13
by @azizat
*MUTUM.....Mugu ne*
13
K'arfe biyar na asuba ya bud'e idonshi, abubuwan da suka faru ya fara masa yawo akai, abinda ya iya tunawa last shine wasu yara biyu da suka tayashi dressing kafad'arsa. Addu'an tashi daga bacci ya karanto sannan ya tashi zaune, k'ara duba wajen da aka halbeshi ya yi, ya ga an gyara mishi aikin, babu tantama wanda yayi aikin ma'aikacin lafiya ne. Da shike d'akin da d'an duhu bai gane yanayin d'akin ba, sai dai ya lura da Naziha da ta kwantar da kanta kan gadon da ya ke kai.
A hankali ya kai hannunsa mai lafiya ya ta'ba kafad'arta, cikin barci ta ji kaman ana ta'bata, ta d'an motsa kad'an, sai da ta ji an sake ta'bata tukunna ta bud'e ido. Tunowa da ta yi halin da suke ciki da bak'o majinyaci, ya sa ta yi firgigit ta tashi.
"Sorry I woke you up, I want to use the bathroom" sanyayyiyar muryarsa ya doki dodon kunnenta.
Ta ma rasa me za ta ce masa, da sauri ta tashi ta je wajen switch na bulb d'in d'akin ta kunna wuta.
Lokaci guda haske ya karad'e d'akin. Daga inda ya ke zaune kan gado ya k'are mata kallo. Silk pyjama ne ajikinta kalar majenta, rigar yana da guntun hannu yana da ɗan tsayi dan ya sauka har ciyarta, sai wandon kuma ta sama a bud'e k'asan kuma ya d'an matse, Kanta sanye da satin bonnet kalan kayan, ba za ta wuce 19 ko 20yrs ba, bak'ace tana da jiki d'an dai-dai dan ba za ka kirata siririya ba sannan ba ka ce mata lukutaba, medium size ta ke.
Babban abinda zaifi jan hankalin mutum gareta shine yadda hips d'inta su ka fito musamman idan ta sa wando, tana da perfect curve da maza ke so a jikin mace.
Ya kauda kai ya fara duba yanayin d'akin, d'aki ne ba wani babba sosai ba, gado biyu ne a d'akin amma k'ananan gado irin kwanciyar mutum d'aya sai akwai reading table wadda cike yake da tarkacen litattafai da kuma wata mini laptop akai. Akwai wall closet mai k'ofa biyu, can saman bangon d'akin akwai k'aton hoton wani bature da Kirista ke kwatantashi da Jesus, sai ta d'aya bangon kuma k'aton cross ne kafe a wajen.
Ya dubi d'aya gadon da Timothy ke kwance ruf da ciki ya yi shame shame yana bacci.
Band'aki ta shige ta fara wankewa a gurguje saboda ta san yanzu ya ke buk'atan shiga. Minti bakwai ta gama komai ta fito ta ce "it's ready sir" muryarta har rawa ya ke yi.
Ya taso ya shiga bayin ta bi bayanshi da kallo " Ya Allah he's so handsome" zuciyarta ya ambata lokacin da ya wuce ta gabanta.
Da sauri ta je ta fara tashin Tim, dama shi asali ba gwanin tashi da wuri bane, da k'yar ya bud'e ido. Ta ce maza ya gyara d'akin kafin Sajid ya fito daga ban d'aki. Ta wuce nasu d'akin bacci ne taf a idonta ga ciwon cikinta da yanzu ya fara damunta sosai. Ruwa ta plugging a heater na wanka sannan ta fara gyara d'akin nasu, ta fito da uniform nata na wajen aiki. Tana ajiyewa akan gado taji cikinta ya murd'a mararta na mata wani irin ciwo, ta rik'e mararta tana tsugunne a wajen saboda idan ta tashi wani azabar za ta ji, k'wank'wasa k'ofar da aka yi ya sa ta d'an yi k'ok'arin tashi dak'yar ta je ta bud'e k'ofar dan tasan Daddy ne, idan da Tim ne kai tsaye zai shigo.
Tana bud'e k'ofar ta tsugunna har k'asa ta gaidashi ya amsa mata sannan ya mik'a mata leda yace maganintane, ya siyo jiya ya manta bai bata ba. Cike da murna ta masa godiya. Dan badan Daddy ba yau ba ta san ya zata k'are ba, gashi babu chemist a kusa dasu balle aje a siyo da sauri. Jiya wajen taimakawa Sajid ta jefar da wanda ta siyo.
Kitchen ta tafi ta d'ebo ruwan zafi a flask ta sirka shi sannan ta sha maganin, ta koma d'aki ta had'a ruwan wanka ta shiga tayi wanka. Tana fitowa wata jallabiyarta royal blue ta sa ta d'an kwanta kan gado dan ta samu ciwon ya lafa tunda tasha magani.
Cikin barcin daya fizgeta ta ke jiyo Daddy da Timothy suna addu'a, dama al'adar gidan kenan, idan sun tashi k'arfe biyar da rabi zasu had'u a d'akin Daddy su yi addu'a.
Ta yi saurin duba wayarta ta ga k'arfe shida saura minti ishirin. Ta tashi ta fito ta nufi kitchen dan girka musu breakfast acan k'uryar falo ta hangoshi yana sallah, tsayawa tayi tana kallonshi sabon singlet farine ajikinshi wanda tasan tabbas Tim ne zai bashi musamman da ya ke ya kamashi sosai dan shi ya fi Tim tsayi da fad'i, wandon jeans d'in da ya zo da shi ne still a jikinshi. Ta wuce kitchen d'in ta gyara a gurguje sannan ta fara fere doya, da ta gama ta d'aura akan wuta ta fara yanka tomatoes onions da pepper da za ta yi egg sauce da shi.
Da ta gama yanka kayan miya sai ta fito da sardine d'aya a cikin fridge ta bud'e ta yi mashing ɗinsa a cikin plate. Doyar na dahuwa ta sauke ta d'aura tukunyar da za ta yi miyan kwan aciki .......
Sajid bayan ya yi sallah d'akin da ya kwana ya koma ya kwanta kan gado yana tantance yanayin mutanen gidan tabbas yaron da suka kwana tare Christian ne amma kuma ita d'aya yarinyar kaman musulmace, jiya da ya ganta tana sanye da k'aramin hijabi, gashi yau yaga tabon sallah agoshinta. Yana cikin tunani Daddy da Timothy suka shigo. Yana ganinsu ya d'an tashi zaune ya kishingid'a. Timothy har k'asa ya duk'a ya gaisheshi cikin harshen turanci, ya amsa masa. Sannan shima ya gaida Daddy ya kuma masa godiya kan taimako da su ka masa. Daddy ya ce " Na yi waya da nurse Rita tana hanya za ta zo ta duba ka so kafin nan ka huta" yana gama fad'in haka ya fita daga d'akin.
Tim ya shiga bathroom yai wanka ya fito yana shiryawa .
Sajid ya tambayeshi sunanshi ya ce "Timothy, but you can call me Tim"
Sajid ya sake tambayarsa " the girl that helped me yersterday what's her name?"
"Funmilayo" Tim ya fad'i yana fesa turare ajikinsa ba tareda ya kalli inda Sajid d'in ya ke ba
'Funmilayo' Sajid ya maimaita a zuciyarsa sannan ya ce "what's her christian name?" Ya yi tambayar ne dan ya tantance gaskiyar lamarin.
Tim ya juyo ya kalleshi na wasu seconds sannan ya kauda kai ya ce " she's not a christian Sir, she's a Muslim just like you"
"Oh! I taught so" Sajid ya fad'i yana sake k'ok'arin gano kan zaren. Idan ita musulmace, to ya aka yi su kuma christians? ko mixed family ne?
"Is she your sister? Sajid ya sake jefo masa wata tambayar.
"She's my cousin" Tim ya amsa masa sannan ya fita daga d'akin.
Tim na fitowa ya ji ana buga k'ofa, ya je ya bud'e, Nurse Rita ce ta iso, ya tsugunna ya gaisheta. Tana zaune a falo Daddy ya fito su ka gaisa, Naziha da ke kitchen ma ta fito ta gaisheta.
Kai tsaye d'akin Tim su ka wuce dan duba Sajid.
Ya yi mamakin ganinta, tace mishi ita k'anwar matar Daddy ce, shi ya kirata jiya. Bayan ta dubashi Daddy ya ke tambayarshi abinda ya sameshi. A tak'aice ya sanar dasu cewa wani case ya ke yi da Madam Bridget wanda kowa acikinsu yasan sunan. Hakan ya sa ta ke farautar rayuwarsa.
Daddy ya jinjina masa sannan ya ba shi tabbacin idan yana da buk'ata zai iya zama dasu har lokacin da zai tafi. Sajid ya masa godiya.
Naziha ta gama jera abinci a dining za ta je ta shirya Daddy ya kirata.
Ce mata ya yi ba za ta je wajen aiki ba yau, ta gyara guest room Sajid zai koma wajen, ta amsa da toh.
A gurguje ta gyara saboda dama ba wani datti ya yi ba, kasancewa duk bayan kwana uku ana gyarashi. Sabon bedsheet ta shimfid'a a gadon ta cire nada d'in, ta kawo room freshner ta fesa.
Koda ta gama su Daddy sun fara cin abinci. Kujera ta jawo zata zauna, Daddy yace ba a kaiwa bak'o abinci ba, kallon Tim ta yi shi kuwa ya kashe mata ido, ta riga ta gayawa Tim ya shiga da abincin Sajid tun tuni ashe bai kai ba.
Ta d'auko flask d'in ruwan zafi da kayan tea ta kai guest room, sannan ta dawo ta d'auka abincin ta kai.
Daddy ya fito daga d'akin Tim ya mik'a mata dubu uku idan akwai abinda za a buk'ata ta yi amfani da shi. Ya wuce suka tafi, Tim yana mata gwalo.
Ganin Daddy ya shiga d'akin Tim kafin su tafi ta yi tunanin ko ya riga ya gaya wa Sajid d'akin da zai koma ne, dan haka ta zauna a dining ta ci nata abincin, da ta gama ta tattara wajen ta shiga d'aki, ta d'auko wayarta ta kunna ta shiga browsing da shike Tim ya mata sub na d'ari biyar shekaranjiya saboda ta cinyeshi a game ɗin Chess da su ka yi.
Shiru shiru ba ta ji alamar fitowa ba ta yi tunanin ko bacci ya yi, kusan minti sha biyar ta ce bari ta duba ko bacci d'in ya yi da gaske.
Ta fito daga d'akinsu ta shiga na Tim. Zaune ta ganshi akan reading table yana faman rubutu a wani takarda kasancewar da hannun hagu ya ke yi saboda shine mai lafiyar yanzu, ya sa rubutun bai yi kyau ba.
Suna had'a ido ta yi saurin kau da kai ta ce "Uncle good morning"
"An tashi lafiya, sannu da k'ok'ari" ya amsa mata
Da mamaki ta juyo ta kalleshi, ya aka yi ya san tana jin hausa. Ganin tana mamaki yace " Timothy told me"
'Ya Allah! wannan Timothy d'in da shegen shishshigi ko mi ya kuma gaya masa oho' muryar Sajid ta ji ya ce "ko zan iya samun ruwan zafi kad'an"
Kar dai ba a gaya masa an tanad'a masa abinci a guest room ba, to ko dai ba ya ci ne? To ai ko ba zai ci abincin ba zai sha tea ai.
Tana cikin tunani ya ce "are you ok?"
Ta yi saurin k'ak'aro murmushi ta ce "Uncle ka yi hak'uri na d'auka Tim ya gaya maka akwai abincinka a guest room ne, please forgive my manners"
"It's ok"
" Uncle mu je na nuna maka guest room d'in" ta fice daga d'akin ya ta so ya bi bayanta.
Suna shiga k'anshin miyar kwan ya bigi hancinsa a zahiri k'anshine mai dad'i sosai wadda zai tada appetite na mutum amma shi k'anshin miyar ta da mai hankali ya yi, tuni idonsa ya sauya kala, kafin ya ankara amai ya biyo ba ya.
Naziha da ke shirin had'a masa abincin ta ji shi yana amai. Da sauri ta juya hankalinta a tashe "Uncle are you ok?, Ko na kira Aunty Rita ne?"
Da yatsarsa ya nuna wajen abincin ya mata alamar ta fita da shi. Ba musu ta je ta d'auki tray d'in abincin ta fice da shi. Da ta dawo ta samu ya zauna gefen gado yana riƙe da kanshi, ta k'arasa kwashe kayan sannan taxo ta goge wajen, da shike rabonshi da abinci tun jiya da rana so aman ruwa kawai ya yi.
Data gama d'akinta ta je ta d'auko turaren tsinke ta kunna ta kawo har lokacin tana mamakin abinda ya sa shi amai.
Ta zauna gabanshi rik'e da bowl na roba da ruwa aciki.
"Uncle ka wanke fiskarka" tace da shi, kallonta ya ke yi cike da mamaki. Ga ta very young amma tana da hankali.
Da ya gama wanke fiskarsa ta shiga bathroom ta zubar da ruwan.
Ta dawo ta zauna still agabanshi dan ta ga, yanzu hakalinsa ya dawo sosai.
"Uncle na san bamuda irin abincin da ka ke ci agidannan amma, idan akwai abinda ka ke so ka ci wanda za mu iya samar maka, I'll gladly get it for you"
" Ba wai na rena bane, it's just that I'm allergic to egg, bana cin k'wai, kwata-kwata ko k'anshinsa bana so"
"Oh sorry Uncle, yanzu mi ka ke son ci?"
"Mi zaki iya girkamin?" Ya tambayeta
"Anything you want, zan iya maka pounded yam, semovita and egusi soup, jollof rice, white rice, amala kai Uncle dayawa fah"
Murmushi ya mata dan ta burgeshi.
"Kin san na loosing jini jiya so kinga carbohydrate foods will not be good for me now"
"Uncle Ina zuwa" ta fita da sauri jim kad'an ta dawo da kayan tea ta had'a masa mai kauri ta mik'a masa.
ta ce da shi "Take this for now"
Har ya k'ar'ba zai sha ta ce "uncle ba ka yi brush ba"
Bai ce komai ba sai da ya kur'bi tea d'in sannan yace "Timothy ya bani sabon brush da safe"
Ta duk'ar da kai saboda kunya
Ganin ta k'i tashi ya ce "Hala tea kad'ai zai k'osheni"
Subhanallahi ta fad'i sannan ta fita da sauri. Tana shiga kitchen d'in ta bud'e fridge ta duba kayan da ke ciki da sauri ta dawo d'akin ta lek'o tace "uncle kana cin kifi?"
Ya d'aga mata kai
Ta tafi bai fi minti biyu ba ta sake lek'owa ta ce "Uncle kowane irin kifi?" Ya sake d'aga mata kai
Ta sake dawowa tambayar ko yana cin manja, ya mata murmushi ya ce " ki girka min komai yadda kikeyi just that ni ba bayarabe ba ne, bana son yaji sannan anything da aka yi da k'wai bana so"
White rice ta yi, sai ta d'auko wani k'aton kifin sukunbiya a cikin fridge ta gyara shi ta yi pepper soup sai dai bai yi yaji ba, yajin d'an dai-dai ne amma ya ji citta da black pepper, sannan ta yi miyar ugwu ta san ana cewa ugwu na k'ara jini dan haka cikin fresh leaf da suke da shi ta gyara ta yi miyan da shi, miyan ya ji stock fish da pomo. Yadda ta ke yin aikin kace gasar abinci ta ke yi tsabar sauri.
Da ta gama ta zuba rice d'in a warmer, su kuma miyan da dama bata dad'e da saukewa ba cikin wani glass dish bowl ta zuba su.
Ta je ta jera akan dining table, da ta gama komai ta shigo d'aki ta ce "uncle everything is ready".
Tana tsaye a bakin dining table d'in ya zo. Da kanta ta ja masa kujera ya zauna.
Ta d'auka babban plate ta zuba mishi rice d'in sannan ta saka miyar ugwu d'in agefe, ta zuba mishi pepper soup d'in a k'aramin bowl ta ajiye mishi maltina mai sanyi da kuma ruwan gora, ta ce "uncle wanne zan zuba maka?"
Yace mata Ruwa, tayi saurin tsiyaya masa ruwan a glass cup da ke wajen.
Still tana tsaye ya fara cin abinci da hannun hagu, kamar ta ce mishi za ta ba shi a baki ta ke ji, amma ta daure saboda tana tsoron kada ya fassara hakan.
Haka dai ya cigaba da cin abincin
"Uncle do you like it?"
Murmushi ya yi kawai yaci gaba da cin abincin.
Ta ji dad'in hakan ko ba komai ta san bayan ya koma ga iyalinsa zai tuna cewa ya ta'ba cin girkin Naziha Funmilayo.......
Tana tsaye ya cinye wadda ta zuba mishi, ta tambayeshi ko ta k'ara masa yace "eh".
Ta sake d'eba masa wani. Bayan ta gama zuba masa yace "what's your name?"
"Naziha Funmilayo" ta amsa masa fiskarta d'auke da murmushi.
"Me ya sa ki ke zaune da uncle d'inki, where are your parents?"
Shiru ta yi tana tunanin rayuwarta a baya, irin cin fiska da ta fiskanta daga wajen matar Yayanta da sharri da aka k'ulla mata.
Ganin ta yi shiru ba ta ce komai ba ya ce " it's ok if you don't want to talk about it"
Hawayen daya gangaro mata ta goge tace " iyayena sun rasu, mommy ta rasu shekara goma da suka wuce, Papa kuma idan wannan shekarar ya kai k'arshe shekara uku kenan"
"Allah ya jikansu" yace mata ta amsa masa da Amin
"Ki bani aron wayarki if you don't mind, zan yi kira da shi"
"Ba komai Uncle barin d'auko wayar" ta juya zata bar wajen ta ji yace "Ziha"
Ta juyo da sauri mutum biyu ne ke kiranta da haka, Papa sai kuma Yayanta AbdulBar.
Ba tare da ya kalleta ba yace "idan kin shiga ciki, change your clothes"
Da sauri ta bar wajen, tana shiga d'aki doguwar rigan ta cire
'Hasbunallahi .....stupid Naziha, foolish Naziha' ta fad'i tana marin goshinta a hankali....
Yanku kenan uncle ya gani, bayan asirina ya tonu a idonshi da wani ido zan kalleshi
Da k'yar ta shiga bayi dan gyara jikinta, dama d'okin karrama bak'onsu Dr Sajid ya sa ta manta cewa ta fara period kuma ta san tana yin heavy flow ne. Gashi yanzu ta staining kayanta kuma ya gani.............
***
....."Ban gane me ka ke fad'i ba Joseph, kanaso kace kun nemi Sajid kun rasa and on top of that he was shot. Are you listening to yourself?"
"Anty B, za mu ganshi duk inda ya shiga, har yanzu muna bincike akai, just relax"
Madam B tayi wurgi da wine glass da ke hannunta ya fad'i k'asa ya tarwatse wanda sau uku tana shanye red wine a ciki.
"Sajid ya riga ya san plans ɗinmu, and he will use that against us, and you tell me to relax"
Joseph da shima abin ya d'aure masa kai na rashin sanin inda Sajid ya shiga ga shi duk wani asibiti da ke area ko kusa da wajen da abin ya faru sun duba amma babu shi.
"Anty B barin kai wayarsa a bud'e mana shi ko zamu samu wani evidence a ciki"
"Now you're talking, just make sure ka dawo da labari mai dad'i"
Joseph ya fita daga falon..
Nickolas da ke mak'e yana jin duk maganar da su ke fad'i yace "tabbas hasashensa gaskiya ne, Uncle Joe da mommy B ba su da gaskiya akan case da ake yi, idan kuwa hakane kenan abinda Dr Sajid ke tuhumarsu da shi zai iya zama gaskiya kenan?. Dole ya nemi Irene su yi magana dan yasan tabbas she knows something about this case"............