Chapter 5
by @azizat
*MUTUM.....Mugu ne*
©AzizatHamza2019
*KADUNA*
Alyasa'a ya bud'e kofan domin ta fito yaji shiru ya d'auka ma ko bacci takeyi, ya kira sunanta amma shiru, ya sa hannu ya tallafota jikinsa nan ya gane suma tayi. Da sauri ya fita chemist d'in yaje ya k'ar'bo ruwa, ya d'an watsa mata kad'an, ya sake watsawa kafin taja dogon numfashi ta bud'e ido, tana kallonshi jikinta ya fara 'bari, ganin haka yace "relax ba abinda zan miki, ki fito a gyara miki fiskarki"
A hankali take tafiya harta isa wajen chemist d'in shikuwa tuni ya isa suna magana da Mai chemist.
Bayan ta shiga ciki, Mai chemist ya goge mata fiska, ya saka plaster a goshinta, saboda wajen ya fashe sosai, AY na waya da wani friend d'insa saboda haka ya juya musu baya.
Shi kuwa Mai chemist irin 'yan iskan nan ne, rigar da Layla ke sanye dashi vest ce ash, bata kamata sosai ba amma kuma shape na breast d'inta sun fito sosai, Mai chemist ganin arzik'i a fili, yasa ya kai d'aya hannunsa kan k'irjinta yana shafawa a hankali, d'aya hannun kuma yana shafa mata balm a gefen kumatunta daya kumbura.
Layla taga shafun da Mai chemist yake yi ya fara wuce gona da iri, har chanja gefe yake yi ya shafa d'aya ya koma kan d'aya. Ta d'aga kai taga AY ba wajensu yake kallo ba, ta sunkuyar da kai tana tsoro kar ta yi magana AY ya mata fad'a.
Caraf AY ya juyo yayi arba da abinda Mai chemist ke yiwa Layla, baice komai ba ya damƙi hannunsa dake kan k'irjinta ya murd'e. Mai chemist yayi shiru dan ya dena komai yana so yayi kuka amma ba hali, still AY na rik'e da hannunsa yace "cigaba da abinda kake mana"
"Wallahi na gama, Allah na gama" ya fad'i cikin tsoro dan tuni ya fara zufa.
AY bai sake hannunshi ba yace "d'an iska idan kana son ta'ba nonon mace so badly kayi aure mana, a ido kaman Ustaz ashe kai munafiki ne"
Mai chemist ya fara bashi hak'uri dan ya ji hannun maza. Ya fi minti biyar kafin ya sake mishi hannun.
Da hannu d'aya ya had'a maganin dan d'aya hannunsa kam ko iya d'agata baya yi, hannu na rawa ya mik'a masa ledar.
"Nawa kud'inka" AY yace dashi
" Dubu d'aya da d'ari bakwai"
AY ya cilla mishi dubu biyu ya wuce abinsa, har ya isa wajen mota bata iso ba, dake a hankali take tafiya. Ya juyo ya kalleta cike da takaici yace " zakimin sauri ne ko kuma na barki da wancan pervert d'in ya cigaba da abinda yake miki d'azu, na ga kaman kinji dad'in hakan"
Tayi saurin girgiza kai sannan ta k'ara sauri.
Har suka isa gida ba wanda yace da wani komai, tana fitowa daga mota ta hango Daddynta zai shiga mota da sauri ta juyar da kanta kar ya hangota, aikuwa ya ganta d'in.
Cike da tashin hankali Alhaji Kadi ya k'araso wajen da take tsaye.
"Layla miya same ki? Waye ya ta'baminke?"
Juyowa tayi ta kalli AY da shima fitowarsa daga motar kenan, babu alamar tsoro a tareda shi, tace "daddy wani sabon club dana je ne muka samu d'an matsala da wasu shine muka yi fad'a"
"Ubanwa ya isa ya ta'ba minke har ya fasa miki goshi, kuma ya zauna lafiya, ba ayi shi ba, kowaye ne ya miki wannan they will pay for this, dasu da iyalensu gaba d'aya"
Ganin yadda Daddynta ke ta masifa tayi saurin shigewa jikinsa tace " daddy plz ka kwantar da hankalinka, police sun riga sun kamasu, kuma talakawane basu san koni wacece ba shiyasa, Kuma daddy ba wani ciwo naji ba fa"
Kafin ya k'ara wata magana Bodyguard d'inshi Jameel yace "Alhaji ya kamata mu k'arasa fa dan sunce ta riga ta sauka"
Alhaji Kadi ya shafa bayanta yace "baby barinje wani emergency yanzu idan na dawo zamu yi maganar gobe, amma ki dena zuwa club na talakawa kije inda aka sanki aka san ke wacece, inda za'a karramaki kinji" ta gyad'a masa kai.
AY yau ya fara ganin Alhaji Kadi kuma jikinshi ya bashi ba mutumin arzik'i bane, Hajiya Zaliha kam bata da matsala tana da mutunci sosai.
Wucewa yayi gaba bai ce mata komai ba itama ta bishi sumul sumul suka shiga gidan,
A falo suka tadda Mom tayi tagumi da alama tana cikin damuwa, tana ganinsu ta taso da sauri.
"Layla k'arfe d'aya saura kwata ina kika shiga inata kiran wayarki baki amsaba"
zaro ido tayi ganin fiskar Layla da sauri ta tambayeta abinda ya faru. K'aryar da ta yiwa Daddynta shi ta sake maimaitawa.
Mom ta tallafota jikinta tace "yanzu duk fad'an dana ke miki akan zuwa club ashe baki dena ba, ai ga irinta nan" ta zaunar da ita sai alokacin ta kalli AY tace "Alyasa'a mungode fa da k'ok'ari, Dan Allah nan gaba tace ka kaita club karka kaita na hana daga yau" shi dai kawai kallonta yake da alamar tambaya. " Ko miyasa ta k'i fad'an gaskiya?" Ya tambayi kansa. Ya mik'awa mom ledar magani yace "ga maganin ciwon jiki tasha kafin ta kwanta"
Mom ta ce "Dan Allah Alyasa'a ka taimaka min ka kaita d'akinta barin had'a mata tea saita sha maganin, kaga masu aiki duk suna sashensu kafin na kira su fito ma wani 'bata lokaci ne"
Ya ce "ba komai"
Layla kan sake narkewa jikin kujera ta yi dan bata son AY ya rakata d'aki har yanzu tsoronshi take ji....
"Ki tashi mana Layla" mom ta fad'i tana shirin wucewa kitchen
Kamar ba zata tashiba ganin kallon da ya ke mata yasa ta tashi da sauri ta ce "kayi zamanka zan iya tafiya da kaina"
"Ba ke kika sani ba" taji yace da ita
Ta yatsina fuska sannan ta wuce gaba madadin su haura stairs sai ta shiga lift shima ya bita ciki, ta danna second floor, yana ganin yadda ta matsa gefe sosai dashi still hannunta na shaking.
"Miyasa baki gaya musu gaskiya ba?"
Lift na tsayawa tayi wuf ta fita ko waigowa batayi ba tayi sauri ta wuce d'akinta. Shikan dariyan shiriritarta yayi sannan yabi bayanta. Tana shiga d'akin zata kulle k'ofa yasa hannu ya tare.
"Ai na riga na iso" ta fad'i still jikinta na rawa, bai kulata ba ya shigo d'akin yana bin ko ina da kallo, d'akine babba akwai kujeru da tv sannan chan gefe gado. d'akuna ne guda hud'u ajere dukkansu manne da stickers d'aya an saka dressing room, bathroom, shoe and bags sai na k'arshe study room.
Tana kallonsa ya bud'e kowanne ya lek'a bata iya ce masa komai ba ita dai tana Allah Allah ya fita.
Sai daya gama dube-dubensa sannan ya dawo inda take tsaye ya sake maimaita tambayarsa ta d'azu. Itakanta bata san miyasa tayi k'arya ba, ta tsaneshi amma kuma idan ta fad'i gaskiya Daddynta ba zai mishi da dad'i ba k'ila a lahanta shi, dan tasan Daddynta ko kad'an bashi da tausayi.
"Nima ban saniba" ta fad'i tana kallon gefe.
"To nizan fad'a musu gaskiya" ya ce da ita
Da sauri ta zaro ido "Dan Allah kayi hak'uri, Daddy will kill you"
Yayi murmushi yace "je ki chanja kaya" ba musu ta shiga dressing room ta cire wad'ancan ta saka rigar bacci riga me dogon hannu light blue da wando iya cinya, ta cire wig d'in datasa, k'ananun kitsone akanta ya sauka k'arshen wuyanta. Data fito ta tadda shi yana zaune kan kujera yana danna waya.
'Wato ma bai tafi ba' tace aranta
Bata mishi magana ba ta kwanta kan gado, mom ce ta shigo d'auke da tray a hannunta.
"Zo ki sha magani Layla" tace da ita.
Ba musu ta taso dan duk ta tsargu AY ya tafi, tana zama AY ya tashi yace "Hajiya zan tafi sai da safe"
"Alyasa'a dare yayi sosai ka kwana anan akwai d'aki a k'asa ka shiga duk wanda ka ga dama"
Yana son gano wani abu a gidan shiyasa ya amince, ya yiwa mom godiya ya sauka....
Tunda ya shiga d'aki yake tunanin tsarin gidan lalle akwai 'boyayyen al'amari atare da gidan nan, a matsayinsa na tsohon d'an bincike zuciyarsa na raya masa abubuwa dayawa.
Can wajen k'arfe uku na dare yaji shigowar mota gidan, ya taso a hankali yad'an bud'e k'ofa kad'an ta yadda zai iya ganin me shigowa, ai kuwa ya hango Alh Kadi d'auke da wani abu cikin bak'in k'yalle yana motsi har ya wuce ya hau lift Bai gane menene ba, amma yana da tabbacin koma minene a hannun Alhaji Kadi to abu ne mai rai, sannan zai iya zama kyanwa ko d'an kwikwiyo koma d'an jinjiri.
Komawa yayi ya kwanta yana tunanin abubuwa dayawa. A da yana tunanin barin aiki ko dan haushi da Layla ke bashi amma yanzu instinct nashi na nuna masa yaci gaba da aiki zai gano wani abu mai girma....
*ABUJA*
Tsaye take jikin mirror tana yin makeover ya rungumeta ta baya, ya fara kissing wuyanta.
"My one zaka fara ko"
Yace "close your eyes"
Ba musu ta rufe idonta, shi kuwa yasa hannu ya fiddo wata sark'a daga cikin wata k'aramar akwati, ya sa mata a wuya.
Bud'e ido tayi cike da farin ciki ta dubi sark'an ta jikin mirror, nan ta zaro ido "Diamond necklace!.....oh I love you My Sajid" ta juyo ta fara kissing ɗinsa kusan minti biyu kafin ta cire bakinta tace "what's the occasion my love, miyake faruwa?"
Ya yi murmushi sannan yace "Happy Anniversary Zaytuna"
"A'a it was two days ago my one, miyasa baka bani a gaban mutane ba, it would have been more special"
"Ni yau shine anniversary a wajena kin tuna how it happens"
Dariya tayi tace "of course, I remembered vividly, you were merciless that night"
Ya kwashe da dariya "but you ask for it Zaytunah, ni ban san amarya mara kunya aka kawo min ba, ni ina tausayinki nace ki huta saboda gajiyar biki, but what did you do?"
"To ai kai ma bakamin bayani yadda zan fahimta ba kace na kwanta na huta, ba dole na ji ba dad'i ba"
Ya fara mimicking nata " haba Sajid kowace amarya aka kawota d'akinta angonta yana d'oki yana Allah Allah a watse amma sai kace min na huta, koda auren had'in gida aka mana ai ni ina sonka kuma ba hutu na zo yi ba"
Ta kai masa duka ya goce yana dariya ya ce " ki tsaya na k'arasa mana, ki ji irin rashin kunyar taki"
Ta bishi da gudu zata dakeshi, suka fara guje guje a d'akin......
Ranar Alhamis
Tana kwance jikin shi yana shafa gashin kanta a hankali ta ce "Dan Allah my one ba za ka tafi dani ba, wallahi sati biyu dakayi baka nan kamar na hau jirgi na bika nake ji"
"Zaytunah case da Madam Bridget is a very dangerous case, kuma kinga Lagos ba kamar Abuja bane da na sani, I don't want anything bad happening to my family"
Cikin shagwa'ba tace "ni dai kawai idan na missing ɗinka zaka ganni a Lagos"
"Ki bar min yara a ina?"
"Zan kaisu gidan Daddyna su zauna a can"
"Ban yarda ba, ki zauna a nan na riga na kawo bodyguard so you're safe"
Ta fara kukan shagwa'ba ita dole ya barta ta bishi Lagos...
*Wacece Madam Bridget? Kuma minene had'in ta da Dr Sajid*
............. Alhaji Abdallah d'an asalin jahar Taraba ne, bafilatani daya gaji dukiya mai tarin yawa, yana da dabbobi da gonakai, kuma yana harkan kasuwanci, yana da mata biyu Khadija da Mariya.
Khadija ta haifa masa yara biyu Umar da Usman sai Mariya ta haifa masa yara shida, maza biyu mata uku.
Duk da Alhaji Abdallah baiyi Boko ba amma ya tsaya wajen ganin yaransa sun yi boko, Umar dai a Nigeria yayi karatunsa har ya k'are ya fara kasuwanci dan fannin daya karanta kenan, Usman kuwa bayan ya k'are secondary school k'asar Canada ya tafi Toronto University. Anan ya had'u da Nihad 'yar k'asar Ethiopia suka k'ulla soyayya k'arshe dai ya aureta. A k'asar Canada ya samu aiki yayi zamansa acan yakan zo Nigeria amma ba sosai ba dan duk cikin 'yan uwansa babu mai son Nihad saboda gidansu yawanci auren had'in gida ake yi yayanshi Umar ma haka aka masa.
Nihad bata haihu da wuri ba sai da suka shekara shida kafin ta haifi 'yan biyu mace da namiji aka saka musu Sajid da Sajida, zuwansu Nigeria lokacin yaran na shekara d'aya taga chanji a wajen 'yan uwan Usman, saboda ba a ta'ba haihuwan 'yan biyu a familynsu ba sai akan nata. Suna son yaran sosai musamman Kakansu. Sajid da Sajida na shekara hud'u Nihad ta rasu, bayan rasuwanta Alhaji Abdallah ya sa dole Usman yayi aure ko kuma ya dawo da yaran Nigeria. Hakan kuwa akayi Ya auri Fatima, Haj Khadija ta nemi Usman ya bar mata Sajida wani zuwan da suka yi da yake tana son 'ya'ya mata kuma Allah bai bata ba, haka Sajida ta koma wajen kakanninta da zama.
Umar shima auren gida aka masa da Saratu inda ta haifa masa Aliyu, saidai shekaran Aliyu uku Umar ya yi hatsari ya rasu, Aliyu ya taso cikin gata da jin dad'i sosai, musamman kakansa yana sonshi sosai.
Bayan Aliyu ya gama karatu aka turashi jahar Imo bautar k'asa, a Isu local government.
Bridget Ndubuisi 'yar k'auyen Isu ne, tana zuwa makaranta a Isu local government, anan taga Aliyu ta kamu da sonshi, duk wani salo na jawo hankali tayi shi amma Aliyu mutum ne da ba ruwansa da neman mata, ana cikin haka ya gama bautar k'asa za su tafi, saura sati d'aya ya gama Bridget ta damu sosai dan ji take idan bata auri Aliyu ba zata iya rasa ranta, nan ta rantaya wajen kakan mamanta dayake boka ne, ta fad'a masa matsalarta tace duk yadda za'ayi tana so ta mallaki Aliyu, Boka yace mata zai mata aiki amma da mahaifarta za ayi aikin dan haka bazata ta'ba haihuwa ba, asalima yace mata Aliyu yara biyu zai samu a rayuwarsa. Ita kan tace ta amince,
Aka mata aiki ai kuwa nan Aliyu ya bircike da tsananin sonta, ya nemi har k'auyensu ya je wai yanaso ya aureta, iyayenta basu yarda ba saboda shi musulmi ne kuma bafilatani, itakam Bridget tace tanason shi a haka, sukayi sukayi tak'i sauraronsu, k'arshe dai suka je cikin Imo aka d'aura musu aure acan.
Gidan Alhaji Abdallah ana marmarin dawowar Aliyu kawai yazo musu da Bridget a matsayin mata, takaici da bak'in ciki da suka ji bazai misaltu ba, tun suna masa masifa har suka koma lallami akan ya rabu da Bridget amma yak'i, ganin sun takurashi yace a bashi gadon mahaifinsa. Abin ya bawa Alhaji Abdallah haushi, cikin 'bacin rai ya tattara masa gadonsa ya bashi yace kuma ya bar masa gida domin daga yau bashi ba gidansa. Aliyu ya tattari dukiyarsa yayi gaba bisa shawaran Bridget suka koma Lagos da zama, a hankali ya fara kasuwanci, yana bunk'asa har ya bud'e kamfaninsa. Bai sake komawa Taraba ba balle ya waiwayi kakanninsa.
Dawowan Usman Nigeria Gaba d'aya ya taradda abinda ke faruwa Dan shi baima san an kori Aliyu ba, yaje har Lagos ya samu Aliyu ya masa fad'a sosai sannan ya tisashi gaba suka taho taraba, lokacin Bridget ta tafi k'auyensu Dan tunda kud'i ya samu iyayenta suka ga kud'i tuni suka manta da wani batun musulmi take aure suka bud'e duniya sabuwa, ganin bazata iya haihuwaba gashi shekara goma da aure yasa ta d'auko k'aramin k'aninsu Joseph ya dawo wurinta da zama dama su uku ne a wajen iyayenta ita da k'annenta maza biyu, d'ayan Isaac ta turashi k'asar waje karatu, sai Joseph da yake shekara sha biyu.
Tunda Aliyu ya je ya nemi gafarar kakanninsa suka shirya, yana zuwa dubasu duk bayan wata uku, babban matsalarsu shine suna so ya k'ara aure amma yak'i, haka dai suna ta mai addu'a.
Shekara goma sha takwas da auren Bridget, lokacin Alhaji Abdallah yana ciwon ajali, ya sa aka d'aura auren Sajida da Aliyu, lokacin Sajida nada shekara ashirin da biyu ta gama degree d'inta fannin aikin jarida.
Shi kanshi Aliyu bai saniba sai dayazo duba jikin Kakansa ya samu labarin, tsananin fushi da 'bacin rai ya nuna musu, daga k'arshe dai ya nuna shi bai aminta ba, bayan kwana biyu da zuwansa, Alhaji Abdallah ya rasu hakan yasa jikinsa yai sanyi, da zai tafi ya tafi da amaryarsa.
Bridget kaman ta mutu da ta ga Sajida, nan ta koma wajen sabon boka dayake wancan ya mutu, boka ya sanar mata duk yadda zatayi akwai yara biyu tsakanin Aliyu da Sajida dan haka ta hak'ura kawai.
Bridget ganin ba mafita ta koma walak'anta Sajida, tana k'untata mata, gashi Aliyu yana gani bazai iya hanawa ba, ahaka har Sajida ta fara laulayin ciki, ta 'boye bata sanar da kowa ba, da shike Bridget bata ta'ba haihuwaba so bata gane da wuriba, har saida cikin ya shiga wata biyar. Wata k'awarta da tazo ta ga Sajida tace mata ai Sajida na da ciki nanfa hankalin Bridget ya tashi, tace tunda boka sunce bazasu iya kashe yaran ba ita zata iya, taje ta k'ar'bo maganin zubar da ciki ta bawa Sajida cikin abinci.
Da yammacin ranar Sajida ta fara ciwon ciki sai jini, gashi Aliyu baya ma k'asar Bridget kuwa dama tunda ta tabbatar tasha maganin tabar gidan, tana cikin ciwo Alhajinsu da Ummi suka shigo gidan, da yake tunda ta tare basu ta'ba zuwa ba sai wannan karan suka mata surprise visit, a nan suka tadda halin da take ciki, suka garzaya da ita asibiti. Bayan an ceci ranta dana cikinta, Alhaji ya wuce da ita Taraba, Bridget ta dawo da niyyar taga Sajida ta mutu sai taga batanan ga kuma jini a k'asa, ta fito ta tambayi Mai gadi dayake tunda Sajida tazo ta sallami masu aikin cikin gidan, ita ke aiki. Mai gadi yace wasu mutane sukazo suka fita da ita bata da lafiya...
Haushi ya kamata waye zai shigo ya fita da Sajida, ta fara bincikan asibitoci amma bata gane inda suke ba kawai tace kila ma ta mutu.
Tunda Sajida ta warke Alhaji yace bazata koma Lagos da zama ba, Aliyu sai daya dawo ya samu labarin abinda ya faru,
Bridget ganin bai damu ya tambayi inda Sajida take ba yasa itama tayi shiru da zancen.
Sajida wajen haihuwa ta rasu ta haifi yaranta 'yan biyu maza.
Da aka sanar da Aliyu kuka yayi sosai dan koda yanajin tsananin son Bridget a zuciyarshi amma kuma zamansa da Sajida yasamu wata ni'ima ta daban, kuma koyaushe yake tare da ita yakan ji shi cikin farin ciki marar misaltuwa.
Ita kuwa Bridget murna tayi, duk da taji haushin haifan yaran da akayi.
*Yamin da Yassar* sun taso wajen kakansu cikin kulawa kafin rayuwarsu ta chanja bayan sun koma wajen mahaifinsu.....
A halin yanzu Yamin da Yassar suna kulle a prison bisa tuhumarsu da kisan Mahaifinsu Alhaji Aliyu Umar Abdallah.
*Koya hakan ta faru?*..........mutum dai mugu ne....
*ABUJA*
Tun daga k'afa ya fara kissing ɗinta har ya garzayo wuyanta kafin ya had'e lips d'insu , sosai itama take maida mishi martani...suna cikin duniyar ma'aurata sukaji ana buga k'ofar d'akin. Sajid ya janye jikinsa ya koma gefe yana maida numfashi.. suka sake ji ana buga k'ofar ana kiran "Dad...Dad open the door plz"...Jin muryar Azra ce yasa Sajid mik'ewa da sauri ya kunna wuta ya nufi k'ofan. Ita kuwa Zaytunah ta tashi ta saka robe d'inta dan night dress d'in dake jikinta shara shara ne kana ganin duk surar jikinta.
Yana bud'e k'ofa Azra ta rik'e k'afarsa tace "dad I want to sleep with you". Ya sa hannu ya d'auketa " oh my baby will sleep with Daddy tonight" yana kawota Zaytunah ta mik'a hannu zata d'auketa "Azra dear, let me take you to your bedroom" Azra ta mak'e kafad'a.
Sajid yace "barmin ita anan take son kwana"
Zaytunah ta turo baki "wallahi baku isa kumin iskancin da kuka saba ba, wai daga zakayi tafiya suzo su mak'ale maka, yau kan it won't work" ai bata k'arasa magana ba suka sake jin bugun k'ofa. Fuuu Zaytunah ta nufi k'ofan tana bud'ewa taga Zunnurain da Aamir dama d'akinsu d'aya, suma suka ce zasu kwana da daddy ....
Zaytunah ta zaro ido "to ku kasheni, nace ku kasheni, jarababbun yara kawai" tana masifa ita d'aya yaran kam tuni sunje sun kwanta gefen daddy Azra kuma na kwance a k'irjinshi yana musu labari...
Zaytunah tazo ta zauna gefen gado tace "Aamir kuje ku kwanta a d'akinku I want to discuss something important with your dad"
Sajid yace "Zaytunah barmin yara na yau wajen daddynsu zasu kwana" ya fad'i hakan ne dan ya k'ulata dan ya san matsalarta.
Itako cikin masifa tace "wallahi ko maganin bacci sai na nemo na baku, 'yan duniya kawai, haka kawai na fara d'aukan chargy kuzo ku katsemin" sukam ba wanda yasanma tanayi sai tad'i suke suna dariya....
Tana zaune gefen gado ta cika tayi fam ji take kamar ta yi wurgi da yaran waje su d'aura daga inda suka tsaya .... Shiru shiru yara sunk'i bacci har k'arfe shabiyu saura.............
Please follow me on
Wattpad: Azizat_Hamza
Arewabooks: Azizat Hamza