Mutum Mugu Ne

Chapter 8

by @azizat



           08



Kai tsaye office ya kai ta, ita kam Layla bata iya tabuka komai ba a office, duk tunanin AY ya hana ta sakat, "mi zai sa AY kuka?" Shine tambayar da yake yawo a k'wak'walwarta. Haka dai ta kasa samun nitsuwa k'arfe sha biyu ta kirashi tace yazo ya kaita wani waje.


Da sallama ta shiga motar, ya amsa mata yana mamakin chanjawarta gashi yau ya ga shigar mutunci tayi, jallabiya bak'a tasa tayi rolling da gyalenshi. 


Kai tsaye Bank tace ya kaita. Suna zuwa ta fita ta shiga ciki, can kusan 15mins sai ga ta ta dawo, tace masa ya kai ta gida.


Suna parking a parking lot na gidan, ta kira sunansa "AY" Bai amsa ba ya juyo da kansa yana kallonta, gaba d'aya da idonsu ya had'u sai ta ji wani yaarr, ya ma ta kwarjini da yawa. Tayi shiru bata ce komai ba.


"Idan ba abinda za ki faɗa zan je na yi sallah" 


Tayi saurin fito da envelope a Jakarta ta mik'a masa, bai k'ar'ba ba yace "minene wannan?"


Ta sunkuyar da kai tana wasa da iPhone d'inta bayan ta ajiye masa envelope d'in a d'aya seat d'in.


Ya d'auka envelope d'in ya bud'e ya ga kud'i ne aciki 'yan dubu dubu, bai ko fitar da su ba ya ninke envelope d'in ya mik'a Mata tare da cewa "miyasa kika bani wannan?"


Still Bata d'ago ba tace "it's 100k nasan zai taimaka maka, and idan ya yi kad'an ka gaya mini zan k'ara maka" 


Sosai abin ya bashi dariya amma ya gimtse yace " Layla wa yace miki Ina buk'atan kud'i?"


" Ba Kaine ka ke kuka ba"


"Kuma sai aka ce miki rashin kud'i ne kawai zai sa mutum kuka"


Ta d'ago ta kalleshi cikin shagwa'ba tace " toh me ya saka kuka?"


Ya ajiye mata envelope d'in a cinyarta yace " Layla kud'i ba shine maganin komai ba, akwai abinda kud'i ko wata dukiya a duniya bazai iya samarwa ba Kuma....."


Shigowar kira wayarsa yasa ya k'atse maganar. 


Da zumud'i ya d'auka wayar bayan ya ga sunan dake screen d'in tareda sallama


Aaliyah : "Abbana kana lafiya?"


AY : " lafiya lau baby nah, ya kike, ya school:+?"


Aaliyah: "Abba ina baka manta ba, jibi ne fah"


AY: "ban manta ba baby, Kuma Ina nan tafe Insha Allah, just be a good girl"


Aaliyah: "ok Abba sai anjima matron tana min magana, I love you"


AY: "I love you too baby nah"


Wani tuk'uk'in bak'in ciki ne ya soki Layla a zuciya, wato ma dan mace yake kuka shine ita kuma ta kasa samun nitsuwa har da bashi kud'i.


Ficewa tayi daga motar ko rufowa bata yi ba ta tafi, daga ganin tafiyar da takeyi kasan ranta a 'bace yake.


AY ganin yadda ta fita a fusace ya sa shi yin murmushi...


Ko abinci Layla ta kasaci, kunnenta sai maimaita kalamen AY na k'arshe take yi "I love you too baby nah" ta rasa dalili amma haushin maganar take.


Shi kam sai da yayi sallar Azahar sannan ya shigo gidan ya mik'a wa mai aiki envelope yace ta kai wa Layla.


Ai kuwa kamar ya k'ara mata wani bak'in cikin ne, tayi wirgi da envelope d'in ta fad'i k'asa tana kuka.... 

Ko kukan minene oho.....


             LAGOS



...... Flashback




Bayan an gama taro kowa ya watse, Joe ya shigo d'akin Madam B a bircike, har lokacin bata chanja kaya ba tana zaune a bakin gado ta k'urawa hoton Aliyu dake manne a d'akin ido, yanayin kallo da ta ke yi tamkar ganinshi a raye take.


"Anty B, wannan yarinyar Irene tana son fallasa abin da ta gani, imagine d'azu tabi Sajid tana son mishi magana, if not na hango sanda ta bishi nima na bita, bamu san mi take shirin fad'a masa ba, it's time we send her back to USA.... Kawai ma ta bi Babanta su tafi ranar Monday"


Ko kallonshi Madam B bata yi ba balle ta san yana magana.

Ya cigaba " Anty B say something if not zan iya mata komai dan kawai asirinmu ya rufu"


" Will you shut up Joseph!" Madam B ta daka masa tsawa...


"Shikenan saboda Irene tasan kad'an daga asirinmu sai mu hallakata, are you that bloodthirsty Joseph?"


"I'm sorry Anty B"


" Isaac k'aninane kamar yadda kake k'anina, although muna da banbancin ra'ayi but still he's my brother don't ever forget that, Irene kamar Emily take a wajena so don't even think of doing anything to her"


"Kiyi hak'uri Anty B, to mi zai hana ta bar k'asar nan kawai, hakan zaisa tayi shiru da bakinta"


Wani walak'anceccen kallo ta bishi dashi, sai da jikinsa yai sanyi....


" Idan kanaso kar asirinmu ya tonu, make sure we win this case, ka dena damuwa da Irene ba abinda zata iyayi"


"But ...Anty..."


" Joseph!"


Yadda ta daka masa tsawa sai da ya tsorata sosai, tunda yake bai ta'ba ji tayi masa haka ba. 


Ta taso ta zo daf dashi "idan baka da sauran aiki ka nemomin yadda aka yi Sajid ya samu will d'in Aliyu na k'arshe"


Joe ya zaro ido " ya akayi ya san da shi?"


"Get out of my room Joseph!"


Da sauri ya fita daga d'akin dan ya ga alama yau fa Madam B a kufule ta ke....




Irene na farkawa ta ganta jikin Nick, da sauri ta fara k'ok'arin janye jikinta.

"Beauty kin tashi" Nick ya rad'a mata a kunne


Bata ce komai ba dan kunyarsa ta ji, ta matsa daga jikinshi tana kallon ceiling....


"My shy angel, yau kin sani farin ciki"


Tayi sauri ta juyo ta kalleshi da alamar tambaya a idonta.


Yai murmushi " ba abinda kike tunani bane Irene, i mean I'm happy because you slept in my arms, how I wish kullum ma haka zata kasance "


"Thank you Nicholas for helping me"


" It's my pleasure angel" ya mata peck a goshi sannan ya tashi ya bar d'akin.


Irene ta tashi ta shiga bathroom itama, ta jima sosai acikin bathtub d'in kafin ta k'arisa wankan ta fito d'aure da towel, ta nufi wajen dressing mirror kawai tayi arba da Madam B, tana zaune akan gadonta. Wani shock ta ji har cikin k'wak'walwarta jikinta ya fara rawa saboda tsoro.


"Zo ki zauna kusa dani my Irene" inji Madam B 


A hankali ta k'arisa ta d'an zauna gefenta cike da tsoro,


"Irene mi kike son sanar da Dr Sajid d'azu da ya zo wajen party?"


Tsoro da fargaba ya cikata ta kasa cewa komai


Bridget ta kamo hannunta da tunda ta zauna yake shaking tace " I know you are a good girl so continue being one, any mistake daga wurinki kin riga kin san mizai faru, and I mean it"


"I'm sorry Mommy B" ta fad'i still jikinta bai bar rawa ba


"Tunda mun fahimci juna barin tafi"


Sai bayan minti biyar da ficewarta sannan ta iya tashi daga wajen da take zaune...


Tabbas abinda yaji Mommy B ta fad'awa Irene bai kama hankalinsa ba, ya tuna abinda Uncle Joe ya mata da safe, tabbas akwai lauje acikin nad'i.... "something is fishy" yace a zuciyarsa, har zai shiga d'akin Irene sai ya fasa ya koma nashi d'akin dan yasan ko ya tambayi Irene bazata sanar dashi abinda ke faruwa ba.


Nick ya shigo zai d'au wayarsa da ya manta a d'akin Irene ya ji Mommy B na magana shine ya la'be yana jin abinda take faɗa.....




     Monday...


 


Duk yadda Isaac yayi da d'iyarsa akan ta bishi su koma USA tak'i, tace mishi zata koma amma ba yanzu ba, yayi mamakin yadda bata damu da rashin ganin yayunta Steve da Praise ba, amma ya danganta hakan da kasancewa grandma d'inta na gidan, shikanshi ba dan mahaifiyarsa ba ba abinda zai kawoshi gidan Bridget saboda kwata-kwata ra'ayin su ba d'aya bane......


Ba yadda ya iya dole ya hak'ura, jirgin k'arfe shida na safe zai bi dan haka tun k'arfe biyar ya gama shiryawa, Irene da Nick ne suka raka shi airport.


A hanyarsu ta dawowa Nick ya tambayi Irene ko akwai matsala tsakaninta da Mommy B da Uncle Joe, ta ce mishi ba komai, shi dai bai yarda ba amma ya nuna mata ba komai ya amince da abinda tace. Can cikin zuciyarsa ya d'au alkawarin gano abinda ke faruwa ....


Tare suka shigo gidan, suka samu 'yan gidan nayin breakfast....


Irene zata wuce d'akinta ta d'an kwanta kafin ta yi nata breakfast d'in saboda ba tare take cin abinci da su ba, zuwan Daddynta nema yasa take zuwa dining cin abinci, taji an kira sunanta "Irene"


Ta juyo ta kallesu ba tareda tace komaiba...


"Ki shirya da wuri zamu wuce court anjima" shine kad'ai abinda Mommy B tace sannan ta cigaba da cin abinci...


Duk da bata yi tsammanin haka ba amma ta ji dad'i saboda koba komai zata ga masoyinta Yamin, koda kuwa hangoshi za ta yi daga nesa......


"Amma Mommy B shine kika hanani zuwa court amma zaki tafi da ita Koh" Emily ta fad'a tana cuna baki 


"Emily kina da class da safen nan, so concentrate on that, bana son carry over this semester kin ji"


"Amma mommy B....."


"Will you shut up, Irene ta riga ta gama degree ɗinta while kina nan kinata shirme" inji Joe 


"But daddy Irene studied abroad fah nima da k'asar waje ka turani dana gama" 


" Idan kika yi k'ok'ari wannan semester I might send you abroad" Mommy B tace da ita.


"Nidai kawai ba kya sona, ai Jane tun da ta gama secondary school kika turata ni kuma kin k'i" ta tashi cikin fishi ta bar dining d'in.....


 ........Zama na farko a court .....