14
by @asmybaliyu
Feeling Disgust..
Wani irin barci yakeyi Wanda tun da yaxo dunia bai taba yin barci irin wannan ba ,kusan karfe bakwai na safe cross ya rika buga masa kofa tamkar kansa xai fita saboda nauyin da yyi ,dakyar ya budewa cross kofa.kallo Daya cross ya masa ya gane barci yakeyi......"Am going to kill you cross,ya fada sounding so pissed up
Tym na tafia Aiman ko ba yau xaka koma kano ba."Ya fada Yana kallonsa,batareda Aiman yace komai ba ya Mike ya nufi bathroom,yafi minti ashirin a toilet Koda ya fito still cross na xaune dakin Yana Danna wayarsa kallo Daya Aiman yayi masa ya dauke Kai ,Yana gama shirinsa yasa aka kawo masu break fast ,shuru dakin yyi bbu mai magana acikinsu sai Kara spoon's dake tashi ,wata ajiar xuciya cross ya sauke .Yana kallon Aiman Wanda har yau yaki cewa komai ,Ni naga kamar baka cikin walwala ko kadan .bakayi murnar xaka samu abunda kakeso ba."wani kallo Aiman ya shiga yimasa still yaki cewa komai , Yana gama Shiri kayansa ya fadawa cross Yana so ya kaisa airport yanxu .cross na ajey sa a airport ya juya yana kallonsa da dukkan kwarin gwiwarsa cikin harshen turanci Yake fadin"karka yarda a samu matsala Aiman ,baka San waye sarki bane......."xai iya kashe yarinyyar Nan ,yau ranar farin cikin Kane dude chill and be happy Mana."Ya fada Yana ware masa ido lokaci Daya Aiman ya saki murmushi Yana ware hannunsa duka biyu batareda ya iya fadar komai ba,cross ya rungumesa Yake fadin "ka sauka lfy sai munyi waya,Aiman ya daga kansa Yake fadin"da na isa xan turo maka sako a account dinki.. please Banda shaye-shaye da caca.shafa kansa cross kawae yyi sai da jirginsu Aiman ya daga sa'anan yabar wurin....karfe goma maheer ya fito cikin Shirin xuwa office da mmki yake kallonta tana kwance a falo ta dunkule kanta wuri Daya ,doguwar rigace ajikinta kalar (Ash colour)marar hannu haka Bata da nauyi ,sai gashin kanta da tayi parking dinsa a tsakiyyar kanta ,da kallo ya bita kafin yyi gyaran murya mikewa tayi xaune tana kallonsa da shanyayyun idanunta .ya xauna gefenta gamida jawota ajikinsa,
"Meyasa baki shirya ba kin fasa xuwa gidan umma ne."cikin sanyi murya take fadin ,bana jin xanje yau ya bude ido Yana kallonta da ido Yake tambayarta meyasa?"ta daga kafada take fadin bana jin ddine?"da sauri Yakai hannunsa kan goshinta sanyi yaji sosai a wajen,
"Amma jikinki bbu xafi bby,na sani doctor kawae bana jin ddine tunda na tashi gabana ke faduwa na rasa dalili"Ya langabar da kansa Yana kallon kyawawan idanunta Yake fadin"komai xaiyi dai-dai kiyi addu'a,ta tsaresa da ido tana kallonsa still kirjinta na bugawa ta kwantar da kanta gefen kafadarsa take fadin"Am scared doctor am very scared."Shuru yyi Yana shafa gashin kanta yake fadin bbu abunda fa xai faru ,kiyi hakuri ki shirya xan ajey ki wajen umma idan na fito clinic sai naxo na daukeki,
Can xakifi samun kwanciyyar hankali,
Shiya taimaka Mata ta shirya har lokacin ranta a dagule,
Mota sai Hira Yake Mata ita dai duk hankalinta baya kanta,
Yana ajeyta a kofar gidansu ya juya ya wucewarsa,motar tabi da ido.jikin sanyaye ta shiga get din gidan nasu motar Abbanta na a wajen da alamar baifita kasuwa ba,sai Kuma motar Yah Abkar da alamar Yana gari,Dan yanxu a kaduna Yake aeki dadynsu maheer ya masa hanyar samun aeki.........sallama tayi a babban falon gidan ,
Abbanta na axaune Daya daga cikin kujorun falon ummanta na a axune a gefensa tana hada masa tea,dukansu suka daga kansu suna kallonta haka lokaci Daya suke amsa gaisuwarta,
Kuruwa abban nata ido tayi na Dan sakanni sai taga ya rame haka idanunsa sun Dan fada.da sauri ta karasa wurinsa ta xauna gefensa gamida kwanciya ajikinsa hawaye suka taru a idonta haka taki magana,baki sake umma ke kallonta Dan Allah dagasa yasha tea sai kace karamar yarinyya."umma ta fada tana hade Rai hawaye suka xubo Mata cikin rawar murya take fadin"bbu Wanda ya fadamin Abba bayada lfy tun yaushe?"ta fada still hawaye na xubo mata,da sauri ta dago kanta tana kallon abban ta take fadin"Abba baka da lfy tun yaushe"Ya shafa kanta da murmushi a fuskarsa Yake fadin "mura fane tun last week na samu sauqi mijinki na xuwa har gida ya dubani Alhmdullhi sauki na xuwa."karki damu mamana na samu sauki ,ta turo baki take fadin"shine yasan baka da lfy "he did not even tell me"tayi maganar so pissed up gamida turo baki,
Abba yay murmushi Yake fadin ni na Hana ya fada maki."tana Dan bude ido take fadin"to meyasa Abba."Abkar ne ya shigo da sallama Yana gaisheda iyayen nasa,
Saukar yaushe Yaya?"
Jia Nan naxo ya kk ya maigidanki."muna lfy duka.....Yar Hira suka taba ,kafin yabar gidan har kusan 2 tana tareda Abbanta....
A kitchen ya samu Yasmeen tana Taya mum aeki tsaye yayi bakin kofa Yana wani hade Rai ,tun dawowarsa mum batayi masa kallon arxiki ba,harkokin gabanta kawae takeyi
"Mum ina jin yunwa.
Ya fada Yana kallonta,
Ko kallonsa mum batayi ba,bayason wannan fushin Yana Bata masa Rai ,
A hankali yayi hugging dinta "Am sorry mum ba gashi na dawo ba nifa ba Yaro bane mum."A fusace ta juyo Dan ubanka sakeni tunda Kai ba yaro bane kaje kayi duk abunda ka ga dama Rayuwarka."jikinsa lokaci Daya yyi sanyi
Ficewa tayi daga kitchen din duka ,
Da kallo ya bita yaci sa'a daddy baya gari da abun xaiyi masa yawa Amma xaiji da mum xuwa Anjima car key kawae ya dauka ya fice daga gidan gaba Daya.....