11
by @azizat
*MUTUM.....Mugu ne*
11
Tunda suka bar hotel d'in ta kasa 'boye farin cikinta, gani ta ke yi kamar a mafarki, duk sadda ta rufe ido shi ta ke gani, haka nan k'wak'walwarta ke tuno mata maganarsa, yadda muryarsa ke da sanyi, ga turancinsa kamar wani bature, saboda accent ɗinsa kwata-kwata baya kama dana 'yan Naija. Tim har su ka iso gida bai bar tsokalanta ba.
...Kaduna....
Sallah Layla ta gabatar sannan tayi shirin Islamiyya, zuwa ta yi BQ ta jira su Zaliha su ma su ka shirya.
Tare suka fito su hud'u kowa sanye da doguwar hijab har k'asa. Tana ta kalle-kalle ko za ta ga AY amma bata gan shi ba, sai da su ka iso gate, tana bud'ewa tayi ido hud'u da shi, ya dawo daga sallar la'asar kenan.
Kallon-kallo suka tsaya yi kusan 30 sec sannan ya kau da kanshi gefe tareda matsawa ta fita, sannan sauranma su ka bi bayanta.
Mamakin ganinta da uniform ɗin islamiyya yayi dan shi bai san ta fara zuwa islamiyya ba. Ta masa kyau sosai dan bai ta'ba ganinta da irin shiga haka ba, gashi fiskarta babu kwalliya, sai asalin kyaunta ya fito.
Wajen da Baba maigadi yake zaune tareda wasu ma'aikatan ya nufa, su kan ba su isa fita su yi sallah a waje ba kamar yadda ya ke yi, saidai idan sallar ne ya riskesu a waje.
Manu gardener na gidan yace "amma na yi mamakin canjawar yarinyar nan, farkon dawowanta gidan nan ko kallon arzik'i mutum ba zai so ya mata ba"
Baba maigadi ya ce "ni kam ban yi mamakiba, dan dama asali ba haka ta ke ba, zuwanta k'asar waje ya maidata haka"
"Da alama Baba ka jima agidan nan sosai?" AY ya jefo masa tambaya.
"Tabbas ina d'aya daga cikin ma'aikatan gidan nan tun farkon tarewarsu"
AY ya ce " kasan dalilin da ya sa Layla bata tuk'a mota?"
Baba ya d'an murmusa yace " Ni ko na sani" haka ya cigaba da bashi labarin abinda ya faru, AY cikin hikima ya dinga tambayar ma'aikatan game da rayuwar gidan.
....washe gari ...
Shigar atampa Layla ta yi d'inkin ya matseta sosai dan haka ta d'auko after dress bak'a ta saka akai... A tsanake ta yi breakfast ta fito, as usual a cikin mota ta same shi tana shiga yana gama wayar da ya ke yi, sallama ta masa, ya amsa tareda cewa "Layla gobe asabar zan yi tafiya, so ina ga inkinada buk'atan fita sai dai wani ya kai ki ko kuma ki jira har na dawo" Bai jira mi za ta ce ba ya ta da mota.
Shiru ta yi duk ta ji ba dad'i, duk da bata cika fita ranar asabar da safe ba, amma ta ji haushin tafiyar da zai yi, musamman da ta tuna wayarsa na jiya.
Maimakon ya wuce office da ita, wani bakery ya nufa, ba tareda yace mata komai ba ya fita daga motar.
Ta yi sa'a bai fita da wayarsa ba ya sak'ala ta a chaji. Ta yi sauri ta d'auko wayar cikin sa'a ta ga ba password a kai. Da sauri ta shiga dialer ta ga last call da ya yi da numbar da ya yi saving da suna baby Aaliyah, take ta ji ranta ya 'baci, kenan da gaske aure zai yi. Ta rasa dalili, amma tunda ta ji wayar da ya yi jiya, ta ke jin haushinsa.
Jiki na rawa ta danna kiran numbar ta saka a kunne, Sai da ta kusa yankewa aka d'auka "Hello Abba ina class" k'iit aka kashe wayan
"Abba" ta nanata sunan tareda murmushi, ta yi saurin maida masa wayan yadda ya ke.
Ba a jima ba ya shigo ya tada mota suka tafi.
Saida ya iso ma'aikatar nasu sannan tace "AY zan bika inda za ka je gobe"
"Me yasa?"
"Saboda ...saboda ...haka kawai, ba ka so na je ne?"
Girgiza kai ya yi yace "ba matsala sai ki shirya da wuri"
Da murna ta fita daga motar dan ta d'auka zai yi jayayya sai kuma ya amince lokaci guda.
.....Lagos....
Da wuri ya shirya saboda dole ne ya je ya ga patient d'insa da aka wa aiki jiya, ya riga ya kira Ishola driver, yana jiransa a waje. Da shirin barin hotel d'in ya fito daga d'akinsa, saboda dama jiya agajiye yake shiyasa bai k'arasa inda ya fara lodging ba. Yana rufo d'akin wayansa yai ringing. Ganin Dr Lakunle ne ya sa shi saurin d'aukan kiran,
"What!, I'm coming now"
Shine abinda ya fad'i kafin ya fita da gudu...
......Saida ya samu patient d'in ta zama stable sannan ya fara musu fad'a, magana ya ke yi amma idan ba kana kusa dashi ba bazaka gane fad'a ya ke yi ba, ransa ya 'baci sosai da abinda su ka aikata
" why is it so difficult to work with you guys? I gave specific instructions before I leave last night, 'don't give the patient anything till I come, she might suffers convulsion when she wake up but don't give her anything'. Is that not what I said?"
"Sorry sir I thought..." Inji nurse Rita da ta yi wa patient d'in allura
" You thought what?..., Are you questioning my abilities? That I don't know what I'm doing, is that it?"
Gaba d'aya su ka yi shiru, ya cigaba "I've worked with many experts in different countries in the world, and not for once was my competency demean"
Ajiyar zuciya ya yi sannan yace " I think my service is not needed anymore" ya juya ya fita daga office d'in. Ko taku biyar bai yi ba ya ji an dafa shi da sauri ya juyo dan ya ga wayene. Wani baturen likita ya gani. Murmushi likitan ya masa sannan yace "I'm Dr James Perkins"
Sajid ya d'an sake fiska yace "Dr Sajid"
Office d'in Dr Perkins su ka nufa, bayan ya zauna, Dr Perkins ya ba shi hak'uri game da abinda aka masa, duk da Dr Perkins ba a 'bangaren ya ke ba amma bai ji dad'in abin ba kwata-kwata. Da k'yar ya shawo kansa ya amince ya cigaba da yi musu aiki kafin ya tafi, field ɗin da ya ƙware a kai a gaba d'aya ƙasar ma ba su da yawa wanda su ka yi karatun.
Dole dai Dr Sajid ya hak'ura ya koma....
......tunda Naziha su ka zo aiki yau ta ke sa ido d'akin da ya k'ar'ba jiya, amma ba ta ji d'uriyansa ba, da alama ya riga ya fita ko kuma ya tafi gaba d'aya ma. Ganin ta damu ne, yasa Tim duba mata record ko ya check out, amma bai yi ba, Dan haka ta ji d'an sauk'i aranta. Duk wani ayyuka da ta ke yi ranar tana yi ne kawai amma tunanin Sajid ne ya ke zuciyarta. Tsokala kam ta sha a wajen Tim tun tana ce masa ya bari harta dena.....
Har yanzu Sajid bai dena jin fargaba ba, haka dai ya daure ya ke duba patients masu matsalolin da suka shafi fanninsa. Sai wajen k'arfe biyar ya bar asibitin kai tsaye masaukinsa ya nufa inda suka had'u da Barrister Idris, sun jima suna tattaunawa kafin daga bisani barrister ya tafi.
Yana sallar Isha ya ordering abinci aka kawo mishi, yana k'ok'arin bud'e take away d'in wayanshi yai ringing.
Dr Lakunle ne, ya kirashi, hak'uri ya bashi bisa abinda ya faru da safe. bayan ya gama wayan ya d'an tsakuri abincin sannan ya fara k'ok'arin cire kayanshi dan shirin bacci. Kwatsam ya lura babu agogo a hannunshi.
" Ya Allah" ya fad'i tareda dafe kanshi bayan ya tuna inda ya manta agogon. Ba wai saboda tsadar agogon zai koma ya je ya d'auko ba, sai dan Zaytunah. Tabbas idan ya koma Abuja ba tareda agogon nan ba, ba za ta ji dad'i ba, anniversary gift data bashine, gashi ita da kanta ta saka mai cikin kayansa da zai taho. Idan ya gaya mata ya manta a wani hotel room ba za ta ji dad'i ba, ya san halinta sarai sai ta yi ta mita akai.
Sanye ya ke da denim jeans ash color, sai shirt wine color, akwatin kayanshi ya d'auko wata ash jacket ya d'aura saboda yanayin garin akwai d'an sanyi musamman area da zai je yanzu. Room slippers ne a k'afarshi dan haka ya d'auko Balenciaga sneaker shi ma wine color d'in ne ya saka. Wayarsa kawai ya d'auka sai wallet. Ya riga ya sallami Ishola driver dan haka taxi zai hau.
A hankali yake tafiya har ya fito daga hotel d'in, zuciyarsa ke bugawa da sauri sauri dan haka ya fara Karanto addu'o'i. Ji ya yi kamar ya fasa zuwa d'auko agogon wata zuciyar tace ya je kawai ba komai.
Fitowa yayi har bakin titi yana tsaye zai nemi taxi ya ji an kira sunanshi da sauri ya waigo dan ganin mai kiran nashi. Sai dai kash yana juyowa aka bud'a mishi wata powder..........
Sanyin ruwan da aka watsa masa ne yasashi farfad'owa, dishi-dishi ya fara gani zuwa abinda bai fi 40sec ba ganinsa ya koma dai dai. An ɗaure shi ne akan kujera an kuma rufe masa baki. Duk da wajen da duhu sai d'an hasken wata lamp da aka ajiye chan gefe bai hana shi gane yanayin d'akin ba, da alama irin uncompleted building d'in nan ne suke....
Wani k'ato sanye da bak'ak'en kaya ne ya watsa masa ruwan, sai wasu da suma da ka gansu ka ga 'yan daba suna tsaye gefe da alama wancan shine ogansu.
Ogan ya zauna a kujera suna facing juna yace cikin pidgin " sunana Debo, zan tambayeka wasu abubuwa wanda na ke so ka amsamin cikin ruwan sanyi, idan ba haka ba zan nemo amsan ta k'arfi"
Ya cire masa igiyar da su ka rufe masa baki ya ce " wani evidence ka ke shirin gabatarwa a kotu?"
Sajid murmushi ya yi yace " Madam Bridget ta sa ku kawoni nan?"
Debo ya kwad'a mishi mari " abinda na tambayeka zaka amsa mini ba wai ka amsamin tambaya da wata tambayarba" ya fito da wayar Sajid daga aljihunshi yace " ka gayamin evidence da ka ke da shi sannan a ina yake?"
Sajid ya riga ya lura da sauran boys d'in dake gefe yaga dukkansu biyu adda ne a hannunsu, Debo ne kawai da bindiga a hannunsa. K'ok'arin saita plan d'insa ya ke yi ya ji Debo ya take masa k'afa, ba k'aramin zafi ya ji ba amma ya daure ya rintse ido.
"Ka amsamin tambaya ta ko kuma kasan wanene Debo" ya daka masa tsawa.
Sajid yace "evidence d'in yana wayata"
Sai a sannan Debo ya d'aga k'afarsa daga kan ƙafar Sajid.
Yace " mi ye password ɗin wayarka?"
Sajid yace "akwai fingerprint dole sai na sa ka hannu kafin ta bud'e"
Debo yace "k'arya ka ke password ne"
"SZ45UMA" Sajid ya fad'a mishi
Yana sakawa maimakon ya bud'e gaba d'aya sai ya nuna masa wajen thumbprint kuma.
"Skewy" Debo ya kira d'aya daga cikin guys d'in yace ya kunce wa Sajid hannusa d'aya saboda yasa yatsarsa wayar ta bud'e.
Skewy ya zo bayan Sajid ya fara kunce masa hannu. Zamanshi a japan da Korea ba a banza ba, karate da judo classes daya attending duk ya fita da certificate mai kyau.
Wani naushi ya kaiwa skewy saida ya had'e da bango, ganin yadda ya taso a harzuk'e yasa d'aya guy din da Debo su ka yo kanshi, nan fa fad'a ta kaure tsakaninsu......... Sajid ya samu ya ka da d'aya guy d'in k'asa yana juyowa kan Debo ji kake 'tash' Debo ya harbeshi da bindiga .. Sajid ya dafa kafad'arsa yayi baya ya fad'i a wajen.
Debo yai saurin d'aukan wayarsa ya kira wata number ya fara magana " Hello Oga Joseph akwai matsala fah na harbe shi...." Bai k'arasaba Sajid ya buga mishi kujerar katako da aka d'aure shi ajiki d'azu Debo ya fad'i sumamme..
Da sauri Sajid ya fito daga d'akin yasa hannu ya danne kafad'arsa wajen da bullet d'in ya shigeshi duk da dare ya fara yi sosai, gashi jikinsa ba k'wari haka ya daure ya fito daga gidan ya na tafiya bai san inda zai je ba, dan gani ya ke yi wajen jejine, addu'a kawai ya ke karantowa har ya samu da taimakon Allah ya iso bakin titi, hannu yasa ya tsare wata taxi da tazo wucewa yana shiga ya tambayi Mai Taxi d'in wani hotel ne mafi kusa da nan, Mai taxi ya ce " Obalende Hotel"
Jin sunan ya yi kama da sunan hotel d'in da zai je ya ce ya kai shi da sauri. Tunaninshi ya samu ya kai hotel d'in dan ya cire bullet d'in sannan ya samu ya treating kansa ba zai iya zuwa asibiti ba cox idan aka ga harbin bindigane dole su sako police a ciki. Har lokacin yana danne da wajen.
Suna isowa ya tuna ashefa bashida kud'i gashi yana tunanin tunda sun cire masa waya k'ila wallet nashima sun cire ya daure ya sa hannunshi cikin aljihu da ƙyar ko zai samu wallet d'in, aikuwa ya ji ta ciki, da k'yar ya zaro wallet d'in ya mik'a masa wallet d'in yace "keep the change" bayan ya tabbatar babu wani ID nasa a ciki. Hanyar shiga gate d'in hotel d'in ya nufa amma kuma wani jiri jiri ya ke ji har yanzu hannunsa yana dafe da wajen da aka halbeshi. Tsayawa ya yi saboda gani ya ke yi yana k'ara takawa fad'uwa zai yi.
"Are you ok Sir?" Wata murya ta doki kunnenshi, da k'yar ya iya d'aga ido ya kalleta. Duk da akwai d'an duhu kad'an amma hasken wuta da ke jikin bangon hotel d'in yana haskasu. Kallo d'aya ya mata ya san ma'aikaciyar hotel d'in ce saboda ya tuna kalar uniform d'insu.
Kamar da wasa Naziha ta hangoshi ya fito daga cikin taxi, da farko ta k'aryata idonta sai da ta matso kusa ta tabbatar cewa shi ne...
Matsowa tayi kusa dashi ganin yadda yake dafe da kafad'arsa ta wajen gefen kirjinshi, saida ta duba da kyau ta ga jini ya fara ratso jacket ɗinsa. Cikin kid'ima ta matso daf dashi tana fad'in "sir you are bleeding, you have to go to hospital" tana shirin juyawa ta buga gate d'in ko za a zo a taimaka masa. Ta ji ya rik'e hannunta, "help me please, take me somewhere safe, I'll pay you any amount you want". Gaba d'aya ta tsaya a wajen ta kasa yin komai, cikin 10sec zuciyarta ya raya mata abinda ya kamata. Jikinta har rawa yakeyi ta yi saurin fito da wayarta ta kira Tim, yana d'auka tace ya fito waje ya sameta yanzu-yanzu. Sajid ya dafata saboda jiri da ke d'ibarshi, ganin haka tace suje wajen wani dakali ya zauna, haka ta tallafa masa suka d'an yi tafiya kad'an sannan ta zaunar dashi. Gaba d'aya a tsorace take sai sannu ta ke masa.
Jin yadda Naziha tayi masa magana cikin fargaba ya sa Timothy yai saurin fitowa, dan dama fad'a su ka yi yace bazai rakata siyan maganinta ba shi ya sa ta fita ita kad'ai.
Yana fitowa ya duba bai gan su ba, ya fara kiranta jin wajen da phone ke ringing ya nufi wajen.
"Funmi ki lo de?"
Cikin kuka tace "please help him Timothy, we need to save him"
Tim bai ma gane wanda take tareda shi ba saidai ya ga jinin da ya ke rigarsa, k'ok'arin komawa cikin hotel d'in yake dan ya samu ya k'ar'ba key d'in mota a wajen Daddy. Naziha ta daka masa tsawa tace ya tare musu taxi. Cikin ikon Allah kuwa sai ga wata taxi ta sauke wasu 'yanmata a bakin hotel d'in, Tim yai saurin tareshi. Tareda Naziha suka kamashi suka saka cikin taxi d'in.
Asibiti Tim yace suje, Naziha tace gida za su je yafi kusa. "Funmi gida kuma! He's bleeding"
Naziha tace "ee"
Har suka isa gida Naziha addu'a ta ke yi tana hawaye, shi kuwa Tim tsoron mi zai biyo baya ya ke yi dan bai ma gane mutumin da Funmin tace su kai gida ba.
Suna isa gida tare suka fito dashi, Tim ne ya bud'e k'ofa dan mama da Ronke sun yi tafiya safiyar ranan.
D'akin Tim suka shi ga dashi, su ka taimaka masa ya kwanta, Sajid murya na rawa yace su kawo masa wuk'a. Da sauri Naziha ta nufi d'akin su Daddy ta d'auko first aid kit ɗinsu. Kafin taxo Tim yasa scissors ya farke rigan dai dai waren bullet d'in.
Tana zuwa ta bud'e kit d'in Tim ya fara dube dube, idonsa ya hango forcep ciki ya d'auka, hannunsa na rawa. Sajid ya kama hannun dake rawa Tim ya taimaka masa dai dai wajen suka fitar da bullet d'in. Funmi ganin yadda suka saka forcep din jikinshi yasa ta rufe ido tana kuka. Har suka fitar da bullet d'in bata iya bud'e ido ba, musamman da ta ji Sajid yana nishin wahala.
Muryan Tim da ke cewa ta mik'o masa bandage ne ya fargar da ita, auduga suka fara sawa kafin ya bandaging wajen. Suka cire mishi shirt da jacket nashi saboda jini daya ta'basu gashi kuma dama Tim ya farke, sai da aka gama komai ta tashi ta fara gyara wajen saboda jini ya ɗan 'bata wajen.
Bayan sun gama komai tukunna Tim ya gane mutumin, tabbas shine mutumin da ya lodging a hotel dinsu jiya.
Tana zuba masa ruwa yana wanke hannu yace " Funmilayo we are in trouble ooo, mi za mu faɗawa Daddy?"
Funmi da har yanzu jikinta bai dawo dai-dai ba tace " daddy will understand"
Suna fitowa daga bathroom d'in wayar Tim yai k'ara ya duba, ya ga sunan Daddy gaba d'aya ya rasa mi zai yi. Can dai ya d'auka.
" Ina ku ka je dukkanku kun fita ba tareda kun fad'i inda za ku je ba" Daddy ya fad'i cikin masifa
Tim cikin tsoro yace " Daddy dama Funmi ne ta fara ciwon cikinta shine na rakota gida"
"It's alright, Ina ta sha magani?"
"Yes Daddy"
"Ok ganinan dawowa nima"
Yana katse wayar ya duba Funmi da tayi cirko cirko a tsakiyan d'akin. Ajiyar zuciya ya yi yana tunani kala-kala a zuciyarsa.
Ta kai duba zuwa ga Sajid wanda tuni baccin wahala ya d'aukeshi...
Ta zuba mishi ido dan tabbatar da shi d'inne dai *Dr Sajid Usman Abdallah*.........