FreeArewaPen original
EYOON ƘALBI
- 1views
- 90chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · EYOON ƘALBI page 1
*EYOON ƘALBI...*💕Page *1* Dandazon matasa ne zaune a cikin wata kyakyawar rumfa dake kafe a ƙofar wani makeken gida wanda ya gaji da tsaruwa tamkar ana gama zanashi aka kafa a wajan. Zazzaune suke akan wani makeken carpet sunyi da'ira suna yin wasan lido, gefe gudu kuma wani kyakkyawan matashin saurayi ne zaune akan wata haɗaɗɗiyar kujera yana ta faman tada hayaƙi gurin duk ya turnuƙe amma hakan baya damun waɗanda ke zaune a wajan saboda yadda suke abunsu ko kallanshi ma basayi. Idanunshi ya kai kan wata kwana da ya hango wasu 'ƴan mata sun nufo hanyar dasuke, yayi saurin gyara zamansa tare da zare cigarette ɗin bakinshi yana wani ɗanbanzan murmushi irin na gefen bakin nan, ya kuma matso da kujerarshi can baki-bakin rumfar ta yadda zaifi ganin matasan ƴan matan su biyu dake tafiya suna hira abinsu cikin nishaɗi. Ƙurawa wadda ya ɗanawa ido tun farkon hangenshi akansu yayi...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.