Mutum Mugu Ne

Chapter 1

by @azizat

*MUTUM.....Mugu ne*

                     0️⃣1️⃣

©AzizatHamza2019

*Wannan labari tsohon labarina ne na sake dawo da shi, shine littafina na uku a jerin litattafan dana rubuta. Na rubuta labarin around 2018/2019. So ya ɗan kwana biyu, Waɗanda suka sanni tun lokacin dana fara rubutu zasu iya tuno labarin MUTUM mugu ne. Waɗanda basu karanta a lokacin ba ga shi nan na kawo shi. Gaskiya bani da lokacin da zan yi cikakken editing wa labarin amma nayi ƙoƙari wajen ganin na editing rubutun sama-sama.*



                

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*



          *GARIN KADUNA*

Da baya-baya yake shiga d'akin hannunsa d'auke da jariri sabon haihuwa, ba komai jikin d'an jinjirin sai wata Jar k'yalle da aka rufe masa ido dashi. Yana zuwa tsakiyar d'akin ya tsaya, bubbuga k'afansa na hagu yayi sau uku kafin ya juya Yana fiskantar wata bak'ar gunki dake daskare akan kujera, Gunkin an sassak'a shi ne kamar yanayin mutum yana zaune, saidai shi hannu shida gareshi kowanne gefe hannu uku, haka nan kuma fiskar gunkin fiskace mai muni ga shi ya zuro harshenshi waje, wata k'warya ce a gaban gunkin tana nan dafe a k'asa sai wata zuk'ek'iyar wuk'a dake tsakiyarta, Jaririn hannunshi ya d'aga sama yana mai fad'in

"Gani nan da abincinka na wannan lokaci ya kai 'ZUNUBU'. Ni Alhaji Kadi Maikud'i ina neman k'arin arziki, d'aukaka da daraja a duk fad'in duniyan nan. Na baka abinda kake buk'ata ina rok'on ka biya mini buk'atata". (Wa iyazubillahi)

Hannu yasa ya d'auka wuk'ar dake cikin k'waryar nan ya yanka jaririn sannan ya tsiyaye jinin cikin k'waryan nan tas, bayan da jinin ya gama tsiyaya sai ya d'auka jinin ya fara zubawa kan harshen gunkin, har ya gama zubawa babu jini ko d'il daya zuba a k'asa domin yana zubawa kan harshen jinin na 'bacewa alamar dai gunkin yana shanye jinin.  Yana gama bawa gunki jinin ya ajiye k'waryar a inda yake sannan ya d'auka gawar jaririn ya ajiyeta kan wani shimfid'a ya lullu'beta dashi, kawai sai gawar ta 'bace. Dariyar k'yak'yatawa Alhaji Kadi ya fara yi, ya fi minti biyar a haka kafin ya had'e rai tareda juyawa da baya-baya ya bar d'akin.......


***


            *ABUJA*

Yana saukowa daga jirki kai tsaye wajen da driver ke jiranshi ya nufa, fari ne sosai kuma dogo, yana sanye da royal blue three piece suit, sak'ale yake da bak'ar jaka, daka ganshi kaga wayayye wanda yasan duniya ko nace duniya ke damawa dashi, yayin daka kalleshi zaka d'auka d'an shekara talatin da biyar ne amma gaskiyar lamari shekararsa Arba'in da biyar. Ganin Ado driver shi kad'ai yasa shi cewa a zuciyarsa 'yau wace rana, Zaytunah tabi umarnin sa' ya riga yace mata kada tazo tararsa baya buk'atan hakan domin ya sani indai za ta zo d'in saita zo da yaransu gashi yau Monday suna makaranta.....

Tun da suka shiga cikin gidan gabanshi ya fad'i ganin motoci da aka parker a compound nasu sunkai goma. "Hasbunallahu! badai Zaytunah ta shirya wani shirmenta ba" a hankali ya fito daga motar ya nufi bakin k'ofar gidan, yana isowa k'ofar ta bud'e saboda facial recognition akayi wa na'urar kofar, matuk'ar shi ko Zaytunah ko yaransa uku ne suka tsaya a bakin k'ofar to bud'ewa zatayi kai tsaye, idan kuwa wani ne daban dole sai dai ya danna doorbell a bud'e masa daga ciki wadda ta cikinma akwai code da ake bud'ewa dashi. Yana shiga parlor yaga duhu, mi zai faru da za a rasa wuta a main parlor, k'ok'arin ciro wayansa ya fara dan ya haska ya kunna wutan sai kuma lokaci guda haske ya karad'e falon tareda shewa da dariya. Sek'ek'e ya tsaya yana kallonsu cike da haushi da takaici abinda ya sake inginzashi ma bai wuce wak'ar Happy Birthday da aka fara rera masa ba harda su tafi.

Sanye take cikin wata doguwar gown ta material peach colour, d'inkin ya kamata sosai duk shape na jikinta ya fito, tasha kwalliya ga wani fitinannen k'anshi da takeyi. Cikin taku na jan hankali da yanayi na gogewa wajen iya catwalking ta tako tazo wajen da ya tsaya, dan shi har lokacin yana tsaye a wajen ya kasa k'arasawa wajen da akayi decorations d'in. Ta manna masa kiss a cheek d'insa tareda kashe masa ido tace "Happy Birthday my one and only" ta kama hannunshi suka k'arasa wajen mitane.

A zuciyarsa yace 'yau Zaytunah kinci albarkacin Daddynki da yaranki da suke wajen nan da kinsha mari' yana k'arasawa yaranshi suka rungumeshi suna masa sannu da dawowa. "Wato ma yaran basuje makaranta ba ya fad'a a ransa, Nurain ne ya k'ar'ba jakar da ke sak'ale a kafad'arsa ya haura da ita sama, itakam uwar taro batama damu da kayan daya d'auka ba, sai wani murmushi takeyi tana wage hak'ora kaman wadda aka mata albishir da Aljanna, daurewa kawai yakeyi shima yana d'an sake fiska har aka gama yanka cake, Dan idan ba ta rik'e hannunsa ba shi bazai yanka ba. Mutane sai congratulations suke masa bisa karramawa da aka masa a k'asar America, shi dai kawai murmushin yak'e yake tayi..

Zaytunah ta ce " Hello guys, I'm going to make a toast to my one and only love, Mijina ni kad'ai" aka saka dariya ta cigaba " As you all know Dr Sajid, my husband clicks 45yrs today, also making it 10yrs 4days of our wedding anniversary, inaso ku tayani yi masa addu'a, ya sake samun shekaru masu yawa, mu zauna tare cikin farin ciki da kwanciyar hankali" ta d'aga champagne glass nata tareda cewa "cheers to Dr Sajid" suma mutanen wajen suka ce "cheers"

Sajid kamar ya mutu dan takaici amma ya daure dai ya 'boye 'bacin ransa. Hotuna aka fara yi musu abinma harda na hauka, dama Zaytunah uwar son hoto ce, mutanen da suke wajen yawancinsu 'yan uwan Zaytunah ne, duk da suma 'yan uwansa ne amma sun fi kusa da ita, yana nan tsaye yaji an shafa kafad'arsa da salo na bariki, da sauri ya juyo yaga wace karuwarce ke ta'ba masa jiki, wani shegen murmushi ta masa tareda wani tsuke baki tace "Happy Birthday handsome" ganin Sadiya agidanshi yasa yaji zuciyarsa na tafasa duk jijiyoyin jikinshi suka tattaso, shikam idan ya k'ara minti d'aya anan bai san mizai iya biyowa baya ba, dan haka kawai yabar wajen da sauri ya rink'a ratsa mutane har ya haura sama, itakam Zaytunah anacan anata selfie da wasu friends d'inta batama lura yabar wajen ba.

Kai tsaye d'akinsa ya wuce yana zuwa ya zauna gefen gado ya rik'e kansa yana jin wani masifaffen ciwon kai, abubuwan da suka faru shekaru hud'u da suka wuce su suke masa yawo a k'wak'walwarshi, ya tsani Sadiya, tsana mai muni....

Sady ta k'arasa wajen Zaytunah tace "babez Sajid ya haura sama kije ki duba ko yana buk'atan wani abu" da sauri ta ce "shit ya ganki ko?" Sady ta girgiza mata kai....

A hankali ta haura sama tana tunanin mi zai biyo baya dan tasan Sajid zai iya hak'uri akan komai amma banda zama inuwa d'aya da Sadiya, ita kam ta rasa dalili. Tana shiga d'akin ta hango shi ya rik'e kai, idonsa yayi jaa. Ta k'arasa wajen ta zauna gefensa zata sa hannu ta shafa fiskarsa ya bige hannun. Tashi yayi cike da masifa ya ce "bayan kinyi duk abinda ranki yake so banyi magana ba, you dare bring that whore to my house, Wallahi Wallahi Zaytunah duk ranar da na sake ganin waccar disgusting bitch d'in a gidana dake da ita saikun fiskamci mummunan al'amari, and ki sani zaki iya rasa aurenki akan haka"

Itama tashi tayi cike da masifa tace "haba Sajid yau fa ranar farin ciki ne bai kamata ace kana irin wannan magana ba, duk irin abinda na shirya maka na alheri baka gani ba sai kuskurena d'aya, kasan ba yadda za'ayi na gayyaci friends d'ina nabar Sady, she's my best friend"

Hannu ya kai zai mareta sai kuma ya fasa cike da takaici yace "mark my words, next time naga whore d'in nan a gidana I'm going to kill her"

"Sajid wai yaushe zaka appreciating d'ina ne, when will you open your heart for me, shekara goma kenan kullum cikin so nake naga na faranta maka amma baka gani, Ko da ace auren had'in gida aka mana amma kai kasan inasonka, I Love you and only you, Kai kanka kasan wannan taro dana had'a dan kai nayi, dan na nuna maka how important you are to me, amma gashi ko godiya baka min ba, sai ma masifa da kake ta min" ta k'arasa maganar kaman za ta yi kuka.

Taku biyu ya yi sannan ya tsaya ya goya hannunsa a baya yace " When you learn to be a good wife then I will love you" ya juyo a fusace yace "shin wai kin kasa fahimtata ne ko kuma bakyaso ki fahimceni, nayi yawo k'asashen duniya sun fi ishirin, I live outside Nigeria for more than 25yrs, but not for once have I celebrated my birthday, ke kanki kinsan wannan, kinzo kin yi almabozzaranci da kud'i kice kin yi domin ni, Kayan da kika sa da accessories da kwalliya da aka miki zai kai 200k, anyi decorations plus cake shima kusan 300k, food and drinks da akayi almost 150k masu hoto plus other workers za a biyasu kusan #300k almost a million or did I miscalculated it?" Shiru tayi "answer me!" Ya daka mata tsawa still batace komai ba ta fara wiki-wiki da ido dan da ta gaya masa 1.5m ta kashe wajen had'a birthday party d'in nan kila dukan ta zai yi.

"Haba Zaytunah kiji tsoron Allah, idan yau mune gobe ba mu bane fa, kin kashe 1m a shirme da shiririta, of course yau birthday d'ina ne but kinsan da cewa exactly this date mahaifiyata ta rasu. This kwalliya da kikayi harga Allah wa mutane kika yiwa ba ni ba, tunda tun kafin na gani an riga an d'aura a media masu yabawa sun gani kuma sun yaba"

"But my one....."

 "Leave my room!" Ya daka mata tsawa, jiki ba k'wari ta yi hanyar waje dan tasan idan bata fita ba zai mata tsiya. Har ta kai kofa taji yace " na Baku 30mins, su gama ciye-ciyen da zasuyi su barmin gidana idan ba haka ba zan koresu da kaina, and kar d'an iskan daya kunna min kid'a a gida" .........

***

       *PLATEAU.....*

Sunfi awa biyu suna jiran yayan nasu amma har yanzu shiru bai dawo ba. Tsaki khairy tayi cike da takaici ta ce "nifa na gaji Nazima, tun tuni muke jiranshi amma yak'i dawowa" wacce ta kira da Nazima ta gyara kwanciyar da tayi akan two seater dake falon tace "kin ga Khairy ko dare zai dawo ina nan ina jiran shi, yau saina k'ure k'aryarsa" suka ci gaba da zama a falon.

Bayan minti ishirin sukaji tsayuwar mota, da sauri Nazima da Khairy suka gyara zamansu dan sun san yayan nasu ya iso. Bud'e k'ofa akayi wani police ya fara shigowa da kaya nik'i-nik'i, sannan yayan nasu ya shigo d'auke da Farida a hannunshi, babu uniform ajikinshi yana sanye da shadda ash color....

Ganin su da yayi ya had'a rai, yace "mi kukeyi anan?" Da sauri suka durk'usa suka gaisheshi ya amsa musu fiska a murtuke. Anty Zainab ta fito daga d'aki sanye da wata riga da skirt na atampa wadda ya sha wani fitinannen d'inki dan kuwa rabin breast d'inta suna waje, skirt d'in kamar idan tayi wani wawan nishi yagewa zai yi. Ta rungumeshi a gabansu ta fara masa deep kiss, ko kunyar Farida dake kafad'arsa ba su ji ba, balle kuma su. Sunfi minti d'aya a haka kafin Anty Zainab ta janye jikinta tace "Baby nah sannu da dawowa gashi sisters naka tun d'azu suke ta jiran ka, har sun gaji".

Nazima a zuciyarta ta ce 'munafukar Allah, tun da mukazo ko kallon kirki bata mana ba balle ta bamu ruwa, k'arshen rowa ma tana gama girki ta rufe kitchen d'in da key, amma yanzu tana nuna kamar ta damu dasu'

Mik'a mata Farida ya yi yace " je ki had'a min ruwan wanka, barin ji mi ke tafe da su"

Ko zama bai yi ba yace "ehen mi kuka zo yi?"

Nazima ta ce "Yaya Isa dama kace idan an biya albashi muzo zaka bamu kud'in Jamb registration"

Cike da masifa yace "wato dama bibiyan albashina ku ke yi, har kun san an biya mu albashi, to jarababbu saura kuma a biya muku ku kasa samun points mai kyau"

Tare suka had'a baki wajen cewa "Insha Allah Yaya za mu yi k'ok'ari"

Ya wuce d'aki yabar su a falon....

"Tab yau mun taki sa'a tunda ya amince zai bamu" inji Khairy

"Tukunna dai, kika sani ko ya bamu rabi kawai" Nazima ta amsa mata.

Yana shiga bedroom nasu ya nufi wajen drawer ya bud'e tare da d'auko bandir d'in d'ari biyar ya fara irgawa.

"Baby nah mi kake yi hakan?" Zainab ta fad'i bayan ta fito daga band'aki.

"Sweetheart kud'in registration na jamb zan bawa su Nazima kin san tun last month suke damu na"

Zuwa tayi ta wafce kud'in a hannunsa tace " akan me zaka biya musu suna nan zuga-zugan 'yan mata dasu ace wai sai kaine zaka biya musu kud'in Jamb, Baby na kar ka wani dami kanka, suna da samari dayawa musamman Nazima tunda naga tafi kyau. Idan ka basu kud'i yanzu kud'in birthday ɗin Farida fah? kaga ko gifts da za a bawa guest baka siya ba tukunna balle kuma kud'in DJ da zamu kira" ta fara shafa k'irjinsa cikin salo da yake nuna gwanancewanta cikin bariki ta cigaba da shafarsa a hankali tana yin k'asa da hannunta. Tuni ya bircike yace "yanzu ya za mu yi kinga sunce wai k'arshen satin nan za a rufe"

Bata dena shafar jikinsa ba tace "Baby basu kud'in mota kawai su tafi kace suyi hak'uri sai wani watan ka biya kud'in makarantar Farida dan haka baka da kud'i"

Jiki na rawa saboda ta fara shafa Engine nashi yace "ki basu dubu biyu to su hau mota"

Ta ja wani dogon tsaki ta cire #500 ta mik'a masa ta koma gefe tace "idan wannan bai ishesu ba su taka da k'afa" ta maida sauran kud'in cikin drawer.

"Shikenan Zee barin basu hakan" sai da ya tsaya yad'an saita kansa kafin ya fita daga d'akin.

Ganin ya jima bai fitoba yasa duk su ka yi jugum. Yana fitowa ya ajiye #500 akan center table yace "Nazima ga kud'in mota ku wuce gida zan ga abinda zai wakana kafin sati ya k'are dan yanzu ba kud'i a wajena na riga na biya kud'in makarantar Farida dasu".

Kallon juna suka farayi sunma rasa ta cewa da k'yar Nazima ta d'auka jakarta tace " mun gode Yaya amma ka sani akwai Allah" taja hannun Khairy zasu fita suka jiyo Zainab na cewa " lah Nazima ku tsaya kuci abinci mana, tun tuni kuke nan ai"

Kallon tsana Nazima ta mata sannan tace "munafikin mutum bai yiba, kuma wuta bal bal idan baki tuba ba" da haka suka fice daga gidan da sauri suna ji Yaya Isa nata zaginsu amma ko ajikinsu...

Kafin su k'arasa bakin Barrack d'in suka samu wani ya musu lift zuwa cikin gari......


***


               *KADUNA*

Da sauri sauri take saukowa daga stairs d'in, ta riga ta makara gashi tanada board meeting saboda Daddynta baya k'asar ita zata wakilce shi. Tana isowa k'asa ta hango Mom na jera abinci a dining. Cike da shagwa'ba tace Mom ina sabon driver da kika ce kin sama min ya kamata yazo ya rik'emin handbag da files d'in nan kuma banga kowa ba"

Wacce aka kira Mom wata mata ce me kimanin shekaru 48yrs ta sha ado cikin shiga ta manyan mutane, " Layla ki fara yin breakfast mana kafin ki fita"

"Oh no Mom I'm late already, sai na dawo" ta fita daga falon da sauri....

Tun da ya d'aga ido ya hangota bai sake maida idonsa ba, sanye take da wata jeans leggings blue, da Jacket light pink akwai farar riga ta ciki domin ba a buttoning Jacket d'in ba, earrings d'inta Bangles, purse da block heel data saka duk kalar jacket d'in ne. Ta d'aure gashinta da wata farar gyale dan kuwa rabin gashin ko ince wig data sa a waje yake. Ta kusa k'arasowa wajenshi ta tsaya ta fara d'aukan hoto, tayi post sunfi goma kafin ta hak'ura ta k'araso wajen motar ta tsaya. Shi dai yana daga ciki yana ganin ikon Allah, tayi minti biyu a wajen kafin ta bud'e motar ta shiga. Cike da gadara tace " Kai new driver ka kiyayi kanka daga zuwa ka karya doka biyu karka kuma na uku dan it means you are fired, nasan an baka rules d'ina k'ila baka karanta bane, to idan ma baka karanta ba kaje ka reviewing da kyau cox failure to follow my rules means loosing your job, na maka alfarma saboda yau ce ranar ka ta farko"

Dariyar takaici yayi sannan yace "Ranki shi dad'e koba komai ai kya min sallama ko, nasan dai ked'in musulma ce"

"What the heck! Kanada hankali kuwa? Lallai kanka ba d'aya yake ba"

Bai juyo ya kalleta ba amma yana ganinta ta madubi yace" kaina d'aya kuwa, naga rules naki amma ni bazan iya binsu duka ba, kince duk safiya idan zaki fita saina shiga na k'ar'ba jakar ki na shigo da shi cikin mota, sannan idan kinzo dole ni zan fita na bud'e miki k'ofa, I'm sorry to say niba aikin bodyguard aka d'aukeni ba, Ni driver ne, ki nemi bodyguard da zai miki wannan bautar amma bani ba, ni d'aukata akayi aiki akan na kaiki duk inda kikeso kuma da kowace mota kikeso a lokacin da kikeso, bayan wannan duk sauran baya cikin aikina"

"OMG! Kai dolon nan kasan da wa kake magana kuwa, Ni *Layla Kadi Maikud'i* the only child to Alhaji Kadi Maikud'i, the only heir apparent to Kadi enterprises, the......."

Ji kawai tayi ya figi mota sun bar gidan mamaki da haushi ya cikata wato ma ya maidata 'yar iska, ganin dai dama ta riga ta makara yasa ta kyale shi bata tanka masa ba, tace aranta "barin gama office work zakaga walak'anci"........



Please Follow me on:

Wattpad: Azizat_Hamza

Arewabooks: Azizat Hamza