Chapter 3
by @azizat
*MUTUM.....Mugu ne*
03
©AzizatHamza2019
*BAUCHI*
Wata budurwa ce ke kwance kan gado baza ta fi 19yrs ba, tana waya sai shek'a dariya takeyi, cikin hirar tasu suna sako maganganun batsa ciki. Wata budurwar ce kuma ta shigo d'akin a gajiye itama baza ta fi 20yrs ba, ta cillar da dogon hijab d'inta tareda jaka, ashe wata doguwar gown ce wadda kamar net aka yi shi, domin ba abinda baka gani ajikinta, ta kwanta kan gado tana nishi.... d'ayar dake waya ta katse wayar da take ta kalli 'yar uwartata tace "Nazira lafiya, ya na ganki a gajiye haka?"
Wacce aka kira da Nazira tace "wallahi Waheeda wancan gayen dana ce miki za mu had'u yau, ashe ina mishi kallon yaro-yaro ashe ba yaro bane, gogeggene wajen harka, na jima ban had'u da kamarsa ba, tun wata biyu da suka wuce dana had'u da wannan Ustaz d'in lokacin da mukaje Kano, in gaya miki yau na jigata sosai"
"Ki ce yau kinje 360° kenan, I envy you oo, ni yanzun wannan shegen cikin ya hana ni jin dad'i wallahi"
Nazira ta tashi ta zauna tace "yawwa wai Waheeda ya zakiyi da wannan cikin ne? kinga Abba ya kusa dawowa kuma kinga cikin ya fara fitowa fa, Ina maganarku da Jameel ne?"
"Ai dama jira nake ki dawo na gaya miki yau har da Alhaji Kadi Maikud'i nayi magana, kuma na gamsu da bayanansa"
"Ban gane ba, waye Alhaji Kadi Maikud'i kuma?"
Waheeda tace "kefa dad'ina dake mantuwa, yanzu tun da muka had'u da Jameel nace miki shi babban yaron Alhaji Kadi ne, wannan d'an kasuwan nan millionaire dake Kaduna"
"Yo ni ina zan tuna da wannan bayan masu kud'in da muke tare da yawa suke"
"Dalla can ke kuma, to dai Jameel babban yaron shine yana ji da shi, dama can da yace karna zubar da cikin wai Ogan shi ne yake son jaririn saboda yana business da su"
Nazira ta zaro ido "wani irin business kuma ana zaune lafiya ko dai yana tsafi dasu ne"
"Ke kuma dad'ina dake ba kya cin riban zance, sai ki tsaya na kai aya mana kafin ki fara naki sharhi, dama wai yana renonsu ne a gidan marayu da yake dashi, to inda yake samun kud'i dasu shine, idan anzo adopting nasu yana bayarwa da tsada, sannan masu kawo tallafi gidan marayu shima yana yagan rabonsa"
"Kai duniya ba gaskiya yanzu gidan marayu ma baza'a yi dan Allah ba sai dan kud'i"
"Nazira kenan ai yanzu duniya kota yayane neman kud'i ake yi, ba a damu da haram ko halal ba"
"Amma Waheeda ki haifi d'an ki sayar da shi, baki fa san gidan da za a kai shi ba, zai rayu bai san asalin uwarsa ba, gaskiya ba ki da Imani"
Waheeda ta k'yalk'yale da dariya tace "lallai Nazira rashin imani ya wuce abinda kika je kika aikata d'azu, ko mai imani yana zuwa yayi zina?"
Nazira ta 'bata rai "karki kawomin wannan zance, ni nace kar kiyi riga kafi har ki samu ciki"
"Ai kema kin san akasi aka samu tunda ba yau na fara ba, shi dai wannan kawai Allah yayi zai zo duniya ne"
Nazira ta tashi ta cire rigan jikinta ta d'aura towel tace "me kuma zaki ce da Abba, sannan matuk'ar kina nan haka dole zai gane"
"Kar ki damu 'yar uwata na riga na tsara komai, dama Jameel yace kawai na taho kaduna, so that ina haihuwa na basu jaririn sai a bani balance d'ina na dawo, Abba kuma idan ya dawo zan ce mishi zanje wata makarantar koyar da sana'a a Kaduna kuma zan zauna gidan k'awata kinga kafin admission ya fito ma na riga na haihu"
"Shegiya tawan ashe har an baki deposit, shine ko ki gayamin nawa aka baki?"
"Ai ba rabonki a ciki tunda kince banida imani zan sayar da jaririna"
Nazira ta matso kusa da ita tace "haba tawan wasa nake miki fah Dan Allah nawa ne?"
"Ya turomin #300k d'azu yace idan na basu jaririn za a bani #700k"
"OMG! Waheeda total fa 1m kenan, gaskiya mun yi kud'i"
"Zan tura miki #100k anjima"
Nazira ta challa ihu tare da rungume k'anwar nata.
*JOS*
Nazima da Khairy tunda suka bar barrack d'in suke cike da bak'in ciki, shekarar da ta wuce saboda bikin yayarsu da akayi basu samu sun biya kud'in Jamb ba, gashi wannan karan ma abin yana so ya gagaresu. Cike da bak'in cikin yayan nasu suka shiga gida. Hajiya Salma na zaune akan sallaya tana zikiri suka shigo. Ganin yadda kowa yasamu waje ya yashe a k'asa yasa tasan ba a dace ba, cike da tausayinsu tace "Ummul Khairy ba a dace ba ko?"
Nazima ce ta amsa mata "wallahi Hajiya Yaya Isa bashi da imani ba abinda ya sani sai kansa da matarsa, kuma wallahi Allah zai saka mana"
Hajiya tace "yanzu dai tashi ki d'auko muku plate kuci abinci sai na baku labari mai dad'i, idan muka dace gobe zamu samu alkhairi"
Bayan sun ci abinci Hajiya ke basu labari "akwai matar nan da nace Hajiya Hinde tawa magana wancan sati, to d'azu Hinde ta bugo mini wai gobe na aika mata da masa na dubu biyu ta gani, idan ya mata to zamu dinga yi mata tana sayar wa a restaurant ɗinta"
"Allah dai yasa mu dace" inji Khairy
Nazima tace "sai dai bak'in ciki amma badai ta ce masar mu be mata ba"
*......Asalin su NAZIMA.*
Malam Abubakar d'inki ya ke yi a garin Jos, asalinsa mutumin Gumel ne, ci rani ya kawo shi Jos daga nan da ya ga ya samu dace kawai yaci gaba da zama a nan, ya had'u da Salma a Jos amma asalinta 'yar Bauchi ce lokacin suna sana'ar masa da mahaifiyarta saboda mahaifinta ya jima da rasuwa.
Abubakar sun had'a shago da Salisu wadda ya kasance wan Salma, dalilin zuwa gidansu suka had'u har suka dai-daita kansu, bayan anyi aure ma Salma bata dena sana'ar masa ba ta cigaba da yi, kuma tana samun alkhairi mai yawa, hakanne ma yasa Abubakar bai hanata yi ba, bayan rasuwan mahaifiyarsu Salma, Salisu yayi aure daga nan ya fad'a harkan kasuwanci inda ta kai shi Kano da zama, ya bar Jos.
Gaba d'aya ya dena sana'ar d'inki.
Haihuwar Salma biyu amma duk suna rasuwa sai data haifi Isa shine ya tsaya. Daga Isa ta haifi Haroon, daga nan har shekara hud'u bata sake haihuwa ba, lokacin Malam Abubakar ya samu k'arin arziki dan ya fara noma, bada d'inki kawai ya dogara ba, ya fara gini tareda taimakon Salma suka k'are ginin gidan suka koma can, ganin kud'i suna samuwa ya auro 'yar uwarsa Hauwa daga Gumel, ita ta haifa masa Abbas da Harira, Salma da kud'in sana'ar saida masa ta tafi hajji, dan ta riga Mijinta ma zuwa. Ganin kud'i na shigowa sosai yasa Alhaji Abubakar k'aro wata bazawara Talatu amma wannan 'yar k'abilar Birom ce, tunda Talatu ta shigo gidan farin ciki ya d'auke musu. Ta addabesu sosai dan tana harka da Bokaye. gaba d'aya sai abinda tace Alhaji Abubakar ke yi.
Ita ta sa aka saki Hauwa lokacin tana da ciki, Hauwa ta koma garinsu, Talatu bata bar Hajiya Salma ba saida ta lalata mata sana'ar ta aka dena zuwa wajenta, kaf idan ta fita bakin hanya inda take tuya masa ko akuya baya zuwa, anyi kwana uku ana haka Hajiya Salma ta hak'ura ta dena yin Masa gaba d'aya.
Anyi shekara biyu da yayen Ummul Khairy, Hauwa ta maido ta Jos wajen Hajiya Salma saboda za ta yi aure, lokacin itama Hajiya Salma tana da ciki, a haka dai ta cigaba da renon Khairy, kwatsam ranar Talatu ta ce zata tafi k'auyensu, ai kuwa daga tafiya bata sake dawowa ba, bayan ta tafi Alh. Abubakar ya lura ashe ta sace duk kud'in da yake tarawa da yake ba kowa ne ke kai kud'i banki ba lokacin, bayan kwana biyu aka zo aka basu notice wai ashe Talatu ta saida gidan, wannan mummunan labarin shiyasa Alh. Abubakar fad'uwa ya zama paralyze.
Hajiya Salma gonar gadonta ta sayar ta kama musu d'akin haya, haka suke kwamatsuwa aciki ba yadda suka iya, sauran kud'in ta fara saida wasu abubuwa a hankali taga ta d'an tara wani abu lokacin gashi cikinta ya tsufa, akwai wani gidan masu kud'i da suke da wata yarinya mai suna Nazima, Hajiya Salma na musu wankin kud'i agidan, da Hajiya ta haihu da kwana uku Nazima ta rasu saboda sickler ce, shekaranta bakwai, shine Hajiya ta sawa yarinyarta Nazima saboda tana son yarinyar. Haihuwar Nazima da wata uku Alh Abubakar ya rasu, abubuwa suka sake kachamewa Hajiya Salma. Gashi cikin 'yan uwa kowa takansa yakeyi ba mai taimakon wani, ganin dai abinda zasu ci yana so ya gagaresu ga ta da yara shida yasa ta nemi aron kud'i a wajen Yayanta Salisu, tace bari ta gwada sa'arta ko Allah zai taimaketa tunda tafi ganewa da sana'ar masa kuma gashi sun chanja anguwa ko za a dace, ai kuwa cikin lokaci k'ank'ani ta fara samun rufin asiri da kad'an-kad'an sana'arta ya bunk'asa har ta kai tana yi da safe da kuma yamma, da sana'ar ta samu har ta siya musu madaidaicin gida mai d'aki uku. Nazima da Khairy suma suna taya Hajiya sana'arta, boarding school suka tafi bayan da suka gama primary ajinsu d'aya dake tare aka sasu makaranta.
Fad'an Jos na farko aka kashe Haroon, lokacin Isa na makaranta. lokacin su Nazima na Jss3 Hajiya ta fara ciwon k'afa, tun abun dai tana iya fita tayi sana'arta har ya kai bata iyayi, asibiti sukace tana da diabetes, ganin haka yasa su Nazima dawowa day school ya zamana da safe za su je school da yamma su yi masa. Isa ya samu aiki da police aka turashi Kogi state, Abbas kuwa da be samu school ba dama ya iya d'inki kawai ya cigaba da sana'arsa.
A Kogi Isa ya had'u da Zainab 'yar Igbiran Okene. Ba yadda Hajiya Salma bata yi ba a kan kar ya aureta amma ya k'i, tinda yayi aure kuwa d'an alkhairi da yake musu ya dena, shekara d'aya kenan da aka maidoshi Jos amma sai ya ga dama yake zuwa ya dubasu.
Da za a yi bikin Harira ma da kyar ya bada dubu ishirin.
Shekaransu Nazima biyu da gama secondary school, yanzu Nazima tana 19yrs, Khairy 21yrs.....
Hajiya ta d'an samu sauk'i ana dai zuwa a mata gashin k'ashi lokaci zuwa lokaci.........
***
*KADUNA*
*Gidan Sheikh Sidi Al-Qasim*
Bayan ya gama bada fatawa na dare an watse ya shiga d'akin sa dan ya kwanta amma gaskiyar lamari ba kwanciyar zai yi ba, yau Aljani Muljahu zai gana da iyalinshi, zama yayi kan wata Tsohuwar buzu, ya rufe ido yana jan carbi amma abinda yake cewa abune da bazai kama hankalin mai imani ba. Tun kusan k'arfe Shad'aya na dare yake wannan abu har k'arfe 1:30am, can wata bak'ar hayak'i ta turnuk'e d'akin, Sheikh Sidi bai bar abinda yake fad'i ba bai kuma bud'e ido ba, haka bak'ar hayak'in nan ya 'bace da shi 'bat. Kai tsaye batareda ya bud'e ido ba ya afkawa d'iyarsa Nana ta baya (Wa'iyazubillah) chan anjima aka maidashi d'akinshi sai a sannan ya bud'e ido ya je ya kwanta.
Nana Khadija ta bud'e ido bayan mummunan mafarki da ta yi, ganin kowa na bacci a d'akin yasa ta koma barci bata fata ta sake wannan mafarki amma kuma ta sani duk wata sai ta yi shi, kusan shekara ashirin da bakwai kenan kowane wata sai tayi mummunan mafarkin nan.
***
.......Layla na fita daga motar da sauri-sauri ta shige gida ko juyowa bata yi ba, tana shiga ta dinga k'walawa Mom Kira, masu aiki suka ce mata bata nan, tsaki tayi ta wuce d'akinta, kai tsaye makeken gadonta ta fad'a tana maida numfashi, saida tayi rabin awa tana hutawa saboda tsorata da tayi d'azu kafin ta shiga band'aki tayi wanka, tana fitowa ta shiga wani d'aki wanda duk cikin d'akin kayayyakine, bayan akwatina da suke jibge sunkai ishirin suma na kaya, ga closet nan cike da kaya, ka d'auka wani show room ne na fashion show, wata Fitted mini gown ta saka bak'a me hannun spaghetti, ta sake shiga wani d'akin wanda zallar takalma da jaka ne a ciki, wani flat pumps ta saka jaa, ta fito dan yunwa takeji, kai tsaye ta sauko k'asa ta nufi dining table ta kira mai aiki aka serving ɗinta, tana ci tana chatting da k'awarta Zahra wadda sukayi karatu tare itama 'yar KD ce.
Dawowar mom ne ya kat'seta, mom zata haura sama Layla ta kirata.
Mom ta zo ta zauna tace "ya akayi Layla na" cikin shagwa'ba tace "Mom gaskiya ki kori wancan Ustazin driver da kika kawo, na tsane shi kinga d'azu wai dan ban iya kiran sunan shi ba ya dinga min fad'a kamar zai dakeni"
Mom ta ja tsaki tace "wallahi Layla idan kika ga na kore shi to sai dai in ke kika nemo wani ko Dad d'inki, ke kenan kowa aka kawo sai kin kawo aibunshi, cikin wata biyar da kika dawo Nigeria an chanja miki driver na goma sha d'aya kenan, ki ce wannan ki ce wancan, the last one da aka d'auka miki kika ce yana da body odour, ranar har amai kika yi, dan gwaninta na baki Malam Iro driver na, shima kika ce ya faye muni wai idan kika ganshi bakya iya cin abinci, ya kike so na miki toh, ni gaskiya na gaji, idan Alyasa'a bai miki ba ki nemo wani da kanki, ko ki bari idan Daddynki ya dawo ya kawo miki wani"
Kukan shagwa'ba ta fara tana bubbuga k'afa "Allah mom tsoronshi na ke ji kin san inada Low BP yanzu wata rana idan yamin fad'a k'ila mutuwa zan yi, mom kin ganshi ne yana masifa kamar wani lion, Ni gaskiya a chanja mini shi"
Mommy da bata son 'bacin ran 'yar tata tace "shikenan bari na kirashi na masa fad'a, idan kika ga kwana biyu bai chanja halinsa ba sai nasa a nemo miki wani" cike da farin ciki tace "yeeee! Thank you Mom"
Mom ta kirashi a waya tace ya zo, jim kad'an sai gashi ya shigo, har wajen dining d'in tace ya k'araso.
Layla na had'a ido dashi tayi saurin sunkuyar da kai tana danna waya.
"Alyasa'a Layla tace min wai d'azu ka mata fad'a, dan Allah ka dinga hak'uri da ita, duk abinda ta maka ka sanar dani zan d'au mataki, dan nasan Laylar tawa akwai rashin ji, ba komai yasa na ce karka mata fad'a ba sai dan tana da low BP, abu kad'an sai ya tayar mata da hankali, gata da shegen tsoro, nasan ka girmeta nesa ba kusa ba amma dan Allah kayi hak'uri" cewar Mom
"Bakomai Hajiya, Insha Allah zan kiyaye, hakan bazai kuma faruwa ba"
"To Shikenan kaje"
Har ya juya zai tafi sai ya tsaya yace "Hajiya Layla zaifi kyau ki dinga rufe gashinki musamman idan zaki ci abinci, gashin kai na asali ma ya aka k'are balle na aro"
"Mom kin ji shi ko" ta fashe da kukan sakalci
"To yanzu mi yace, ba gaskiya ya fad'i ba, so nawa ina hanaki saka wig amma ba kya ji "
Tashi tayi ta bar dining d'in tana kuka.
Ranar Layla ko fita bata kuma yi ba dan haushin Alyasa'a ta ke ji, washe gari kuwa dan ta bashi haushi ko rufe kan bata yi ba ta fito, haka ta baza wig d'in iska na k'ad'ashi, gashi yau shigar fashion pants suit da long sleeve fari tayi, yadda kasan bata had'a dangi da musulmai ba haka take tafiyarta ko damuwa bata yi ba, da tazo ta shiga mota tana tunanin zai mata magana sai ta ga bai kulata ba, har sanda ya dawo da ita ma bai ce komai ba, da yamma ta sake shigan wani fitted gown turquoise color, shima ba gyale balle hula haka tace ya kaita shopping, daga nan su je nan su je can har dare, duk bai ce mata ko uffan ba, abin ya bata haushi dan so take yi yayi mata magana ta had'ashi da Mom a kore shi.
Washe gari bayan ta dawo daga office, da yamma taje gidansu Zarah a nan ta wuni har bayan Isha kafin suka nufi club, Zahra da motarta taje dan ita take tuk'a kanta. A club Layla ke sanar da Zahra halin da take ciki, nason koran Alyasa'a, Zahra tayi shewa "tace haba k'awata har sai kin tsaya kina mishi a hankali ai kawai ki nuna masa makircin Mata"
"What do you suggest I do?"
"Haba Layla kina abu kamar wadda bata waye ba, just seduce him if he gives in ki zage shi tas ki ci mishi mutunci, kunya zaisa da kansa ya hak'ura da aikin"
Layla cikin rashin fahimta tace "how?" Zahra ta rad'a mata magana a kunne, nan Layla tayi dariya.
K'arfe goma da rabi Layla tayi sallama da Zahra har zata tafi tace "but Zahra ina tsoron shi fa"
Zahra ta mik'a mata kwalba tace sha wannan ki mance da duk wani tsoro. Layla ta k'ar'ba ta kwankwad'a.
Tana shiga mota, ya ja motar da gudu dan Allah Allah yake ya je gida dan ba a gidansu Layla yake kwana ba.
Sun yi tafiya na minti biyar yaji hannu a wuyarshi, can aka fara shafashi a hankali, duk bai ce komai ba, Layla ta lek'o da kanta tana hura masa iska a kunne, tana cewa "haba d'an Ustazu kai ba kya jin wani feelings ne, kad'an tsaya da motar mu d'an huta mana" jin bai ce mata uffan ba sai ma cigaba da tuk'i da yayi yasa ta fara 'balle masa button na riganshi daya ke shirt yasa ranar, ta fara shafa k'irjinsa a hankali tana kissing wuyanshi. Shikuwa neman wajen da ba alamar mutane yake yi shi ya sa bai tsaya ba. Kaman minti biyu sai ya samu wani waje ya faka motar, jin ya tsaya tayi murmushi dan tasan plan d'inta yayi aiki. Fitowa yayi daga cikin motan yana huci, ya bud'e b'angaren da take ya fincikota da k'arfi had'e da zabga mata mari saida ta fad'i k'asa, ya sake jawota ya k'ara mata wani marin. Cire belt d'insa ya yi ya fara bugunta dashi tana ihu sai cewa ya ke yi " 'yar iska, duk iskancin da kika yi a club bai isheki ba sai kin had'a da wajena, wallahi yau sai kin gane kuranki" ya cigaba da jibgarta tana ihu tana kuka, tun kayan mayen da ta sha na jikinta har wahala yasa suka fita. Sai da ya ga ta fad'i ta dena ma ihun saboda wahala tukunna ya k'yaleta, ya jefa mata key d'in motar yace "ki kai kanki gida" ya juya yayi tafiyarsa.
Ganin fa da gaske tafiya yayi, yasa Layla ta taso da gudu ta bishi ita kanta batasan inda ta samu k'arfin gudu ba, tana isoshi ta rik'e k'afarsa tana kuka "Dan Allah AY ka kaini gida, bazan iya tuk'i ba, ka taimakeni ina tsoro, AY Dan Allah dare ne sosai, kafin a zo daga gida komai zai iya faruwa da ni, Dan Allah"
ya shureta da k'afarsa yace "sai shegen iskanci amma kin fi kowa tsoro" yaja tsaki yace "muje"
Tunda ta shiga motar jikinta ke kakkarwa gashi ko ina ciwo yake mata, a rayuwarta babu wanda ya ta'ba marinta balle duka, sai nishi take yi na wahala. Suna cikin tafiya ta ji ya tsaya wani tsoro ya kama ta dan ta d'auka wani dukan zai kuma yi mata, tuni ta sume a motar...
Shi kuwa wani chemist ya iso dan ad'an bata first aid tunda yaga bakinta da goshinta ya fashe shiyasa ya tsaya da motar ........
*ABUJA*
Yinin ranar Zaytunah bata gane kan Sajid ba dan shareta ya dinga yi, duk hirar da take mishi lokacin da suke cin abincin dare baya sa mata baki...
Bayan tayi wanka ta tsantsara kwalliya, ta saka wani shegen fitinannen rigar bacci mai kyau, ta d'auko wani had'i da aka mata tun daga Chad ta sha cokali uku bayan da ance cokali d'aya zata sha.
Zaytunah mace ce me son farantawa mijinta rai wajen raya sunna, sai sa bata wasa wajen gyara kanta kullum gani take budurwace a gaban mijinta. Kai tsaye d'akinshi ta nufa bayan ta saka hijab, dama tuni yaran sun yi bacci.
Tana shiga d'akin taga ashe shima har ya kwanta ta cire hijabin ta kwanta gefensa tareda rungumeshi ta baya.
Ganin bai kulataba baima nuna yasan ta shigo d'akinba yasa ta fara aika masa da s'ak'onni still shiru, bai responding ba. "Haba My one sati biyu fah baka nan, kasan na missing ɗinka"
"Zaytunah not today na gaji" taji yace mata
"My one na riga nasha abubuwa fa, kuma bak'aramin missing ɗinka nayi ba"
"Zaytunah ke kikasan abinda kika sha ni bai dameni ba, yanzu kin iya zuwa ki wani ce kin missing ɗina bayan tunda na dawo ban samu kulawa mai kyau daga gareki ba"
"Haba my one, please don't say that, I really miss you, kuma ai da rana kasha bacci ka huta"
"Zaytunah sleep, ina da abubuwa dayawa a kaina, I need to rest"
"Wallahi baka isa ba, na riga nasha abubuwa so you don't have a choice"
Ganin ta fara k'ok'arin cire mishi pyjamas nashi yasa shi tashi yabar gadon yace "barin kwana a falo to"
Da sauri ta tashi itama ta bishi amma ina tuni ya shige d'aya d'akin yasa key.
Haka ta tsaya tana buga mishi k'ofa amma yak'i bud'ewa, tsoron kar yaran su tashi yasa ta dena bugawa ta zauna a bakin k'ofar tana hawaye, dan magani ya fara aiki gashi Sajid ya gujeta.
Shi kanshi so yake ta gane cewa bai ji dad'in abinda tayi ba da rana, na barin Sadiya ta shigo masa gida, shiyasa ya mata haka, da yake ita k'aramin tunani ne da ita, batama san ta bashi hak'uri akan haka ba.
Jin sheshsheqar kukanta yasa ya ji tausayinta, Dan yasan Zaytunah da shan kayan Mata, bud'e k'ofar yayi ya ganta tayi jigum abin tausayi, ya d'auketa cak ya kaita d'akinsa sai daya kwantarta kan gado yace "jarababbiya kawai" dariya tayi tace "Kai ka koya min"......
Washe gari Zaytunah na serving breakfast tana yi tana rawa,
Azra tace " mommy why are you dancing?"
Zaytunah tayi murmushi tace "baby nah because I'm happy, jiya mun yi yawo da Dad d'inki sosai"
Aamir yace "mom Ina kuka je?"
"Mun hau jirgi me gudu, muka je London, America, England, France, kai mun yi yawo sosai"
Zunnurain da ya ke shi yana da wayo sosai yace "mommy yaushe kuka je, kuma ya akayi kuka dawo da wuri haka?"
Zaytunah zata yi magana Sajid yayi gyaran murya tareda cewa "eats your breakfast, you know your mom is crazy" gaba d'aya yaran suka saka dariya.
Zaytunah tace "my one yau kan jirginmu zai je har Iraq ko?"
Tasan ya gane maganar da take yi
Hararanta yayi, su kuwa yaran sai dariya suke yi wai mommynsu is crazy tana musu k'aryan jirgi me gudu..............