FreeArewaPen original
Ya Za A Yi ?
- 1views
- 79chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · 1
1Tunda na ji Tokar na maganar dawowarsa gida nayi saranda! na riga na san kuma shikkenan ni da samun walwala da farinciki har sai ya tafi ban san me yasa ya tsane ni ba, shiyasa nima kwata-kwata bana 'kaunarsa duk da kasancewar mu 'yan uwan juna na jini, amma tsakanin mu, kamar Annabi da kafiri! bama jituwa kuma duk lokacin da za mu had'u wani guri sai mun yi rikici! kamar masu ya'ki! Ya zage ni Ya ci mutuncina watarana ya kai hannu ya dake ni duk da karfin ba daya bane amma ina kokarin ramawa domin ba na iya hakuri da cizo da yakushi nake kwatar kaina na yi ta kuka ina zaginsa, aikuwa ya sha zubar mini da jinin bakina domin har ha'kora biyu ya fitar mini inda Allah yasa na gefe da gefe ne wannan dalilin yasa na ke bala'in jin haushinsa kuma har yanzu ina kan bakana sai na salwantar masa da wani sashi na jikinsa kamar yanda yasa nayi asarar ha'kora na biyu.Zaune kawai nake ina tufka da warwara! ta rarrafo tsakar gidan ta fito tana surutai kamar koda yaushe bakinta baya shiru ita kad'ai magana take, idan ba haka ba kuma za ka same ta tana taune-taune! koda kuwa babu komai a bakinta.Kallonta nayi na sha kunu! domin na riga na san irin soyayyar da take tsakaninta dashi, na san yanzu za ta zo mini da son zuciya to ba zan lamunta ba.Tasa hannu ta shafa yamulallan gashinta da gabad'aya yake dabaibaye da furfura! ya cukurkud'e! kamar audiga kuma iya tsakiyar kan ne kawai ke da gashi amma gefe da gefe da k'eyar duk sumul kamar ba a ta'ba tsirar gashi a gurin ba, amma saboda fitina irin tata duk sati sai ta sanya ni nayi mata tsifa na wanke mata kan sa'an nan nayi mata sabon kitso.Ta kalle ni da cewa" Ma'kiyin ki zai dawo shine ki ka fito tsakar gida ki ka zauna kina k'unci! wai ke Jamila yaushe za ki daina nunawa d'an uwanki kiyy.....Katse ta nayi ta hanyar daga mata hannu da cewa; Kin ga Tokar don Allah ki rabu da ni da maganar wannan d'andaban! ni ina ruwana da dawowarsa, abinda na sani shine yana shiga harkata zan keta masa rashin mutunci, domin wallahi na daina raga masa."Ta ja tsaki tare da sa tsinke tana sakace ramuka da kugunan ha'koranta! aikinta kenan sakace! ta ce" To ai ga ki gashi nan ai, tunda kina ganin za ki iya gwada kwanji dashi." Zuciyata tayi zafi ruwan hawaye ya ciko idona! na ce" Tokar ban san me yasa ki ke fifita Bahago a kaina ba, alhalin duk ke ki ka haifi iyayenmu! a gabanki fa ya zubar mini da hak'ora har biyu, amma baku d'auki mataki ba, babarsa ma har yanzu ba tace komai ba, kodan mahaifina yana da kawaici da hakuri ya yi muku shiru shiyasa kuke nuna mana wariyar launan fata! Tokar na jima fa da gane ba kya kaunata saboda ba kya son mahaifiyata duk da irin dawainiya da kaunar Babana yake nuna miki." Ina maganar hawaye na gar...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.