Surayyahms
by @halimahz
Surayyahms mace mai shekaru 31 a duniya, ita ce marubuciyar littafin Ahumagga, Ajalin So, Arne da sauran su. ita ɗin ma'aikaciyar lafiya ce kuma tana girmama masu karatun littafanta saboda goyon bayansu gareta.
TAMBAYA: Da fari zamu so jin cikakken sunanki da kuma taƙaitaccen tarihin rayuwarki?
AMSA: Cikkaken sunana da iyayena suka bani shi ne Thurayah. So i go by Thurayyah Muhammad Sule. Ni ƙabila ce daga yankin middle belt nigeria, amma mahaifiyata bafulatana ce. Bauchi da kano duk garin zama ne a wajena. Sannan nayi islamiya mai zurfi dan zan iya cewa nafi shekaru 15 ina zuwa islamiya a rayuwata kuma nan gaba ma zan iya komawa. Nayi karatu a medical line fannin ilimin kare lafiyar ɗan adam da na muhalli, na gama shi a 2013. Na kama aiki a 2015 sannan a yanzu kusan ince na kammala karatuna na biyu shima degree ne fannin engineering and management, so na karanta course ɗin environmental engr/technology.. Familyna sune abu mafi muhimmanci arayuwana, Ni kusan uwa ce kuma babbar Yaya ga mutane da yawa. A taƙaice rayuwata dai cike take da tarin responsibilites ina ga iya abunda zan iya tsakuwa kenan a ciki.
TAMBAYA: wacce shekara kika fara rubuta? Kuma me yaja ra'ayinki ga fara rubutun littafai?
AMSA: inaga na fara rubutu around december 2017 bari dai na ce 2018 gaskiya. Babu wai abu kawai daga gwadawa sau ɗaya na tura sai naga ya karɓu fiye da yadda na ke tunani. Amma harga Allah ma bana bin hausa novel saboda ko kaɗan ba ya burgeni, ban ma san anayin shi a online ba hasalima sai da na zama idle a rayuwata ma kafin na san da shi.
TAMBAYA: daga fara rubutunki kawo yanzu kin fuskanci wani ƙalubale ne?
AMSA: A wajena ƙalubale ai shine manunin nasarar duk wata marubuciya. dan zan iya ce miki ƙalubale na sune suke jawomin nasararori masu girma, dan bantaɓa rubuta littafi a online na ƙare lafiya ba. sai na samu irin "satar fasaha, Gulmace gulmace, Cece kuce akan littafina, hassada ƙarara, ɓata suna, haushin gaira ba dalili, ƙyashi, da kuma mugunta. cikin waƴann babu wanda ba su zuwamin muddin na saki littafi..sai dai na wani yakan fi na wani.
TAMBAYA: matsayin me kika ɗauki rubutunki?
AMSA: Matsayin da na ɗauki rubutuna, na ɗauke shine a matsayin madubin rayuwa wanda yake haskawa mai hankli aibunsa dan ya nutsu ya gyara, ya ke kuma tsoratar da mai laifi dan ya shiryu. Rubutuna na kan ɗaukesa kogon ilimi ne wanda tamkar haskene ga rayuwan ɗan adam.
TAMBAYA: shin sai da kika nemi ilimi akan harkar rubutu kafin farawarki ko kuma kai tsaye kika tsunduma a harkar?
AMSA: Gaskiya kai tsaye ne. sabida harga Allah abu ne wanda bana ra'ayinsa ko da na gwada rubutuna na farko ina yi ina cewa na farko kuma ƙarshe, ashe dai kana naka Allah na nashi.
TAMBAYA: A cewar wasu mutanen karatun littafi na ɓata tunani da tarbiyya. shin kina ganin hakan ne? akwai shawara ko tsokaci dangane da wannan batu?
AMSA: Maganarsu gaskiya ce kuma ba gaskiyar bace kai tsaye. za'a iya cewa ba marubuta duka ba ne zamu taru mu zama ɗaya, dole akwai na ƙwarai akwai bara gurbi. Dalilin haka ya saka a yanzu mu ke da littafai masu faɗarkarwa da kuma wanda su ke lalata tarbiyan. Fatanmu dai shine Allah yay ruƙo da hannunmu ya kuma taƙaita mana yaɗa ɓarna dan kuwa bashi ne akanka da zuri'arka.
Shawarar da zan bayar shine rubutu domin lalata tarbiya ba ya ƙarko sannan baya tasirantar da ɗaukakar marubuci, sai dai ma ya shafa masa baƙar fenti na har abada. Sannan kar dan wani yanayi kai mai masa nasiha ka zaƙe kowa na laifi sanan mafi kyawun nasiha shine wanda ake yinshi a cikin kyayakkwan lafazi.
TAMBAYA: Ya mu'alarki tsakaninki da ƴan uwanki marubuta da makaranta littafanki?
AMSA: Na kasance mai son keɓantaccen rayuwa in an cire ƴan ƙungiyata da mu ka shaƙu. ata ɗaya fannin na gwada yin Mu'amala da wasu marubuta sai dai banji daɗin ko ɗaya ba. Dan haka na dena, na soke shi, kuma in sha Allah ba zan kuma aje wata ƙarƙarfan mu'alamar da ta wuce musulunci ba tsakanina da marubuta. tsakanina da makaranta Kuma gaskiya zan gaya miki bani da kalman da zan fassara miki yadda mu ke da wasu dan kuwa tamakar uwa ɗaya uba ɗaya haka su ka ɗauke ni. wasu kamar babban ƴa, wasu sun ɗaukeni abokiyar shawara da sirri. Kaɗan ɗinsu ne bamu jituwa saboda bana faukar raini ko kaɗan.
TAMBAYA: zan iya kutsawa cikin rayuwarki na miki tambaya akan wani abu da kika taɓa danasani akansa? kuma mene ya jawo hakan?
AMSA: Eh; danasani ai kamar fitsari muddin ka fiye shan ruwa sai kayi shi. Na kan yi danasanin amsa mutumin da ke neman husuma da ni, hakan ya faru da ni ne a online, ranar da wasu marubuta manya da su sai su ɓadda kamanni su nemu su ɓatawa littafina suna, ni kuma saina hasala na zazzagesu kuma na maida musu martani mai zafi, a ganina kana marubuci kana ƙarya da munafurci wa wani marubucin dan kawai kasan ya fika ko tauraronsa yana haskawa fiye da naka tamkar mugunta ce da rainin wayo. So amma nayi danasanin kula faɗar da nayi duk dama na cire fushin da ke raina.
TAMBAYA: kasancewarki me iyali, ɗaliba kuma ma'aikaciya, ta ya kike samun damar yin rubutu? hakan bai takura rayuwarki? ba ya taɓa lafiyarki?
AMSA: Alhamdullhi rubutu tashi tashi yake min. Muddin zanyi sallah, xan je aiki ko schook ko zanyi wani aikin gida to aje rubutu na ke a gefe abuna. Duk wani free time da na samu saina yi rubutuna hankali kwance, na fiyi da dare ko da safe.
TAMBAYA: matsayinki na marubuciyar littafin hausa. me yasa kike yawan saka turanci a labarinki?
AMSA: A farin farko dalilina shine na taso bana jin hausar, so ban jima da iya magana da hausa ba. Dalili na biyu kuma shine ban fara rubutun da niyyar ɗorasa akan wani yare ba. kawai na ɗauki hausa novel matsayin general name ne. Sannan tunda street writing nake yi babu wata doka ko licence, babu kakkarfan ƙungiyar rubutu na jaha ko na ƙasa da nake mata rubutu, to banga dalilin da zai saka na takurawa kaina ince sai nayi da harshen hausan ƙarara ba.
Dalili na uku shine ina son matan arewa su waye, su fi ƙarfin raini a wajen ƴan kudanci da suke ganin kamar in baka iya turanci ba kai jaki ne ƙasƙantacce, sannan su samu buɗe ido, a dama da su a ko ina in sun shiga a san da su. English official language ne, yau a kace kina bahaushiya kema kin iya shi sosai to wallahi ƙaruwa ce babba a gareki da rayuwarki dan duk inda za ki buɗi ba ki kiyi magana a cikin mutanen da ku ka bambamta zai zamo babu mai raina ki.
TAMBAYA: yayin da za ki fara rubutu, shin kina tsara komai da komai ne kafin ɗora alƙalami ko kuma da zarar labari ya haska a kwanyarki kike fara rubutu?
AMSA: Ai ba rubutu ba ma, komai a rayuwa in zanyi sai nayi tunani akai.
so fannin rubutu ma hakan na ke, dan sai na tsara labarin book daga farko har ƙarshe na ke fara rubuta shi.
TAMBAYA: kin taɓa rubuta labarin da kike jinsa a zuciyarki? Dalili?
AMSA: A'a bantaɓa ba amma nan gaba ina ga dole ne a samu. Yanzu dai na kan ji tausayi ne wajen tausayi na kan yi dariya wajen dariya. Daga zarar nagama littafi na mance shi kenan.
TAMBAYA: Cikin littafanki wanne ya sanya sunanki ɗagawa? Wanne ya ba ki wahala a rubutawa? da wanne Mutane su ka fi saninki?
AMSA: Cikin littafaina kuɗi ƙumbar susa shi ya kawo mun ɗaukaka fiye da kowanne.
Wanda ya ban wahalar rubutawa shine kuɗi ƙumbar susa saboda littafin nayishi akan masu ciwon ƙarfin sha'awa, dole ne akwai kalaman batsa a ciki.
Littafan da aka fi sani na da su Ahumagga da Ajalin So.
TAMBAYA: akwai wacca kike kallo matsayin madubi ko uwar ɗaki a cikin marubuta?
AMSA: A'a babu saboda bani da masaniya akansu sosai.
TAMBAYA: ban da ahalinki. mutane biyu da Allah ya haɗaki da su a rayuwa kike jin sun zama tsagi na jikinki?
AMSA: A online akwai Dr Siyama da Dr Asmeenat Zeeyan. A normally kuma ina da ƙawaye biyu wanda zan ce miki tamkar jini ɗaya haka muke da su tun yarinta har yau. Akwai Hajiya Zainab lawal da barister Patience.
TAMBAYA: Hajiya Zainab Lawal da Barister patience za ɓi mutum guda cikinsu?
AMSA: Zainab lawal zan zaba always.
TAMBAYA: me yasa Zainab Lawal always?
AMSA: Saboda ana ɗaukawa mu ƴan biyu ne kominmu tare muke yi kafin jami'a da sha'anin rayuwa taxo ta rabamu. Yanxu ina aiki a bauchi ita kuma tana aiki a lagos amma babu abunda ya sauya har yau, Ko ciwo nake itama sai kiga tayi. Inna shiga damuwa itama ta shiga kenan. Da mu ke school In aka bamu hutu a gidanmu take zama har muka yi shekara shidda ahaka. Sannan iyayenta suma kamar dai su suka haifeni haka suke jina. Da wuya ma dai ki ganmu kiyi tunanin cewa bamu haɗa jini da ita ba gaskiya.
TAMBAYA: a rayuwa me ke faranta ranki? me ke ɓata miki? me kika fi so a baki matsayin kyauta?
AMSA: Abunda yake faranta min rai inga ina da cikaken lafiya da kuma kuɗiii😂. Na tsani ƙarya, ƙazafi da uwa uba wanda ya tsana kuma ya raina min addinina da iyayena. Kyauta da nake son abani shine na agogo da na kuɗi.
TAMBAYA: wanne kafafen yanar gizo kika fi amfani da su wanda zai zama sauƙaƙar hanya da masoyinki zai sadu gare ki?
AMSA: Whatsap gaskiya.
TAMBAYA: zamu iya samun hotonki?
AMSA: A'a..bawai dan bana son aganni ba sai dan saboda ba ni da shi, na taso ne da matsalar photobia wato asali shi hasken camera na razana ni shiyasa hoto bamu jituwa in kin ganni a hotu to na dole ne yanzu haka babu ma hotona a wayata.
TAMBAYA: me za ki iya cewa daga ƙarshe?
AMSA: A ƙarshe dai ina miƙa godiyata wa Allah da yake bani dukkan wata dama a rayuwata. sannan ina godiya gareki Halima Zakariya you are one of the few people i know online da suke da mutunci a idona sosai. Allah ya ƙara hazaƙa da ɗaukaka.
Sannan ina godewa dukkan masoyana a duk inda su ke ina musu albishir da cewa in sha Allah gaba yafi baya yawa. Ina muku fatan alheri...
TAMBAYA: wanne albishir xaki yiwa wanda yaci karo da wannan tattaunawar?
AMSA: Albishir bai wuci in ce su kasance a GAMJI HEALTH PROGRAM GROUP ba, gaskiya Gamji health program group wani babban group ne wanda a zamanin nan sai an tsaga dubu kafin a sami irinsa. Group ne na ma'aikatan kiwon lafiya. Babban abun mamakin shine experts ne su ke koyarwa acikin wann group namu wanda kyauta ce bada ko sisinka ba, muna aiki tuƙuru wajen wayar da kan Mata, Ƴan mata, Tsofi da yara ƙanana akan zamantakewar Aure, tarbiya, mu'amala, Maganin mata, family planning, muna bada shawara kowacce iri, da uba uba muna koyarwa akan dukkan wata cuta da ta shafi mace, muna dealing da shi daidai gwargwado..misali cutar infection, rashin haihuwa fibroids, cancer, matsalar ulcer, basir,.muna wayar da kai akan hakkin mace da kuma hakkin miji da kuma hakkin ƴaƴa, sannan muna yin online classes Kamar sex master class, vagina infection master class family planning, etc. don haka ƙofar mu kuma kullum a buɗe take wa baƙi zaku iya tuntuɓana ta wann lambar *** domin jin ƙarin bayani.
___________________________
Alhamdulillah! Ƙarshen Interview ɗinmu kenan da Surayyah Muhammad Sule wadda aka fi sani da Surayyahms. fatan kun ji daɗin tattaunawar tamu. kuna iya ajiye saƙon ra'ayoyinku a comment section ko kuma ta DM ***, dangane da tattaunawar da muka yi da ita marubuciyar, ko tambaya a game da ita, tsokaci akan shirin, ƙarin haske dangane da abin da ya shige muku duhu. ku ci gaba da kasancewa tare da ni Halimahz a shafin ArewaBooks domin katari da muhimman abubuwa, ku yi following domin ta hakanne shirye shiryen da zan ke gabatarwa zai ke riskarku akan lokaci.
FATAN ALKHAIRI...