12
by @asmybaliyu
Cikin banbamin fa'da Auntyn maska ke fadin"wae wannan wane irin barci ne Kawayen amarya keyi da amarya"
Hajja ta kalleta tana fadin"ya kamata kije ki dubasu.
da haka Auntyn maska ta nufi part dinda suke Wanda part dayane aka ware masu.
Aliyu taci karo dashi yana kokarin shiga sashen Hajja,
da alamr daga part dinsu yafito Wanda iyayensu ke ciki.ware ido yyi yana kallon Aunty,
"Sae ina haka Aunty?"ya fada yana kallonta ."wajen kawayen amarya zani daita kanta amaryar ,yaufa daurin aure kowace ta saki baki tana barci .akwae ayukka masu yawa agabanmu."
"Ya kamata kam."
"Aliyu maska yyi mganar yana shigewa sashen Hajja.
Wani irin tsoro da fargaba ,
Tareda faduwar gaba Auntyn Maska ta tsinci kanta ciki,
Murza idonta takeyi tana fatar mafarki takeyi ,
Nafeesa ta fara kaiwa duka .
gaba daya ya'mmatan amarya kwance suke akan Rug din parlorn ,tamkar waya'nda zaa yanka.feena maska CE ta fara bude idanunta ,ta sauqesu cikin na Auntyn maska lokaci daya kuma take kallon su Amra da meermah.
Cikin Rawar murya Auntyn maska ke fadin" Ina lailah?"wannan wace irin kwanciya che haka?"baa cikin bedroom ku ka kwana ba."lokaci daya take Jero masu tambayoyin.,su kansu sunyi mmkin ganin su anan .haka kuma cikin su bbu wadda zata iya bada lbrn abunda ya faru adaren Jia.
Auntyn maska tayi karfin halin nufar hnyr Master bedroom haka zuciyar ta na wani irin dokawa.
Wanda ta nemi dalilin haka ta rasa,
Kwance take cikin bargo fuskarta che kurum awaje .
da sauri Auntyn Maska ta qarasa kusa da gadon."lailah!
"Lailah!"
"Lailah!" Kawae take iya fada ,jin bata motsi zuciyarta tayi wani irin harbawa .
A hnkali ta yaye duvet din,
Atsorace ta shiga Jada baya ganin laylah cikin wani irin yanayi mai wuyar misiltawa ,
Noooo!"aunty kawae ke iya fada ,
Cikin wata irin murya take kwalawa su feena maska kira.
dukansu aguje suka shigo cikin master bedroom din.
A rude suke kallon Aunty!"cikin Rawar murya take fadin"waye ya shigo maku da dare Baku sani ba."?
zare ido dukan su sukayi suna hngo wani mummunan al'amari tare da ya'r uwarsu mai wuyar misiltawa.
Hnnu Auntyn maska ta aza akai ,
Ta shiga jera Kalmar "innalillahi wainnah ilaihir Raji'un".
Wani irin duhu take gani cikin idanunta, hka
Takasa tsayuwa akan kafafunta .
Tamkar wata zararra ta zube akasa ,sae sa'annan kuka mai cin rae yazo mata kukan dake fitowa tun daga karkashin zuciyar ta ,
Kuka takeyi tana fadin." Ku kiramin Aliyu maska awaya." Ku kiramin shi Dan Allah."...
Cikin su aka Rasa wadda zata fita kiran Aliyu maska,
Cikin buga masu tsawa take fadin"don ubanku kun tsayamin akae,
da gudu Amra maska ta fita. A parlorn Hajja ta shiga arikiche lokacin Aliyu maska ,
Yana sipping bakin tea acikin mug .
Hajja che zaune agefensa tana lissafa kalolin abinci da zaayiwa ya'n zuwa daurin aure.
"Lfyn ki zaki shigowa mutane a haka.?" aliyu maska yyi mganar cikin buga mata uwar uban tsawa."
Muryar Amra na rawa haka hawaye na rolling akan fuskarta take fadin."yaya !
"Yaya laylah che." Kasa karasawa tayi kuka ta fashe dashi agigiche Aliyu maska ya miqe tsaye ,gamida dire cup tea din hnnunsa akan center table ,
da sassarfa yyi sashen da suke. Hajja na famar tambayr Amra "meya faru wae?"itama hajjar duk ta rikice ,Hnnunta Amra taja cikin kuka take fadin."zo mutafi Hajja !"
Haka taja hnnun hajjah sukabar parlorn.............
Kukan Aunty da yakeji yana Neman ya hargitsa masa kwakwalwa.
ganinsu Meermah a tsaye suma suna nasu kukan ya wani buga masu tsawa.
Cikin fushi yake nuna masu hnyr fita bbu musu suka fita da gudu.
Banging door din yyi da qarfi.
Kafin ya maida hnkalinsa kan Auntyn maska shima Jin yake zuciyarsa kamar zata Rabe gida biyu.
"Kiyimin bayani Aunty dan Allah." Meya sameta,
Aliyu maska yana mganar cikin wani irin yanayi tattare da fuskarsa ,
nuna masa gadon da laylah take kwance da hnnu ta shigayi.
Jikinsa na wata irin Rawa hka zuciyarsa na harbawa ya maida kallonsa awurin.
da azama ya dauke kansa akanta,
"Mutuwa tayi ne Aunty?" Aliyu maska na maganar hawaye na Rolling akan fuskarsa ,
Shi duk tunaninsa dauka yakeyi laylah maska ta mutu."
ganin Bazai fahimta ba haka zay yi wuya ya iya fahimta a yanzu irin qalar Rudewar da Aliyu maska yyi cikin kankanin Lokaci ,
Jin muryar Hajja sukayi akansu .tana fadamr fadin."wae meyasa mu laylah ake koke 2 haka?"tsakanin Auntyn maska da Aliyu bbu Wanda ya iya bude baki yyiwa Hajja mgana,
Saema Aliyun dake ko'karin shangabanta."kinga Hajja mutafi laylah barci takeyi ,
girgiza masa kai Hajja keyi tana binsa da ka'llon rashin Yarda haka yaki yarda su hada ido.
"Aliyu yaushe kafara rainamin hnkali kamar Dan uwanka khaleepha?" Jayemin a hnya kona haureka ,
Hajja mutafi plss laylah bata Jin ddi ne."kinga tasha mgani kibarta ta huta dan Allah karki tasheta ."Auntyn maska tana mganar still hawaye na Rolling akan fuskarta.
Afusace Hajja ke fadin"karku Rainamin hnkali!" kubani hnya ina jin zuciyata ba dai -dai ba.
Aliyu maska ya riqo hnnuta cikin fushi yake fadin"kibarta haka Hajja.!"..............Karo na farko da Aliyu maska ya daga harshensa akan kakarsa,
Mugun kallo Hajja kebinsa dashi hka lokaci daya ta fisge hnnunta cikin nasa."kai ba ubana bane Ali kabarni nasamu saidah."
"Lalailatu "
"Mamana''..Hajja kawae ke fada,Hnnunta takai kan goshinta akwae zafi sosae haka fuskarta akwae gumi ,
Yaye b/k din jikinta tayi . idonta sukayi mata mummunan gani ,lokaci daya zuciyarta ta hautsine ganin yanayin da Hajja ke ciki yasa sukayo kanta ,
" Aliyu dauko mota muje Asibiti ."Aunty tana mganar sabon kuka na taho mata.nan take Hajja ta some sae lokacin idon Aliyu sukayiwa jikin laylah maska mugun gani.Muryar baban Kaduna suke Juyowa a falo.
"Yaya taimaka ka dauko laylah." Meya sameta su?"baban Kaduna yana mgana cike da tashin hnkali ,
Is a long story.............."da haka tabi bayan Aliyu maska tana sharar kwa'llah...
kai da kawo baban Kaduna da Aliyu maska sukeyi a harabar Hospital din.
Sae lokacin Auntyn maska ta samu qarfin gwiwar yimasu bayanin cewar fyade akayiwa laylah maska."
Jin Kalmar fyade ta daki zuciyar Aliyu maska.
Tsaye yake da qa'fafunsa baisan lokacin da ya zube kafafunsa akan gwiwonsa ba.
Wannan karon hawayen da Aliyu maska keyi bana wasa bane,
Ciwon hawayen yakeji har cikin zuciyarsa ."noooo!aunty fadamin mafarki nakeyi dan Allah."Aliyu maska yana maganar yana saka taffukan hnnunsa akan fuskarsa,
Hawaye na mugun zuba afuskarsa hka zuciyarsa na wani irin dokawa.
Addu'a yake ta karyata hakan tache masa mugun mafarkine kawae yakeyi.
"da gaske nakeyi Aliyu maska fyade akayiwa laylah maska."
Tana iya Rantsewa tanajin bugun zuciyar Aliyu maska akai-akai.
da jajjayen idonsa ya dago yana kallonta ,wani irin kallo yake binta dashi Wanda bata ta'ba ganin hakan cikin idon Aliyu maska ba.
Ciwon bakone agaresu bakowane zay fahimta ba ,sae way'andda ke da danganta ka akan mummunan Al'amarin,haka bakowane zay fahimta ba sae Wanda dukkan abun yasamesu ,hka ba kowa zaiji ciwo ba.sae Wanda Abun ya shafi jininsa .wannan karon hawayen idonsa sun tsaya chak!"azuciya suke sauka da ciwo marar misiltawa.
So yake ya bu'da baki yyi mgana ya kasa ,kwallah kawae ke taruwa a idanunsa.Yau Aliyu maska ne da Arhar hawaye hka?"
Hawaye Auntyn maska tasa hnnu tana gogewa
Cikin rawar murya take fadin"Aliyu ka sassautawa zuciyarka dan Allah ."idan Kaine na ukkunsu akwanciya a gadon Asibiti bamusan yazamuyi ba ,
zama yyi akasa yasaka kansa acikin cinyoyinsa baiqara mgana ba.
*
Sororo ta tsaya tsakiyyar falon tana ka'llon khaleepha maska Wanda ke dunkule cikin duvet yana rawar sanyi.
da gudu ta isa garesa ,
Tana fadin"Yaya!"yaya khaleepha meya sameka hka?"Amra maska tana mganar cikin Rawar murya.
Numfashi yakeja yana sauqesa da sauri-sauri,karfin halin mikewa zaune yyi ganin Amra maska tsaye akansa .
Hnnu ta kai kan goshinsa zafi taji radau agoshinsa,bbu musu tayi saurin jayen hnnunta.
Hawaye na taruwa a idonta take fadin"bakada lfy ne yayah khaleepha? "Tana mganar kuka nazo mata.
Girgiza mata kai ya shigayi ,,wannan ciwon ba irin Wanda tasani bane.
bata nemi shawarar khaleepha maska ba ,ta dauki wayrsa dake ajeye akan center table dan kiran mami.taga wyar akashe ,
Karamar Nokia ta dauka tayi sa'a abude take lambar mami tayi dialling.
Bugu daya ta dauka ,
" mami yayah bayada lfy yana boy's quarters .
da haka Amra tayi saurin katse wayar ,lokaci daya taga khaleepha maska yasha toka.
"Amra yaushe muka fara wannan wasar?
Bata basa amsa ba.ta koma gefe tana kallonsa,
Muryar mami taji akansu .
Cikin tashin hnkali take fadin." Yanzu kuma meya faru?"
Langabe kansa yyi yana kallon mami ,
Cikin sanyin murya yake fadin"ki manta kawae zazzabine kawae mami !"kallon Rashin yarda take yimasa ,
"Ga babban likita har likita amma kai ke fara karya dokar likitoci .yasan inda mami ta nufa shiyasa ku'rum yyi shiru.
" Asibiti zamu Je kasamu Amra ta hada maka break fast kasha magani.
"Waye ba lfy mami?" Ya tambayi mami da sauri yana kallonta,
"Laylah maska akayiwa fyade wae adaren jia."
ya nemi ciwon da yakeji ya rasa.
da sauri yake girgizawa mami kae yana riqe da kansa Wanda ke Neman ya rabe gida biyu.
Kirjinsa yake masa zafi Wanda bai taba jin haka ba ,
A iya tsawon Rayuwarsa.
"Mami"........ Ki fadamin wasa kk dan Allah?" Yana mganar muryarsa na hardewa ,tsoro mmki suka kama mami.tana fuskantar wani irin yanayi afuskar khaleepha maska.
"Nidai na fada maka kasha tea ka kwanta kafin zuwa anjima.
da haka Mami ta nufi kofar fita Amra na biye daita.
da gudu ya nufi mami yana fadin" tsaya na kaiku mami.
Yana mganar muryarsa na rawa,
Shaye da toka take fadi"kaida baka da lfy.
Ina jin zuciyata ba dai dai ba mami."
Tsoki mami tayi tayi gaba ,farar jallabiyya kawae ya jona ajikinsa ya dauki car key zuciyarsa na wani irin bugawa.
*
Gaba daya zuriar maska sun cika hospital din zuwa yanzu ,kowa ya fahimci meke faruwa.kowa ya fahimci mummunan Al'amarin da ya shigo cikin zuri'ar maska lokaci daya ya tarwatsa masu zukata.
Bayani Dr.Hambal yakeyiwa ko'wa cikin natsuwa,
Matsalar Hajja jininta kawae ne ya hau.
"Laylah maska kam sae gyaran Allah." Harda dinki akayi mata awurin."dan ko waye wannan yyiwa Rayuwarta mummunan Illah!"sae da akayi mata dinki Awurin.
Haka kuma ya haddasar mata da tabuwar kwa'kwalwa koda taga namiji akanta ,
Tana iya suma .bbn tashin hnkalinsu akanta ,
Kukan da take yawan yi da kuma buge-buge kuka takeyi da zuciya da gangar jiki.
Mgana na karshe tana kiran wani waishi badar!"
Waye shi?"Dr .hambal ya fada yana gyara zaman gilashin sa,
"Shine Wanda zata aura." Baban Kaduna yyi mganar muryarsa a rikice,
"Waye yyi mata wannan mummunar iilar?" Khaleepha maska yana mganar muryasa cike da gajia ,
Idanunsa cike da abunda yakeji .
Hawayen da yake jarumtar mayarwa kar suyi nasarar sauqa akan fuskarsa sudin suka shiga ambaliyya akan fuskarsa ,
Juyawa yyi da gudu yabar cikin office din Dr.hambal"
Kansa ya daura akan sitari jikinsa na kakkarwa koina ,yana wani irin shesshekar kuka.
Bakin ciki sosae ke sauka azuciyarsa ,bai ganin laifin kowa sai nata. Maybe ma da saurayin nata suka hada kai .wayasani ko tasan abunda takeyi ita tabada kanta,
Wani sashen zuciyarsa yana son ya tsani laylah maska yana son ya tsinke sonta acikin zuciyar sa ya kasa.
Ta Riga da tagama cutarsa har Abada."but why?"
"Meyasa?" Meyasa Aysha."
Jin yyi gaba daya ya tsani Asibitin haka bayajin zai qara koda minti goma acikin garin zari'a.
duk da baya cikin natsuwarsa haka yyi rever's ya fisgi motar aguje ,
Burinsa awanan karon yajisa garin Kaduna.
Komae da kowa na duniar yafice masa arae.
Wani irin emotions ke taruwa a zuciyar sa Wanda baisan kalar su ba.......
#ASMY B ALIYU
#Lailah Khalifa
#maska family