14
Ganin ina ta cuku-cukun saukowa daga babur d'in ne yasa da sauri ya fara taimaka mini amma duk da hakan sai da salansar babur din ta k'ona ni a wajan 'kwaurin 'kafata, na sauko ina yamutsa fuska, shi kuma da sauri ya kafe babur din, hannunsa rike da akwatin kayana duba gurin dana 'kone d'in janyewa na dinga yi domin gabadaya haushinsa na ke ji ganin abinda yake wai lallai sai ya ga gurin, wayarsa ya kunna yana haskawa.
A daidai lokacin Bahago ya fito daga cikin gida ya riske mu a haka ina tsaye Uncle Sadiq din na gurfane a gabana ga zanina a tattare dalilin k'onewar da na yi yasa na tattare zanin.
Ganinsa ya sanya ni cikin fargaba, sai kuma na tuna alkawarin da ya yi mini cewa; Zai fita daga rayuwata har abada.
Yana zuwa bai yi wata-wata ba, yasa 'kafarsa dake cikin kambos ya buge hannun Uncle din katuwar wayarsa mai tsadar gaske ta yi tsalle ta fada cikin kwatar dake gefen mu.
Cike da mamaki Uncle din Ya kalle shi.
"Ali kan ka daya kuwa?" Ya fada yana kallonsa zuciyarsa cike da jin zafin abinda ya yi masa.
Tsaki ya ja mai tsayin ya kama hanya ya bar gurin cikin tsananin bacin ran dana gani a tare da shi. Ni ma ban yi wata magana ba na dauki akwatina na shige gida domin shi kansa Uncle Sadiq din haushi yake ba ni saboda abubuwan da yake aikatawa, ina zargin dai yana cin amanar Anti Hamida domin duk ga alamun rashin gaskiya nan ya bayyana a tare da shi.
Bahago kuwa wani matashin saurayi ya turo da wata kibiya mai tsinin gaske lokacin da Uncle din yake kokarin dauko wayarsa da ta tarwatse a cikin kwata, a sannan saurayin ya sanya kibiyar duk ya caccaka masa a tayar babur din, da sauri ya bar gurin bayan ya gama abinda aka sa shi, A takaice dai Uncle da turi ya je gida domin ko da ya fita titi masu faci sun tashi haka ya dinga tura babur din ransa idan ya yi dubu ya 'baci! Bahago ya janyo masa asara wayarsa dubu dari da tamanin ya saya amma ta tashi daga aiki, kawai don yana jin nauyi ne amma wallahi da sai ya hukunta yaron, haka ya shiga gidansa cikin k'unci da takaici mai tsananin gaske.
Ashe da sauran rina a kaba domin yana shigowa gidan, ya hargitse da hayaniya ganin yana 'kokarin ya yi mini sharri yasa Na ce.'' Wato ka 'dauka abinda ka ke aikatawa kowa ma haka yake, to Allah ya sawwak'e ya tsare ni da aikata zina, kaima ina rokon Allah ya shirye ka."
Duk da na kauce sai da dukan da ya kawo min ya same ni a gefen kafad'ata! na mike tsaye tare da rarumar wani kwanon sha mai nauyin gaske na jefa masa ya sauka a goshinsa. Tokar ta rushe da kuka tana kiran "Ya Wahidun Ahadun ka shiryi zuri'ar Malam Zangina mai 'yan makaranta, Ni 'yasu ya zanyi da rayuwata yara za su kashe kansu.'' Kuka take tukuru! Hawaye na zuba majina na dulala!
Ya tsallake kafarta ya nufo ni da zafinsa!
ganin idan na tsaya zai iya yi mini illah ya sanya na fara 'kokarin guduwa domin ceton rayuwata, amma sai da cimma mini, ya shak'e mini wuya ido jawur! yake magana. " Waye ya ce ki hau babur d'insa?"
Kamar mahaukaci haka ya zama ya tara zufa! jikinsa sai kyarma! yake.
Ido kawai na zuba masa babu halin magana tunda ya sha'ke mini wuya watakila kashe ni yake so ya yi, duk sambatun surutan da yake yi ba na fahimtar komai.
Sama-sama na ke jin maganar Kawu 'Danjuma shima Allah ne ya dawo da shi gidan a lokacin, da k'yar, ya kwace ni daga hannunsa.
Rungume shi nayi ina kuka tare da kiran Innalillihi wa'ina ilaihi raji'un.
Ya zaunar da ni a kusa da shi yana tambayata, na kasa yin magana tsoro da fargaba sun gama kashe mini jiki, gabadaya duniyar ta fice mini daga rai, cikin zuciyata nake raya cewa watakila Bahago shine ajalina.
Ya kalli Tokar dake ta koke-koke! sai surutai take marasa kan gado da ma'ana, Ya ce." Tokar kada ki yi sa'bo don Allah ki yi mini bayanin abinda ya faru."
Kafin Tokar din ta yi magana shi ya rigata cikin fitar hayyaci yake fada masa wai iskanci nake da maza ya ga ni da idonsa wani gardi ya kawo ni a babur na tattare masa zanina yana haska jikina da wayarsa."
Ina kuka Na ce." Ka ji tsoron ALLAH yanzu Uncle Sadiq din ne gardi? YA ZA'AYI na yi iskanci da mijin 'yar uwata, wannan sharri ne kake kokarin yi mini."
Ya fara rantsuwa da k'arya yana kara tabbatarwa da Kawu D'anjuma maganar. Sai kawai na dinga kallonsa ina mamakin sharrinsa 'kiri-'kiri ya lauya maganar, amma na san ko daga bacci ya ta shi zai sheda fuskar mijin 'yar uwarsa.
Kawu 'Danjuma Ya ce." Bari na kira Sadiq din na ji komai daga gare shi." Ya fito da wayarsa daga cikin aljihu yana ta gwada kiransa sai ace masa wayar a kashe take.
Ya ce." Kawu Yanzu ka gazgata maganata ko?" ai ba yaro ba ne ni, kuma na san Sadiq sosai, wannan dogo ne baki, shi kuma mijin Anti Hamida gajere na mai kiba kuma fari, don haka duk cikin maganata babu sharri ko 'kage!"
Kawu ya waiwayo kaina fuskarsa ya murtuke Ya ce." Jamila abinda za ki yi mana kenan?" Shiru kawai na yi hawaye na bin kumatuna, bakina ya mutu murus! na rasa a wane mizani zan ajiye wannan al'amari, kiri-kiri ana kokarin kulla mini sharri.
Gabadaya haka muka kwana da bakinciki da damuwa, dan Babana ma da ya dawo daga gurin sana'arsa ya samu labari bai d'ora laifin akan kowa ba sai akaina, Kawu Sammani ne kawai yace shi bai yarda da zargin da ake mini ba dole sai ya bibiyi al'amarin.
Washe gari da kansa ya nufi gidan Anti Hamidan domin jin karin bayani daga gare ta.
Sosai ta ji takaicin abinda Bahagon din ya aikata wato iskancin nasa ya wuce kanta ya koma kan mijinta, sharri zai yi masa, haba shiyasa ta ga ya dawo gidan fuskarsa babu walwala ashe abinda ya faru kenan.
Da Kawu ya dawo gidan ya sanar da 'Yan Uwansa gaskiya lamari, Kawu Danjuma ya yarda kuma ya ji haushin hakan a cikin ransa, amma Babana bai nuna yardarsa ba, a cewarsa wai ba'a shedar mutum tunda na kai munzalin aure shekara ashirin da biyar to komai zai iya faruwa, kafin na d'auko musu abin kunya zai yi k'o'karin aurar da ni, wannan maganar ta daga mini hankali sosai! na shiga damuwa mai tsanan da adduar Allah ya kawo mini mafita a rayuwata.
Na shiga zullumi! babu wanda ya damu da damuwata sai Baba Iyami, ita ce ke dan kwantar mini da hankali a duk lokacin da na shiga gurinta, amma Tokar da Baba Hama yanda na fahimta kamar suna farinciki da halin da nake ciki.
Sai na yanke shawarar zuwa gurin Mamana domin samun sassauci. na nemi izini a gurin Tokar ta ce na tambayi Babana ita bata da hurumin bari na fita tunda ga irin abubuwan dana fara.
Na kalleta ina jin wani abu mai nauyi a makogwarona Na ce."Tokar har yanzu zuciyarki tana zargina ko? a gabanki fa na rayu kin fi kowa sanin halina ashe za ki iya yarda da wannan sharrin? wallahi Allah ne daya ban aikata komai ba Bahago 'kage ya yi mini."
Jikinta a sanyaye ta ce." Jamila ba'a shaidar mutumin yau kamar yanda babanki ya fada kin kai kin kawo, gaki nan tubarkallah nono cike a kirjinki, a yanzu babu abinda ki ke bukata sai namiji don haka ni ba zan amince da maganarki ba."
Girgiza kai na yi tare da cewa; Wannan ba hujja ba ce Tokar, kada ranar lahira Allah ya tsayar daku domin ku nuna masa shaida akan abinda kuke zargina da aikatawa wallahi ban ta'ba sanin wani da namiji ba tunda nake, kuma kin san sharrin zina yana da muni! wallahi ban aikata ba, ku daina zargi na sharri ya yi mini.
Shiru ta yi tana kallona da alamun rusuna a tare da ita.
Na ce." Kiyi hakuri ki tambayar mini Babana ya bar ni na je kin ga na kwana biyu ban je ba."
Shiru ta yi ba ta ce komai ba ta dauko goronta tana gurzawa.
Da asuba ina kwance ya shigo dakin kamar yanda ya saba suka gaisa, na ta shi zaune na gaishe shi, ya amsa ba tare da nuna kulawa ba.
Sai na koma na kwanta jikina duk a mace, wato Babana ya fi kaunar Bahago da ni, tunda ya kasa fahimtar matsalata.
Ina jin Tokar tana rokar mini shi ya bar ni zuwa gurin Mamana yana turjewa tare da kawo hojjoji. wai dole idan ina so na je sai dai Bahago ya kai ni, don ba zai lamunci tafiyata ni kadai ba.
Tokar din ta nuna yardar ta akan hujjarsa.
Bayan fitarsa take sake jadadda mini maganar. Na ce." To shikkenan sai mu je tare da shi din, idan ya shigo sai ki fada masa.
Muna karya kummalo ya shigo dakin yana tambayarta ruwan zafi zai yi wanka. Ina jin tana tambayarsa wankan me zai yi da sassafe! sai ya rufe ta da fad'a wai mai yasa take masa kutse a cikin al'amuransa.
Da yake tana jin tsoron b'acin ransa ta 'dauko fulas dinta da ruwan zafi a ciki ta mika masa ya kar'ba ya fita daga dakin.
Bayan minti talatin ya sake shigowa cikin gayu sai kamshin turare yake mai sanyi, saurin dauke kaina na yi daga gurin da yake tsaye don tunda al'amarin ya faru wata magana bata sake shiga tsakaninmu ba sai dai kallo.
Ta ce." Ka yi kyau sai dai bana son wannan sarkokin na wuyanka ka da fa ka manta kakanka babban Malami ne a cikin garin nan."
Ya ce." Ni ma malami ne, sanya sarkoki ba shi ne yake nuna zahirin mutum ba, tsoron Allah a zuciya yake."
Sai ta girgiza kanta da cewa; Dama Babanku Danlami ne ya ce wai za ka kai Jamila gidan Babarta saboda yana jin tsoron faruwar wani abu.
Ya ce." Hakan ya yi, amma sai da daddare don yanzu ina da uzuri." Da sauri ta ce " To shikkenan Allah ya kaimu lafiya."
Hanya fita ya nufa yana taje tarin sumar dake kansa da mataji.
To tun yamma na yi wanka na kimtsa jikina, na kalleta da cewa." Tokar ko na tafi da kayana kala biyu sai na kwana a can."
Kai ta girgiza lokaci guda ta murtuke fuska, "Ina lefi ma ku gaisa ki dawo gida, zaman me za ki yi a gidan mutane."
Ganin yanda ta cukune! fuska yasa na bar maganar ban sake cewa komai ba, har akayi isha'i bai shigo ba.
Sai wajan tara shaura sai ga shi wai na fito mu tafi, Tokar ta ce" Anya kuwa dare bai yi ba?"
Ya ce." Babu wani dare ai motar abokina za mu je."
Ta ce." Da sauki tunda a motar gida ne.
Ba tare da ya kalle ni ba Ya ce." Ki fito mu tafi." Ya fada bai saurari wata magana ba ya fita daga dakin.
Turare na fesa a hijab dina nasa ya sauka har kasa, na daura nikab a fuskata nayi mata sallama na fito, nan na ga sabuwar mota Peugeot mai kyau a fake a can gefe, cikin raina nake raya cewa; Yaushe ya iya tuka mota? kawai dan dai ina bukatar ganin Mamana ya sa na amince da tafiya da shi, amma na san Bahago yana sawun farko gurin ma'kiya na.
Yana zaune gurin driving na bude kofar baya zan shiga. Ya ce." Malama waye direbanki?" Na bude kusa da shi na zauna tare da rufe kofar. ya kwanto jikina yana jan murfin motar tare da cewa; 'Yar kauye kawai kada ki bar mana mota a bud'e." Sai da ya tabbatar da cewa murfin ya rufu sannan ya ja motar ya kama hanyar fita daga layin domin hawa babban titi.
GOBE IDAN ALLAH YA NUFA ZAN GAMA FREE PEGES, INA FATAN ZAKU NUNA MINI KAUNA GURIN SIYAN WANNAN LITTAFI. YANZU NE MUKA FARA TAFIYAR AKWAI RIKITA-RIKITA A GABA DA KUMA TSANTSAR MUGUWAR SOYAYYA DA SADAUKARWA. KADA KU BARI A BAKU LABARI.