EYOON ƘALBI

EYOON ƘALBI page 7

by @hajjace22522

*EYOON ƘALBI*



Page *7*


Zaune suke suna breakfast lionman ne kawai babu a gurin hakan yasa Raudah matarsa da suka rabu wato mahaifiyar Hanan ta miƙe tsaye, sanye take cikin shiga ta alfarma kasancewarta ma'abociyar san gayu da kuma san ƙamshi. Kai tsaye side ɗinsa ta nufa tana zuwa ko bugawa batayi ba ta murɗa ƙofar ta shiga. Baya cikin parlour hakan yasa ta wuce bedroom ɗinsa, kwance ta ganshi daga shi sai singlet da boxer ya baje tamkar wani me jin jiki, abunda ta tsana shi tagani a duka fatar hannuwanshi wato tattoo ɗin jikinsa, idan tana ƙalla sai ta dinga ganinsa tamkar wani ƙaton arne kuma wai shi ɗin musulmi ne ɗan gidan musulmi da yake amsa sunan Aliyu Hydar. Taja tsaki tare da ƙarasawa wajan gadon tasa hannunta tana tashinsa cikin bubbuga masa kafaɗarsa. Wani irin juyi ya yi yana sakin wata irin miƙa. Ƙamshin jikinta kawai yaji yasan cewar Raudah ce a cikin ɗakin, yasa hannunsa tamkar wani me magagin bacci ya riƙota tare da janyota zuwa cikin jikinsa ta faɗa kan gadon ya riƙeta sosai idanunsa a lumshe tamkar me baccin gaske yake faɗin.


"Please baby karki gujeni allow me..." Da ƙarfin tuwo Raudah ta kwace jikinta ta sauka daga kan gadon tana huci take cewa.


"Aliyu wai meye hakan ne? Kasan nice fa amma dan iskanci zaka wani rungumeni, toh zuwa nayi na tasheka dan nasan daƙyar idan kayi sallah yau, ina zuwa tashinka ne badan komai ba sai dan banson ƴata ta taso ace kaine mahaifinta, wallahi nasan sai tayi kuka sosai dan bazata taɓa yin alfahari dakai ba a matsayin ubanta, nasan sai ta yi min kuka cewar na zaɓar mata uba irin ka, please wake up...!" Ta faɗa tana narka masa harara. 


Kuma gyara kwanciyarsa yayi sannan ya buɗe idanunsa yana kallonta yayi murmushi irin na I don’t care ɗin nan yana cewa.


"Ohh Rau...Rau, (Raudah) ya kike min shouting da sassafiyar nan ah? Kinzo kina wani cewa kinyi nadamar haɗa zuriya dani and so what? Ko da muka haɗa ɗin ma waye yace? Sannan Baby Hanan nace ko bake na fara aura ba dole ni zan amayar da ita a kuma haifa min ita tazo cikin duniyar nan da kike taƙamar kina ciki, dan haka babu ruwanki da yadda mahaifin Hanan yake rayuwa, tunda dai ke kin gudu daga cikin jikina karki sake gaya min nonsense ɗin magana, idan kuma ba haka ba zaki gane kuranki am telling you, and now get out ko kuma yanzun nan nasa ki sake haifar wani ɗan a cikin cikin ki..."


Kallonsa take cikin tsananin mamakin kalamansa, tabbas tana son lionman sosai amma ɗabi'arsace kwata-kwata bata yi mata ba, saboda shi ɗin namiji ne da kowace mace zata yi alfaharin ya zamo mijinta kuma mahaɗi na rayuwata. Sai dai amma sam bashi da hali mai kyau, gabaki ɗaya ya mai da kanshi tamkar wani bature dan kuwa komai irin nasu yake yi. Harararsa tayi tana daga tsaye ya kuma kallonta tare da zabura kamar zai kamota Raudah ta juya da gudu ta fice daga cikin ɗakinsa dan tasan zai iya aikata abinda ya faɗa mata ba damuwarsa bace na cewar babu aure tsakaninsu yanzu. Ta koma parlourn tana sauke wani irin numfashin wahala.


"Raudah lafiyarki?" Cewar kakah yana ƙoƙarin fita yaga ta shigo da gudu, baki ta turo tare da cewa,


"Kakah Hydar ne wallahi ya wani taso min daga zuwa nace ya tashi yayi sallah shine zai wani taso kamar zai dakeni."


"Bari naje amma ina tunanin yayi sallar ai dan da zan fita asuba na tashesa kuma sai da na tabbatar ya shiga toilet sannan na fito." Komawa tayi ciki ta zauna kusa da Latifa tana mamakin lionman tare da yi masa addu'ar shiriya, gashi itama ta kasa yin wani auran sabida soyayyar da take masa har yanzu tana maƙale a ranta ta kasa cire shi bare ta samu damar amsawa ɗaya daga cikin masu san auranta


******

Hajja kuwa koda wasa bata zuwa unguwarsu lion ɗin tunda suka dawo, dan ko ita da Atika sai dai a waya ko koma ita Atikan taje gidansu amma sam bata yin hanyar wajen. Yau kam tana dawowa daga gurin aiki wanka tayi sannan ta kwanta ta ɗan huta. Ana yin sallar la'asar tayi light makeup sannan ta sanya riga da skirt na atamfa tare da hijjab ɗinta ta fito tana kallon Ummanta.


"Umma yau dai zanje gano kayan lefen Atika na huta da ciwon bakin da take ta yi min." Umma ta kalli Hajjan cikin mamaki tace. 


"Hajja kina nufin yanzu zakije wannan unguwar? Gaskiya a'a Hajja ki bari sai zuwa dare idan yaso sai kije babu wanda ya ganki bare wani abun ya faru kijanyo mana tashin hankali muna zaman-zaman mu lafiya." Hajja tace cikin sanyin jiki. 


"Umma idan banje yanzu ba toh babu halin zuwa kuma, gashi tace min zata ɗauki wasu za'a kai ɗinki zan taya ta zaɓe, kuma daddare Umma akwai aikin da zanyi idan na dawo wanda zan tafi dashi wajan aiki gobe, yanzu zan tafi sai na saka niqab ɗina Umma please dan Allah ki barni." Kuma kaɗa kai Umma tayi sannan tace. 


"A'ah Hajja yanzu ne dai-dai lokacin fitowar dabar ƴan iskan yaran nan marasa mutunci, ki bari kawai zuwa daran Hajja zai fi miki kwanciyar hankali da kuma mu kan mu, bana san tashin hankali Hajja bana so." Da yanayin damuwa take cewa. 


"Shikenan Umma amma daddare bazan samu zuwa ba gaskiya, kawai na gaya mata a waya tayi hakuri dama cewa tayi idan naje saina zaɓar mata wanda zata yi amfani dashi. Ni kenan bani da ikon zuwa wancan tsallaken bayan kuma ba abin yi ne bani dashi acan ɗin ba." Umma najinta tayi mata shiru. Shigowar Mubarak yasa shi cewa. 


"Umma ki barta mana taje tunda zata saka niqab, kai Allah ka yaye mana wannan masifar, ace da ranka da lafiyarka amma a hanaka sakatawa cikin gari bayan kuma anan kake rayuwarka." Umma tana dariya take faɗin. 


"Mubarak kenan, ai idan kana da arziƙi a duniyar nan toh duk wani laifin da zaka yi babu wanda zai gani, amma talaka yana yin ba dai-dai ba cikin sani ko rashin sani sai kaji ana cewa ya saba, Allah ya shiga tsakanin nagari da mugu kawai." Duk suka amsa da. 


"Amin" sannan Hajja ta naɗa niqab ɗinta a fuska ta ɗauki jakarta tare da sake fushe jikinta da turare tasa takallimi tana faɗin.


"Umma na tafi"


Umma da Yaya Mubarak suka yi mata fatan dawowa lafiya sannan ta fita cikin kwanciyar hankali. Har taje zata tsallaka titi kawai ta hangi dandazon rufar su lionman sun fito, sai da ƙirjinta ya wani irin buga, ji tayi kamar ta koma gida sai kawai ta daure ta tsallaka tana kallon kowa ta cikin niqab ɗin, sai dai ita basa ganinta haka taje ta wuce su zuciyarta kamar zata ciro dan tsoro.


"Tiger wai ya akai naga mata suna ta wuce mu kamar wasu kwari ne? Wai bana ce ku hanasu zuwa hanyar nan bane ba?"


Hajja taji lionman ya faɗa cikin ɓacin rai, tana ganinsa zaune kamar yadda yake yi a baya kafin ta gifta su, sanye yake da 3quarter da farar vest yayin da power ɗinsa ta mimmiƙe wacce tasha zanan tattoo ƙatoto. Wanda aka ƙira da Tiger yana zuƙar sigari yana tada ƙaramin gajimare a wajan ya kalli bayan Hajja data wuce yana cewa.


"Ahhh lion wannan young lady ɗin ina jin dai baƙuwa ce dan ban saba ganinta ba da wannan munafukin abun a fuska ba, but let me check naga ko wacece ita.."


Tana gab da shiga cikin gidan su Atika kawai taga an tare mata gabanta, cikin sauri taja da baya zuciyarta na wani irin bugawa, Tiger man yana busa mata hayaƙin sigari a fuskarta, tayi saurin kawar da kai ya yiwa Hajjan wani banzan kallo tare da kai hannu zai yaye mata niqab ɗin fuskarta yaji tana faɗin.


"Auzubillahi minashhaitanur rajim, bismillahir rahmanur rahim karka taɓa ni dan Allah ni musulma ce."


"Kanbala'in can...! Lallai ma yarinyar nan kinzo da rainin hankali ni kuma me kika mayar dani? Samuel ko Ezikwe?" Ya faɗa yana yi mata wani irin kallo. 


Bata yi magana ba ta gotashi zata wuce kawai taji ya shaƙo mata hijabi ta bayanta, nan da nan ƴan majalisar su lion duk suka hangosu sai dariya suke yi, Tiger yasa hannu zai cire mata niqab ɗin yaji an riƙe masa ya ɗago yana huci zai yi bala'i sai yaga lionman ne yana kaɗa masa kai tare da cewa.


"Barta ta shiga but..” Ya nunata da yatsa ba tare da ya kalleta ba dan yaga niqab yana ganin shima be cancanci kallonta a hakan ba yace.


"Last waning.... karki sake biyowa ta hanyar nan da muke idan kuma ba haka ba zaki yi nadama kin gane ko?"


Hajja ta ɗaga kai ba tare da ta san tayi ba sannan ya juya shima Tiger yabi bayansa suka tafi ita kuma ta shiga cikin gidan su Atika hannunta dafe a ƙirjinta. Da kyar tayi sallama bakinta sai makerketa yake yi, Atika ce kawai a tsakar gidan tana yanka albasa a kan chopping board, ganin Hajja yasa ta ajiye da sauri tana me amsa mata sallamarta fuskarta ɗauke da murmushi kai daka gani kasan taji daɗin ganin ƙawarta ta. Lokaci ɗaya kuma ganin yanayin Hajjar ya sanya Atika tasowa da sauri ta isa gareta cike da damuwa ta riƙe kafaɗar Hajjan tana yi mata magana. 


“Ƙawata ya haka kuma? gayamin me akai miki kinganki kuwa? sanardani damuwarki please..” Atika ta ƙarasa maganar cike da kiɗimiwa don yanayin kawartata ya gigitata ainun. 


“Uhmmm ba... Bakomi.” Cewar Hajja cikin rawar murya.


“Bakowa a gidan nan fa ƙawata, ni kaɗai ce dan Allah ki gaya min menene? Okay toh taho muje cikin ɗakin idan a tsakar gidan ne bakya son faɗa ni wallahi duk kinsa zuciyata sai wasi-wasi take yi.” Cewar Atika tana magana tana jan hannun Hajjan har suka ƙarasa ɗakin Atikar.


“Faɗa min abunda ya faru dan Allah karkiyi min shiru please..”


“L.. lionman ne fa shi da tawagarsa..”


“Sukai miki me?!” Cewar Atika tana ware idanuwa.


“Bakomi kawai dai wani acikin sune ya biyoni yake neman ciremin hijabi na,shine lionman ɗin ya dakatar dashi tare da bani last warning akan kada na ƙara bin hanyar da suke zaune..” Mteew... Atika taja tsaki tare da hura hanci tana me gyara zaman da tai akan stool ɗin madubi kafin tace,


“Shine zakizo kina wani ɗari-ɗari baki zabga masa mari ba ko ki gaya masa baƙar magana? aida kin sani kin kirana naga uban abunda zeyi don ko a dokar ƙasa (constitution) sai anci tarar sa wallahi. Tukunna ma sai kace layin na ubansu ne su kaɗai, wannan jaraba da me tai kama ni Atika, kuma arasa me magana a cikin unguwar nan da yake ƴaƴan masu farcen susa ne ƴaƴan fata kawai.”


Ta kara she zancen tana mai zabga uban tagumi cike da takaicin abubuwan dasu lionman suke yiwa mutanan unguwar duk lokacin da sukazo. Ganin haka ya sanya Hajja tuntsirewa da dariya tare da zare niqabin fuskarta wanda duk ta haɗa uban gumi, abinka da ba sabunba sai shararowa gumin yake yi. Binta da kallo Atika tai na tausayawa ganin haka kawai ansa ƙawarta cikin rayuwar wani hali, murmushi Hajja ta kakaro tana duban Atika tace. 


“Calm down ƙawata ni wallahi ya riga ya wuce a gurina Allah karki damu kanki, kuma ma alhakin Ummah na ne dan sai da tace nabari sai dare na kafe sai nazo Yaya Mkay ya taya ni shawo kanta sannan na taho, ai gashinan dama ance wanda beji bari ba yaji hohoho.” Ta ƙarasa tana ƴar dariya ƙasa-ƙasa.


“Allah ke madai haba gaki very educated person amma kina wani tsoron mutum kamar kasheki za’ai, Allah ni abun nan yana kona min rai harda wani saka niqabi duk dan karsu ganki. Toh Allah ya saka miki wallahi..” Cewar Atika cikin ɓacin rai. 


“To Ameen dai ƙawata dan kuwa an sani a tasko. Yanzu dai ina kayan lefan namu nagani na san inda dare yai min ina da aiki a gida..”


“Allah bazaki tafi yanzu ba mutuniyar ki ma nake shirin soya miki kika ganni atsakar gidah..”


“Ah kai..kai..kai! godia nake tawaje na, kamar kinsan tun jiya nake craving wainar flour, nagode sosai..”


“Ba godiya a tsakaninmu, ga kayan can wajen kusurwar locker kije ki gani bari ni kuma na soyo mana na dawo..” Cewar Atika sannan takoma tsakar gidah ta ƙarasa yanka albasarta ta wanke da gishiri sannan ta haɗa kayan wainar tafara soyawa.


A hankali Hajja ta goge hawayen daya silalo mata domin tun ɗazu take tare shi duk dan kada Atika ta gani, sannan ta miƙe ta isa wajen locker ta janyo akwatunan masu kyau dasu kalar sararin samaniya da ƴan kwalliyoyin furanni ajikinsu baƙaƙe, saiti huɗu ne da kit.. Cikin nutsuwa Hajja ta fara buɗe kayayyayakin tana dubawa murmushi kwance a fuskarta. Sai da taga komai na ciki sannan ta marmayar dasu, lokacin Atika ta shigo da plate ɗin wainar da aka soya ta da manja, agefe kuma yankakkun albasa ne da tumatir sai yaji a roba mai daɗi dashi.


“Wai har kingama gani ƙawata?!” Cewar Atika tana ajiye plate ɗin. 


“Nagama mana wallahi komai yayi Allah ya sanya alkhairi ya kaimu lokacin, yaushe akasa date ɗin?”


“Toh Ameen Allah ya kaimu naki kema tawan, Allah yasa ma yazo lokaci ɗaya mu haɗeshi, shegiya ni tsiyata dake korar samarin kike shi yasa har yanzu babu tsayayye.” Ƴar dariya Hajja tayi kafin tace,


“Wai kora sai kace wasu tumaki, kinfiya sharri kedai. Abin ne kawai dai duk bana aure a cikin su tunda kikaga hakan kuma Allah da kansu suke ɗauke wuta duk wanda yaji labarin abinda yake faruwa dani sai ya dena zuwa, but I know mr right yana nan tafe ke dai kawai Allah ya kaimu lokacin..” Atika ta zabga mata harara tana faɗin. 


“Allah ba sharri ba tawan korarsu kike yi, toh ko tsoron don kina degree suke ne ohon masu, amma ba wani abinda yake faruwa dake, Anyways Allah dai ya kaimu hmm da saura fa, nan da watanni bakwai masu zuwa..”


“Ah wallahi ba wani nan mutum nawa ne sukai fiye da nawa karatun kuma suka auru? ba haka bane kawai lokaci ne baizoba kin sani, amma fa sa ranar nan tayi don kinsan nan da watanni 6 zan kammala kinga kuwa komai acan-acan kenan abu namu..” Hajja ta faɗa cikin murna. 


“Eh haka ne to Allah ya sanya alkhairi ta wajena. Muci kafin tai sanyi..”


Suna ƴan hirarrakinsu suna cin wainar har suka kammala sannan Hajja ta taya Atika zabar kayan da zata kai ɗinki. Sai bayan magrib ainun tana shirya-shiryen tafiya Ya Mkay ya kirata awaya akan cewar ta fito yana ƙofar gidah su tafi. Leda me ɗan girma nylon Atika tabawa Hajja irin kayan lefan nan da ake bawa babbar ƙawa, dakyar Hajjan ta karɓa sannan ta haye babur ɗin Ya Mkay suka tafi gidah. Bata bawa Ummah labarin abunda ya faru ba saboda tasan harda lefinta tunda an hanata taki hannuwa sai da ta nace, ta dai bata ledar tace Atika ce ta bata, Ummah ta buɗe tana dubawa. Turmin atamfa ne samfarin kamfanin daviva royal da Rani lalle guda uku da powder da jambaki sai kajol eye liner. Ummah tayi godiya sosai ita kanta Hajjan bata san abunda Atikan ta bata ba kenan domin kayan sunyi sosai, a nan ta kirata a waya ta sake yi mata godiya harma tabawa Ummah tayi matata ta godiyar itama.





*HAJJA CE* 👈