya kan cross cikin rawar murya Yake fadin kana jin meyake fada?"A hankali cross ya dafa kafadan sa yana fadin"haka aikin sarki Yake idan akace a juya to tabbas xai dauki rayuwar Wanda akaxo dominsa."cikin tashin hankali Aiman ke fadin"meyasa baka fada min ba meyasa Cross,,na hakura da Farhaa inhar xan rika samunta ta hanyar xina ."saboda ba irin wannan son nakeyi Mata ba,,haka Kuma bana son tabar duniyar Nan saboda Ni."dole ko kayi abunda sarki keso muddin kana son kaceci Rayuwarta,naceci Rayuwarta Kuma na saka Rayuwarmu cikin mummunan kaddara!"wlhi nayi da na sanin Farhaa a rayuwata."minti biyar sarki ya bayyana ,

Ya kalli Aiman yake tambayarsa ya ake ciki akwae inda yakeso yaje."da sauri cross yace sarki ya amince wani irin murmushi sarki yayi ,

Yana buga hannunsa saiga xoben axurfa ya bayyana fari Kal!''wannan xoben xai baka farin ciki fiye da tunaninka, muddin kana tare da wannan xoben yayanka bai isa yayi maka musu ba,haka ma matarsa,ko agabansa xaka kwanta da matarsa komai baxai ceba."umurni yyiwa Aiman yabasa hannunsa na haggu ya saka masa xoben ya rike hannun ya runtse ido Yana karanto wasu kalaman tsafi a hankali Aiman yaji hankalinsa na tafia bbu abunda ke cikin xuciyarsa sai hoton Farhaa ,

Wani irin xabura yyi gamida kwalawa Farhaa Kira,

Ahankali sarki ya saki hannunsa Yana wani irin shu'umin murmushi ya kalli cross Yake fadin"Abokin ka ya dawo Nan da two weeks idan yaga aiki yyi kyau haka xai xo da naira miliya biyu cash.........daganan Ya shafa masu kyalle sai gasu a bakin Titi ,

Wani irin ciwon Kai Aiman ke fama dashi Wanda baisan ko na menene ba,sai da cross ya raka sa hotel ya nufi gida akan gobe xasu hadu....

★★★

Wata irin shagwaba take xuba masa ta wani narke ajikinsa ,

"Haka kawae kin hanani xuwa office ,ta gyada Kai tana wara ido tana fadin." yau Ina son wannan tym din ya kasance nawa Ni kadai  doctor ....."murmushi yyi Yana shafa hancinta Yake fadin"kice yau Ni na xama dangata ?"dage gira Daya tayi tana fadin fiye ma da wannan sunan"ko Abinci yau maheer ya hanata shiga kitchen sai dai suna yin wanka suka fita ,a restaurant suka tsaya suka ci a Abinci 

Saanan suka wuce clinic ,sai kusan 5:30pm.suka bar clinic maimakon su wuce gidan su ,Farhaa tace Bata San xancen ba.shopping sukaje sukayi ,haka ta saka shi yawo cikin gari kallo Daya xakayiwa maheer kasan yau ya gaji.........Ana sallar magrib suka nufi gidansu Maheer har ishaai suna gidan ,

Sai da akayi dinner dasu kusan 10 suka nufi gida wanka kawae sukayi sukabi lfyr gado Nan maheer yace bai San xancen ba,,akanta xai huce gajiar da tabasa a ranar yau.sai shagwaba take xuba masa tana fadin barci takeji , hka maheer yaki saurara Mata sai kusan 2 sukayi barci....