EYOON ƘALBI page 9
*EYOON ƘALBI...*
*Page* 9
Da sauri ya ƙarasa wajanta har yana tuntuɓe, tana tsaye jikinta sai karkarwa yakeyi saboda iskar da ake yi kamar zata ɗauketa a wajan, ya lura da hakan saita bashi tausayi sosai ganin yadda ruwan ya hanata ƙarasawa gidansu gashi dare yayi bugu da ƙari gata ɗiya mace..
“Assalamu Alaiki..” Ya faɗa yana ƙarasawa inda take a tsaye. Husky voice ɗinsa ne ya daki dodon kunnenta, a razane ta juyo don sam batasan mutum ya ƙaraso wajen ba, jiki na sake kyarma ta amsa mishi da.
“Wa'alaikas salam..” Ta faɗa cikin zazzaƙar muryarta. Lumshe idanuwa yai yana ƙare mata kallo duba da yadda take sake takurewa waje ɗaya da alama tsoransa takeji, ya jinjina kai dan tabbas tanada gaskiya saboda duniyarce yanzu ta riga ta gama ɓaci mutane na gari sunyi ƙaranci a cikin ta, yana kallanta yace.
“Ko zansan ya sunan ƙanwartawa? sannan ina taje har ta bari dare yayi mata haka ga ruwa ya sakko har ya sameta a waje?!” Kamar Hajja bazata amsa mishi ba sai kuma ta gaya mishi cewar.
“Sunana Khadija, kaga wallahi gidansu ƙawata naje bamu fargaba ashe har hadari ya haɗu haka..” Jin-jina kai Muhammad Areef yai kafin yace,
“Toh Khadija ni sunana Muhammad Areef kuma anan unguwar nake idan bazaki damu ba ko naje gidah na ɗako motata sai na kaiki gida saboda wannan tana bani ƴar matsal..” Bai ƙarasa ba Hajja tai saurin girgiza masa kai tana cewa.
“A’a nagode zan jira har ya tsagaita ruwan sai na tafi..”
“I mean no harm Khadijatu, kawai gani nai irin wannan ruwan daɗewa yake ana yinsa, toh muje na rakaki gidan naku dan idan kikace har sai ya tsagaita lallai ba yanzu zaki tafi gida ba..” Bata amsa mishi ba tai gaba yana biye da ita agefe bayan ya gangarar da motar daya fito da ita, sai ɗakko zance yake yi yana bata labari ita dai daga uhm sai um’um ruwa sai dukansu yake amma a haka Muhammad Areef ya kai Hajja har gidansu sannan sukai sallama ya tafi zuciyarsa fese kai kace bushara akai masa da gidan aljannah. Da sallama Hajja tashiga cikin gidansu Ummah ta leƙo da sauri tana faɗin.
“Sannu Hajja yi sauri kicire kayan jikin ki dama yanzu nake cewa Abban ku Allah dai yasa dai kitaho ruwan nan be ritsa ki ba.”
“Eh wallahi Umma ai yau kam ruwa yamin dukan tsiya, kinsan muna zaune a shagon Murtala tailor ashe hadari ne yake ta haɗuwa bamu sani ba? Wallahi muna fitowa kuwa ruwan nan ya sakko, Na jima a tsaye a runfar shagon Iliya mai chemist na bayan gidan mu na da, Wallahi sai wani ne ya rakoni har nan shima kuma ruwan ya masa duka.” Hajja ta ƙarasa maganar tana ƙoƙarin cire mayafinta da ya jike jagab da ruwan sama.
“Allah sarki bawan Allah ya temaka miki, Allah yasaka mai da alkhairi, ki cire kayan kisanya wasu ga paracetamol can akan kujera ki ɗauka kisha saboda kar ruwan yasa maki zazzabi..” Hajja tace.
“Tam Ummah na wallahi nagode sosai..”
Hakan kuwa Hajja ta cire kayan ta saka na bacci tashafe jikinta da robb sannan taci abincinta ta haɗiyi paracetamol ɗin bata jima ba kuwa tai bacci a ranar ko karatun dare bata samu tayi ba sai da asubah. Ƙarfe biyu ɗan adai-data ya dire Hajja a ƙofar gidansu da alama daga makaranta take, kuɗinsa ta bashi ta shiga cikin gidan. Ummah ta tarar a tsakar gidah tana duba littafin hisnul-Muslim. Da sallama Hajja ta ƙarasa tana zubewa a tabarmar da Ummah take zaune, da murmushi Umman ta amsa sallamar tana duban Hajjan datai male-male akan tabarma tana maida numfarfashi.
“Sannu Hajja ya jarabawar yau?!”
“Alhamdulillah Umma tayi daɗi wallahi saboda duk abunda na karanta shi ne ya fito, Nifa tsabar daɗi extra sheets uku na karɓa nayi amfani da ita. Saura kuma last paper zamuyi ta next week Insha Allah..”
“Masha Allahu toh itama Allah yasa tai muku daɗin kamar wannan, Allah kuma ya baku sa’a yasa kufito da kyakkyawan sakamako.”
“Ameen Ummah godiya nake..”
“Ki tashi kici abinci gashi can a kitchen mutuminki akai yau..”
“Kai nagode Ummah dama kuwa shi nake sha’awarci..” Tashi tai ta shiga banɗaki tayo wanka sannan ta zubo ɗanwaken da yasha su cucumber da albasa da tumatir sai ƙamshi yake harda yankakken kwai dafaffe. Buɗe freezer tai ta ɗakko robar zoɓo guda ɗaya ta dawo kusa da Ummah ta zauna tana juya ɗanwaken tana cewa.
“Naga zoɓo ya kare ma sauran robobi uku..”
“Eh yau kam anyi cinikinsa da wuri, ɗazu can gidansu Nazeeru roba takwas suka siya su kaɗai bare kuma ƴan makarantar gangare suma ɗazu cika gidan nan sukai ana ta siya..”
“Masha Allah, haka muke so mu ai.” Sunata hira harta gamacin abincin ta wanke ƴan kwanukan da suka ɓaci sannan ta ɗakko wayarta tashiga group ɗin su na novel tana dubawa, wani yaro ne yashigo yana sallama,
“Salamu Alaikum... wai ana neman Khadija a waje..” Zaro idanuwa Hajja tai tana duban yaron kafin tai magana Ummah ta rigata cewa,
“Toh.. jeka tambayo kace wanene?”
“Ummah nifa bansan waye ba anya kuwa ni ake nufi ma?!” Itadai Ummah batai magana ba saima murmushi datai, jim kaɗan yaron ya sake dawowa yana cewa,
“Wai Muhammad Areef ne..”
“Kace gatanan fitowa..” Inji Ummah sai kuma ta maida kallonta wajan Hajja datai zuru-zuru tana mai-maita sunan Muhammad Areef.
“Kin gane waye ne?!”
“Ummah ni gaskiya bansan wani Muhammad Areef ba, hana rantsuwa sai wanda ya rakoni gidan nan sanda ruwa ya tsareni a wajan shagon Iliya, shine dai kamar haka sunan nasa yake na manta dai..”
“To koma dai wanene ki tashi kije babu kyau wulakanci kin sani dai, sannan idan ma yaron daya rakoki ne ai be cancanci haka ba ko? ki tashi kawai ki shirya kije jira babu daɗi..”
“Toh Ummah bari na leƙa..” Cewar Hajja sannan ta tashi ta shiga ɗakinta, Hijab babba har kasan gwiwarta ta saka maroon color me hannu ta faffesa turaruka masu ƙamshi batai kwalliya ba ta dai ɗan shafa maroon ɗin jambaki kaɗan. Ba ƙaramin kyau tayi ba sannan ta fice bayan ta cewa Ummah ta fita. Jingine yake ajikin motar sa ƙirari Element fara ƙal da ita yana ta danna wayar hannunsa, sanye yake cikin yard black color da yasha aikin fari, komai na jikinsa fari yasa agogan dake ɗaure a hannunsa ne kawai baki. Sosai Hajja take kare masa kallo, tabbas shine wanda ya rakota har gida lokacin da ana ruwan sama, ɗago da kansa yayi dai-dai lokacin da ta karasowa wajen. Wani sanyayyan turarukan jikinta ne suka sanya shi lumshe idanuwa wanda ita ɗin ma hakan take awajenta, don oud ɗin jikinsa ba ƙaramin ƙamshi ya yi mata ba. Sake gyara tsaiwarsa yai yana duban kyakkyawar halittar dake ƙarasowa wajensa zuciyarsa na wani irin zillo tamkar zata fito.
“Assalamu alaikha..” Ta faɗa tana ƙoƙarin tsayawa nesa dashi. Amsawa yai yana murmushi ganin yau dai burinsa ya cika na ganinta da yayi.
“Malama khadijatu..” Ɗan murmushi tayi kafin ta ce dashi.
“Na’am barka da rana..” Yace,
“Barkan mu dai.. Nasan zaki mamakin ganina a gidanku ko?” Murmushi kawai tai bata amsa shi ba ganin haka ya sanya shi cigaba da magana,
“To ya mutan gidan naku..?!”
“Lafiya lou ..” Ta faɗa cikin sake sunkuyar da kai.
“Wato Khadija azahirin gaskiya tun ranar da naganki naji kin kwanta min a rai na, tun kafin naganki a rumfar Iliya ɗin nan na fara ganin kine a bayan layin gidan mu kina tafiya, Kuma tun daga wannan memorable moment ɗin ne naji kin kwanta min a cikin zuciyata, dan zan iya kiran hakan da love at first sight. Kuma Ni Gaskiya ba da yaudara na zo wajan ki ba Khadija, dan ni wallahi na kasance ma mai tsoron mata domin na taɓa san wata yarinya so na hakika na aure wallahi ta yaudare ni, shi yasa ni yanzu duk tsoranku nake yi..” Murmushi Hajja tai kafin tace,
“Toh ai ba duka aka taru aka zama ɗaya ba ko?” Areef yace.
“Hakane shi yasa ma nazo da kokon barata ki taimakeni ki agajeni ki bani dama na dama a fagen yakin neman zuciyarki dan mu fafata da duk wani rival ɗina har sai naga na ciri tutar mallakarki tukun, Ina fatan kuma zaki yadda da wannan barar tawa?.” Murmushi Hajja tayi har saida hakoranta farare suka bayyana. Areef ya sake cewa.
“Baki ce komai ba Khadija uhmm?!” Sai da ya maimata har sau biyu sannan Hajja tai magana,
“Toh Allah ya zaɓi abunda yafi alkairi.” Yace,
“Ameen Khadija Insha Allah ma alkairi ne tare dake don nikam nayi mata uwar ‘ƴaƴan a koba haka ba??”
“Uhum....” Cewar Hajja. Ɗan shiru ne ya biyo baya, ita dai sai wasa take da ƙasan hijabinta ganin haka yasan ya gogan naku sake yin magana,
“Ina ta zuba zance ban bari munyi introducing junanmu ba, Toh da farko dai ni sunana Muhammad Areef Muhammad ana kirana da MRM ni ne ɗa na fari awajen iyayena, Allah yayiwa mahaifinmu rasuwa shekaru biyu kenan jirginsu yai crashing zasu tafi zuwa kasa me tsarki..”
“Allah ya jikansa da Rahama..” Hajja ta faɗa cike da jimami.
“Ameen ya Allah, Inada ƙanne biyar mata uku maza biyu. Akwai Raudah, Ra’eesah, Raheenah sao mazan Adeel da kuma Aseem, Mahaifiyarmu ita kadaice awajen mahaifin mu, mu asalinmu ƴan yola ne, asalin fulanin yola. Mahaifiyarmu kuma ƴar garin Kano ce kauyen Rano. Nayi makaranta tun daga kan primary da degree ɗina a yola inda nayi msc ɗina a ƙasar Singapore akan fannin international economic relations, nayi serving a Lagos state daga nan ne na fara aiki a federal inland revenue (FIRS) dake Lagos, amma mahaifiya ta tafi so na a kusa dasu shi yasa nayi transfer na dawo nan FIRS na kano dake unguwar state road saboda mun dawo nan garin gaba ɗaya. A tsallaken unguwar nan muke da family house na cousins ɗin mu. Toh wannan shine takaitaccen labari na Khadijatu kuma wallahi ni neman aurenki ne ya kawo ni gareki dan tun sanda na ɗora idanuwana a kanki satin baya Allah ya dasa min sonki a cikin zuciata, kuma da aure na zo wajenki dan banki ace next week a ɗaura mana aure ba dan ni a shirye nake, kinga shekaruna sunja fa 35years kar naje na tsofe babu mata..” Murmushi me kayatarwa Hajja tayi kafin tace masa.
“Tohm ai baka tsofan ba, dan haka sai ka daure ka kuma zage damtse. Ni sunana Khadija amma ana kirana da Hajja saboda sunan kakata ta wurin babana naci, sannan nice ƙarama awajen iyaye na, dukan mu yaran gidan uku ne kawai, yaya Jazuli da kuma Yaya Mubarak sai ni mu kaɗai ne. Nayi primary ɗina nima da secondary kuma alhamdulillah yanzu ina final exams ɗina na bsc akan mass communication a jami’ar ado bayero (BUK) Insha Allah next week Monday zan kammala finals ɗina, wannan shine takaitaccen tarihi na..” Jinjina kai Muhammad Areef yai yana furta.
“Masha Allah ashe tare da ƴar jarida nake? bugu da ƙari auta nake dating...? lallai dole na ƙara lallaɓaki da taraira yaki don ku ƴan autan nan komai naku special ne..” Murmushi kawai Hajja tayi tana kallon ƙasa.
“Tohm Khadija kar Mama tace kin daɗe inaga muyi sallama kawai sai kin sake ganina na biyu ko na uku zance? kafin nan dai ataimaka abani digits ko?” Karanto masa numbern Hajja tai yai saving a wayarsa kirar Samsung galaxy S8 edge plus. Kuɗi ya zaro ya miƙa mata amma taƙi karɓa, yai-yai da ita taki karɓa haka sukai sallama ta shiga gidah shi kuma yaja motarsa ya tafi. Koda taje gidah zama tai tagayawa Ummah duk abunda ya faru bata ɓoye mata komai ba, sannan Ummah ta yi addu'ar Allah yazabi abinda yafi alkairi. Shima daya koma gidah haka ya bawa Raudah labarin duk yadda sukai da Hajja, ta yaba kwarai dagaske da yadda ya bata labarin yadda Hajja take.
****
Ranar litinin su Hajja suka rubuta jarabawarsu ta ƙarshe a finals ɗinsu. Sanye suke dukkansu ƴan ajin da rigar grad ɗinsu ta jacket kowa da sunansa abayan rigar. Hakama ta Hajja wadda boldly aka rubuta mata *HAJJA CE* a jikinta, duk sunsha hotuna da cima kala-kala suna ta farin ciki abinsu wanda lamarin sai wanda ya gani. A daren ranar ne kuma Muhammad Areef ya kawo mata souvenirs kala-kala wanda zata rarraba, agoguna na bango fal da jakanku na da sunanta ajiki, sai jotter da biro da handkerchief kowanne da sunanta ajiki, tayi masa godiya sosai bayan sun ɗebi na dangi da na ƴan unguwa haka ta tafi dasu makaranta ranar sign out day ɗinsu ta rarrabawa course mates ɗinsu. A week later sukai graduation dinner ɗinsu a Meenah event center. Sosai dinner tayi kyau inda Hajja ta saka floral cave dress maroon color da mayafin rigar, sai clutch bag kalar baby silver da half covered shoe shima na jakar hakama Atika data rakata sosai tayi kyau cikin bakar riga doguwa. Muhammad Areef ne yakai su wajan domin yanzun sunyi shakuwa sosai wanda alqalami da hannu bazasu iya rubuto yanayin ba abunda sai wanda ya gani kawai. Taro ya watse bayan anci an sha an raba kyaututtuka da awards inda Hajja takarbi na wadda tafi kowa ƙoƙari wato ‘Most Brilliant student of the year' murna harda hawaye tayi, su ya Mubarak sai photo suke mata.....
*HAJJA CE*👈