14
by @azizat
14
Fitowar Naziha daga bayi ta saka wata bak'ar broomstick skirt da farar T-shirt, ta rolling kanta da bak'in gyale. Zama tayi tana tunanin yadda za a yi ta kaiwa Uncle Sajid waya, kunyarsa take ji sosai.
Tayi kusan minti goma zaune tana tunanin yadda za a yi ta fita, k'wank'wasa k'ofar da aka yi yasa tayi ajiyar zuciya "shikenan Naziha kin sa ya taso da kanshi" tayi saurin isa bakin k'ofar amma sai ta tsinci kanta da kasa bud'e k'ofar. Toh yanzu idan ta bud'e da wani ido zata kalleshi? shine abinda take maimaitawa aranta. Sake k'wank'wasa k'ofar aka yi wannan karan ya had'a da kiran sunanta "Naziha" jin dad'in kiran sunanta da yayi batasan lokacin da ta bud'e k'ofar ɗakin ba, suna had'a ido ta yi saurin sunkuyar da kai tareda mik'a masa wayar. Bai karɓi wayar ba sai ma barin wajen da yayi.
Jikinta yai sanyi, cike da fargaba ta bi bayanshi.
Zama yayi a d'aya daga cikin kujerun falon sannan ya kalleta tana tsaye d'an gefe da shi idonta a k'asa hannunta rik'e da wayarta ƙirar Tecno Y2.
" Ziha I have a daughter"
Yai shiru ya ɗan kalleta sannan ya ci gaba "sunanta Azra, she's 5yrs old, amma nan da wasu shekaru zata zama budurwa kamarki, kullum ina cikin shiri, idan Allah ya kaimu lokacin, ina so na zama mutum mafi kusa da ita, ina so na zama best friend ɗinta, ina so ya zamto cewa zata iya gaya mini duk wani matsala nata ba tare da ta ji kunyata ba.
" ina so ya kasance nine mutum na farko da zata dinga tunkara idan tana cikin matsala ba tareda wani shamaki ba"
ya yi shiru na wasu seconds sannan yace mata ta zauna. Kujeran da ke saitin nashi ta zauna amma ba ta iya d'agowa ta kalleshi ba.
" Inaso ki d'aukeni a matsayin Uba, kin rasa mahaifinki, but ni Sajid na miki alk'awarin zan kula da ke irin kulawar da zan ba wa Azra, daga yau tamkar Azra kike a wajena, so kin ga batun kunya ki cireshi tsakaninmu"
( oops! Dr Sajid kar kayi saurin yanke hukunci.......father daughter relationship .....hmmmm kamar da wuya Lol)
Ajiyar zuciya tayi, anya kuwa zata iya? ta tambayi kanta.
"How old are you?" Ya katseta
"19yrs oh saura wata biyu na cika 20yrs"
Murmushi yayi ya ce " kinga dana yi auren wuri first born d'ina zai kai ki a shekare"
"Yanzu first born ɗinka shekaranshi nawa?" Ta tambayeshi
" Ya aka yi kika san first born d'ina namiji ne?"
' oh Allah Naziha kin kwafsa, yanzu zai gane you're crushing on him tun ma ba ki ta'ba ganinsa ba' ta d'an shafa goshinta tace " kawai nayi hasashene"
"11yrs oh saura wata hud'u ya cika 12yrs" ya kwaikwaya magananta.
Batasan sadda ta fara dariya ba, shima d'in ya murmusa. Ganin ta d'an sake jikinta da shi yace ta bashi wayar. Tad'an risina ta mik'a masa wayar da hannu biyu ya k'ar'ba.
Kallon wayar ya ke yi yana jujjuyata cikin zuciyarsa yana k'ara godewa Allah, ya sani yanzu cikin 'yan uwanshi na kusa kai na d'an nesama ba mai iya rik'e wannan waya saboda Allah ya bud'a musu.
"Zo ki koya min wayarkin nan, tafi k'arfina" dariya ta yi tace "haba uncle kai dai kafi k'arfinta"
Ta zauna gefensa ta k'ar'ba wayan ta shiga dialer ya karanto mata wasu numbobi ta saka, ta mik'a masa wayar yasa a kunne, Saida ta kusa katsewa aka d'auka.
Zaytunah ya kira, daga yadda ta ji yana tambayar yara yasa tasan matarsa ya kira. Tashi tayi taje wajen dining dan ta gyara.
As usual Zaytunah da ƙorafi ta fara tarbanshi. Ce mata yayi wayarsa ya 'bata a asibiti d'ayar Kuma ba chargy shiyasa ta ji shi shiru, da k'yar ya lallasheta da cewa zai kirata da d'aya wayarsa idan ta yi chargy ya kashe wayar, yasan halin Zaytunah idan ya fad'a mata gaskiyar abin da ya faru to ba hankalinta kad'ai zai tashiba duk wanda ya sanshi sai ya ji zancen, shi yasa bai gaya mata ba. Bayan ya gama waya da Zaytunah sai ya kira numbar Barrister Idris ya sanar da shi abin da ya faru, suna cikin magana kud'in wayar ya k'are, sai shi barrister d'in ya kira shi suka ci gaba da magana, bayan sun shirya komai ya kashe wayar.
"Ziha" ya kira sunanta tana zaune a dining table tana sauraron gulmansa a ranta, da sauri ta taso taje ta sameshi. Ya nuna mata gefensa alamar ta zauna, ba musu ta zauna.
"Ziha I need your help, na san taimakon da kika mini jiya bazan iya biyan ki ba, but I still need your help"
"Uncle koma mene ne zan maka"
" Nan da minti talatin ina so ki je wani address ki k'ar'ba min kayana akwai taxi da zai zo ya kaiki ya dawo da ke"
Shiru tayi tana tunani, ba wai bazata iya zuwa bane amma tana tunanin idan Daddy ya ji labari ba zai ji dad'i ba, amma kuma Dr Sajid nefa, idan ta taimakeshi ai ba komai bane. "Shikenan Uncle zan je"
"Nagode" ya fad'i tareda mik'a mata wayarta yace "da alama kin wayeni tun kafin mu had'u"
Zaro ido tayi tana tunanin ya aka yi ya sani. Kodai Timothy ne ya fad'a masa?
" Ba dai tsakanin jiya da yau kika samu hotunana dayawa hakaba?"
'Innalillahi Naziha shikenan asirinki ya tonu, he has seen the pics' tace aranta
Ta rufe idonta saboda kunya
"Tell me ya aka yi kika samu hotona?"
Shiru tayi ta kasa d'ago kai, kamar ta nutse cikin kujeran take ji
"Bana hana ki jin kunyata ba"
still bata ce komai ba
"Shikenan tunda baza ki yi magana ba, may be kema kina cikin wanda sukeson ganin bayana ne, ko kuma ma kina aiki da Madam Bridget" yai kamar zai tashi yana fad'in "kafin a k'arasani barin tafi"
Da sauri ta sauko k'asa tana hawaye " wallahi Uncle a Facebook na gani ranar birthday ɗinka shine na saving, please believe me, bazan ta'ba cutar da kai ba"
Murmushi yayi wadda fararen hak'oransa suka bayyana, ganin ta kid'ime yace " its ok, I'm just joking, Ziha"
"Kina so kisan labarina ne?" Ya tambayeta bayan ta koma ta zauna, ta girgiza masa kai.
"Zan baki labarina amma sai kin bani naki"
Shiru tayi na kusan minti biyu sannan ta fara bayani
Sunana Naziha Funmilayo AbdulSamad
AbdulSamad AbdulLateef Adeyemi shine sunan mahaifina, d'an k'aramar hukumar Offa ne dake Ilorin state, amma acikin Ilorin ya taso gidan wan Babanshi saboda mahaifanshi sun Jima da rasuwa, mahaifiyarsa wajen haihuwa ta rasu, 'yan biyunsa ma baifi kwana uku ba ya koma, k'anwar mahaifiyarsa ita ta reneshi har ya kai shekara uku kafin Babanshi ya k'arbeshi lokacin da ya sake aure. AbdulSamad yana da shekara bakwai mahaifinsu ya rasu, daganan Alhaji AbdulWasi'u yayan Babansa ya d'auke shi shi da k'anwarsa Kudirat da matar Babanshi ta haifa, lokacin tana 5yrs.
Alhaji AbdulWasi'u shi ya zame musu tamkar Uba dan yana sonsu sosai, musamman AbdulSamad saboda lokacin ba shi da d'a namiji yaransa biyar duka mata ne, daga bayane ya haifi maza biyu Lukman da AbdulFatah.
Mahaifina yayi karatu a Federal Polytechnic Offa, daga baya ya koma BUK yayi degree da masters, daya gama kuma ya samu lecturing a can. Zamanshi ya dawo Kano gaba d'aya, ya auri Sikirat itama 'yar Offa ce suka haifi 'yan biyu AbdulBasid da AbdulBar, bayan shekara uku ta haifi AbdulWahab. AbdulWahab na da shekara biyar Sikirat ta rasu. Ya zamto Daga shi sai yara, kasancewar AbdulWahab shi ne k'arami sai ya kai shi wajen k'anwarsa Kudirat dake aure a Jos.
Victoria Anike Martins shine sunan mommy nah.
Asalinsu 'yan cikin Ogun state ne, ita ce k'arama a gidansu, Peter Adeniyi shine babba, sai David Adebayo (Daddy kenan) sai Samuel Ayobami sai autarsu Victoria.
Pastor Emmanuel Ajayi Martins shine mahaifinsu yana da tsauri wajen rik'on addini, shi yasa suka tashi da irin ra'ayinsa.
Victoria tun tasowarta cikin kulawa ta taso kasancewa ita kad'ai ce mace a gidan, amma Babansu na sa mata ido sosai akan lamuranta saboda yana gudun ace 'yarsa ta yi abin kunya. Hakanne yasa Victoria ta ji tanason ta yi nisa da gida ko dan ta d'an samu ta sake, da ta gama secondary school ta cika Jamb d'inta BUK, da Babanta ya gani dukane kawai bai mata ba saboda haushi, ya tsani Hausawa. Da k'yar dai ya hak'ura ta tafi BUK d'in bayan ta samu admission.
Zaman Victoria a Kano ya wayar mata da kai musamman akan addini da al'adu. Tana da wata friend Aisha 'yar department ɗinsu kuma Allah yasa Aisha tana da rik'on addini sosai, gashi gidansu gidan malamai ne. Ta dalilin Aisha Victoria taji sha'awar musulunci, lokacin suna final year ta kar'bi musulunci a hannun mahaifin Aisha.
Victoria ta canja suna daga Victoria Anike Martins zuwa Fatima Anike Martins. Duk abin da ake yi babu wanda ya sani a gida, har suka gama makaranta.
Ranar convocation ɗinsu dukkan 'yan gidansu suka zo, basu zargi shigan da tayi ba saboda dama tun asali tana saka kaya da suke rufe mata jiki, saida sukaji ana kiranta Fatima tukunna hankalinsu ya tashi amma suka danne sai da suka dawo gida Ogun kenan ta fad'a musu ta musulunta, ai kuwa ta ga tashin hankali, gaba d'aya iyayenta da 'yan uwanta suka gujeta, ta sha duka kaman baza ta yi rai ba, k'arshe dai ganin ta kawo musu abin kunya gidan Pastor sai Babanta ya koreta daga gidansa.
Babu wanda ya damu da korar da aka mata sai yayanta David, ya ji tausayinta ya bata kud'i ya ce ta koma Kano ta zauna kafin su huce. Ta koma Kano tana zaune gidansu Aisha.
Shiru shiru abu kamar wasa har wata uku amma babu wanda ya nemeta, gashi ana shirye shiryen bikin Aisha. Haka dai aka k'are biki Aisha ta tare gidanta.
Malam Adamu mahaifin Aisha ganin bata jin dad'in zaman gidan saboda babu Aisha ya mata maganar ko zata auri wani abokinshi bayarabe lecturer a BUK matarsa ta rasu. Yace mata ya amince da shi dan yana da rik'on addini sosai. Bata musa ba dan ta ɗauki Malam Adamu tamkar mahaifinta ne.
Malam Adamu shi ya had'a AbdulSamad da Fatima Anike kuma cikin lokaci kad'an suka fahimci juna. Har Ogun suka je da AbdulSamad akan su bawa iyayenta hak'uri amma sam suka k'i ta. David ne kawai ya nuna bai damu wai ta chanja addini ba shi har yanzu 'yar uwarsa ce.
'yanbiyu Fatima ta fara haifa duka mata, Aisha ce ta za'ba mana sunan Nazifa da Naziha. Sai dai Nazifa ta rasu tun bamu cika shekara uku ba. Koda mommy ta haihu David ne kawai ya zo Kano lokacin shima yana aiki a Lagos, babban yayansu Peter yana k'asar waje shi da iyalinshi, Samuel ne kad'ai a Ogun da Babansu.
Haka rayuwa ta cigaba tsakanin mommy da 'yanwanta ba wani shiri Yayanta David ne kawai yake kula ta, mommy ta sake haifan 'yan biyu maza anma duka basu zo da rai ba dan tun kafin haihuwar bata da lafiya, tana fama da hawan jini tun daga lokacin bata sake haihuwaba.
Sau biyu tana kaini Ogun amma babu wanda ya damu da ita balle ni. Idan ta je Lagos wajen Daddy kad'ai nake jin dad'i.
Na taso cikin gata Papa da mommy suna sona sosai balle yayuna da suke ji dani. Na shak'u da Papa sosai fiyema da mommy. Ina shekara goma Pastor Emmanuel mahaifin mommy nah kenan ya fara rashin lafiya sosai an kwantar dashi a asibiti, David ya gaya mata, ta yi shiri ta je Ogun duba jikin mahaifinta amma ananma babu wanda ya kulata hatta Babanta cewa yayi bayason ganinta a wajenshi. Cike da bak'in ciki ta juyo. A hanyanta na dawowa motarsu tayi hatsari mommy nah ta rasu.
Naziha ta goge hawayen fiskarta ta ci gaba muryarta na rawa
labarin mutuwar mommy nah shi ya sawa Pastor Emmanuel heart attack ya mutu a take lokacin da Samuel ya gaya mishi bayan David ya sanar da shi mutuwan. Asali dama pastor Emmanuel kawai k'arfin hali ya ke yi saboda tsoron maganar mutane cewa 'yarsa ta musulunta a matsayinsa na pastor na church amma yanason mommy nah sosai.
Mutuwar mommy ya girgizani ya girgiza Papa sosai. With time komai ya lafa amma Papa bai sake aureba har shima ya rasu.
Papa shi yake kula dani har na zama 'yanmata shi yake min duk abinda uwa za ta yiwa 'yarta. He loves me dearly.
Zan shiga SS 2 Papa ya chanja min makaranta zuwa boarding school, nayi kuka sosai a lokacin, nace bazan je ba, da k'yar ya lallasheni na tafi. Abin da ban sani ba ashe Papa bashi da lafiya ne, yanaso na koyi zama babu shi shi yasa ya min transfer zuwa boarding school.
Yana zuwa duk lokacin visiting ya duba ni, tun ban saba ba har nazo na saba.
Yayana AbdulBar yana karatu a Madina shi kuma AbdulBasid a BUK yayi karatunsa, lokacin yana service a Jos ya had'u da Zainab. Papa baiso yai aure a lokacin ba amma Ya AbdulBasid ya nace yana son aurenta. Ina hutun k'arshe da zan shiga SS3 akayi bikinsu.
SS3 last term Papa ya rasu lokacin muna rubuta jarrabawar
WAEC, babu wanda ya sanar dani, Haka na gama makaranta cike da fishin Papa saboda bai zo ya dubani ba kuma bai zo ya d'aukeni ba kamar yadda ya saba idan munyi hutu.
Danaje gida ban ga Papa ba, na dai tarar Hajiya Kudirat da Ya AbdulBar shima ya zo Nigeria da AbdulWahab duk suna gida. Sai danayi kwana uku ban ga Papa ba idan na tambaya sai su ce min yayi tafiya, a ranan na hud'u Hajiya Kudirat da sauran yayuna suka zaunar da ni suka gayamin mummunan labarin da har yau ina jinta ajikina, cewa Papana ya rasu. Farko na k'aryata abin lokacin dana tabbatar da gaskiyar fah sumewa nayi, nafi sati biyu a asibiti da k'yar Ya AbdulBar da yake shi Ustaz ne ya dinga taimakamin da nasihohi da kuma addu'o'i har na samu kaina. Lokacin da Mommy ta rasu bangama mallakar hankalina ba, amma Papa.........kuka ya k'wace mata.
Shi kanshi Sajid yaji tausayinta sosai, ya d'an matso kusa da ita yana bata hak'uri sai da ta kusan 10minutes kafin ta dena kuka tana goge hawayenta tareda ajiyar zuciya.
Wayarta da ya fara ringing ya katsesu, Sajid ne ya d'auka bayan ya gama amsa wayar yace " minene address ɗin gidanku?" Ta gaya mishi
Sai kuma yace "ki texting address d'in wa wannan numbar" ya mik'a mata wayar.
Tunda ta tura text d'in ta kasa k'arasa labarinta shima d'in bai ce ta ƙarisa labarin ba saboda yasan a halin yanzu ko ya ce ta ƙarisa ba lallai ta iya cigaba ba.
Ganin shirun yayi yawa tsakaninsu sai ya miƙe ya je ya kunna TV dake falon...
.....KADUNA
Yana zaune bakin system ɗinsa yana rubuta report kan Alhaji Kadi amma kuma hankalinsa ya kasu gida biyu d'aya yana kan aikin, d'aya kuma tunanin Layla ne fal azuciyarsa tabbas har yanzu abinda ya wakana tsakaninsu bai bar jikinsa ba, ko dan ya jima baya tareda mace ne yasa yau d'aya tsuminshi ya tashi. Da k'yar ya samu ya kammala abin da ya keyi ya kwanta amma bacci yak'i zuwa masa.
Tunda matarsa ta rasu yau ne kad'ai ya ji buƙatar tsananin son kasancewa da mace a wannan dare, gashi hakan ba zai yiwu ba. Da ya rufe idonsa hoton Layla ke masa gizau, ganin fa abu yak'i k'arewa ya sa shi tashi yai alwala ya fara jero nafilfilu sai kusan k'arfe biyu na dare ya samu yai bacci.
......Washe gari
Layla tunda ta tashi maganganun Charlotte suke mata yawo a k'wak'walwarta, anya idan zuciyarta ya fad'a soyayyar AY iyayenta zasu amince? Ta san Mom bata da matsala amma Daddy kam ko kad'an baya son talaka, toh ma shi AY d'in yana sonta ne?.
Da wannan tunani ta yanke shawaran sanin asalin AY kafin ta gama yanke hukunci, a iya tunaninta koda AY talakane toh yayi karatu saboda maturity da intelligence nashi yafi k'arfin ace baiyi karatun boko ba.
A Islamiyya tama malaminsu bayanin abinda ya faru shekarun baya, ya kuwa shaida mata sai tayi azumi sittin na kaffara.
Gaskiya tanada raki wajen Azumi amma ya zamar mata dole kuma tayi alkawarin daga tayi tsarki zata fara yin azumin.
Tsakaninta da AY yanzu wani bond ne mai k'arfi ya shiga tsakaninsu ita kanta tayi mamakin yadda AY d'in ya chanja mata, idan zai kaita wani waje tad'i suke yi tsakaninsu, tana bashi labarin k'asar waje inda tayi karatu da k'asashen da ta ke zuwa shak'atawa, shima yakan bata labarin wasu abubuwa na al'ajabi. Abu d'aya ta lura dashi idan ta masa tambaya akan aikin da yayi a baya kafin ya zama driver sai ya kau da zancen k'arshe dai ta dena tambaya, sannan ta lura yakan yawaita yi mata wasu tambayoyi gameda Alhaji Kadi wanda ta rasa dalilin hakan. Lokaci zuwa lokaci suna waya da Aaliyah tanason yarinyar sosai.
Layla ta fara azumi lafiya, Mom kawai ta fad'a ma ko AY bata sanar da shi ba, sai da ta yi guda ishirin tukunna fah ido ya raina fata gashi ana yanayi na d'an karen zafi. Yanzu kam idan ta fita office 8am to 11am ta dawo gida. Sai alokacin AY ya gane saboda duk ta wani rame, daya tambayeta me yake damunta sai ta gaya mishi ta fara azumin kaffara ne. Ya tausaya mata musamman yadda yaga tana wahala.
Zaune take a office ɗinta tana bincike akan laptop, wani saurayi ya shigo office d'in, tana ganinshi tayi murmushi " Munnir fatan ka gama min aikina ko?"
Munnir ya ajiye mata wani file yace "Hajiya Layla ai komai ya kammala amma gaskiya zaki d'an k'ara min kud'i saboda gaskiya nasha wahala sosai kafin na samu information d'innan"
Layla ta janyo file d'in gabanta tayi murmushi tace " wannan ba matsala bace zan adding 30% akai indai duk abinda nake buk'ata ka samo min su"
Munnir yai dariya yace "komai yana ciki Hajiya, sai naji alert" ya fice daga office d'in.
Ta bud'e file d'in hoton AY ne a farkon page d'in amma bai kai yanzu girma ba yana sanye da bak'in suits na Versace da bak'in eyeshade, ta fara shafawa tana murmushi cikin zuciyarta wani shaukin sonsa na fizgarta. Ta dad'e tana kallon pic d'in kafin ta rufe file d'in tace sai ta je gida ta sha ruwa tukun ta karanta.
A d'aki tasha ruwa, tana idda sallar Isha ta d'auko file d'in ta bud'e ta fara karanta labarin Alyasa'a Ahmad, tun daga shekarar da aka haifeshi zuwa karatunshi zuwa lokacin da yayi aure yana 20yrs, har lokacin da ya ajiye aikinsa na CID saboda kashe masa iyalansa da aka yi, wanda daga lokacin ya dena aikin gomnati ko wani irine.
Kuka Layla ke yi lokacin data gama karanta labarin, abu biyu suka sakata kuka, na farko tausayin AY irin yadda ya rasa iyalinsa lokaci guda. Na biyu, idan AY tsohon d'an bincike ne toh fah da alama yazo gidansu bincike ne, saboda mutum kamar AY ba zai k'ask'antar da kansa da aikin driver ba dan albashin da za a bashi yafi k'arfin haka, tunaninta kan Daddy ya tsaya tabbas AY akan Daddynta yake bincike. To idan hakane ya zatayi da soyayyarshi.
"Ina sonka AY, koda Kai ba agent bane kai normal driver ne I still love you, Dan Allah kasoni" ta sake fashewa da kuka.
Washe gari ....
Ta riga ta gama tsara komai aranta amma dole ta k'are azumin da take yi kafin ta aiwatar da abin da ta ke shirin yi
Yawon shak'atawa tacewa Daddy zata je, amma mom tasan ba haka bane akwai abinda take 'boyewa ta dai yi shiru dan tasan halin 'yartata.
Cikin kwana biyu aka shirya komai na tafiyarta, text kawai ta yiwa AY ta sanar da shi zataje k'asar waje ta k'arasa azuminta acan saboda Nigeria akwai zafi azumin yana bata wahala. Mom ce ta rakata airport sai Russia ko cikin jirgi hawaye kawai take yi tana tunanin wani hali zata shiga idan ta dawo ta sanar da AY burinta kuma yak'i amincewa da hakan?
"I love you Alyasa'a, I really love you" shine abinda ta fad'a lokacin da jirginsu ya tashi.......