Page 21
_Typing🤳🏼_
*_....🌪️ZULFAH🌪️...._*
_UMMU MAHER_
*@MRS GREEN🍏*
_GAWURTATTU 3_
Book 2 page 21
*_follow Zulfah on Arewa books_*
https://arewabooks.com/book?id=64ff0277d73b80a18ea59540
*_VIA GROUP ZULFAH FANS_*
***
KVTgSsodCRZGcEjERSEsBY
...........cikin nutsuwa ya buɗemin murfin motar,sannan yaja ya tsaya tamkar wani mai gadina na ɗanyi murmushi mai ƙayatarwa,saboda ni arayuwata inason mutum mai girmama ni na miƙo masa jakata ya riƙe cikin girmamawa,gaba nayi yana bina a baya har cikin hamshaƙin office ɗina,ya gyaramin kujera ta sannan ya juya zai fita na tsira masa ido ƙur ina kallonsa,inason faɗa masa wata magana kuma ina jin nauyin yin hakan,amman ya zamar min dole in furtata ko don in samu sauƙin abinda yake damuna.
A hankali na tashi na fara tafiya cikin rangaji da ƙwarƙwasa har na isa gabansa,don na ɗan haɗa da ɗan sauri sauri wanda a ƙidata sam ban iya sauri ba,sai gashi yau na haɗa harda ɗan gudu kallona yake nima ina kallonsa,ina furzar da wani irin numfashi sosai na wahalar danasha wajen takowa inda yake,don aganina wahala nasha don ni sam bana son wahala arayuwata don daman ban saba da rayuwar wahala ba don tunda na taso bazan iya faɗar abu ɗaya dana wahalarsa ba,sai hatsarin dana yi ƙwanaki sai kuma wahalar dakon soyayyar wanda bai san ina yi ba,ban taɓa tunanin cikin lokaci guda rayuwata zata koma haka ba?ban taɓa tunanin zan iya wata aba soyayya ba tunda dai ban ɗauke ta awani ma'auni mai tushe ba,sai gashi na faɗa soyayyar wani wanin ma talaka?wanda ada nake ƙyamatar duk wani mutum wanda in har ya fito daga tsatson talakawa ko kallon arziƙi baya samu.
wani ɗan murmushin gefen fuska nayi,don ganin tarkona ya kama Zulfah amman ko kusa ban bari ta gani ba dom yadda na ɗarsa mata tarko ta faɗa to so nake inyi ta rufta mata har sai na kai ta inda nake son kaita ɗin,sannan in kaita in baro sannan alokacin zan nuna mata shi talaka abin sone ba abin ƙyamata ba,kuma abin ajashi ajiki ne domin bakasan inda rana zata faɗa maka ba.
wani irin haÉ—e rai na yi,sannan na ce"lafiya dai Hajiya"?.
ɗan haɗiye wani malolon baƙin ciki na yi,don gani nake ni Xulfah nafi ƙarfin komai awajen ko wani namiji,amman tunowa danayi ni nake buƙata sai na ƙwantar da kaina ina kallon jyint ɗin fuskarsa,mai cike da ƙwarjini da kuma sihirtaccen kyau.
Aliyu dai ba fari bane,baƙi ne amma ba can ba sai dai Allah ya yi masa baiwar kyau mai tsayawa azuciya,yana da ɗan ƙaramin baki wanda yake zagaye da gashin baki baƙi siɗik wanda ya ƙwanta luf gashi da pink lips mai matuƙar sheƙi da kyau,haƙoransa kuwa farare tar tar tamkar wata acikin zara,sannan yana da gashin gira wada tacce sosai wanda ya kusa haɗewa saboda yawansu,idanuwansa ba wasu masu girma bane sosai ammanfa cikin suke da wata irin baiwa da haibar da ba kowa ke samun hakan ba,gami da zara zaran gashin idonsa wanda har ɗan shga idon suke,saje ne dashi wanda ya kewaye doguwar fuskarsa mai matuƙar kyau,sheƙi yake a kowani lokaci don idan ka kalleshi kallon farko zaka ɗauka ko shamfo yake musu,amma idan ka ƙura masa ido zaka gano zallar kyau ne uwa uba tsaftar Aliyu,don duk da shi talakane kuma ba wasu kaya ne dashi ba Amman bai hanashi tsaftace su tare da bumbuɗa musu turaren ɗurin da yake siya awajen masu tallan turare wato 'AMRAJ MAN' turare ne na maza ɗan misra mai matuƙar daɗi da sanyi.
Aliyu dogone amman ba irin can ɗin nan ba,amman dai za a iya kiransa da dogo kuma yana da ɗan faɗi amman ba shida ƙiba,yana da faɗin ƙirji sosai da kuma ƙwanji don zaka iya kiransa da ɗan restilin saboda ƙwanjinsa,haka yake ƙaƙƙarfa ne shi shiyasa wasu abokansa ke tsokanarsa ya koma ɗan dambe mana?sai dai kawai yayi dariya don shi sam damben ma bata taɓa burgesa ba,barshi dai da kallon ball don yana bugata sosai don yana son wasa ƙwallo da motsa jiki.
ɗan haɗe hannayena nayi a ƙirji ina kallonta,amman fuskata har yanzu a haɗe ina motsa pink lips ɗina masu laushi da kyaun kallo na ce mata"ke nake jira kinyi shiru".?
da sauri na buɗe baki zanyi magana,ina kallon idonsa sai naji na kasa faɗar abinda nake son faɗa ɗin,sai dai zuciyata tana gargaɗi na dana faɗa masa ko da hakan zai janyo wata matsalar,sannan zuciyata ta ƙara sakani a ruɗu doni aganina yadda Allah ya tsaramin komai mai kyau ne ajikina,ni aganina babu namijin da zai ce baya sona,don turawa ma ba hausawa sunsha kuka akan naso su, samari da dama sunsha jinya akaina amman fir naƙi so saboda ina motsa kambuna sosai.
Ahankali na ce"dama Aliyu wata magana nake son muyi,amman da da hali da ka É—an zauna".
na faÉ—i hakan cikin yanayin mutuwar jiki.
Kallonta nayi sannan na kalli agogona na ce"ina jinki amman kada ki wuce minti biyar zuwa shida don aƙwai abu mai muhimmanci da zanyi,don yau ne za'a kai lefe na."
wani irin mugun shork naji,na fara tari tamkar na ƙware ga mamakina sai naga bai ma damu da hakan ba,da kaina na buɗe fridge ɗin dake cikin office ɗina na ɗakko ruwan swan na fara ɗaɗɗaka har sai dana kaishi ƙarshe duk kuwa da sanyinsa.
zama nayi ina ajje gorar ruwan,na kallesa sosai naga shi wayarsa ma yake dannawa,haushi ya kamani don gani nake tamkar rainin hankaline don yasan abinda nake son faÉ—a masa tunda ba yaro bane,don Aliyu ayanzu haka yana da shekara 31 ne.
juyarwa da yayi na tsura masa ido,shap ɗin zaki ne dashi baki ɗaya faffaɗan ƙirji da kuma ƙugu irin na mazan fama.
ganin bai tanka min ba sai na buɗe baki cikin rashin ƙwarin gwiwa na isa inda ya ke daf dashi na ce"Aliyu don Allah ku dubi idona."
Kallona yayi É—in kuwa,sai naga ya juya ya ce"menene acikin idon naki?don ni dai banga komai ba"?.
ɗan rainin hankaline Aliyu na bugawa a jarida sai kuwa na ce"ƙarya kake Aliyu ka gane abinda ke ƙwayar idona,ba komai bane sai zallar Sonka Aliyu........"
na faɗi hakan ƙwallah na zubomin a idanuwa na,don tsahon wata biyun da mukayi a tare idan na ganshi sai inj wani feeling ɗina na tashi na sonsa.
a hankali ya tashi sannan ya ce"and that ni kuma bana sonki ba".
Da wani irin mugun sauri na rungumesa,tuni wani irin shork ya ziyarce mu a tare da sauri na jefar da ita gefe sannan na nuna ta da yatsana na ce"ayanzu haka zuciyata tana rayuwa ne da son wata yarinya,wacce at the age É—inta 16 ne budurwa ba budur bazar ba,don ni a tsarina bazan auri uwar mata ba kamar ke dake shekara kusan talatin".
da wani irin mugun sauei na tashi,idanuwana suna yimin wani irin yaji da raɗaɗin masifa na rasa wani irin kalami zan faɗa masa don zuciyata ta huta,da haushin waɗannan gwalagwalan ɗanyun maganganun nasa masu matuƙar zafi da yayyafin aman wuta.
bala'i nake son yi,amman na kasa saboda yadda zuciyata ta cika da baƙin cikin kalamansa na fara nuna ƙirjina da hannuna ina motsa bakina cikin kuka na fara ce wa.
"NI!
NI!!
NI!!!
Aliyu kake faÉ—awa irin waÉ—annan kalaman?ni kake kira baka so wata kake so ni ce uwar mata,wanda a shekaruna da har yanzu ban kai 20 ba ni kake zagi saboda wata kucaka maras galihu?wata tsinanniya........"
Tau tau ya wanke ni da wasu maruka har guda biyu,waɗanda sai dana ga wucewar wasu taurari masu matuƙar haske da aman tartsatsin wuta.
abinka da farin mutun nan da nan sai rawn face ɗinta ta kumbura tayi jawur yadda kasan nayi hatsari,gefen bakina ya fashe sosai jini ya fara ɗigowa tamkar an yanka ƙosashiyar kaza.
a hankali na ƙwanta zuciyata na yimin wani irin ciwon irin rayuwar dana ke ciki,tabbas ƙaddara tana zuwarwa ɗan adam a sanda baiyi tunani ba gashi ni ya ƙadartawa mahaifiyata haihuwar ɗan shege,yaro kyakkyawan gaske mai matuƙar kama dani tamkar an tsaga kara,ɗan kuɓul kuɓul dashi tunda sanda yana ciki ba shida yunwa,tunda kullum ana bani kuɗi dubu ɗaya kullum na wankin mota dashi muke cin abinci da sauran buƙatu,gashi kangon da muke ciki tunda muka taso har zuwa yau mai shi bai zo ya amsa ba,har mamaki nake ko dai mai shi ya mutune?.
da sassafe na tashi na buɗe idona da ƙer,saboda kukan jaririn daya tashe ni don kuka yake sosai tamkar za'a cinyesa ko za an sanyashi cikin wuta.
Da sauri na ɗaukesa jikina har yana kakkarwa,cikin zanin dana ƙudundune ina yi masa kissing ina rarrashinsa.
Kamar an ce in waiwaya gefen hagu na,abinda na ganine yasa na ƙwalla wata irin muguwar ƙara gami da saki yaron ikon Allah sai naji tamkar wani ya riƙe sa na juyo don inga waye ga tsoron abinda na gani yanzu wanda ya kusa zautar dani............ ✍🏻
*hum kuna son jin cigaban ko?cigaban me zai faru da Xulfa da Aliyu?zai so ta ko kuwa ba zai so ta ba?me zai faru idan har ya yarda ya aure ta É—in?ga aurensa na matsowa?*
*Me Zulfah ƴar mahaukaciya ta gani?me ya tsoratata har ta saki ƙaninta tilo?waye ya riƙe ƙanin nata?*
Wannan duk sai a book 3 in sha Allah wanda zai zamo paid ne littafin aƙwai har book 4 amman zaki biya 500 ɗinki don jin ƙarshen wannan gawurtaccen labarin?.
Ku boyoni don jin yadda zata kasance,wasan yana gaba inda zan nishaÉ—antar daku da abubuwa da dama,ciki kuwa harda kalolin girke girke da kuma hanyoyin sarrafa magunguna da kanki na mata.
Ga acc ga masu tura kuÉ—insu.
0037219728
fatima Rabiu sunusi
stanbic IBTC bank
ko kuma ku ƙwaɗomin kira ta no ɗina
***
sai na jiku,MRS GREEN ɗin ku ce.✍🏻