EYOON ƘALBI page 8
*EYOON ƘALBI...*
Page 8
Haka rayuwa take ta tafiya yayin da Hajja ta fuskanci karatunta ta kawar da duk wani soyayyarta na tsallaken su Atika, babu ruwanta da hanyar komai zai faru kuwa. Shikenan kafin kace mene har su hajja sun fara rubuta jarabawar finals ɗin su, kuma Alhamdulillah tana karatu sosai shi yasa komai yazo mata cikin sauki. Gefe ɗaya kuma bikin Atika ne ya keta ƙaratowa wanda shima sauran wata ɗaya ayi har sun fidda anko nasu na ƙawaye.
Jarabawar safiya tayi a yau, don haka 12:00pm tayi mata a cikin gidah, maimaicin karatun jarabawarsu ta gaba tayi sannan tayi wanka da yake ba sallah takeyi ba ta ɗan ɗauki wayarta tana buga game ɗin temple run, Har sai da akai mata game over sannan ta jefar da ita gefe tana tsakin takaicin cinyetan da akai. Tunowa da alkawarin da taiwa Atika kan zataje yau ya sanya ta hanzarin tashi ta shirya cikin baƙar doguwar riga abaya ta yane kanta da mayafin rigar, batai wani kwalliya ba ta dai shafa ƴar powder da lipstick ta shafa kwalli cikin idanunta da turaruka masu sanyin ƙamshi tabi jikinta dasu(mild).
Ummah taiwa sallama ta bita da addu'ar Allah ya dawo da ita lafiya sannan kuma karta bari yamma tayi mata, kada kuma ta soma bin layin dasu lionman suke ta samu tayi zagaye. Cike da nutsuwa Hajja take tafiya da takun nan nata kamar bata son taka ƙasa, kamar yadda Umma tace tabi ta bayan layi wanda koka ɗan bai da hayaniya. Tundaga nesa idanuwan Muhammad Areef sukai masa tozali da kyakkyawar matashiyar budurwar da lokaci ɗaya ta tafi da duk wani ilahirin ruhinsa da gangar jikinsa. A hankali ya taka birki ɗin motarsa tare da zare farin gilashin dake maƙale a idanunsa yana binta da wani irin mayataccen kallo tun daga samanta har ƙasan takalmanta wanda har sai da yaga ƙurewa ganinsa da ita sannan ya cije lips ɗinsa yana me dukan sitiyarin motar ganin ta kubcewa ganinsa. A wahalce ya furta.
“Holy shiit... damn it..!” A kasalan ce yaja motar zuciyarsa na ayyana masa abubuwa da yawa game da yarinyar da ta wuce yanzu.
Kai tsaye gida ya nufa in da ya tarar da su Lionman sunyi da'ira suna sana'ar ta su kasancewar duk yammacin duniya sun mai da shi kamar wata ibadah. Ko tsayawa beyi ba ya ɗaga musu hannu don ya tsani wannan akidar tasu Lionman. A falo ya tarar dasu Kaka an baje kolin hira ko jin sallama basayi, ga Hanan kuma a gefe tana ta tsalle-tsallen ta. Raudah ce kawai ta lura da shigowarsa, sai dai a wani yanayi da yake nuna tsantsar damuwa ta ganshi. Binsa tayi da ido har ya wuce zuwa ɗakinsa. Miƙewa tayi tabi bayansa da sauri. A zaune ta tarar dashi ya bawa ƙofar baya ya zurfafa cikin tunani.
"Broth Areef..." Ta kira sunan sa tana ƙarasawa ciki.
"Na'am sis, akwai labari ne?" Ya tambaya yana gyara zaman sa.
"Ba komai broth, kawai na ga ka shigo ne ba yadda ka saba ba, it seems kamar akwai abinda ke damunka." Jin haka yasa Areef dawowa kusa da ita, cikin jimami ya shiga sanar da ita cewar.
"Wallahi sis yau nayi gamo da wata cute baby, baki ganta ba sis kamar ita tayi kanta dan tsaruwa. Wow black beauty ce fa."
"Seriously Broth? Amma na maka murna wallahi. How did you go abourt it? Ina nufin kun gama magana dai ko? Kai am very very happy wallahi."
Kallon ta yayi yaga yadda take wani murna, sai yaji ransa ya ƙara ɓaci da har ya bari ta kufcewa ganinsa. Cikin jimami yake cewa.
"Kinsan me sis?"
"A'a sai ka faɗa." Ta faɗa cikin zaƙuwa.
"Ban samu na faɗa mata even a single word ba, ta kauce ma ganina."
"Kai broth amma banji daɗi ba gaskiya."
"Ba komi sis, naji a jikina zan sake ganinta very soon. So karki damu destiny will bring her back to me." Murmishi tayi tana kallon yayan nata.
"Ina matuƙar son confidence ɗinka broth Areef."
"Thank you ƴar ƙanwata." Dariya sukayi gaba ɗayan su.
"Yauwa baki bani labarin yadda kukai da Hydar ba last time. Kinsan nace ki daina ƙoƙarin biye masa don shi ba kai ne dashi ba sosai." Raudah tayi murmushi tana cewa.
"Ai na daina Insha Allahu. Zan jira the right time da za'a samu me koya masa hankali." Ajiyar zuciya tayi sannan ta ɗora da faɗin.
"Duk da ina son shi broth, amma irin wahalar dana sha a gidansa har na haifi Hanan ya kan sa naji bazan iya koma masa ba."
"Gaskia nima bana miki sha'awar komawa, bana tunanin akwai abinda zai chanja shi nan kusa, just pray for the best kinji sis." Ya ƙarashe maganar cikin sigar lallashi. Daga haka kuma sukayi ta hira har aka kira sallah sannan ta koma cikin gidan.
****
A tsakar gida ta tarar da Atika tana daura ɗankwali. Tana ganin Hajja ta ɓata rai tana cewa.
"Allah ƙawata ke ƴar jirgi ce ta karshe. Tun yaushe nake jiranki amma sai yanzu kika ga damar zuwa?"
"Toh am sorry uwar mita, kin bari ai na ƙarasa shigowa ko? Daga shigowa ta kin wani hau sababi." Hajja ta faɗa tana dariya. Umman Atika dake gefe tayi dariya itama tana cewa.
"Ku dai aikinku kenan, in ba'a hadu ba ayi ta kewar juna, da an hadu kuma shikenan sai faɗa."
Dariya sukayi gaba ɗaya sannan Hajja ta sugunawa har ƙasa ta gaida Umma sannan suka fice don zuwa wajen telan da Atikar ta kaiwa ɗinkunan nata. Achan suka ɓata lokaci wajen zaban style ɗin da za'a yi mata a kayan. Ganin zai ɓata musu lokaci ne yasa Hajja shiga Instagram tayi searching pages na manyan teloli suka masa sending ta wayarsa sannan suka tafi. Sai da suka fito daga shagon suka ga wani irin bakin hadari ga magriba ta ƙarato.
"Innalillah Atika haka hadari ya hado bamu sani ba?" Cikin tsoro tayi maganar don a rayuwarta ta tsani dukan ruwa. Da sauri ta shiga neman layin Ya Mkay.
"Ya dai kid sis?" Ya tambaya bayan ya ɗaga wayar.
"Dama so nake ko zaka taimaka kazo gidan su Atika sai mu tafi tare. Naga hadari ya haɗo."
"Ayya sis kiyi hakuri ki tafi kawai, sai ki chanja hanya mafi sauri, dan kin ganni nan yanzu ina Gadon kaya naje wajen antinki. Kuma mu nan babu hadarin ma." Ya ƙarasa maganar ɗauke da murmushi. Ta fuskanci me yake nufi, hakan yasa ta sakin dariya, cikin zolaya itama tace.
"Shikenan Ya Mkay don Allah kace ƙanwaka me sonta tana gaida ita da kyau da kyau." Amsawa yayi bayan yayi dariya sannan ya kashe wayar.
"Kinga ashe baya kusa ma, bari kawai na tafi kafin ruwan nan ya sauko." Tsayawa tayi ta gyara na ɗin veil ɗin kanta saboda iskar da ta fara kaɗawa.
Cikin sauri-sauri suka dinga tafiya tana roƙon Allah yasa har ta kai gida lafiya don hadarin damina cikin ƴan sakanni yake haɗuwa ya kuma bada ruwa. A ƙarshen wani layi suka raba hanya ita da Atika. Tsakanin wajen da gidansu kuwa akwai tafiya sosai, kuma sai tayi zagaye don bata son duk abinda zai haɗa ta da ƴan gidan Alhaji Marwan. Tsoro ne ya ƙara kamata bayan sun rabu da Atika, ta shiga sauri kamar zata tashi sama har tana harɗe ƙafarta.
****
Areef na zaune a cikin ɗakinsa yaji yana son fitowa waje. Miƙewa yayi ya sauya kayan jikinsa zuwa ƙananan kaya masu ɗan nauyi duba da yanayin sanyin garin. Yana son damina sosai a rayuwar sa dan ya kan fito a irin lokacin da iskar hadari ta taso musamman in bata ɗauke da kura. Yanayi ne me matuƙar tasiri a zuciyarsa. Kaɗan-kaɗan yake tafiya iskar na kaɗashi. A hankali kuma iskar ta soma rikiɗewa zuwa iska me karfin gaske.
Gaban Hajja ne ya faɗi ta ƙara sauri tana danasanin yin zagayen nan ta tayo. Ita kam da ta sani tabi ta layin su Lionman tun da dare ne be zama lallai su ganta ba. Dai-dai wajen wani shago da yake a rufe taji ruwa ya tsuge da karfin gaske. Da gudu ta ƙarasa ta shiga rumfar shagon ta maƙale tana faman ɗora hannu akanta. Wayarta ta ciro daga cikin jakarta taga missed calls ɗin Abba da Ya Mkay. Ƙoƙarin kiransu take yi amma gaba ɗaya network ɗin ya ɗauke gashi ruwan da gaske yake yi don har wani kara tsugewa yake yi sosai.
"Wayyo Allah nah yanzu ya zanyi?" Ta faɗa tana sake lafewa cikin rumfar. Ita kaɗai take ta sumbatunta cikin tashin hankali. Walkiya ake yi sosai ga wata irin tsawa me firgitarwa. Hajja ta shiga tashin hankali tana ta trying kiran Abbanta da Ya Mkay amma sam kiran yaki shiga. Hakura tayi ta cire rai ta samu kan wani ɗan ƙaramin dutse ta kankame jikinta saboda sanyi.
"Yawwa ga wata rumfa chan bari na maƙale kafin ruwan nan ya tsaya." A cewar Areef ya nufi rumfar da ɗan gudunsa.
Dal... Hasken wata mota ta dallare cikin rumfar tun kafin ya ƙarasa. Hajja dake tsaye tai saurin rufe idanuwanta da tafukan hannayenta don hasken ya mata yawa har sai da ya kusan kashe mata ƙwayar ido. Dai-dai lokacin Muhammad Areef yai saurin fiddo da idanuwa waje dan in bazai manta ba wannan ce budurwar yarinyar da ta tafi da duk ilahirin nutsuwarsa a ɗazu. A hanzarce ya ƙarasa wajan don baya son wannan karan ma ta ƙara kubcewa damarsa karo na biyu......
*HAJJA CE* 👈