A SANADIN SOYAYYAR SHAN MINTI

003 Sanadin Soyayyar shan minti

by @jameelarhsadiq6388

*A SANADIN SOYAYYAR MINTI*


   Na 

*Jameey yar'mutan kankia ce❣️*


***


003


Washe gari da safe Yaya Aisha ce ta fara zuwa asibiti ita da mijinta da yake ita bata da mota sai tare suka shigo dan ta gaya mashi komai ya faru dani ina zaune muna labari nida Dija sama sama sai gasu sun shigo suna shigowa muka gaidasu sannan suka zauna wa'azi mijin Yaya Aisha yayi man sosai sannan ya tafi yace zuwa mangariba zai dawo ya wuce da ita gida, rakashi tayi sannan ta dawo tace. "Auta ya jikin naki."? Da yake haushinta nikeji bugun da tayi man, dan komai ya faru dani a yanzun gani nike itace silar komai shiyasa bance mata komai ba na kauda kaina gefe, samun waje tayi ta zauna sannan tace. "Khadija nasan kina kullace dani akan abunda nayi maki amman ki sani a lokacin hankali ya gushe shiyasa na biye ma Mama mukayi maki haka, dan Allah Khadija kiyi hakuri ki yafeman ko naji saukin abunda nikeji a zuciyata mudun baki yafe man ba wallahi Khadija ba zan sake farinciki ba, dan Allah Auta ki yafeman."hawaye take yi tana maganar, kinsan ace yar'wa rabin jiki ba'a shiga tsakanin yan'uwa take nace na yafe mata har abada kuma ya wuce wajena muna cikin haka Yaya Amina da Yaya Fatima suka shigo lokaci guda suma da breakfast dinsu haka muka gaisa sukayi man ya jiki sannan suka saman abincin naci suna ban labarin ban dariya har na koshi nasha Magani, waya suka kira Yaya sukace kar yazo da abincin rana sunzo dashi, likita yazo yayi man allura yace masu zuwa anjima zai sallamaini dan yaga jikin da sauki sosai sannan sai sun kara kula da lafiya ta sosai sannan ya fita, bayan Yaya yazo ya sake dubani sannan yace masu su taso su tafi nan suka ce man zasuje su dawo kafin anjimar sannan suka tafi a asibiti suka bar motar Yaya Amina suka tafi da mota biyu, gidan Baba Ali suka nufa da yake a kwaɗo katsina bayan sunyi parking suka shiga suka fara gaisawa da matanshi sannan suka shiga parlourn shi samun waje sukayi suka zauna sannan suka fara gaidashi bayan sun gaidashi shiru ne ya biyo baya sannan Yaya Jamilu ya fara magana. 


"Baba daman munzo ne mu gaya maka wata magana." kallonshi Baba yayi sannan yace. "Jamilu maike tafe daku Ku dukanku? lafiya kuwa dan naga kamar baku cikin natsuwarku."? Yaya ne yace. "Ba lafiya Baba, daman munzo mu gaya maka Mama ce tace zatayi ma Auta Aure kuma wai Alhaji Salahu zata aura mata." cikin zafin nama Baba Ali yace. "Wai ni maike damun Hafsat ne dan Allah dan Annabi? Ita Mamana rasa masoya tayi shiyasa zata hadata da sa'ar haihuwata ko ta isheta ne."? Girgiza kai Yaya yayi sannan yace. "Aa Baba kaddara ce ta hau kan Auta, ciki tayi amman ya zube yanzun haka tana asibiti, to dan tayi ciki shine tace zata aura mata shi wai dan ya rufa mata asiri ba yanda bamuyi da ita ba amman sai tace idan muka sake yi mata maganar sai ta tsine mana albarka." cewa Baba Ali yayi. "Subuhanalillah assha ai kaddara ce kuma hannunka baya rubewa ka yanke ka yarda ku kwantar da hankalinku yanzun nan zan tafi nayi magana da ita komai kenan zakuji ku tashi ku tafi Allah yayi maku albarka." "Amin ya Allah Baba." suka ce sannan suka tafi suna fatan dacewa.koda Baba Ali yaje gida wajen Mama bai damu da tarbar da tayi mashi ba, dan daman ba shiri suke ba tunda ya nemi ta bashi Yaya Amina ya rike da Babana ya rasu tace bata ba kowa ɗanta ita zata rike daga nan suke yar'ga maciji bayan sun gama gaisawa yace mata. "Hafsat nazo ne kan maganar aurar da Mamana da kikace zakayi ba tare da izinina ba ni kanan ubanta kinsan nine dai madaurin aurenta kuma an bata aure ko zuwa gaisuwar iyaye babu."? Cikin masifa Mama ta fara yi mashi magana. "Wato Ali zuwa sukayi suka hadani dakai ko? Dan sun kasa to bari kaji wallahi baka isa ka hana wannan auren ba nan da kwana sha ukku za'a daura masu aure, dan ma kun samu Alhaji Salahu zai rufa maku asiri zai aureta a haka, ai nasa bayana zaka goya a matsayinka na mai hankali da hangen nisa ba nasu ba,amman sai naga akasin haka to kasani aura tuni akayi shi aka gama ko dakai ko babu."Baba Ali Allah yayi mashi zuciya, zuciya gareshi sosai shiyasa shima ya taso mata yana cewa. "Ni kuma wallahi zan nuna maki karfin ikona akan Khadija baki aura mata wannan tsohon banzan kuma ki sani nike da iko sa iyalan Hashim bake ba, tunda ni nono daya muka sha dashi kuma mu biyu iyayenmu suka haifa a fadin duniya ke baki isa ba kiyi mata auren dole dan kawai tayi ciki bayan zubda mata cikin da kikayi bai isheki ba sai kinyi mata auren dole ki godema Allah kece kika haifeta wallahi da sai nayi shara'a dake akan zubda mata ciki da kikayi muna son cikin a haka duk da ba na halak bane mu cikakun musulmaine tunda mun yarda da kaddara." yana gama fada mata haka ya tashi zai tafi itama cewa tayi. "Baka isa ba wallahi Ali nida kai mu zuba mu gani." bai ce mata komai ba ya fitowarshi ya hau motarshi ya wuto asibiti. 


Koda Baba Ali yazo asibiti, baice ma su Yaya komai ba ni ya fara dubawa sannan ya tambaye ni jiki nace mashi da sauki, kallon su yayi sanann naga ya fita sai kuma ɗaya bayan ɗaya suka kama fita, take jikina ya bani da matsala su Yaya suke boyeman, hawaye ne suka fara zuboman dan ni yanzun kuka ya zama abokin fira ta, Dije ta kama bani hakuri ba dan na hakura ba nayi shiru sai dan naga yanda itama ta tada hankalin ta shiyasa nayi shiru amman ni kaɗa nasan irin ciwon da nakeji a kasan zuciyata. Koda suka je wajen Baba wucewa sukayi office din Doctor suka zauna suna kallon Baba suna jiran suji abunda zai gaya masu, dan hankalinsu ba kwance yake ba yanda suka ganshi sunsan ba'a dace ba, numfasawa Baba yayi sannan yace. " na rasa wata irin mahaifiya Allah ya baku Jamilu baki ɗaya Hafsat idan tana abu sai ta koma ƙaramar yarinya wanda bata son komai ba a duniya inba nonon uwarta ba, kuyi hakuri karkuce ina gaya ma mahaifiyar ku maganganu mararsa dadi dole tasa haka har nike fadi ba yanda banyi da ita akan kartayi ma Khadija wannan Auran amman tace sai tayi, sai dai ku kwantar da hankalinku wallahi ba ta isa tayi mata aure ba sai inda karfi na ya ƙare a matsayina na uba a wajen Khadija, karku samu damuwa."

Yaya Fatima ce tayi karfin halin cewa. " Baba kayi hakuri munja maka Mama ta gaya maka maganganu mararsa dadi, dan Allah kayi hakuri kuma insha Allah muma zamu tayaka yaƙar Mama ganin bata yi ma Auta wanann auren ba."

Murmushi yayi dan Yaran dan'uwanshi suna burgeshi suna ta tarbiya sosai kuma yasan wajen mahaifiya suka samaita, sai dai idan Mama tana wani sai abun yaba kowa mamaki dan abu take kamar wanda bata taɓa zuwa makaranta ba, tashi yayi yana cewa. "Wannan abun dole nane karki damu, ku taso muje dan naga jikin da sauki ya dace ace ansallamaita haka nan.Yaya Jamilu ne yace. "Eh Baba ɗazun da safe aka sallamaimu, daman kai muke jira kafin mu tafi, mungode Allah ya saka da alkhairy Baba" haka suka fito suna kara tautaunawa akan matsalar Mama, da yanda yazasu shawo kan matsalar ba tare da wani yaji ba har azo daga baya ana yi mana dariya, tunda ba wanda yasan nayi ciki sai yan'uwana sai kuma Alhaji Salahu da Mama taje ta gaya mashi, bayan sun dawo muka hada kayanmu sannan muka taho gida. Koda muka koma gida kallon banza Mama tayi mana ta watsar, kallon da naga Mama tayi mana shi yasa jikina ya mutu take naji ban da lafiya dan ina tsoron abunda zatayi man, tunda ni daya za'a bari gidan nida ita zaunawa mukayi muka gaidata amman abun mamaki maimakon ta ansa gaisuwar sai ma ce masu tayi. "Wato ni zaku kai ƙara wajen Ali ko? Kunsa Ali ya isa yasani balle ya hanani? Kin nuna man ban isa da Khadija bako? Da har zaku kai ƙarata wajenshi dan nace zanyi ma Khadija... Katse ta Yaya Amina tayi tana cewa. "Mun isa mu kaiki ƙara wajen Baba wallahi Mama mudai ce mashi Khadija bata lafiya kema baki lafiya shine yace bari ya fara zuwa ganinki sannan yaje ya ga Khadija bamu ce mashi komai ba bayan nan ko Yaya Fatima."!? Cikin tsoro ta ida maganar tana kallon Yaya Fatima, take nasan ba lafiya mai Mama zatayi man wanda yasan yan'uwa suka kaita ƙara wajen Baba Ali, nidai kallonsu nike da tambaya a bakina dan inason nasan abunda Mama zatayi man wanda su Yaya basu son nasani, ji nayi Yaya Jamilu yana cewa. "Auta tashi ki shiga ɗakinki ki huta dan naga kamar bacci kike ji, ke kuma Aisha shiga kitchen ki dafa mata ruwan sanyi wanda zata dan gasa jikinta mana." naso nayi gardama amman bani iya yi ma Yaya Jamilu gardama dama Yaya Aisha ce da sai nayi tunda nike bi mata daga ita sai ni, tashi nayi na shiga room din na, ina kallon sanda Yaya Amina ta leko taga mai nike sai akayi sa'a kwance ta tadda ni bisa gado na lumshe ido, ni kuma ina ganin haka nasan magana ta zasuyi amman basu sun naji, tasowa nayi na laɓe jikin kofa yanda zanji komai zasu ce. 


Ji nayi Yaya Jamilu yana cewa. "Mama dan Allah muna ƙara baki hakuri akan abunda Auta ta aikata insha Allah ba zata kuma ba, sannan kuma dan Allah karki aura mata Alhaji Salahu ki bata dama ta fiddo wanda take so sai a daura mata, amman aurar da ita ga Salahu da kike niyar yi shine barazanar lalacewar Auta Mama." ji nayi hawaye sun zuboman wai ni za'a daura ma wannan tsohon mutumin wanda ko gaidashi baniyi a unguwa tunda na lura da yanda yake kallona idan na fito zani islamiya ko kuma boko, ina cikin yin hawaye na naji Mama tace. "Duk ki tashi ku bani waje wanda basu da hankali sannan kuma sani wallahi sai na aura mata shi nan da kwana goma dan haka ku fita ku bar man gida kafin raina ya ɓaci." tashi naga sunyi nayi sauri komawa bisa gadona na share hawaye dan ban san na nuna masu naji abunda suke cewa haka suka shigo suka kara dubani suka ce na ringa tsarki da ruwan zafi ina gasa jikina dan naji kwari sannan suka tafi gida, ai suna fita naji tashin motocinsu na tashe da kuka mai cin rai, aiko Mama ta shigo ta fara yi man fada akan nayi shiru na tashi na shiga wanka yau bako zanyi. Ba yanda zanyi haka nayi duk abunda Mama tace harda bani kayan kwaliya nayi , haka yazo ya gama yi man surutanshi ya tafi, ni kuma na fara shirya kayana cikin wata yar'karamar jikka ina jiran dare yayi na tafi na barma Mama gidan tayi yanda zatayi da shi, idan taga ban nan ai sai ta samu wanda zata aura ma tsoho haka na kama hidimata kamar ba abunda ke damuna ana kiran mangariba Mama ta shiga daki danyi sallah ni kuma na dauki jikka da wayata da komai nawa harda sarƙar zinarina guda biyu wanda Mama da Yaya Jamilu suka saya man sai kudi masu dan yawa na fitowata, ina fitowa naga mai naped nace ya kaini tasar jibia. 


Tafiya mai naped yake amman ni ba abunda nike idan ba kuka ba, sai zuciyata ta bani ko naje gidan Yaya Amina sai kuma naga kamar Mama taje ta dauko ni ta daura man aure da Salahu haka na kama saƙesaƙe ina hawaye dan ni yanzun so nike na kurma ihu na kama kuka ko naji saukin abunda nike ji a zuciya ta, amman ba halin yin haka haka muka shiga kofar guga har cikin tashar jibia sannan ya saukeni na bashi kudinshi ya bani chanjin, aiko nan aka fara zuwa aka anshi kayana akasa cikin boot din mota sannan na shiga, ɗari uku na bada kudin mota ba wani daɗewa nayi ba motar ta cika mu tashi zuwa garin jibia, tafiya mukayi mai dan nisa sannan muka iso magamar jibia nan nace zan sauka aiko aka saukeni na dauki kayana, a cikin wani novel na taɓa karanta sunan gari mai sunan HIRJI daga magama ake yanke hanya ake shiga cikin garin Hirji . Garin Hirji gari na karuwar duk wata karuwa maiji da kanta ita karuwa ce to a garin Hirji take zaune, nima garin Hirji na nufa dan ban iya zama naga Mama tayi man auren dole kwara naje hirji nima na zama karuwa nayi zaman kaina ba kwalkwasin wani ba...Haka na hau mashin na bashi naira dari ya kaini har hirji, nan fa akeyinta bansan ina zani ba dan bansan kowa ba balle na nufa gida gashi takwas na dare har yayi haka na kama yawo bansan inda zani ba, har tara da rabi ta tayi bansan kowa ba, tsoro ne ya fara kamani ganin yanda mutane suke kallona wasu har dariya suke man, wani kofar gida mai dakali na samu naje na zauna dan ni a niyata idan dare yayi sai na kwanta bisa dakalin kafin gobe tayi na cigaba da tafiya naga yanda Allah zaiyi dani. 


A bangaren Mama kuwa bayan tana gama sallah ta fito koda taga bani cikin parlour tasa na shiga ɗakina ne dan ba huta shiyasa bata nemaini ba, sai ma shiga kitchen da tayi ta daman ruwan zafi da magunguna sannan ta dafa man indomie da kwai, kaima ruwan wankan tayi a toilet din dakinta sannan ta fito tana cewa. "Auta maza fito kije ki ƙara watsa ruwa sai ki zo kici abinci na dafa maki abunda kika fi so." jina shiru tayi bance komai ba tashi tayi ta nufo ɗakina tana cewa. "Haba Auta ya kamata ace kin fito kinyi wanann wankan fa, ko kina son indomien ta huce baki ce ba."? Idan shiga cikin ɗakin tayi bata ganni ba, zama tayi bisa gado tasa ko na shiga toilet ne, ganin shirun yayi yawa yasa Mama leƙa toilet din bata ga kowa ba, nan ta dawo ta fara kallon ɗakin nan taga bataga ƙaramar jikka ta ba, da gudu taje ta buɗe dirowata nan taga na kwashe kayana amman ba duka ba, dan karamin box din sakarkokina ta bude nan taga har zinaraina duk na kwashe, ba ta kawo komai a ranta bata, tasa guduwa nayi na tafi gidan Yaya Jamilu, nan ta fito ta kirashi waya bawan Allah yana zaune duk abun duniya yayi mashi yawa lokacin karfe takwas da rabi na dare Mama ta kirashi waya, cikin Mamaki ya dauki wayar Mama cewa yayi. "Hello Sallama Alaikum Mama lafiya kika kirani cikin dare."!? Cikin faɗa Mama ta fara magana. "Wato Jamilu ni zaka nunama iyakata ko? Shine kace ma Auta ta dawo gidanka ko? To komai kake ka tabatar da ka dawo man da ita gida wallahi tun kafin raina ya ɓaci." zufa ce ta keto ma Yaya sannan yace. "Wai Mama kina nufin Auta bata gida a yanzun haka."!? Cikin tsoro yayi tambayar dan hankalinshi bai kwanta ba, cewa Mama tayi. "Wato tambayata ma kake ko Jamilu? Bayan kun zigeta kun hure mata kunne har ta'iyya gudowa wajenku to wallahi ku sani aure ba fashi kuma yanzun nan nace ku dawo gida." cewa yayi. "Wallahi Mama ba gida na tazo ba, amman bari na kira su Fatima ko gidansu taje, taya zamuce ta gudu ta dawo gidanmu Mama? Sa kanta tayi bari na kirasu naji am.... "Yi man shiru Jamilu mudun baku maido man ita ba cikin daren nan ni kaɗai nasan hukuncin da zani yanke maku wallahi." nan ta kashe wayar tana faɗa, shiko Yaya waya ya kama kiran su Yaya yana tambayarsu ko nazo gidansu sai suce ban zo ba. 


Lokacin karfe sha ɗaya yayi, haka bawan Allah Yaya Jamilu ya taso ya taho gidanmu yana shigowa Mama ta taso tana cewa. "Ina Autar take? Harni zakuyi ma haka Jamilu? Maiyasa kuke son ja'inja da nine."? Hawaye ne kawai yake yana kallon Mama sannan yace. "Mama Auta gudawa tayi kenan? Nidai bata zo gidana ba haka bataje gidansu Fatima ba Mama." cikin tsoro Mama tace. "Ban yarda ba Jamilu nasan tarbiyar da na Khadija ba guduwa tayi ba, tana gidan Amina ta boye ta wuce kaje gida gobe da safe naje na taho da ita." duk da Yaya ya yarda guduwa nayi dan har rantse mashi Yaya Amina tayi banje gidanta ba, dan kawai hankalin Mama ya kwanta yasa ya juya ya koma gida haka ya kwana zaune..Haka na zauna ina tunanin mafita dan kuwa nasa a raina ba zan sake komawa gida ba, wata matace tazo wucewa misalin sha biyun dare wajen gidan da nike zaune tazo zata buɗe kallona tayi sanann tace. "Kefa daga ina haka."? Tayi man tambayar tana tauna chigum kallo ɗaya nayi mata na gane karuwa ce dan daga yawonta ta dawo fuskarta tasha bilicin tadai kogu da duniya, shiru nayi ina hawaye murmushi tayi sannan tace. "Na gane matsalarki yan mata,taso shigo gida komai kenan gobe munyi magana, ai baki da gidan da zaki kwana ko."? Cikin sauri nace mata. "Eh wallahi ni bakuwa ce bansan kowa ba anan, dan Allah kiyi hakuri na zauna a gidanki zan ringa yi maki wanke wanke da shara." dariya tayi sannan tace. "Karki damu yanmata zaki yi amfani ne, nagaji sosai dan na kwaso gajiya shigo gobe munyi magana, kema daga gani yunwa kikeji ko."? Ɗaga mata kai kawai nayi sannan na dauki kaya nabi bayanta muka shiga gida, gida ne mai kyau wanda ake kira mu hadu parlour sai manyan kujeruta na zamani gaskiya gidanta ya hadu dan ba abunda babu a cikinshi na more rayuwa dan har mota naga a compound din gida guda biyu mamaki duk ya isheni, kallona tayi sannan tace. "Ba abun mamaki bane dan karuwa kamar ni na tara wannan dukiyar ba, abunda zaki tambaya ana shine taya akayi na zama karuwa shine abun tambayar ba mamakin tara dukiya ba yan'mata." nidai shiru nayi ban ce komai ba, sai ma murmushi da nayi mata kawai, nuna man wani ɗaki tayi tace shine nawa, sannan tace na shiga nayi wanka itama zatayi wanka sannan nazo muci abinci sai mu kwanta dan dare yayi kuma tana jin bacci. Bayan mun fito kaza ce ta fiddo gasarshiyar kaza sai hollondia mai sanyi sosai, nan muka fara cin muna gama wa tace. "Kije ki kwanta ki huta dan naga alamun kina jin bacci sosai, nima baccin nikeji kuma na kwaso gajiya sosai yau, gobe munyi magana." tashi nayi ina ce mata. "To Aunty nagode sosai." itama tashi tayi tana tafiya tace. "Karki damu yi ma kaine." haka na shiga ɗakin da tace nawane mallakina na haye bisa gado nayi Addu'a na fara bacci hankalina kwance dan ko tunanin gida banyi ba dan na cire gida a rayuwa ta nasa ma raina bani da kowa bansan kowa ba sai ni kaɗa, dan nayi alkwarin yin rayuwar mai dadi wanda tafi ta gidanmu dadi."


Washe gari da safe Yaya Jamilu yaje gidan yaya Amina zaune ya tadda ta bisa dining dinta ta buga uban tagumi dan tunda jiya yace mata ba'asan inda nike ba ta kasa kwanciyar hankali dan ko bacci sai dai ya saceta, tadda mijinta yayi sai lailashe yake yana bata baki, zaunawa Yaya yayi sannan yace. "Amina hakuri zamuyi haka kaddarar Auta take, sannan kuma ki sani komai ya faru laifin Mama ne abunda muke son mu nuna mata kenan amman ta kasa mahimfa." cikin kuka tace. "Yaya ni abun ne ya tsaya man a rai, ace wai Auta tasa ƙafa ta gudu ta barmu bata damu da wani hali zamu shiga ba, kuma wallahi sai nayi ƙarar Mama a court sai dai ta tsine man na gwanma ce amma... "Haba Amina ai idan rai ya ɓaci hankali naya gushewa, maiye ribarki dan kinka mahaifiyar ki a court eh."? Ji sukayi ance. "Wallahi Yaya idan har Amina bata kai Mama court ba to mu sai mun ƙaita court ko ya kika ce Aisha."? Yaya Fatima tayi maganar shigowarsu kenan ita da Yaya Aisha sunzo ne su tafi da Yaya Amina suka tadda suna magana da Yaya..Tashi Yaya yayi yana cewa. "Idan har na isa da ku, kuma kun daukeni a matsayin ubanku ba Yaya ba to ina son ku kyale Mama ku barta da abunda ya isheta mana, kuna son a dunga zaginmu a unguwa ace mun kai mahaifiyar mu kotu."? Cikin kuka Yaya Fatima tace. "Amman Yaya bakaga abunda Mama tayi ba? Ba yanda bamuyi da ita ba akan ta rabu da Auta karda tayi mata auren dole amman tace sai tayi shikenan tunda ka hanamu amman ku taso muje mu gaya ma Baba Ali halin da ake ciki." tashi Yaya Amina tayi ta dauko gyalenta dan ko motarta kasa dauka tayi a motar Yaya Jamilu ta shiga ita kuma Yaya Fatima ta dauki Yaya Aisha kamar yanda suka zo suka wuce gidan Baba Ali, bayan sun gama gaisawa dashi suka gaya mashi halin da ake ciki, baice masu komai ba har suka gama sannan yace. "Abunda ai Hafsat din tayi kenan ai ko? Shikenan amman ku sani sai na kai ƙararta wajen sarki dan ba zan barta ba." Allah sarki ance ɗa da mahaifi sai Allah nan suka kama bashi hakuri, har Yaya Jamilu yace. "Baba hakuri shine dai dai, kuma nayi alkwarin zan sa a nemo man Khadija duk inda taje a cikin garin katsina, yanzun haka Mama bata yarda da Khadija ta gudu ba tace tana gidan Fatima yanzun zamuje mu gaya mata gaskiya ta gudu." haka suka kama bashi hakuri sannan suka fito sai gida wajen Mama dan su gaya mata gaskiyar magana Auta bata wajensu guduwa tayi... 


Ayi hkr babu editing yau ina busy


*Akwai Data available masoya akwai ko wane network kuma cikin rahusa 270 1GB ko wane network,banda 9Mobile shi 300 1GB*


*Zaki biya kudin data idan kina bukata ta wannan account din *** Jamila Bello Abubakar Opay bank,*** for call or whatsapp*