EYOON ƘALBI

EYOON ƘALBI page 3

by @hajjace22522

*EYOON ƘALBI....*



Page *3*


"Kiran Hajja a keyi a gidan alhaji Marwan ɗankwangila yanzun nan." Cikin sauri ta kalli inda take. 


"Hajja kinje gidan mutanan nan yau ne?!" Ummanta ta faɗa ranta a matuƙar ɓace, kai kawai Hajja ta gyaɗa ba tare da tace komai ba. Cikin takaicinta Umma tace,


"Toh ai kin san kwanan zancen sai ki tashi ki bita, yau dai kam babu inda zanje tunda bakya jin magana."


Kwal-kwal Hajja tayi da idanuwa sai hawaye, ita kam ta shiga uku da waɗannan mutanen, kuma wai dan tsabar rainin hankali ƴan gidan kawai take yiwa haka a garin nan nasu, kuma ma akan ƙaramar yarinya da bata tsare mata komai ba bare tace ramawa zata yi akan ta, dan haka take ganin kawai tsabar rainin wayo ne da kuma sabon wulakanci irin nasu.


"Ba zaki tashi kijeba sai kin tara mana muta ne ko?!"


"A'a babu inda zata je ke yarinya koma kice musu inji mahaifinta yace baza zoba."


Abbanta ya fad'a cikin ɓacin rai, kallon Umma yayi kamar zai yi magana sai kuma ya fasa yi ya shiga cikin ɗakinsa. Yana zama ba daɗewa kawai yaji sallama a ƙofar zauren, duk da yake cikakken namiji sai da ƙirjinshi ya buga, kanshi yai wani irin sarawa, ya miƙe da kyar ya maida hularshi saman kanshi sannan ya fito yana amsa sallamar tare da fita. Tsaye ya tarar da wani ɗan sanda hannunshi riƙe da kulki yana bubugawa a ɗaya hannun, gaban Abba ya faɗi ya daure dai ya ƙarasa wajan tare da bawa ɗan sandan hannu suka yi musabuha, cikin karayar zuciya Abban yake tambayar ɗan sandan.


"Lafiya dai ko?!" Ɗan sandan ya kuma kallon Abba fuskar shi babu yabo babu fallasa yake cewa,


"Eh toh bana ce ba dan kuwa ba ƙalau ba, muna buƙatar a fito mana da Hajja ta cikin gidan nan domin mun samu sanarwa cewar ita ɗan mayya ce yanzu haka ta kama Hajiya Rahinatu matar Alhaji Marwan ɗankwangila, sannan an shaida mana cewar dama ta taɓa kama jikar gidan, sun aiko akan cewar taje ta tsallaketa amma kunce bazata jeba, dan haka yanzu ina son ku bani Hajja dan kuwa ƙafata-ƙafar Hajjan zamuje ta tsallaketa sannan muga abinda hukunci zai mata na wahalar da bayani Allah da takeyi."


"Innalillahi wainna'ilaihir raji'un wannan wace irin musiba ce? yallaɓai mu fa ba mayu bane ba, shekarun mu nawa a cikin garin nan kuma a unguwar nan amma bamu taɓaci ko kama kowa ba sai yanzu kawai dan ana son ɓata mana suna? wallahi ni ba maye bane ba, sannan matata ma ba mayya bace, sannan duk cikin ƴaƴana babu maye sabida kaf zuri'ar mu babu mayyu."


Abba ya faɗa cikin tashin hankali, ɗan sandan ya buga kulkin hannunsa jikin bango sannan ya kalli abba yace,


"Yanzu dai duk baza mu shaida hakan ba har sai kun bamu ita munje gidan sannan zamu tabbatar da maganarka ina ita yarinyar take?!"


Cewar ɗan sandan yana ƙoƙarin shiga cikin gidan, da sauri Abba ya dakatar da shi sannan ya juya ya shiga yana kiran sunan Hajja cikin tashin hankali. fitowa tayi tana kuka sabida tasan zuwa aka yi tafiya da ita, Abba ya kalleta cikin tsananin tausayawa kafin ya kama hannunta suka fito. Hajja na kuka aka tasa ta a gaba har zuwa gidan Alhaji Marwan, a dai-dai ƙofar shiga falo suka tarar da Hydar sai faman bugun iska yake yi da hannu. Suna ƙarasawa ciki yasa hannu hankaɗa keyar Hajja zuwa cikin falon tayi taga-taga zata faɗi Allah ya temaketa ta riƙo kujera bata kai ƙasa ba, ya biyo ta yana cewa.


"Keee..! Billahil azim idan baki cire ranki akan mutanan gidan nan ba sai na illataki a banza a wofi. Ashe baki da mutunci? Ni daman tunda na ganki nasan baki da gaskiya."


"Hydar please rabu da ita bana son kana tada jijiyoyin wuya akan yara mata kasan wannan halin naka ne yaja Raudah guduwa ko? So please dan Allah ka dinga sassautawa ranka."


Da gudu Hanan ta zo ta kamo hannun Hajja cikin murna kamar dama sun saba da juna, ta shiga buɗe mata baki zata yi magana taji Hydar ya sunkuce ta yayi baya da ita sai faman huci yakeyi yana cewa.


"Ke..! look.. Mayya...! wallahi ki kiyayi kurwar ƴata domin tafi ƙarfinki idan ba haka ba sai na sa an kulle gabaki ɗaya zuriyarku... nonsense kawai..."


Hawaye ne suka dinga bin kuncin Hajja, ita kam yau ta shiga uku taga takanta ya zata yi da wannan bala'i?. sake kallonta Hydar yayi cikin tsananin ɓacin rai jijiyoyin kanshi duk sun tashi saboda ɓacin rai yana cewa.


"Kije ki sakar min Mahaifiya ta daga shigowarki ɗazu shine baki fita ba sai da kika kamata ko? Toh wallahi idan maitarki bata fita daga cikin gidan nan ba sai nayi ajalinki kinji na rantse, mahaukaciya kawai stupid girl, oya ke nake jira kije ki tsallaketa...!"


Jikin Hajja na rawa tana kuka kamar ranta zai fice ta ƙarasa inda Mamah ke kwance ƴan aikin gidan sai ririƙeta suke sabida wani irin fisga da take yi ga wani baƙin yawu da take fitarwa daga bakinta. Hajja tana hawaye harda shasheƙe taje wajan, tana tsallaketa kuwa sai Mamah ta miƙe a razane tana furta kalmar,


"Hasbunallahu wani'imal wakil."


Hydar ne ya ƙarasa kusa da ita tare da janyo ta cikin jikin shi hannunshi maƙale dana Hanan wacce ke ta faman kallon Hajja da kuka ya kuma tsananta a idonta, jikinta sai faman kakkarwa yake Hydar ya kalleta a wulakance cikin *IZGILANCI* yake cewa.


"Mayya kawai...! Toh ki tattara duk wani kwaɗayinki da yake cikin gidan nan don wallahi ko masu aikin gidan nan ne kika sake kamawa sai nasa an ɗaureki kuma kaf danginki babu wanda zai iya koda belinki ne ballantana su fito dake, wawuya kawai, dallah tashi kibar gidan nan karna ji miki rauni a banza a wofi, ƴar baƙa mummuna kawai, gawayi ma yafiki kyan gani da fasali."


Durkusawa Hajja tayi akan gwaiyoyinta hawaye na zubar mata saman fuskarta kalaman lionman suna sake zafafa mata zuciya ta kalli lion ɗin cikin tsananin kuka muryarta ma da kyar take iya fitowa tana cewa,


"Dan Allah kayi hakuri wallahi na rasa ta yadda ake wannan abubuwan suke faruwa akaina, wallahi banajin ko wane irin yanayi wanda zai tabbatar min da cewar ni ɗin mayya ce, sai dai kuma bani da wani makari wanda zai nuna cewar ni ɗin ba ita bace ba tunda gashi idan nazo suna samun lafiya, kuyi hakuri insha Allahu hakan baza ta kuma faruwa ba insha Allahu... kayi hakuri ka temaka kasa a fito da ɗan uwana dan girman Allah, dan dararjar manzon Allah (s.a.w) ba dan muba ba dan halin na ba."


Tsaki yaja mai mugun tsayi sannan ya kamo hannunta da iya ƙarfin shi yayi waje da ita har bakin gate inda Abbanta da malam Ayuba suke tsaye suna jiranta. Hankaɗa ta Hydar yayi ya kuma nuna ta da yatsan shi yana murzasu suna wani irin ɗas-ɗas yake cewa.


"Karki kuma dosar gidan nan wallahi, idan kuma ba haka ba sai na lahira ya fiki jin daɗi."


Yana kaiwa nan ya koma cikin gidan Abba ya kamo hannun Hajja wadda keta faman yin kuka suka wuce gida malam Ayuba na ta faman basu hakuri, lokacin mutane har sun taru suka bisu sai habaici ake yi musu daga bakuna masu daraja da akasin haka. Har suka shiga cikin gida Abba ya kulle ƙofar dan yaga alamar har ciki mutane suke sun biyo su.


Suna shiga suka tarar da Umma itama a tsaye hawaye sai faman zuba suke a fuskarta, Hajja tayi saurin ƙarasawa jikinta suka rungume juna cikin kuka Hajjan ke cewa.


"Wallahi Umma ban san ya ɗanɗanon maita yake ba, Umma ban taɓajin wani sabon yanayi ba a jiki na ko a cikin baki na ba, ta yaya zan tabbatarwa da kaina zargin da bayin Allahn can suke yi min? Umma yanzu mafa ina tsallake matar gidan nan ta tashi lafiya lau, na shiga uku ni Hajja ya zanyi da wannan masifar?! Umma ya zanyi ne ko gaya min please....?!"


Ta kuma rushewa da wani sabon kukan, shi dai Abba yana tsaye ya kasa cewa komai dan gaba ɗaya lissafinshi ya canza mai tunanin shi ya ɗauke zuga kunnuwan shi da suke jiyo mai maganganun ƴan ƙofar gida masu ƙara dagula mishi lissafi, ya kallesu jiki a sanyaye yace.


"Ku koma daga cikin ɗaki, sannan ku dena kukan nan Allah yana bayan mai gaskiya."


Komawa ɗaki suka yi Umma ta share nata hawayen ganin yadda Hajjan keta faman kuka ta fara lallashinta, suna nan zaune suka jiyo ana bubuga gidan, Abba ne yaje ya buɗe, ga mamakinsa sai yaga Mubarak ne, ya matsa mishi ya shiga ciki sannan ya kuma rufewa yabi bayan shi.


"Yaya Mubarak." Hajja ta fad'a tare da rungume shi, ɗago da kanta Mubarak yayi cikin takaici yake cewa. 


"Wato mutanan nan ko Umma? basu da mutunci wallahi, wato idan kana da kuɗi a duniyar nan babu abinda bazakayi ba a rayuwar nan tamu. Kai ya Allah kayi mana arziki mai albarka." Da sauri Umma tace,


"Amin kuma masu amfani." Mubarak yayi murmushin takaici Hajja ta kalleshi idanuwa jawur sai a lokacin ya lura cikin tashin hankali yace,


"Hajja me aka yi miki kuma?!"


Shiru tayi masa dan bata san abinda zata ce ba sai Umma ce tayi mai bayani ranshi ya kuma ɓaci yana shirin yin magana Abba ya leƙo yace.


"Mubarak karka yadda ka kuma yin wata magana, yanzu kamata yayi mu bari har mu gano ta inda matsalar take faruwa domin duk inda mukaje bamu da sheda hasalima sune masu shedar a hannu dan anyi hakan ba sau ɗaya ba kuma yanzu haka ina son ke Hajja karki kuma fita ko ina daga yau, wannan sharaɗi na ne akan ki. Kai kuma Mubarak karka yadda ka kuma zuwa gurin yaron can bana son fitana." Tabbas ba haka Mubarak yaso ba amma babu yadda zai yi ya kalli Abba zuciyar shi na zafi yace.


"Toh Abba insha Allah amma cin fuskar ne yayi yawa wallahi." Abba yayi murmushi mai ciwo sannan yace,


"Karku damu insha Allah komai zai warware, ku dena sanya komai a cikin rainku Allah yana tare da mai gaskiya."


Tun daga wannan lokacin Hajja bata sake fita ba haka kuma ba'a sake aikowa kiranta ba akan cewar ta kama wani ba. Sai dai kuma wata sabuwa da ta ɓullu domin kullum sai Hanan taje ƙofar gidan su, tana son shiga ciki amma tana tsoran karsu kore ta, amma kullum sai taje wajan gidan ba tare da kowa ya sani ba.





*HAJJA CE* 👈