SABO DA KAZA

Chapter 4

by @surayyaibrahim

5&6.

*Free page*


Sakina ta zuba masa ido tana hasashen 'kanin nata, tana son tuno yaushe rabon da ta gan shi a gidanta, ta kasa tuna when last da ya zo mata. Kaso mafi yawa ta fi zaton so na yake yi, sai dai rashin alkiblarsa ya sa ba za ta yi saurin gaskatawa ba. Amma a ranta addu'a ta shiga yi, Allah ya sa hakan ta kasance domin ta riga da ta fahimci ina son shi, da zarar ya furta da gudu zan amince, duk kuwa da rashin mutuncinsa.

Ya katse tunanin Sakina da cewa, "Yanzu saboda Allah ruwa sai na ro'ka?"

Na tashi ina cewa, "Bari a kawo maka Yaya Sadik!"

Na dawo dauke da robar ruwa ta sona mai sanyi na ajiye masa ha'di da tumbler.

A lalace ya kalle ni ya ce, "Ke kam ina tausayin mijinki wallahi wanda zai kwashe ki abin a yi masa jaje ne, kin wani taho sankamkam tamkar ra'kuma".

Ba'kin cikin kalmar rakumar da ya jingina mini yasa na zauna a sanyaye, hawaye kuma ya kwace mini, abin mamaki sai ya jikinsa ya yi laushi, ina kallon yadda Sakina ta tsananta kallon mu musamman Yaya Sadik.

Tsawon lokaci ina shar'be Sakina ta 'ki yin magana, ya ja tsaki ya ce, "Ki dubi Allah Sakina! Me na yi mata da za ta dinga yin irin wannan kukan?"

Ta nisa ta ce, "Ta yi maka abin arziki, kai kuma ka zage ta?"

"Sakina ban son 'karya! Gidan uwar wa na zage ta?"

Kai tsaye ta ce, "Gidan uwarka".

Ya yi kanta tamkar zai dake ta, ko gezau ba ta yi ba. Ya tsaya yana nuna mata yatsa cikin fishi ya ce, "Kar ki yi zaton don na zo gidanki shi ne za ki zage ni, ki kwashe 'kalau".

Uffan ba ta ce masa ba, ta ci gaba da yi wa 'yarta kitso da take ta barci.

Share shi da ta yi, yasa ya koma ya zauna.

Cikin kara'di ya ce, "Guduyo kin sani ban son irin wannan iskancin, ta ya ya ke da kike yar lukuta da ya kamata ki nisanci za'ki, kin 'dauko lemo kina sha, ni kuma sai ki ba ni tsurar ruwa. Ban da rowa mene ne hakan? Na yi magana kin saka mini kuka, har wannan tana neman 'kulla munafuncin na zage ki, me na ce da yake nufin na zage ki?"

A tunzure Sakina ta ce na fuskanci a tsiyace ka zo , sai dai kar ka shiga ru'du ba gidanku na je ba, bare ka tisa ni a gaba da cin mutunci, nan gidana ne don haka ka iya harshenka".

Ya mi'ke yana cewa, "Idan ni 'dan halak ne a cikin Habu da Saude, ba za ki kuma gani na a gidanki ba, da'din abin namu gidan ba kango ko kufai ba ne".

Ya kalle ni ya ce, "Zo mu wuce na rage miki hanya".

Na galla masa harara na ce "Ina ce ba kai ka kawo ni ba?"

Ya wuce yana cewa, "Me za a yi da shiga lamarin mata, daga wacce za ta yi maka sharri, sai wacce idan ka fa'di ainihin yadda take za ta ce ka ci fuskarta, yo mene ne don na ce miki ra'kuma? Alhalin dangantakar danjuma da 'danjummai ne a tsakaninki da ita."

Muka bi shi da ido domin lamarin nasa tamkar a buge yake musamman yadda idaonsa suke tamkar mai jin barci ko wanda ya tashi a barcin.

Sakina ta kalle ni ta ce, "Iyashegensa kullum 'kara tsananta yake yi, amma ba komai ba za mu gaza da yi masa addu'a ba har Ubangiji ya amsa mana".

Na yi shiru ina jin tausayin Sakina saboda yadda take cikin bacin rai, a dalilin ba 'karamin so take yi wa 'dan uwan nata ba, amma shi ko ka'dan ba ya mata ragayya har gara ita ma a hakan a kan manyan yayun nasu.

Bai zame masa abin kaico ya ci mutunci duk wacce ta nemi yi masa fa'da irin na gyara kayanka ba. Yana isa gida kai tsaye shashinsu ya nufa, ya samu Abba a falonsa. Ya shiga ya zauna, ya gaishe da mahaifin nasa ba sukuni a tare da shi.

Ya amsa cikin kulawa.

Ya numfasa ya ce, "Abba so nake na ji me ake ciki a kan tafiyar tawa".

Abba ya ce, "Ba za ka je waje ba, idan karatun kake so ka nema a nan k'asar."

Ransa ya kai 'kololuwar baci ya ce, "Abba wai ni kam ba ni da hakki a dukiyarka ne?"

Abba ya harzuka ya ce, "Ilimin da na yi bai yi zurfin da zan gane kana da hakkin ko ba ka da shi ba, sai dai ka fahimtar da ni yanzu. Daga haihuwarka zuwa yau adadin dukiyata nawa ka lashe mini? Amma ban tsira daga ba'kin cikinka ba, shin ba ni da hakkin ka mini biyayya ne?"

Sosai ya sake daure fuska ya ce, "Tsakanina da Allah Abba na fahimci ba ka ta tawa, a kullum adawa kake da duk wani 'kudirin da zan zo gabanka da shi da zummar ka lamince mini."

"Akan me zan yi ta taka Sadik? Har yau din nan fa ban huta da yi maka hidima ba, amma ba ka gane irin kyautatawar da nake yi maka ba, yau kwana nawa ina cewa ka je ka rage wannan sumar da ka tara?

Dubi wani irin gemun rashin mutunci da ka ajiye! Tamkar wani 'dan akuya".


"Abba Sunnahl ne fa!"

Ya fa'da cike da iyashege.

Ya masa da'kuwa ya ce, "Ungo naka! Wannan kam gemun raini ne ba na Sunna ba, ba za ka ji da'dina ba har sai ka yarda da ra'ayina ko da ba a ra'ayin ka ba ne, in ko ka ci gaba da yin fito na fito da ni, ni kuwa ba zan fasa nuna maka cewar ka zo duniyar nan ka same ni ne a cikin shekarun girmana, ma'ana ko da ban same ka ba, ba abin da zai shafi ni'imomin da Ubangiji ya yi mini. Uwarka ta cusa maka ra'ayin iska wai Gudale, to ina tabbatar maka a wajenta kake Gudale domin ba a kanka na samu haihuwar namiji ba, tuni da ma Ubangiji ya ba ni su da yawa, Ga su Abdallah, ga Ashir ban ta'ba kallon ka fisu ba, don haka ka ri'ke wannan".

Takaici ya kama Umma da take gefe tana kallon su, haka ma Sadik din, don haka ya mike yana cewa, "A wannan era din dai babu na biyunka. Madalla da kai Abba! Mai fifita 'ya'yan dangi akan biological son d'insa, na hakura da karatun, digiri biyun da na yi ka daure ka saka mini albarka, sannan ka mini alfarmar samo mini aikin yi, domin a yau na fahimci ya kamata na fara tsayawa on my leg, domin dukiyarka ba tawa ba ce, bal ma 'ya'yan 'yan uwanka sun fi ni dama a cikinta".

Tsoro ya kama Abba! Yana kallon Sadik yana nazartar sa, anya kuwa a she'dantarsa bai fara afa 'kwaya ba? Ya sani ba 'karamin tsoron sa yake ji ba, amma a watannin nan wani zubin yana iya zama a gabansa ya fa'di duk maganar da ta zo bakinsa babu fargaba, da za a jima kuma ko washegari sai ya ga wannan shakkar sa da yake yi ta dawo, tabbas ba zai yaudari kansa ba, tilon 'dan nasa yana shan wani abu da idan yana cikin wannan yanayin zai iya keta kowa.

"Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un!" Abba yake ta fadi yayin da Sadik ya fice da sauri.

A fili Abba ya nisa ya ce, "Allah ka kawo mini 'dauki, Allah ka shirya mini Sadik, ka sani ban ta'ba jin rashin da'di akan 'ya'ya matan da ka ba ni ba, ban taba zakuwar sai ka ba ni namiji ba, Allah ina tawasili da adalcin da na yi wa 'ya'yana mata ka shirya mini wannan yaron da kullum yake sake kangarewa".

Umma ta yi wuki-wuki da ido domin ta ji a jikinta tamkar da ita mijin nata yake.

Ta nisa ta ce, "Abban yara tsakani da Allah ya kamata ka ba shi damar tafiya karatun nan, irin haka yara suke shiga wani hali, kana da damar kai shi ko'ina a duniya, amma ka 'ki. Saboda Allah ka kai wasu ma bare shi, ai kamata ya yi mu gode masa da ya yarda ya yi karatun yake kuma son ya ci gaba".

Takaicin ta mai tsananin gaske ya kama shi, ya nuna ta da yatsa ya ce, "Ina gargadin ki ki kiyayye ni, ki bar ni na ji da ba'kin cikin sangarta yaron nan da kika yi, an 'ki gode masan, da bai yarda ya yi karatun ba, wa ya yiwa asara?

Kansa ya yiwa wallahi, domin ko ke uwarsa da arzikina kika same ni, kuma Ubangijina ya suturta ni ta yadda ba zan jira wani ya taimake ni ba. Ke dai da zuciyarki ta zarme akan sai 'da ya zo ya tallafa miki sai ki yi ta yi, da ikon Allah ni kam sai dai yaro ya mini abu don neman ya yi albarka, amma ba don ya tallafe ni ba".

Sanin da ta yi ba ya kashedi sau biyu yasa ta mike sum-sum ta bar falon.


Washegari da safe na fito daga shashen Umma inda nan nake kwana bisa umarnin Abba, domin tunda aka yi auren Sakina na gudu, a dalilin rashin samun fuska a wurin Umma, sai idan Abba yana gari.

Amma a yanzu da girma ya cim ma masa bai cika ma yawace-yawace ba, sai Yaya Abdallah ne ya fi yin harkokin Abban shi yasa ma ba ya aikin gwamnati amma Babban lauya ne mai zaman kansa.

A hanyar da ta raba shashin Umma da na Mama muka yi kicibus da Yaya Sadik, na yi kamar ban gan shi ba, na wuce shi, ina ganin yadda ya tsaya ya bi ni da kallo, ba tare da ya ce mini uffan ba, na dai san ya 'kulu da dauke kan da na yi masa.

A tunzure ya isa gurin Umma, tana kicin tana saka wa masu aikinta ido kan abincin da suke yi. Ganin da ta yi masa a tunzure yasa ta fice ta ri'ke hannunsa, sai da suka shiga 'dakinta ta zaunar da shi a bakin gado sannan ta dafa kafadarsa ta sassauta murya ta ce, "Mene ne kuma na bacin rai yanzu da sassafe nan?"

A zafafe ya ce, "Wula'kanta ni da waccan 'katuwar yarinyar take yi a gidan nan ne yake mini ciwo".

Gaban Umma ya buga, ta 'kare masa kallo ta ce, "Gudale mene ne abin damuwa akan Halimatu? Na fara jin tsoro fa". Sai ta fashe da kuka sosai!

Ya ce, "Saboda Allah Umma kin so ki sake bata mini rai ne, mene ne abin kukan kuma?"

Da hawaye face-face ta ce, "Ina jin tsoron kada Safiyya ta kwace mini kai, tamkar yadda 'ya'yanta suka kwace mini Abbanku, ina jin tsoron yawan damuwa da ka yi da lamarin yarinyar nan, mene ne da har za ka dinga 'bacin rai saboda ita? Anya Gudale ba son ta kake yi ba?"

Ya mike da sauri zuciyarsa tana tsananin bugawa, bakinsa na rawa ya ce, "Wanne irin ba'kin hasashe ne wannan? Ni kike ganin zan so wannan yarinyar, to na yi yaya da ita? A yanzu haka ta fi ni girma, ta fi ni tudu to nan gaba kuma ai ban san me za ta zama ba, wallahi kin b'ata mini rai Umma! Shike nan sai ba zan yi zumunci da ita ba, ai tunda jini ya ha'da mu dole zan ji zafi idan ta gan ni ta bagarar".

Cikin kara'di ta ce, "Ban son wannan damuwar da ka yi da ita, tunda har take bagarar da kai, mene ne kai ba za ka yi watsi da dukkan lamarinta ba?"

Ya nisa ya ce, "Haka ne zan yi yadda kika ce".

Ta goge fuskarta ta ce, "Na dade da gane duk kinibibin uwarta ta kwashe su tsaf, duk namijin da tsautsayi yasa ya kwashe ta ya shige su! Domin an yi ittifakin zuri'arsu ba sa barin namiji salin alin, ga tabbaci ma ina gani ba iya mijinta ta gama da shi ba, hatta kurwar Abbanku tana karkashin ikonta. Shi ne kuma ake son sai an ha'da da kai ka'dai da Ubangiji ya ba ni! Wallahi da hakan ta faru gara a ce ina kushewa".

Ya ce, "Yanzu Umma a yadda nake din nan har ki yi tunanin zan so Guduyo?

Ban da farar fata mene ne da ita ne, ai ni sam ba na son 'yan lukutayen mata, ba sa burge ni. Kawai dai ina son na samu damar da zan rika ganin surarta, domin tana matu'kar kidima ni".

Ihu Umma ta fasa tana cewa "Shike nan ta faru ta 'kare, ashe da gaske kana shaye-shaye Gudale? Ni ka furtawa wannan 'kazamar kalmar?".

Ya mike ba tare da ya ji wata fargabar komai ba ya ce, "Ni irin wannan abin naki ne yake ha'da ni da ke, to idan ban fa'da miki damuwata ba, wa zan fa'dawa ya fahimce ni? Ba na son ta, ban ta'ba raya zan so ta ba, amma idan ba zan rufe ki ba, da gaske ina son ganin ta, ai abin ki yi murna ne, Gudalenki ya zama man".

Salati kawai Umma take yi tana 'karawa tana cewa, "Haka za ka yi mini?"

Ya fice ya bar ta cikin bacin rai iri-iri. Shi kuma bai ga laifinsa ba, to idan mutum bai fa'dawa uwarsa damuwarsa ba wa zai fa'dawa a duniyarsa? Washagari da hantsi ya sake tarar da iyayen nasa. Kusa da Abba ya zauna a nutse tamkar gaske ya ce, "Abba fa'da mini don Allah kana da shekaru nawa ka auri Umma?".

A matu'kar sanyaye Abban ya ce, "Ina da shekaru ashirin da biyar Mahaifina ya ce ya gaji da zamana haka, shi ne kuma ya za'ba mini ita, a dalilin ya saba da mahaifinta wajen saye da sayarwar dabbobi".

Kai-tsaye Sadik ya ce, "Shekaruna ashirin da shida next month Abba!".

Ido sosai dukkansu suka zuba masa, sun kasa gane me yake damun tilon 'dansu, ba a buge yake ba, amma kuma sun tabbatar ba a cikin hayyacinsa yake ba.

Da mamaki Abba ya ce, "Aure kake so ke nan?"

"Ya ka'da kafadarsa ya ce "No! Ina dai son na gane irin adalcin da tsohonka ya yi maka, mahaifinka yana da hangen nesa, ina yi maka ta'aziyyar rashinsa Allah ya jikan sa."

"Amin summa amin."

Abba ya tsinci kansa da furtawa cikin ru'du.

Tsawon lokaci yana kallon Sadik sannan ya nisa ya ce, "Ka fara koyon sana'a, idan na gamsu ka mayar da hankalinka akan sana'ar sai a je ma nemo maka auren a inda ka ga yarinyar".

A sanyaye Umma ta ce, "Abdallah da Babangida kai ka samo musu mata fa Abban Yara".

Da sauri ya ce, "Su ma sai da na ba su damar su kawo zabinsu, sai da na ga ba su da niyyar kawowar ya sa na zabo musu da kaina, suka karba kuma babu musu. Har yau din nan ba wanda ya kunyata ni."

"Shi ma ai ba zai kunyata ka ba". Ta fa'da a tunzure.

"Allah Ya sa! Amma dai ya kawo wacce yake so da kansa, domin shi da su ba 'daya ba ne".

Daga Umma har shi duk sun san magana ya fa'da musu shi yasa suka yi tsit.

Sadik ya mi'ke yana cewa, "Ni dai ka samo mini aiki, ka riga ka san ni ba zan iya sana'a ba, tunda Allah ya sa na yi karatun".

Ya sake cewa, "Ka samo mini matar, ba zan ba'da maka 'kasa a ido ba, amma dai Abba plz! Bari ka ji ra'ayina, ba gajeriya kamar Umma ba, sannan ba mai jiki ba. Yar shawalwala, doguwa, fara, mai dogon gashi, wacce ta kammala karatunta na jami'a. Bayan haka ta kasance yar attajiri ce, ba na son a kwaso mini 'yar talakawa su zo su cika mini gida tamkar yadda dangin Umma suke yi, idan za su zo. Babu lissafi sai su 'dungumo da yawansu tamkar gidadawa".

Cikin wani irin yanayi Abba ya mi'ke. Sanin da Sadik ya yi duka za a kawo masa yasa shi kwasa a guje, ya fice.





# Team Gudale

# Team Guduyo

# Surayya Dee✍️

# Ana tare 🤝.