EYOON ƘALBI page 2
*EYOON ƘALBI....*
Page *2*
Hajja idanunta a runtse zuciyar ta na wani irin bugawa bakin ciki kamar zai kashe ta. Sumul ƙalau lafiyar Allah kamar ba ita ba haka Hanan ta miƙe zaune tana faman kalle-kallen mutanan cikin parlorn, sai kuma idanuwa suka koma kan Hajja kowa ya fara ja da baya-baya ban da Ummanta da malam Ayuba da suka daskare a wajan saboda tsabar ganin abinda ya faru yanzu. Tsayawa kawai Hajja tayi tana kallon ikon Allah, jikinta banda ɓari babu abinda yakeyi. Da wani mugun sauri lionman ya rungume Hanan ɗinshi, ita ma rungumeshi tayi tana kallon mutanan gurin ɗaya bayan ɗaya har idanunta ya kai kallonta wajan fuskar Hajja, sai kuma ta sakar mata murmushi dan ta tuna inda ta ganta.
"You see ba..? Da kuna ta wani ƙaryata mutane, dama mayu ai haka suke da shegen taurin kai da yawan rantse-rantse na rashin gaskiya. Kai kuma malam da kake cewa zaku ɗaukaka ƙara, shin har yanzu kana nan a kan maganar ka ko ka janye ta...?!"
Lionman ya faɗa yana kallon malam Ayuba a wulaƙance ce. Kai kawai malam Ayuba ya shiga ɗagawa dan bashi da ta cewa gaba ɗaya kanshi ya ɗaure yana buƙatar ƙarin bayani na wannan lamarin. Nan da nan guri ya fara kus-kus ana magana ƙasa-ƙasa alamun gulma.
"Heyyyyy layya..! see your way out...."
Bam-boy ya faɗa yana tsuke bakinsa irin na mararasa mutuncin nan. Kawai wasu zafafan hawaye suka shiga zubowa Hajja daga cikin idanunta, ƙasan zuciyarta na tafarfasa kamar zata tarwatse dan zafi da raɗaɗi. Ummanta ce taje da sauri ta riƙe hannunta tare da janta suka bar gidan, gaba ɗaya mutane suka bisu a baya sai habaice-habaice ake yi musu har suka shiga cikin gidan su.
Suna shiga gidan Hajja ta kuma fashewa da wani irin kuka mai tsananin gaske, kuka take na wani baƙin ciki wanda bata san yadda zata yi ta misaltashi ba. Umma ma kukan take dan yau kam taga ƙarshen wulaƙanci da rashin mutunci a cikin duniyar nan. Jira kawai takeyi maigidan ya shigo ta shaida mai, bata ko gama tunanin ba sai gashi ya shigo ranshi a haɗe da alama shima yaji zancen dan yadda fuskar shi take a murtuƙe kamar wani zaki.
Guri ya samu ya zauna tare da kallon Hajja wacce ke zaune tasa kanta tsakankanin cinyoyinta tana kuka cikin murya mai sanyi yace mata,
"Zo nan Hajjaju na, dawo kusa dani kinji yarinyata."
Kamar jira take tana komawa inda ya nuna mata ta kuma sakin wani gigitaccen kukan mai ratsa zuciya, kanta ya hau shafawa yana jin kukanta har cikin ranshi yace.
"Yi shiru Hajjaju na bana san shi, hakiƙa bake aka wulaƙanta ba ni suka wulaƙanta kuma na barsu da Allah domin kaf danginmu uwa da uba babu mayu a ciki wallahi." Girgiza kai ta shiga yi tana sake zubar da hawaye take cewa.
"Abba ko dai ni ɗin ba ƴarku bace ba? Hakika abun akwai ɗaure kai Abba duba da yadda kai ɗin fari ne, kuma Umma ma fara ce, Yaya Mubarak fari ne Yaya Jazuli shima fari ne Abba nice kawai baƙa a cikin ku, ni nasan wataƙila ni ɗin shegiya ce kuka rikeni a wajan ku na zama tamkar ƴarku, yanzu gashi yau na girma zan zame muku matsa...."
Da sauri Abba ya rufe mata baki da hannunsa yana jin wani irin zafi a ranshi, cikin gazgatawa yake mata magana. Umma dai shiru tayi tana share hawaye lokaci zuwa lokaci tana jin Abba na bawa Hajja labari,
"Khadijatul Mustapha shine sunanki na yanka, kuma ni ne nan mahaifinki, sannan kuma Ummanki itace mahaifiyarki, sai Mubarak da Jazuli duk yayunki ne uwarku ɗaya ubanku ɗaya. Hajja kin san Allah shine yake hallitar kowane bawa, domin babu wanda ya hallici kanshi Allah be bamu wannan damar ba. Amma duk wanda yake raina halittar wani toh dole shima fa a yiwa tashi dan befi Allah ya ɗora masa ba shima ko don a nuna mai izzina da kuma ishara. Toh a kullum mahaifiyarki takan yiwa 'ƴaƴan wasu dariya ko habaici musamman idan ta gansu baƙaƙe, ita ta ɗauka cewar farin fatarta zai hanata ta haifi baƙi ko baƙa a cikin zuriyarta. A lokacin da ta haifeki farace ke tarr Hajjaju, amma daga lokacin da kika fara wayo kina girma sai kika fara canza kala zuwa baƙa. Mahaifiyarki ta ɗauka ko rashin wanka ne kullum yasa kike dilewa, sai ta dawo yi miki wanka sau biyar ko goma a rana ɗaya kacal, har sai da taja cutar limoniya taso kamaki Allah ya temaka aka tareta da sauri, sai da nayi mata gargaɗi sosai tukunna ta dena tayi miki sau biyu ko ɗaya. Kina shekara 2 baƙinki ya fara yawa, har asibiti ta kaiki ban sani ba waiko rashin lafiya ce yasa kike hakan, nan likita yace mata halilttar Allah ce sai daga lokacin ta hakura, kuma daga lokacin bata sake haihuwa ba har zuwa yau. Tana sonki tana kaunarki dan tafi sonki akan yadda take son sauran fararan 'ƴaƴanta kinga kuwa ke jinin muce."
Share hawaye Hajja tayi bayan taji tabbacin cewar ita ɗin ƴarsu ce, sai ta kallesu tana sauke wata boyayyar ajiyar zuciya alamun taci kuka sosai, murya ƙasa-ƙasa take cewa,
"Toh amma Abba maganar maitar nan fa? kaga fa ina tsallaketa wallahi Abba ta miƙe tsaye. Anya ba gaske bane ba? wannan abun ya ɗaga min hankali na shiga uku ni Khadija ya zanyi?."
Shiru abba yayi yana kallon Ummanta dake faman share kwalla, cikin sanyin jiki ya shafi kanta yace,
"Wannan ne kuma bamu sani ba Hajjaju, Allah kaɗai ya barwa kanshi sanin wannan lamarin. Sannan kuma zamu tsaurara bincike dan gano inda matsalar take, gashi tunda na shigo unguwar nan zancen ake tayi, hakiƙa lamarin nan akwai ban al'ajabi, kiyi hakuri sannan ki dena yawan fita har sai abun ya lafa sosai kinji ko?!"
Kai ta ɗaga alamar toh sannan ta share hawayan ta, shigowar Atika ne yasa Abba miƙewa ya shiga ɗakin shi, itama Umma tashi tayi tabi bayan shi yayin da aka bar Hajja da Atika a wajan suna jajantawa juna. Yadda su Wizi suka damƙeta yayi mata ciwo matuƙar, sai dai babu yadda ta iya domin aikin gama ya riga ya gama.
**** ****
Sai da Hajja tayi wata ɗaya cur bata zuwa ko ina sabida abinda ya faru da ita. A lokacin Yaya Mubarak ya dawo kwanan shi ɗaya da zuwa a daran Hajja ta guntsa mai zancan maitar, ai kuwa dama Mubarak ɗan zafi ne dan haka ana idar da sallar asubahi be koma gida ba ya wuce gidan Alhaji Marwan ya dinga buga musu gate, me gadi naji amma tsoro ya hanashi buɗewa dan besan ko su waye ba da sassafiyar nan.
Lionman dake ƙoƙarin kwanciya kasan cewar idar da sallar shi kenan yaji bugun gidan yayi yawa, hakan yasa shi fitowa a fusace yana wani haɗe rai zuciyar na wani irin suya. A bayan gate yaga maigadi yana leƙa ƙofar yana cewa,
"Waye ne anan?!"
"M.M (Mubarak Mustapha) ne malam dallah zoka buɗe gate ɗin nan ko baka san aikin kaba ne ba?."
Wani mugun kallo Hydar ɗin yayiwa maigadi ganin yadda yake ɓoyawa jikin shi na rawa. Sannan Hydar ɗin yaje ya buɗe ƙaramar ƙofar ya fita dan ganin ko waye. Tsaye ya tarar da Mubarak ya wani murtuke fuska kamar wanda yayo dame yasha kaya ya kalli lion da ya fito yana yatsina fuska, shima yana mai wani kallo na kaskanci sannan yace.
"Kai arziki da rashin shi duk na Allah ne, amma me yasa baku ɗauki rayuwar ɗan Adam a bakin komai ba? Kaf dangin mu bamu da mayu wallahi, amma shine kayiwa sister na cin zarafi mai matuƙar muni a cikin rayuwarta? toh wallahi ba tsoro bane kuma a juri zuwa rafi kullum wata rana dole tulun zai fashe..."
Mubarak ne keta zazzaga rashin mutumci yayin da lionman be kula shi ba sai ma wayar shi da yake daddan nawa, kafin kace mene sai ga motar 'ƴan sanda a wajan. Ko ɗar Mubarak bejiba, suna ƙarasawa lionman yayi musu umarni da su Mubarak sannan ya shiga gida ba tare da ya furta musu ko da kalma ɗaya ba. Ran Mubarak ya kuma ɓaci ya fara ƙoƙarin fizge kanshi daga hannun ƴan sandan amma ina sun riƙe shi sosai a haka suka sanya shi cikin motar suka wuce dashi station ɗin su.
****
"Assalamu alaikum."
Malam Ayuba ya faɗa a cikin zauran gidan su Mubarak ɗin, daga cikin gidan Alhaji Mustapha ya amsa mai sannan ya fito hannunshi riƙe da hular shi yana gyarawa harya ƙarasa cikin zauran.
"A'a malam Ayuba ne barka da asuba."
"Barka dai Alhaji Mustapha ya gida ya yara kuma?!"
"Lafiya lau alhamdulillahi."
"Lafiya dai ko Malam Ayuba?!"
Malam Ayuba ya kalleshi bayan yayi kalar jimami, tsoro da fargaba suka kciki ɗarsuwa a zuciyar Alhaji Mustapha ganin yadda yanayin maƙocin nashi ya sauya kafin malam Ayuban yace.
"Wato gani nayi ƴan sanda sun kama Mubarak yanzun nan a can ƙofar gidan Alhaji Marwan ɗan kwangila, kuma daga gani rigima ce aka yi da yaron nan nasu Aliyu." Ras gaban Alhaji Mustapha ya buga jin abinda yake faruwa.
"Yanzu dan kafiya sai da yaron nan yaje gidan nan? Jiya ya dawo ina jin ƙanwar tashi a ɗakin shi tana gaya mai tunda ai baya nan aka yi koma menene, naji shi yana ta faman rantse-rantse akan sai yaje yayi musu rashin mutunci suma, shine fa na leƙa ɗakin na tsawatar mai akan kar yaje. Amma kaga da yake ɗan yau ne haifarsu kawai kake yi amma sai abinda ka gani a rayuwar su."
"Haka ne Alhaji yaran namu ne sai addu'a, yanzu dai kazo muje muji abinda ke faruwa a can station ɗin ko?!"
Malam Ayuba ya faɗa yana kallon Alhaji Mustapha, kaɗa kai yayi sannan yace.
"Toh bari naje na sanarwa da mahaifiyar tashi sai nazo muje."
Cikin gidan ya koma ya tarar da Umma ta shiga kitchen tana haɗa karin kumallo, nan ya sanar mata da abinda ya faru ta fara salati tana sallallami a haka Abba ya fita gurin da malam Ayuba ke jiranshi suka ɗunguma sai police station.
Suna zuwa suka tarar har an sanya Mubarak a cikin kanta sai hayaniya yake yi musu, nan Abba da malam Ayuba suka ƙarasa inda ƴan sandan suke, Abba yayi musu bayani cewar ɗan shi suka kamo yanzu. Wani ɗan sanda ne ya kalleshi sannan ya watsar cikin rashin bawa maganar tashi muhimmanci yake cewa da Abban Hajja,
"Okey mun kama ɗanka ne da laifi, sai kun bari munyi bincike dan gano gaskiyar lamarin."
Nan Abba ya fara basu haƙuri tare da bawa Mubarak laifi dan sai da yace mishi karya tada zancen amma yaki jin maganar shi, ganin basu da niyar basu shi yasa suka juya suka koma gida.
Hajja na cikin ɗaki ta jiyo Abbanta na gayawa Umma yadda aka yi, sai da ta bari sun shiga ɗaki dukan su sannan ta fita da sauri ta fiye ce. Police station ta wuce ta dinga bawa ƴan sandan hakuri amma sukaƙi sauraranta ba kuma wai gano gaskiyar ne basu yi ba, a'a kawai tsagwaran suna tsoran kar lion an yayi musu wata aika-aikar cikin aikinsu.
Fita Hajja tayi daga station ɗin cikin tashin hankali, ta ya zata bari saboda ita a kama ɗan uwanta? Kai tsaye ta wuce gidan Alhaji Marwan, tana zuwa cikin sa'a mai gadi ya zagaya cikin followers yana basu ruwa tayi saurin shigewa cikin gidan. A babban parlor taga Mamah da Hanan zaune suna breakfast, ta durkusa har ƙasa tana gaishe da ita. Tsoro ne ya shiga Mamah dan ta tuna ta cikin kaɗuwa ta bita da kallo, ganin haka yasa Hajja saurin cewa.
"Hajiya kiyi hakuri banzo da nufin komai ba sai ne man alfarmar ku."
"Ta mefa?!" Cewar Mamah tana faman kallan yanayin Hanan.
Gyara zama hajja tayi ba tare da ta kalli Mamah ba, tana shirin yin magana kawai sai ga lionman ya shigo parlorn yana faman danna wayarsa, hakan yasa be ganta ba sai da ya samu guri ya zauna, ita kuma da kanta ke ƙasa bata ɗago ba taci gaba da magana cewar,
"Hajiya dan Allah da manzan sa kiyiwa lion magana yace a saki yayana dan girman Allah ba dan halina ba."
Sai a lokacin Hydar ya kalli inda suke, cikin tsananin mamaki ya miƙe tsaye a fusace yana kallon inda Hanan ke zaune yaga ko lafiya lau take, Kafin ya maida kallon shi wajan Hajja yana cewa.
"Ke..! Meya shigo dake har cikin gidan nan? ko yauma zuwa kika ki ƙara lashe min yarinya ta ah?!" Kai hajja ta shiga girgizawa jin yadda yake maganar cikin tashin hankali, ba tare da ta kalleshi ba, cikin karyewar kai murya ƙasa-ƙasa tace,
"Dan Allah dan annabi ku temaka kuce a sake shi, wallahi in Allah ya yarda babu mu babu ku koda kuwa da kallo ne sai dai ayi sa cikin tsautsayi.."
"Ke..! Ke..! Malama dallah tashi kibar gidan nan, kuma wallahi ko ciwon kai wani yayi a cikin gidan sai kunga rashin mutunci gaba ɗaya danginku." Cikin zabura Hajja ta buɗe baki...
"Dan..."
Zata yi musu magiya yayi kanta zai nausheta da hannunsa kaka dake ƙoƙarin zama yayi saurin tarewa yana girgiza mai kai, yayin da Hajja tayi saurin miƙewa tsaye tana hararar shi cikin takaici taji kaka yana cewa.
"Kayya Aliyu, nasha gaya maka ko zakai komai banda haɗa kwanji da ƴa mace, ina gaya maka wannan abun ya kamata ka riƙe shi a kanka." Lionman ya dunƙule hannunsa yana cije baki yake faɗin.
"Ok naji amma ta tashi tabar gidan nan dan bama tarayya da irin su mayu."
Da sauri Hajja ta juya tabar gidan zuciyarta na kuna, wai shin meyasa mutane basuda adalci ne? dan ita sam bataji wani abu ko wani yanayi ba a jikinta bare ta gasgata maganar lion na cewar ita ɗin mayya ce, sai dai kuma ta kasa ƙaryata cewar ita ɗin ba mayya bace, duba da yadda tana tsallake yarinyar nan ta tashi tamkar babu abinda ya sameta.
Tana zuwa ƙofar gida ta tarar da Abban su, nan da nan jikinta ya hau rawa dan tasan sai ya tambayi daga ina take, gashi ba daga hanyar gidan su Atika ta ɓulloba bare tayi karyar daga can take. Da sai kawai tayi ƙasa da kanta zata wuce taji ya yi mata magana.
.
"Ke..! Hajja daga ina kike baki sanarwa da kowa ba kika fita..?!"
Sunkuyar da kai tayi jikinta na rawa alamar rashin gaskiya a tattare da ita, sai Abba ya matsa mata tare da cewa,
"Zoki wuce ciki kafin ki fara taramin mutane tunda kinsan yanzu da anganki ake dasa gulmarki..."
Sim-sim ta shiga ciki. Tana zama Abban na shigowa ya sake kallonta fuska a murtuke sannan ya kuma cewa,
"Daga Ina kike?!"
Kafin ta bada amsa sai ga Furera da gudu tayi sallama gidan, Umma na ganinta taji kirjinta ya buga dan ta gane fuskarta tun a ranar da tazo tace ana kiran Hajja a gidan ɗangwangila.
"Lafiya dai ko yarinya?!" Furera ta kalli inda Hajja ke zaune sannan tace dasu.....
*HAJJA CE*👈