EYOON ƘALBI

EYOON ƘALBI page 4

by @hajjace22522

*EYOON ƘALBI ...*



Page *4*


Kusan kullum haka Hanan takeyi sai taje ƙofar gidan su Hajja ta dinga leƙensu, tana so ta shiga tana kuma jin tsoron karsu koreta. Yauma kamar kullum yadda ta saba tana zuwa ta kafe kekenta a wajan ƙofar gidan sannan ta shiga cikin zauran, leƙensu ta farayi can ta hango Hajja na wankin kayanta gefe kuma ƴar wayar techno ɗin tace takejin waƙoƙi a ciki da alamar kuma ko wuyar wankin bataji yadda take yinshi cike da nishaɗi.


"Ke mekike nema anan?"


Yaya Mubarak ya faɗa yana kallon Hannan cikin tsamanin mamaki, jikinta ne yahau wani irin rawa kawai sai ta sakar masa kuka. Mamaki ya kuma cika Mubarak kafin yayi magana sai ga Furera da gudu ranta a matuƙar ɓace. Ganin Hanan ɗin tana kuka yasa ta ƙarasa gurunta ta riƙo hannunta cikin zaro idanuwa take kallon Mubarak kafin ta tambayi Hanan.


"Meyayi miki Hanan?"


Kai ta dinga kaɗawa hawaye na ambaliya a saman kyakkyawar fuskarta, janta Furera tayi suka fita tana ta faman masifa.


"Ke dai yarinyar nan wallahi yanzu kin koyi shegen son yawon jaraba, ga mahaifinki da iya masifar tsiya sai kace shi kaɗai ne ya taɓa haihuwa a duniyar nan, yanzu daga ya laluba yaga be ganki ba sai ya sauke min yatsunsa a saman fuskata, aikin banza kawai mutum sai dukan mata jaraba."


Tun a bakin gate Hanan ta sanƙamewa Furera, nan da nan hankalin Fureran yai mugun tashi ta fara kurma ihu. Su lionman da su Bam-boy su Wizi dake tsaye a parking lot suka fito da sauri Amman banda lion ɗan ya ɗauka ko yaran unguwa ne. 


Yana saman motarsa yana yana danna laptop yaji Wizi yana kwa&a mai kira amma yayi masa banza tamkar beji kiran ba. Sai da yaji alamar shigowarsu sannan ya ɗaga kai yana kallonsu a yatsine, ganin Hanan rungume a hannun Bam-boy yasa shi saurin dirowa daga kan motar cikin tashin hankali yake furta.


"Hajja ce nan....!" Ciki suka shiga da ita Mamah da kakah suka karɓeta, hankalinsu duk a tashe, wannan abu yana basu mamaki matuƙa, me yasa Hajja take son ganin bayan Hanan ne? Kuma ma yarinya ƙarama da ita? Koda yake kamawarta ta karshe da tayi Mamah ta kamawa kurwa, wato dai so take sai taci wani a cikin gidan kenan? lallai tana da ɗanyan aiki.


Ko sallama beyi ba ya kutsa kai cikin gidan, yana zuwa ya tarar da Mubarak yana goge takalminsa ita kuma Umma tana wanke kayan miya yayin da Hajja ke tsaye tana shanyar kayanta jikin igiya sai bin wakar da akeyi a cikin wayarta takeyi. Zanin atamfa ne a jikinta da riga t.shat yaluwa me kajeran hannu kanta kuma ɗaure da ɗankwalin zanin, kawai ji tayi an juyo da ita gaba ɗaya an shaƙe mata wuyanta.


A ruɗe su Umma suka kalli gurin kasan cewar basu san ya shigo gidan ba, cikin sauri Mubarak ya miƙe shima yayi kan Aliyu Hydar yana ƙoƙarin kwatar Hajja daga shaƙar da akai mata dan sai wani irin kakarin mutuwa takeyi. Kin sakinta Lionman yayi burinsa kawai yaga bata numfashi a hannunsa. Umma sai bashi hakuri takeyi amma yaki sakin wuyanta, ganin haka yasa Umma rugawa da gudu cikin kitchen idanunta suka sauka akan muciya, cikin sauri ta ɗakko ta tana zuwa taga har Hajja tayi ƙasa amma still hannun lionman yana jikin wuyanta. Cikin ruɗani Umma ta sauke mai muciyar nan a ƙeyarsa. Besan lokacin da ya saki wuyan Hajja ya dafe gurin ba yana neman faɗuwa ƙasa sai ga Wizi ya taroshi dan kamar yasan za'ayi tashin hankali shi yasa ya biyo bayansa.


Kafin kace mene tuni an cika gidan sabida wasu sunga shigowar lionman da wizi sun san dole akwai abinda yake faruwa. Umma ta jah ƙafar Hajja dake yashe a ƙasa cikin ruwa suka shiga ɗaki da sauri ta rufe tana yayafa mata ruwa dan ta farfaɗo. 


Lion kuwa yadda yaji kansa yana wani irin juyawa shine silar da yasa shi riƙo Wizi da sauri. Jansa ya farayi Lionman yana riƙoshi yana lumshe ido murya a sarƙe sabida jirin da yake neman kayar dashi yake tambayar.


"Hanan ta... dawo...dai-dai kuwa?"


Ya tambaya a wahalar ce idanuwansa na shirin lumshewa, ko kafin Wizi ya bashi amsa tuni lionman ya rufe idanunsa. Cikin sauri yasa aka temaka masa suka fita da lionman zuwa gidan su. Suna zuwa a mota aka sakashi Wizi da kakah suka wuce dashi zuwa asibiti yayin da aka bar Mamah da su Bam-boy a gurin Hanan wadda aka samu da ƙarfin addu'a ta ɗan dawo hankalinta sai dai ta shige cikin Mamah tamkar wacce zata koma ciki a sake haifota.


Hajja kuwa da kyar su Umma da Mubarak suka samu ta dawo da numfashinta, a razane ta miƙe zaune tana kallonsu, kuka na sarƙe mata, ta ɗauka tashin alƙiyama akeyi lokacin da taji hayaniyar Mubarka da yake ma lionman magana, ashe zuwa yayi ya kasheta, yau kuma me tayi musu ita da ko ƙofar gida bata zuwa bare suce ta kama wani a gidan?.


"Umma yau kuma me nayiwa mutanan can? Anya ba rayuwata suke nema ba Umma? Wallahi Umma da bawan Allah nan yana matuƙar birgeni saboda nutsuwarshi da miskilancinsa, amma yanzu a duniyar nan babu wanda na tsana irin ƴan area ɗin su, sun takura min wallahi shin mena tsare musu a duniyar nan da suke min haka.?!" Cike da masifa jin kalamanta take faɗin. 


"Kaji wawuya, har meye abun burgewa a gurin waɗannan mutanen? yara ƴan iska, daga me dukan mace sai mai hana matarsa abinci sai marasa kwanan gidan iyayensu, da masu shaye-shaye har meye abin burgewa a gurinsu? Karna sake jin ma kin wani ce suna burgeki sakarya kawai shashasha, musamman ma shi lionman ɗin nan duk shi yake haɗa musu dabar unguwar nan har da wani ɗan iskan tattoo a jikinsa sai kace tsohon arne. Mubarak kira Abban ku a waya gara yazo dan nasan yanzu zakuji ƴan sanda a cikin gidan nan, nasan yaran nan so yake kawai ya tozartamu a cikin garin nan kuma babu inda zamuje tunda su dama basu fiye caka shekara a garin ba, ni bansan ma me yasa wannan karan suka daɗe basu tafi ba."


"Wallahi Umma rabu dasu kawai, babu wani Abba da zamu kirawo, yau Hajja ai bata fita bare ace tayi wani abun, shine ma ya kamata mu kaishi ƙara sabida ya shigo muhallinmu without any excuse."


"Rayuwata dai tana cikin danjah tunda har an fara zuwa cikin gidan mu ana neman kasheni da rai na. Ni kam na shiga uku ni Hajja ya zanyi?."


Kallonta sukayi cikin tausayawa, Mubarak ji yakeyi tamkar shi aka dorawa sharrin maitar nan, wai shin meye gaskiyar al'amarin nan tunda gashi Hajja bata leƙa waje ba amma ya aka yi lionman ya biyo ta har cikin gidan nan zai kasheta? Koda yake babu wanda yasan Hanan ta leƙa gidan shine kawai ya sani, yasan dole Fureran zata iya bada tambacin cewar a gidan nan ta ganta amma bata san cewar Hanan ɗin bata shiga cikin gidan ba, shin ta Yayya za'a warware wannan cakwakiyar?.


Mubarak ya dinga tunani amma babu mafita, Hajja na kwance dan yanzu tsoron fita tsakar gidan nasu ma takeyi sabida kartaje taji wuƙa a bayanta. Suna zaune suna tattaunawa Mubarak yana bada shawarar kawai tayi jamb taci gaba da karatu dan ta rage zaman gidan a dena ganinta ana mata ƙage. Hajja dai tayi shiru idanunta babu abinda suke hangowa sai haduwarta da Lionman yadda zata kasance....




*HAJJA CE* 👈