FreeArewaPen original
Mutum Mugu Ne
- 1views
- 63chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Youtube: Marubuciya Azizat Hamza ***: Azizat_Hamza Tiktok: Marubuciya Azizat Instagram: Marubuciya Azizat ***: ***
Sample · Chapter 1
*MUTUM.....Mugu ne* 0️⃣1️⃣©AzizatHamza2019*Wannan labari tsohon labarina ne na sake dawo da shi, shine littafina na uku a jerin litattafan dana rubuta. Na rubuta labarin around 2018/2019. So ya ɗan kwana biyu, Waɗanda suka sanni tun lokacin dana fara rubutu zasu iya tuno labarin MUTUM mugu ne. Waɗanda basu karanta a lokacin ba ga shi nan na kawo shi. Gaskiya bani da lokacin da zan yi cikakken editing wa labarin amma nayi ƙoƙari wajen ganin na editing rubutun sama-sama.* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *GARIN KADUNA*Da baya-baya yake shiga d'akin hannunsa d'auke da jariri sabon haihuwa, ba komai jikin d'an jinjirin sai wata Jar k'yalle da aka rufe masa ido dashi. Yana zuwa tsakiyar d'akin ya tsaya, bubbuga k'afansa na hagu yayi sau uku kafin ya juya Yana fiskantar wata bak'ar gunki dake daskare akan kujera, Gunkin an sassak'a shi ne kamar yanayin mutum yana zaune, saidai shi hannu shida gareshi kowanne gefe hannu uku, haka nan kuma fiskar gunkin fiskace mai muni ga shi ya zuro harshenshi waje, wata k'warya ce a gaban gunkin tana nan dafe a k'asa sai wata zuk'ek'iyar wuk'a dake tsakiyarta, Jaririn hannunshi ya d'aga sama yana mai fad'in"Gani nan da abincinka na wannan lokaci ya kai 'ZUNUBU'. Ni Alhaji Kadi Maikud'i ina neman k'arin arziki, d'aukaka da daraja a duk fad'in duniyan nan. Na baka abinda kake buk'ata ina rok'on ka biya mini buk'atata". (Wa iyazubillahi)Hannu yasa ya d'auka wuk'ar dake cikin k'waryar nan ya yanka jaririn sannan ya tsiyaye jinin cikin k'waryan nan tas, bayan da jinin ya gama tsiyaya sai ya d'auka jinin ya fara zubawa kan harshen gunkin, har ya gama zubawa babu jini ko d'il daya zuba a k'asa domin yana zubawa kan harshen jinin na 'bacewa alamar dai gunkin yana shanye jinin. Yana gama bawa gunki jinin ya ajiye k'waryar a inda yake sannan ya d'auka gawar jaririn ya ajiyeta kan wani shimfid'a ya lullu'beta dashi, kawai sai gawar ta 'bace. Dariyar k'yak'yatawa Alhaji Kadi ya fara yi, ya fi minti biyar a haka kafin ya had'e rai tareda juyawa da baya-baya ya bar d'akin.......*** *ABUJA*Yana saukowa daga jirki kai tsaye wajen da driver ke jiranshi ya nufa, fari ne sosai kuma dogo, yana sanye da royal blue three piece suit, sak'ale yake da bak'ar jaka, daka ganshi kaga wayayye wanda yasan duniya ko nace duniya ke damawa dashi, yayin daka kalleshi zaka d'auka d'an shekara talatin da biyar ne amma gaskiyar lamari shekararsa Arba'in da biyar. Ganin Ado driver shi kad'ai yasa s...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.