Chapter 7
by @azizat
07
*Lagos*
Taro ne akayi na manyan mutane, gidan marigayi Alhaji Aliyu dake Victoria Island cike yake mak'il. Madam B uwar gayya tana sanye cikin shiga ta alfarma, da ka ganta ka ga wacce taji kud'i.
Wani kukan munafurci Madam B ta fashe dashi bayan an karanta tarihin Aliyu, Joe da Mama dake gefenta suka fara bata hak'uri, da k'yar ta samu ta nitsu, tazo ta yanka cake na cikar 40yrs anniversary ɗinsu, gurin ya karad'e da tafi da shewa.
Tana zaune gaba d'aya zuciyarta tayi bak'i, ganin Aunt Bridget da Uncle Joe suna taka rawa a fili son ransu, ta ja dogon tsaki, itakan idan ba dan Dad d'inta ba bazata fito wajen taron nan ba.
Ta maida dubanta ga hoton Yamin dake screen d'in wayanta, tanajin tsananin sonshi na fizgarta..
Ji tayi an rungumeta ta baya, tasan babu me wannan hali sai Nick.
Cike da masifa tace "Nick please leave me alone"
Ya kissing cheek d'inta yace "haba angel miyasa kike wahalar dani ne" ya cigaba da shinshina wuyanta.
Tayi saurin fizge jikinta ta juyo ta kalleshi "Nick leave me alone, ka bar shiga harkata, na riga na gaya maka abinda kake tunani ba me yiwuwa bane"
Murmushi yayi sannan ya jawo kujera ya zauna yana kallonta, ganin kallon yayi yawa tace " kallon yayi yawa plz"
"Ban san miyasa ba, komi kikayi birgeni kikeyi, your anger, your laughter, even when you throw tantrums, I find it beautiful"
Ya rik'e hannunta guda d'aya yana murzawa a hankali "see, I love you, yes nasan ni Playboy ne but that was before I met you, yanzu na chanja, my feelings for you are real......"
"Irene!" Aka kira sunanta cikin tsawa
Dukkansu biyu suka juyo suna kallonta.
Irene tayi saurin cire hannunta daga cikin na Nick tana jiran mi Emily zata ce.
Cike da 'bacin rai ta iso wajen, wani red mini gown ta saka iya cinya, heel d'inta bak'i, sai purse ma bak'i, tasha kwalliya sosai.
"Hi Emily" Nick yace da ita
"Irene kije Uncle Isaac yana nemanki" ta na magana tana harararta .
Irene ta mik'e zata wuce Nick ya rik'e hannunta, ta juyo ta kalleshi, yace "muje na rakaki"
"No thanks ka zauna yanzu zan dawo"
Ta juya ta nufi cikin taron, Nick zai bita Emily ta rik'e hannunsa " haba Nick wannan wani irin cin fuska ne haka, muna tare da kai acan ka gudo ka dawo wajen wannan jakar yarinyar, why?"
Nick ya fizge hannunsa "Emily sau nawa zan gaya miki cewa Irene na ke so ba ke ba, don't you get it, I love Irene not you "
"Baka isa ba Nickolas, bayan na baka kaina wai yanzu daga ganin Irene sai kace ita kake so, i won't let that happen"
Wata k'aramar dariya yayi kafin yace "you throw yourself to me Emily, ban ta'ba zuwa na nemeki ba, ke da kanki kika kawo kanki har d'akina, and you're not a virgin balle kice nina fara, plus ban ta'ba ce miki ina sonki ba, so I don't owe you anything" ya wuce ya barta tsaye tana cize le'be.
Wajen da Dad d'inta ke zaune Irene taje ta rad'a masa magana a kunne, murmushi yayi yace " tunda kinzo zauna anan, bana so kina ke'bewa ke kad'ai d'innan"
Ta zauna tana masa murmushi....
Babu wadda ya lura da shigowarsa. Juyowar da Madam B zatayi tayi arba dashi, ya jawo kujera ya zauna opposite da ita, kowa ya koma kallonsa a table d'in, Madam B, Mama (mahaifiyarta kenan), Joe,da matarsa Ngozi sune a table d'in.
Su biyu suka ganeshi a wajen.
"Welcome Dr Sajid, dama bazai yiwu ayi taro irin wannan babu d'an uwan Aliyu ba, I expected you much earlier" tayi smirking
K'aramar dariya yayi kafin yace "Dole nazo wannan taro koba komai daga yau zan fara lissafta iya kwanakinki a gidan nan"
Joe yace "kodai ka fara lissafta iya kwanakinka a garin nan ba"
Sajid ya waiga gefe da gefe yace "gaskiya Yaya ya iya k'era gida, ace gidan nan kusan shekara talatin da ginashi amma har yanzu yana tafiya da zamani, wow"
Madam B tayi murmushi " kasan architect da engineers d'in turawa ne, sunyi aiki mai kyau wajen tsara gidan"
Sajid ya tashi ya tako har wajen da Madam B ke zaune ya rad'a mata a kunne " gidan nan da miliyan biyar...."
Zuciyarta ya buga jin abinda yace amma ta dake tace " see you in court Dr Sajid"
"Absolutely Madam Bridget Ndubuisi" ya gaya kafin ya smirking ya bar wajen...
Irene tana ganin ya yi hanyar fita daga garden d'in tayi saurin cewa Dad d'inta zata shiga gida, da sauri tabi bayansa.
"Dr Sajid...Dr Sajid..." Ta fara k'wala masa kira .
Ya tsaya tareda juyowa a hankali ya kalleta.
Kafin ta k'arasa wajensa taji an dafa kafad'arta ta juyo a tsorace ganin Uncle Joe ne yasa ta k'ara razana,
"You know what will happen if you open your mouth right?" shine abinda ya rad'a mata a kunne.
Ta k'ak'aro murmushin dole tace "Dr Sajid... I ..I..want to congratulate you for the award"
"Oh Thank you dear, and you are?"
Joe yayi saurin cewa " she's my niece Irene, 'yar yayana Isaac ne, kasan bata jima da dawowa Nigeria ba may be a USA ta sanka"
"Oh really nice meeting you Irene"
Joe ya mik'a masa hannu suka yi musabaha yace "see you on Monday"
Sajid yai murmushi tareda barin wajen.
Sajid na barin wajen, Joe ya shak'ota "mikike son gaya mishi? Wato bakisan ki rufe bakinki ba ko, then I'll make you"
Ya shak'eta da k'arfi idonta suka firfito tama kasa magana.
"Uncle Joseph!" Nick ya kira da k'arfi
Joe ya hankad'ata ta fad'i k'asa, yace "idan baki jin magana, kin san mizai biyo baya ai"
Nick ya kalleshi cike da mamaki, Joe ya dafe kafad'arsa yace "Nickolas, karka damu ba komai bane, kasan Irene tasowan k'asar waje ce, so I've to teach her some Naija Manners, kwata-kwata bata jin magana wai wani yaron Musulmi ta ke so imagine"
"Still uncle bai kamata ace ka shak'eta ba"
Joe ya ce "tafi da ita cikin gida, zamuyi magana daga baya"
Nick da sauri ya k'arasa wajenta, har lokacin tana rik'e da wuyanta sai tari take yi. Ya sa hannu ya d'auketa yayi cikin gida da ita.
Kan gadonta ya kwantar da ita sannan ya fita yaje ya samo mata ruwa mai sanyi, ya zuba a glass cup ya tallafota ta shanye tas sannan ta fara ajiyar zuciya akai akai.
"Kiyi hak'uri Irene, Uncle Joe bazai kuma miki haka ba I'll make sure of that kinji" ya jawota jikinshi ya rungume yana bubbuga bayanta a hankali, itakam kuka ta fara, tunowa da tayi da abubuwan da suka faru watanni hud'u da suka wuce".
Shikam sam hankalinsa bai gamsu da abinda Uncle Joe ya faɗa d'azu ba, there's more to this, ko ma minene dole ya ganoshi, dan bazai bari Uncle Joe ya walak'anta mishi angel d'inshi ba.
Haka dai ya cigaba da bubbuga bayanta har bacci ya kwasheta, ya kwantar da ita, zai tashi yaji ta sake k'ank'ameshi, "plz don't leave me alone" yaji tace.
Duk da yasan cikin magagin bacci ta fad'i hakan amma har zuciyarsa yaji dad'in maganan. Ya sake hugging ɗinta sosai yana shafa bayanta a hankali.
Ina ma Irene ta zama tasa, ina ma ace yadda suke taren nan su kasance a haka ko da yaushe.
ya tuna farkon ganinta da yayi, tana kitchen tana yin pancake, ya shigo ganin tun daga bayanta tana da shape mai kyau , ya sa shi rungumeta ta baya ya fara shafa k'irjinta yana kissing wuyanta, "wace damsel muka samu agidan nan, yaushe kika zo ban san dake ba" ji yayi kan kan kan da sauri ya yi baya yana dafe da kansa "ke miye haka" pan d'in da take tuyar dashi ta kwad'a masa aka, "that's how pervert like you should be treated"
Bai isheta ba ta d'auka sauran batter d'in ta watsa mishi, duk da ya kauce amma saida kad'an ya zuba mishi, tayi tsaki tabar kitchen d'in.
Tun daga ranar yaji Irene ta shiga ransa, duk matan daya nema ba wanda suka ta'ba resisting ɗinsa, wasu ma da kansu suke kawo kansu wajensa, but Irene was different. Ya mata peck a goshi yana murmushi......
***
Hotel d'insa ya koma cike da tunani iri iri, tabbas akwai abinda Irene ke son fad'a mishi kafin Joe ya zo, kuma ya lura da yadda ta chanja bayan Joe d'in ya rad'a mata abu a kunne, gaskiya dole ya had'u da Irene.
Kiran wayarsa ce ta katse masa tunani, ganin sunan Zaytunah yasa shi k'aramar tsaki kafin ya d'auka, muryan Azra ya fara ji dan haka ya saki ransa, sun jima suna hira da yaran kafin Zaytunah ta k'arbi wayan da alama tabar wajen da yaran suke dan ya dena jin hayaniyar su.
Gaisawa suka yi sama sama yace mata sai da safe, kawai ya ji ta fashe masa da kuka, har ga Allah bayason ya ga mace na kuka balle kuma matarsa.
Ya sani Zaytunah tana iya k'ok'arinta, and he respects her for that, amma shekara goma da aurensu but still har yanzu bata gama gane shi ba, Shi mutum ne da when he says NO he mean it, amma kusan fiye da rabin fad'arsu akan sa'ba masa da take yi ne.
Lallashinta ya fara yi da k'yar tayi shiru, suka d'an ta'ba hira, tana kawo maganar Sady yace mata karta kuskura ta kuma kira masa sunan nan. Haka dai suka yi hira kad'an kafin suka yi sallama bayan ta sanar dashi ran Monday zata koma wajen aiki.
*Kaduna*
Cikin 'yan kwanaki biyun nan Layla ta chanja, tana k'ok'arin sallah akan lokaci, ta yiwa kanta fad'a sosai, ran Sunday Zahra ta zo mata wai su je club Layla tace ba zata ba, abin har ya kusa jawo fad'a k'arshe dai Zahra ta tafi tana 'yen zage-zage. Ita kam Layla zuciyarta wasai taji haushin kanta sosai data biyema muguwar shawarar Zahra harta yi k'ok'arin seducing AY .
Mom ma kanta ta ga chanji a wajen Layla, dan tanajin muryanta idan tana tilawa bayan ta idarda sallan asuba...
Suna zaune ta shigo falon Mom d'in ta tsugunna ta gaishesu, Alhaji Kadi yace zo baby nah ki zauna kusa dani. Ta taso ta zauna kusa dashi tace "Daddy dama zanje nayi ragister a Islamiyyan da su Zaliha ke zuwa ne (Zaliha 'yar Mai gadinsu ce), shine nace na sanar daku kafin na fita"
"Islamiyya kuma?, at what age Baby nah, ai kin girmi zuwa irin wannan wajajen"
Mom tace "haba Alhaji ya za ka ce ta girmi karatu, ni inaga hakan da tayi dai dai ne, bokon da tayi ya isa haka sai a koma ilimin neman lahira kafin tayi aure"
Alhaji Kadi ya wayance yace "Hajiya nifa ina nufin ta shiga cikin yaran da ta girmesu ana musu karatu tare ba yi bane, kawai ta nemo malami ya dinga zuwa yana koya mata a gida"
Cike da shagwa'ba tace "Daddy I can handle it, karatu cikin mutane yafi dad'i"
Ya pecking goshinta yace "as you wish my princess.
Kina buk'atan kud'i ne?"
Tace "no Daddy ina dashi"
.....yammacin ranar suka je Islamiyya tareda su Zaliha, islammiyyar da d'an tazara sosai da gidan amma haka suka tafi da k'afa tace bazata hau mota ba, ko hijabin da tasa ma Zaliha ce ta bata aro dan itakam bata da hijab ko d'aya.
Yana fitowa daga sallar Isha yaji k'aran shigowar text wayansa, ya fiddo da wayar ya bud'e sak'on kamar haka
*Dan Allah gobe kazo ka kaini office...
Layla*
Yayi murmushi ganin tarkonsa ya kamata.
....Monday
Yana cikin mota yana jiran fitowar Layla, wayarsa tayi ringing.
Ya amsa kiran
"Agent SY ya aka yi ne?"
"Oga abu baiyi kyau ba fa, gaskiya it's not fair"
"Subhanallahi, miya faru?"
"Kasan file na Alhaji Kadi an ajiyeshi gefe, yau inajira abani assignment akanshi kawai aka bani wani, ina tunaninma ko an bawa wani agent d'in ashe totally an dropping case d'in, imagine fah"
AY yai dariyar takaici yace " SY mutum da kake gani mugu ne, yanzu haka k'ila shi Alhaji Kadi d'in ya ji labarin za a bincike shi shiyasa ya bada toshiyar baki aka rufe case d'in,
Look at what happened to me, daga k'arshe me aka yi, aka manipulating evidence dana kawo sannan aka dismissing case d'in"
"Sai hak'uri Oga, gashi nasa ka fara min digging kuma gashi anyi watsi da case d'in"
"Karka damu, zan cigaba da bincike a hankali, may be with my findings za a sake reviewing case d'in"
Yana kashe wayar wasu zafafen hawaye suka fara gangaro masa,
Abubuwanda suka faru shekaru biyar da suka wuce ya fara ganinsu a idonshi.
"Aisha ku bar gidan nan yanzu, basai kun d'auki komai ba, just get out of the house all of you, koda makwabtane ku shiga Ina zuwa yanzu"
Shine maganarshi ta k'arshe da matarsa. Tunda ya shigo layinsu gabanshi ke fad'uwa ganin wasu police da Mai anguwa da wasu tsirarun mutane ak'ofar gidan ya sashi fitowa daga cikin mota a bircike.
Wani police na k'ok'arin dakatar dashi amma ina ya bangajeshi ya shige falon, jini daya gani na malala a k'asa yasashi freezing a wajen.
Da k'yar yake taka k'afafuwansa ji yake kamar wuta yake takawa,
"Aisha, Surayya, Ahmad, Imamu" ya kira sunan kowanne gawa daya gani kwance a wajen cikin jini.
"Ummah, Ina Ummah na"
Da sauri ya shiga d'akin Ummanshi, itad'inma kwance take Kan sallaya rik'e da carbi ba rai.
Da sauri ya je ya rungume gawar yana wani irin kuka me tada hankalin me sauraro....
Gwamnati tace 'yan fashi suka kashe iyalenshi, amma shi yasan wanda ya aikata hakan.
Azzaluminda har yau yana rayuwarsa cikin jin dad'i, kotu tayi watsi da hujjoji da ya kawo saboda an riga an gur'bata evidence d'in.
Saboda wannan ya ajiye aikin shi a matsayin shi na CID agent, aikin da yake tsananin so.
Mahaifiyarsa, k'anwarsa, matarsa da yara biyu duk an hallakasu. Aaliyah ce kawai ta saura masa itama badan lokacin tana boarding school ba da tuni itama an hallakata.
"Ka barwa Allah komai Alyasa'a, kada kad'au fansa, Allah na nan, zai saka maka" shine kalaman mahaifin Aisha, kuma shine kalaman daya hanashi daukan fansa har yau..
....tunda ta shiga take sallama amma bai ji ta ba, jin sheshsheqar kuka da yake yasa jikinta yai sanyi.
Ta daure ta sa hannu ta fara bubbuga bayansa tana kiran sunansa.
Ya d'ago a firgice tareda juyowa ya kalleta, idonsa jaa zir.
Gaba d'aya ya bata tsoro miya sameshi yake kuka haka?
"AY are you ok?"
Girgiza mata kai yayi tareda tada motar suka bar gidan ba tareda yace mata komai ba.
Ita dai tana satar kallonsa lokaci zuwa lokaci, tunanin abinda yasa AY kuka takeyi amma ta kasa ganowa k'arshe dai kawai ta danganta hakan da rashin kud'i, tayi alkawarin taimaka masa da ko nawa zai buk'ata.
Har ya kaita office babu wanda yace da wani komai.......