Page 20
_Typing🤳🏼_
*_....🌪️ZULFAH🌪️...._*
_UMMU MAHER_
*@MRS GREEN🍏*
_GAWURTATTU 3_
Book 2 page 20
*_follow Zulfah on Arewa books_*
https://arewabooks.com/book?id=64ff0277d73b80a18ea59540
*_VIA GROUP ZULFAH FANS_*
***
KVTgSsodCRZGcEjERSEsBY
_*AMMA ARAB!AMMA ARAB!!
AMMA ARAB!!!*_
_kai daga jin sunan kasan sunan
ya amsa sunansa,AMMA ARAB
ta kawo muku wani supplement
na gyaran jiki mai sanya daɗi
da ƙamshi AMMA ARAB gidan ƙamshi_
*MUSUK*
*MADARAR TURARE*
*KAJIJI*
*ROT*
*SANDAL*
*HUMFUR*
*SANDAL FLASK*
*SANDAL WUD*
*AALUT*
*GAF-GAF*
*JANNAMI*
*ƘWALAKCA*
*MAHAHABSUFYAN*
*WANNAN SHINE GRP ƊINA
NA WHATSAPP,KI ANTAYO SABODA
KADA AYI BABU KE*
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
***
mBHnDN6KUJYnkBDT7S
*ADDRESS👇🏻👇🏻👇🏻*
Zaria road kwankwasiyya sabon gari ɗangwauro house number 224
Kano
OR CALL MY CONTACT
***
*AƘWAI WANI SUPPLEMENTA NA GYARAN JIKI DA TAZO MUKU DASHI KE DA KANKI IDAN KIKA YI ZAKISAN EH LALLAI ZAKI GIGITA ME GIDA,KINSAN MAZA SAI DA ƘAMSHI DUK MATAR DA BATA SAYI WANNAN SUPPLEMENT ƊIN BA TO AN BARTA A BAYA*
*AƘWAI BABBAN MAGANI NA INFECTION,WANDA ZAI DAWO MIKI DA MARTABARKI NA ƳA MACE,ZAI CIKO MIKI DA NI'IMARKI KI KOMA ƳAR GATAN MEGIDA*
*AƘWAI BABBAR KAMBASA,TA TURARA KAYA HAJIYA KI BUƊE BAKIN ALJIHU KI JIƘO DA ƘAMSHI,KINA ZAMA AN SAN KIN ISA MACE HAJIYA DON AMMA ARAB TA SHARA SOSAI WAJEN KAWO MUKU KAYAN GYARA NA MATA*
*AƘWAI SABULAN GYARAN JIKI SUNE KAMAR*
*MULATO SOAP*
*FACE CREAM*
*FACE SOAP*
*MULATO WHITENING LOTION*
*HAIR GROW OIL*
*HAIR GROW CREAM*
*KAR-KAR OIL*
*MINT LEAVE OIL*
*ANTI PIMPUS SOAP*
*AƘWAI SABULUN NANKARWA*
sannan ina harkar👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
*ABIN BUKI*
*ABINCIN OFFICE*
*SNACK*
KAMARSU👇🏻👇🏻
*WAINAR MASA*
*SINASIR*
*MEAT PIE*
*CINCIN ƊAN LAUSHI*
*CUP CAKE*
DA DAI SAURANSU.
AMMA ARAB GIDAN GYARAN AURE😄👏🏻.
______sosai hankalinsu ya tashi don sun tabbatar wannan tijararriyar tsohuwar taji komai,Hajiya Bilkisu ta ɗora hannu aka wacce kaf gidan itace mata ta farko da aka fara aurowa,itace matar ɗan hjy Innah na farko saboda haka tafi kowa sanin halin Hjy Innah,indai har tace zata aikata abu sai ta aikata straightforward ce.
ta ce"wannan tsohuwar ya zamar mana wajibi muyi maganinta,idan kuwa ba haka ba wallahi ina mai tabbatar muku ba zata yarda ta barmu ba,aƙwai wani mummunan abinda ta shirya ni daman a jikina inaji kamar wannan maganar da muke wani yana jinmu."
Hjy Maryam kuwa gani take komai zai faru ya faru,tunda ta rasa ɗanta bata ga wani abu da zai dame ta ba kamar mutuwar ɗanta ba,saboda haka tunda ma suka fara maganar bata ce musu komai ba.
hjy Raihana ta taɓe bakinta sannan ta tashi,amman bata ce musu komai ba ta wuce ɓangarenta kai tsaye,don aƙwai abinda take son shiryawa yanzu a ɓangarenta,tana shiga sashen nata ta tarar dasu Hajara,Munira,Rabi,Ramla,duk ƴaƴanta ne Rabi da Hajara suna da aure sunzo ne saboda rasuwar da akayi,suna gaishe tama bata amsa ba ta wuce cikin sauri don a wannan halin da take ciki bata son kowa ya tsare ta.
tana shiga Hajara ta kalli Rabi ta ce"oh wai ni me yake damun Momi ne ƙwama biyu?haka rannan fa da mukayi faɗa da Abban Taslim nazo gida ina faɗa mata bata saurareni ba,ita dai hankalinta yana wani wajen?kuma nayi nayi don in gano abinda ke damunta na kasa ganowa?".
ta faɗi hakan tana kallon sauran ƴan uwanta ko su sunsan abinda ke damun mahaifiyar ta su?dukkansu babu wanda yace komai don suma suna cikin halin da take ciki,sai Ramla ce wadda suke cewa Hibba ta ce"i dont no gaskiya don bana ce ga abinda ke damunta ba,amman ya rasa alaƙa da baƙin cikin waccen tsinannaniyar yarinyar da Dady ya ƙwallafa rai akanta?yarinyar da Dad ɗin mu ke wulaƙantamu saboda ita."
Munira duk tana jinsu ta kasa magana,don ita tunda aka rufe mata baki baƙin ciki ya isheta gashi dai tana son yin magana amman ta kasa,don alokacin da ta gane halin da mahaifiyarta ta jefa kanta wato nutso cikin ƴan tsafi sai gaba ɗaya ta gaza nutsuwarta,don abin har ya shafi karatunta don kon exam ɗin da sukayi a skull babu wani abin arziƙin da ta taɓuka,gashi har yanzu ta kasa faɗawa Dad ɗinsu sakamakonta na skull ɗon babu abinda tayi na azo agani,a ranar da ta kama mahaifiyarta taso ace kowa ma ya ganta,amman da yake ta iya takunta sai ta nunawa mutane babu abinda ya faru har aka fara ganin Muniran a matsayin mai ɗan taɓin hankali,tsoronta ɗaya yadda mahaifiyarta tayi mata jan ido akan sanya mata ido idan ba haka ba duk abinda ya shafeta ita taso,ita da take ƴarta tayi mata haka ina ga wani kuma?.
saboda haka take tausayin Zulfah,saboda yadda suka sako ta agaba bata manta maganar da taji jiya mahaifiyarta nayi ita da wata ƙawarta,wai akan lallai sai sunga ƙarshen Zulfah ɗin,ita ta rasa me Zulfah ta tsare musu aduniya da suke son dole sai sunga bayanta,kuma ba iya mahaifiyarta ke farautar Zulfah ɗin ba,rabi da ƙwata na gidansu suna farautarta a hannu.
sai alokacin hawaye masu zafi suka zubo mata,tana nadamar tono sirrin mahaifiyarta me girma don ma wani abun ba zata iya faɗarsa ba,bayan wannan halin na tsafi aƙwai wani mummunan hali na mahaifiyarta,wanda matuƙar ta tonawa mahaifiyarta wannan sirrin shikkenan ta koma abin tausayi,don babu wanda zai ƙara kallonta da idon rahama.
share hawayenta tayi ta tashi ta wuce ɗakinta,tana zuwa ta buɗe wayarta sai taga misscalled ɗin Nurain har biyar,ta ɗauka bakinta na kakkarwa don zazzaɓine ke neman rufe ta,don duk sa'adda ta tuno da abinda mahaifiyarta ke aikatawa sai taji kamar ta kashe kanta.
Nurain ya ce"Munirat wai ni ƙwana biyu na kasa gane kanki?ba dai wani abu ke damunki ba ko"?.
Share hawayenta tayi gwanin tausayi sannan ta ce"babu komai i'm feeling fine".ta faɗi hakan tana wasa da ƴan ƴatsub hannunta.
"yanzu ba kida lafiya shine kika yi shiru?kinsan yadda hankalina ya tashi kuwa?don Allah yanzu ba sai an jima ba ki fito ni zan kaiki asibitin,da adaidaita sahuna kinsan yanzu na fito aiki ma".
murmushi tayi sannan ta ce"no no ka barshi kawai gidanmu fa rasuwa akayi".da sauri ya ce"ya subhanalillah waye ya rasu?".
cikin mutuwar jiki ta ce"Yaya Bilal ne ya rasu".
ciki kiɗima ya saki sitiyarin yana neman yin hatsari,kansa na juya masa ya samu waje ya tsayar da adaidata sahun akan titi,mutanen da suke adaidaitan suka fara ce wa"haba malam idan shaye shayenka zakayi ka bari mana sai ka saukemu?wannan ai rashin hankali ne".suka faɗi hakan ba don sun tabbatarwa kansu yana shaye shayen ba,saboda kamalarsa da ƙwarjininsa kana ganinsa kaga salihin yaro,sun dai faɗi hakan ne don sunji haushin yadda yayi wasa da ransu.
sosai Nurain yake jin duniyar na juya masa,wanda ya ɗauki nauyin karatunsa tun yana ƙarami,wanda ya ɗauki nauyin komai nasa na rayuwa yau shine ya bar duniya?bai san Munira ba sai ta dalilin Bilal,saboda yana yawan zuwa gidan wajensa in har yana gari ko jiya jiyan nan sai da sukayi waya dashi,tsabar yadda ya furgici haka ya kira amininsa Faisal awaya yace yazo ya tuƙasa zuwa gida.
_HAJIYA RAIHANA_
tana shiga ɗakinta ta ɗauki wayarta,ta danna wata number kiran farko aka ɗaga da alama kuma namiji ne,sai kuwa ta ce"ɗan tsitu ina so yanzu ba sai an jima ba,sunan wannan tsohuwar dana baka ƙwanaki inaso ayi min aiki akanta,a doɗe mata kunnuwanta duka biyu yadda babu yadda za'ayi ta iya wata magana."
tana faɗar hakan Boka ɗan tsitu ya ƙyal ƙyale da dariya sannan ya ke ce da wata irin mahaukaciyar dariya sannan ya ce"to uwar ɗakinmu an riga da an gama kiyi barcinki da munshari".
Ƙit......... ta kashe wayarta tana wata irin dariya ta ce a fili"hmm yau xanyi maganinki tsohuwa".
sai ta tashi ta koma sashen Hjy Maryam don tana son taga komai a idonta,tamkar dai yadda bokanta ɗan tsitu ya yi mata alƙawari.
*Bayan wata 2*
abubuwa da yawa sun faru,cikinsa kuwa har da rashin kunnuwan Hjy Innah,ƴaƴanta da jikokinta duk sunyi baƙin cikin faruwar hakan sai dai wasu acikin jikokinta cewa suke Allah ya ƙara,don sam bakinta baya gajiya ko baka shirhinta ba sai ta shiga taka.idan ka ganta yanzu sai ta baka tausayi don kurum kurum take anyi maganin har an gaji.
ZULFAH 1
a ɓangare na ma kuwa ba ƙaramin daɗin hakan naji ba,saboda daman bayan Bilal sai ita waɗanda ke damar min rayuwa,saboda haka na ƙara naɗe ƙafufuwana ina cin kare na babu babbaka,ga shi na samu direba wanda ko me nace ya yi sai yayi.
yau ma kamar kullum na tashi zan tafi aiki,na shirya cikin riga da wando,rigar tsukakkiya da ita ta bayyanar da shap ɗina tsaf wandon farado ne mai buɗewa sosai ta ƙasa don sai ka ɗauka ma siket ne,amman wando ne kawai na masu ido da ƙwalli wandon blue ne light mai haske,rigar kuma fara ce sol na sanya belt na yane kaina da ita.
na sanyq siririn glass ɗina fari sol amman babbane mai cika ido.
takalmina kuwa irin kombus ɗinnane na zuwa aiki babba dashi shima fari sol dashi.
ina fitowa na fara shiga ɗakin hjy Innah,na samu mai aikinta tana wanke mata banɗaki na ƙarasa bakin gadonta na fara tashinta daga barci,a hankali ta tashi tana ƙaremin kallo,nima kallon natw nake na ce"ya akayi ne ƴar kurma?ko kina da magana ne?".na sanya dariya ina kissing ɗin kumatunta sannan na fita.
sai dai har zuciyata bana jin daɗin canzawar Hajiya Innah,don tunda Bilal ya rasu ta daina sakarmin fuska kullum fuskarta a tamke tamau.
Tun daga nesa na hangosa yana tsaye a bakin motar yana jira na,kallon tsaf nake masa wanda arayuwata ban taɓa kowani namiji ba,ban san me yasa kullum sai inga yana ƙara min wani irin ƙwarjini ba,ko na yi niyyar ci masa mutunci idan yayi min ɗan abinda bai kai ya kawo ba,saui inji na kasa sai dai ma in samu kai na a mai sunkuyar da kaina ƙasa tamkar wani ubana,don ko Dady na bana tsoronsa saboda sabon da ke tsakanina dashi.
tun kafin in ƙaraso ya taho da sauri ya buɗe min murfin bayan jibgegiyar motar tawa,na shiga na zauna ina jin gabana na dukan uku uky kuma na rasa na meye?ko me ke damuna aduk sanda naga Aliyu?wannan tambayar ce na kasa samun mai bani amsarta?saboda a kaf gidanmu yanzu Dadyna ne kawai ke sakarmin fuska,sai ko Munirat don ma ni ɗin bana sakar mata don dukkaninsu ban yarda dasu ba,tun abinda ya faru akan mahaifiyata.
hatta Murash-sha yanzu ta daina zuwa inda nake,tun abin yana damuna har na haƙura don ko naje sashensu wajenta bata ko kallona,ƙarshe ma sai ta fice ta barni a zaune saboda haka nima sai na daina zuwa sashen nasu baki ɗaya,na mayar da kaina tamkar ba nida wasu ƴan uwa agidab,don na fahimci suna ɗora mutuwar Bilal akaina ne,ni kuwa ko ajikina don a ganina mutuwar Bilal tamkar hutu ce agare ni.
dai dai Aliyu zai rufe motar idanuwanmu suka haɗu a na juna,wani abu na fara hangowa a idanuwansa,sai naji jikina duk yayi sanyi duk masifa da tsiwa ta na rasa abinda yasa bana iya yi masa,kome yasa hakan oho???????✍🏻
UHM FANS KU BANI WANNAN AMSAR NI DA ZULFAH MUNA JIRAN AMSARKU?????😂😂😂😂😂😂😂😂😒💃🏼
_MRS GREEN CE_
domin chart dani kai tsaye ***
*_GAWURTATTUN UKU🔥🔥🔥2023 SEPTRMBER._*
_1-ƘWAI A BAKA...!!!🥚_
👇🏽
*(Ummu Affan)*
_2-NA FAƊO DAGA BENE NA ZARCE RIJIYA...!!!🫗_
👇🏽
*Badi'at Mrs bukhari*
_ZULFAH_🍏
👇🏽
*Ummu maher(mrs green)*
_Littafi ɗaya;400_
_Littafi biyu;800_
_Littafi uku;1000_
Ga masu son tura kuɗinsu ta acc sai su tura a wannan acc ɗin👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank
Sai ka tura da shaidar biyanka ta wannan no ɗin👇🏽👇🏽👇🏽
***
Masu tura kati kuma sai su turo screenshot na katinsu Mtn ta wannan no ɗin👇🏽
***
Ƴan Niger zasu turo katin Moov ko Airtel ta wannan number.
***
*GA MASU SON A TALLATA MUSU HAJARSU A DUKKANIN SHAFINMU na facebook,whattpad,telegram,youtube,group da status,zamu tallata muku ne akan farashi me rahusa*
10K ne kacal.
Sai ku tuntuɓe a numbobinmu kamar haka👇🏽👇🏽👇🏽
***
***
***
Domin tallata muku hajojinku a cikin littafinmu na sati ɗaya ya kama👇🏽👇🏽👇🏽
2K
sati biyu
3k
idan kuma kanason har mu gama book muna ɗora maka ya kama
10k kacal.
Mun gode da zaɓar gawurtattu uku ako da yaushe.🙏🏼