EYOON ƘALBI

EYOON ƘALBI page 11

by @hajjace22522

*EYOON ƘALBI*



*Page* 11


Rungume juna sukayi da Atika suka saki kuka a tare. Babu wanda yake ƙoƙarin rarrashin wani, sai da sukayi mai isar su sannan Atika tayi ta maza ta goge hawayen fuskar ta, sannan ta shiga gogewa Hajjan tana girgiza kanta.


"Ba kuka zamuyi ba bestie, addu'a zamu tashi tsaye muyi saboda Allah ba azzalumin bawan sa bane. Duk mai ƙoƙarin tozartaki insha Allahu sai Allah yayi mana maganinsa."


"Ya zanyi Atika?" Hajja ta furta a raunane. 


"Kin fuskanci abinda ya faru ɗazu kuwa Atika? A gaban Areef fa aka cimun wannan mutuncin, a gaban wanda yake sona yake da burin aure na Atika, wannan wanne irin wulakanci da tozarci ne? shikenan ni a haka zan ƙare rayuwa ta babu farin ciki bare walwala kenan?" Ta ƙarashe maganar cikin sakin kuka.


"Na ga komai Hajja, amma hakan bazai sa mu karaya ba, in sha Allahu zamu samu mafita." A cewar Atika tana ƙoƙarin kwantar mata da hankali. Cigaba da kukan tayi ƙasa-ƙasa kamar wadda aka tsikara ta ɗago da sauri tana cewa.


"Ammm.. Amma... Atika yaushe zan fara jin daɗi kamar ku..?" Ta faɗa a duburburce . Kallonta Atikan tayi a nutse kafin Hajja taci gaba da cewa. 


"Atika nifa na shiga uku na, wayyo Allah na shiga uku har bansan yadda zanyi ba. Kinsan kuwa Muhammad Areef yana da alaƙa da gidan ɗanƙwangila?" Ta faɗa a gaggauce kamar wadda tayi gudun tsere.


"Kamar ya kenan? bangane abinda kike cewa ba, Waya faɗa miki hakan?" Cikin kaɗuwa Atikar tayi mata tambayoyin dan son gasgata abinda takeji.


"Wallahi Atika da gaske nake yi miki, saboda ɗazu a asibiti tare sukazo da wannan yarinyar ƴar gidan Lionman. Kuma naji tanacewa Areef ɗin Uncle."


"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un." 


Atika ta shiga maimaitawa, gabaki ɗaya ta kasa fitowa daka tashin hankalin data shiga. A hankali ta sulale a wajen dafe da kanta tana faɗin.


"Hajja ya zamuyi kenan?" Ta tambaya bayan ta haɗo kalmomin da ta faɗa da kyar. Tabbas tasan ba ƙaramin so ƙawarta ta takema Areef ba, sunyiwa juna alƙawarin zama inuwa ɗaya a cikin so da kuma kaunar juna. Lokuta da dama takan zauna tana tunanin irin saurin shakuwar su. Soyayya suke me tsafta da wayewa. Wani tausayin Hajjan ne ya kamata, ba zata hana ta kuka ba don ta cancanci tayi shi a yanzu. Riƙo hannayenta tayi cikin sanyin murya tace. 


"Duk abin da kika ga ya samu bawa toh mukaddari ne dama chan daga Allah ne, abin da ya faru bazai hana Areef aurenki ba indai da gaske san Allah da annabi yake miki, kuma in dai Allah ya tsara shi ɗin mijinki ne, toh babu wanda ya isa ya chanza wannan kudurar. Ni dai ina son ki cigaba da yin addu'a Allah zai kawo mana mafita." Kanta kawai ta iya ɗagawa alamar gamsuwa da bayanin Atikar. Kira ne ya shigo wayar Atikar, *LOML* (Love of ma life) ne taga yana yawo akan screen ɗin. A gaggauce ta ɗaga wayar tare da ɗaukar excuse ɗin cewa zata kirashi idan sun gama magana da Hajja sannan ta kashe.


"Hajja..." Atika ta kira sunan ta a nutse. Kafin tayi magana kuma Umma ta shigo ita da ƙanwar Atikan.


"Kingansu nan sokwayen anan, ke Atika kin bar baki kinzo kina tayata kuka ko? Toh maza tashi ga angon naki chan da kansa ya biyo sawunki." 


Miƙewa Atika tayi a kunyace ta gyara mayafin kanta sannan tayima Umma sallama bayan ta ƙara kwantarwa Hajja hankali. Gefe Umma ta samu ta zauna ta jawo Hajja jikinta ta shiga rarrashinta da nasiha mai ratsa jiki. Alhamdulillah an samu ta ɗan ji sauki a zuciyar ta. Ƙarar text message ɗin Areef ne ya shigo. Wannan shine karo na biyar da yake turo mata text masu sanyaya zuciya, duk don ya mantar da ita damuwarta. Wajen ƙarfe 10 na dare ya kirata, sun sha hira ko nace yayi mata hirar mai daɗi da taso ta mantar da ita damuwar ta gaba ɗaya. Sai daya tabbatar babu sauran damuwa a ranta sannan suka yi sallama. A daren ranar Hajja bata runtsa ba, addu'a ta ringa yi akan Allah ya kawo mafita a cikin wannan masifar da take ciki.


******

Bayan an kai Atika da kwana biyu ta ziyarci gidanta dan bata samu halarta duk bikin ba saboda gudun abinda zai je ya dawo. Murna sosai Atika tayi, ta cika mata gaban ta da kayan gara dangin su alkaki, nakiya, dubulan da gireba. Sannan Lemon kwakwa da ya sha dabino da wadatacciyar madara ta dire a gabanta.


"Kin ga yadda kika yi wani fresh ƙawata? Ahhh lallai Habib ya iya kiwo." Dariya suka fashe tare da tafawa, Atika sai iyayi ake ana tsokanar Hajja. Habib ne ya shigo ɗauke da leda me tambarin shoprite a jiki. Da sauri Atika ta miƙe ta taro shi haɗe da hugging nasa ta right side.


"I missed U baby, don ma Bestie tazo ne da sai naci tararka." Murmushi yayi ya lakace mata hanci sannan yace. 


"Kin bari na gaisa da ƙawarta mu kafin ki yi mitar ko baby?" Murmushi tayi sannan ta wuce zuwa kan dining don ajiye kayan. Gaisawa sukayi da Hajja ya ɗan tsokane ta a matsayin sa na mutum me barkwanci sannan ya shige cikin bedroom ɗinsa. Take away ne na jollop rice da pepper chicken sai kuma salad haɗe da lemon exotic. Atika ta jiyewa Hajja a gaban ta sanna tace. 


"Bestie bari naje na watsawa oga ruwa, ga abinci nan kici." Ido ɗaya ta kanne mata alamar tsokana. Da sauri Hajja ta ɗauki trow pillows ta jefeta dashi tana dariya. Gwalo tayi mata ta wuce tana taka rawar shakiyanci. Jay rice ɗin ta jawo ta cika tunbinta ta kora da sanyayyan exoctic ɗin. Hamdala tayi ta jawo wayarta tana duba whatsapp ɗinta. Hoton Areef me kyau ta gani ya ɗora a status ɗinsa. Hawa tayi kai tai comment sannan ta rufe datarta ta. Anan kuma ta faɗa kogin tunanin rayuwarta. Ganin soyayyar Atika da Habib sai taji gaba ɗaya son aure ya kamata. Ta dinga hasasowa gata da Areef ɗinta suna shan soyayya mai cike da tsafta. Gabanta ya faɗi tunowar da tayi akwai babbar badaƙala a cikin aurensu. Hawaye ne ya silalo mata a hankali tayi sauri ta goge jin tahowar Atika.


"Sorry bestie na barki ke kadai."


"No ba komai amaryar Habib karki damu wucewa ma zanyi." Ɓata rai Atika tayi, tayi wuf ta miƙe tana ƙwala kiran Swtiee. Habib ne ya fito da sauri. Cikin shagwaɓa tace. 


"Wai kaji bestie tafiya zatai." Cikin mamaki yake cewa. 


"Haba dai ƙawar mu ya zaki tafi daga zuwan ki?." Ya furta yana murmushi. Dariya tayi ta basu hakuri akan su kyaleta ta tafi saboda yamma tana yi, da kyar Atika ta barta bayan ta zuba mata kayan gara ta kaiwa Umma.


••••

Zaune take tana duba wata jari hankalin ta kachokam yana wajen jaridar har bata ji karar wayar ta ba. Sai da akayi mata 4 missed calls sannan ta ankara kasancewar dama wayar a silent take. Da sauri tabi kiran don tasan akwai wani important abu da zai sa ya kira.


"Chief class rep na ga kiran ka, ina wani aiki ne. " ta fad'a tana k'ara wayar bayan ya d'aga.


"Kaji zata rufta mu, kina chan kina zuke boko yadda xaki defending project, zaki wani ce kina aiki ne. Toh wallahi Malam Audi ne ke nemanmu gobe gaba d'aya. Kuma yace kar mu wuce 10 inaga zeyi coaching namu ne akan yadda zamuyi da external supervisors idan munje yin defense”


"Wayyo Allah. Toh nagode class rep." Ta faɗa tana kashe wayar.


******

Zaune take tana duba wata jari hankalin ta kacokam yana wajen jaridar har bata ji ƙarar wayarta ba. Sai da akayi mata 4 missed calls sannan ta ankara kasancewar dama wayar a silent take. Da sauri tabi kiran don tasan akwai wani important abu da zai sa ya kirata.


"Chief class rep na ga kiranka, ina wani aiki ne." Ta faɗa tana kara wayar bayan ya ɗaga. 


"Kaji zata rufta mu, kina chan kina zuke boko yadda zaki defending project zaki wani ce kina aiki ne. Toh wallahi Malam Audi ne ke nemanmu gobe gaba ɗaya. Kuma yace kar mu wuce 10 inaga zeyi coaching namu ne akan yadda zamuyi da external supervisors idan munje yin defense ɗin.”


"Wayyo Allah. Toh nagode class rep." Ta faɗa tana sauke wayar. 


Washegari ta shirya tsaf cikin doguwar rigarta ta atamfa mai ratsin ja, ta kawo mayafi ɗan madaidaici ta ɗora saman kafaɗarta. Sallama tayiwa Umma sannan ta tari mai napep ta wuce. Tana tafiya cikin napep ɗin taji karar shigowar text message, dubawa tayi inda yake cewa. 


"Zan shigo Buk yau, wait for me, With lurv Areefullah." 


Murmushi tayi ba tare da tayi reply ba ta maida wayar cikin jakarta. Around 9:30am ta isa makarantar lokacin har Malam Audin yazo. Wata paper ya basu kowa ya saka sunan sa da reg. number sannan ya sake basu wasu papers ɗin mai taken guidelines of a project defense. Bayan sun gama suka fito harabar department ɗin su ita da wata kawarta Miss xoxo. Hira sukeyi suna tafiya har suka ƙaraso wajen inda mutane ke danƙare ana hirar yadda zasu ɓullowa lamarin external supervisors ɗinsu samu su fita da excellent cgpa. Kamar daga sama Lionman ya hangota a tsaye tana ta faman dariya. A take yaji gabansa ya faɗi. Wani irin yanayi ya tsinci kansa da ya kasa tantance mai yake faruwa dashi. Tabbas ba zai taɓa mantawa da wannan fuskar yarinyar ba. Tuni abubuwan da suka faru a baya suka shiga dawo masa a kwanyar kansa. Ya tsane ta tsana mai tsanani, tabbas da yasan idan ya shigo BUK zai ganta da be biyewa Areef ya rakoshi ba. Ɓalle murfin motar yayi ya fito cikin wata irin tafiya ya doshe wajen da suke a zazzaune.


"Keeee Mayya...!" Ya faɗa da ɗan ƙarfinsa. Sakin kayan hannunta kawai tayi da sauri ta zabura tana zaro idanuwa, banda bugawa babu abinda kirjinta keyi.


"May i have ur Attention all?." Ya faɗa da ɗan karfi yana kallon cikin idonta. Lion ya kuma matsawa inda take, gabaki ɗaya ƙamshin turaransa ya cika wajan. Duka hankalin students ya dawo wajensu, wasu har sun jawo waya sun shiga cikin camera sun fara vid clip sun ɗauka ko proposing mata zai yi, don yanzun haka ake yi. Hannunsa ya shiga tafawa yana zagayeta kafin yace. 


"Kun ga wannan?..." Ya nuna Hajja da yatsa, cike da tabbatarwa yake cewa.


"Mayya ce....! Mayya....!! Mayya ce.... !!!" Ido waje mutanen wajen suka zaro suna kallon ta. Amsa kuwwa kawai maganar takeyi mata a cikin kunne, gaba ɗaya ta kasa tantance mai ke faruwa a wajan. Wani ɗan kanzagi ne yace;


"Bamu gane bafa, mayya kamar ya?" Murmushin gefen baki lion yayi sannan yace. 


"Yes! Mayya ce wannan yarinyar, ina nufin mayya dai da kuka sani, mayya mai lashe mutane, kuyi a hankali kafin a lashe muku kurwarku." Ya faɗa bayan ya ga tasirin maganar a fuskokinsu. Durkushewa tayi a wajen ta dafe kanta da ya shiga sara mata. A dai-dai lokacin Areef ya ƙaraso wajen da sauri yana duban su, da yake lokacin da suka ƙaraso department of mass communication ɗin, shi sai ya tsaya a wani eatery joint siyowa Hajja lunch saboda shi Lionman gaba yai abinsa yana jiransa ya dawo don ya matsu yaga wacece mystery girl ɗin da Areef kullum ya isheshi da bashi labarinta, shine har ya mai alkawarin yau zai haɗasu su ga juna. Kafin Areef ya ƙaraso su Hajja suka fito daga classes ɗin nasu har hakan tafaru. Hajja durƙushe tana faman hawaye friend's ɗinta sai bata baki sukeyi Miss xoxo dake gefan Hajjan tai saurin ɗagowa tana kallonsa ranta a ɓace take cewa,


“Amma malam baka kyau taba wallahi, Wannan wane irin IZGILANCI ne?! Kai baka santa ba bakai komai ba zaka zo kana faɗar wasu ƙarairayinka..” Cikin wata irin fuska ya juya yana kallan miss xoxo yana cewa. 


“Miss glasses.... Na miki kama da makaryaci ne?! Okay naga alama bakisan ita ɗin mayya bace shi yasa kike cewa haka. Toh shawara nake baki da duk wanda ya keson lafiyarsa yabar wannan y...”


Be ƙarasa ba wata agefe mai suna Stylish bch wacce da alama itama ƙawar Hajjan ce tafara magana tana watsa hannuwa sama,


“Ke xoxo gaskiya ne, shekarun mu huɗu kenan da Hajja bata taɓa kama wani da sunan maita ba gaskiya bamu yarda ba kawai dai yayi ɓatan hanya ne..” Cikin gasgatawa Hafsat Rano tace. 


"Wallahi Hajja ba mayya bace, kaga malam kila mai kama da ita ka sani amma ba wannan ba ce." 


“Hakan yake Rano, wallahi gaskiya ne..” Cewar class rep ɗin su. 


Siririn tsaki Lionman yayi yana wani hura hanci ganin suna neman karya tashi yasa shi ɗaga hannu da niyar sake yin magana Areef ya tsaida shi. 


“Please say no more Hydar.. I heard enough... Ashe kaima kana cikin wanda suka yadda da abinda ake mata IZGILANCI akanshi?! Kai ɗin da nake ganin zaka goyamin baya wajan ganin ta shiga cikin rayuwata kaine kake mata haka?!” Cikin zaro idanuwa haɗe da ɗinbin mamaki Lionman yake duban Areef. Girgiza kai ya shiga yi yana cewa. 


“Bangane ba, karka ce min wannan mayyar dake barazanar lashe kurwar ƴan gidanmu bi-da-bi itace mystery gurl ɗin naka?!” Girgiza kai Areef yai cike da takaicin kalaman Lionman sannan ya ƙarasa inda Hajja take durƙushe tana hawaye ya durkusa saitin ta yana mata magana ƙasa-ƙasa. 


“Am so sorry please, I do not have the exact words to apologize you for. please kiyi hakuri Mon Amour ki tashi mutafi gidah, you guys are creating a scene here. Nd it’s annoying I knw be kyautaba but kiyi hak’uri ki tashi please mutafi.. please mon amour..” Shessheƙar kuka kawai Hajja tacigaba da yi, dan wannan abun kunya Ina zai barta ta iya haɗa idanuwa ta kalli ƴan ajinsu. 


“Hajja ki tashi ku tafi kawai..” Cewar Hafsat Rano. Amman Hajja ta kasa koda motsi. Ganin haka yasa Areef cewa. 


“Ko zaku ɗan taimaka ku kamata sai ku sata a mota mu tafi..” Areef ya faɗa cike da tausayinta. Miss xoxo da rano suka ɗagota, stylish bch ta ɗauki handbag ɗin suka k’arasa da ita cikin mota. Dogon tsaki Lionman yaja ganin an sanya ta cikin motarsu, zuciyarsa na tafasa ya fara tafiya zuwa titi, da sauri Areef ya bishi yana kiran sa. 


“Dude..” Ƙin tsayawa Lionman yayi yaci gaba da tafiyarsa yana jin mugun haushin Areef. 


“Dude please wait..” Areef ya faɗa yana isa wajan sa. A fusace lion yace. 


“What again ahh?! me zakace dani Areef? ka nuna ni ɗin makaryaci ne a gaban mutane abi? Ni nasan wannan yarinyar mayya ce idan baka sani ba kasani dan yanzun babu zancen karya ko wani abun. Na faɗa mayya ce tun wuri ka sake sheƙa ka nemo wata babe ɗin ba wannan ba. Wallahi dana san wannan ce so called mystery girl ɗin dakai dying akanta idan nazo Allah ya tsine min. Kai karasa wacce zaka ɗebo mana sai wannan black ɗin yarinyar kuma mayya dangin mayu? Itace yarinyar data kama hanan fa da Mamah and again...”


“Ssssh....!” Areef yai shushing ɗinsa cikin ɓacin rai. 


“Haba Lionman...Haba....?? Idan hankali ya tafi hankali ke nemo shi fa, ya za’ai acikin course mate's nata kazo kana cewa mayya ce bayan ba hakan bane?.” Cikin fusata Hydar yace. 


“Oh ka zabi budurwarka kenan akan jinin ka ko?! Well Allah ya baka sa’a, kaga nina wuce kawai..” Cewar lionman bai jira Areef ya sake cewa komai ba yai gaba abinsa tare da zaro kwalin Aspen cigarette da lighter ya kunna ya fara zuƙa..


Girgiza kai Areef kawai yai sannan ya koma wajan mota, Hajja na ciki a zaune ta haɗe kanta cikin jikinta sai kuka take yi. Areef ya tashi motar sukabar makarantar zukatansu fal da takaicin furucin lionman wanda shima lionman ɗin harya karasa titi yana mita. Cigarette kuwa yasha tafi kara biyar kafin ya ƙarasa gidah. Kodah suka shiga layin gidan su Hajja a ƙofar gidah Areef yai parking ahankali yake sauraron kukanta harta gama bai hana taba saboda sometimes idan mutum yana cikin ɓacin rai idan yai kukan ya kan ɗanji relief.


“Mon Amour... (my lover)." Areef ya kirata da wata murya mai kama da ta shakku. Shiru bata amsa masa ba saboda zuciyarta har lokacin zafi take mata. 


“Babe please ki ɗago muyi magana..” Murya a dakushe Hajja tace. 


“Kabarni na shiga cikin gida please, wallahi zuciyata ƙuna take yi min..” Areef ya rintsa ido tare da buɗewa yace. 


“Na sani mon amour, shi yasa nakeso ki bari muyi magana tukuna..” Kaɗa kai tai a hankali ba dan tanaso ba.


“Hmmm Mon Amour before anything first kiyi hakuri please da abunda Lionman ya yi miki, cousin ɗina ne first cousin ɗina ma kuwa, shine wanda nace maki agidansu muke yanzu. Ni nasan halinsa idan ya tsani abu haka yake baya yi da sauki, duba da irin area ɗin da suke ta mutane da yawa, so kinsan tsegumi dole yai yawa yau da gobe shi yasa ina jin ya yadda da hakan. Amma dan Allah kiyi hakuri da yanayin IZGILANCIN da yai miki. Abu na biyu kuma ina son ki ƙara dagewa da addu'a da neman tsari akan miyagun mutane dama aljanu. Allah kadai yabarwa kansa sanin komi saboda haka kidena sawa kanki damuwa kada wata lalura ta kama ki please, nima zan tayaki da addu'a har Allah yasa na mallakeki ki zama matata mubar musu garin ma mu koma can peaceful environment daga mu sai babies ɗin mu ko?!” Murmushi Hajja tai tana wasa da ƙasan mayafinta. A hankali tace.


“Ni zan shiga ciki..” Areef yace. 


“Tohm shikenan kigaida Ummah, May be da dare na bullo mu gaisa, ungo wannan tun ɗazu na maki takeaway nashi nasan yayi sanyi ma yanzu sai kin sake reheating nashi..” Ya ƙarasa maganar yana miƙa mata ledojin takeaway ɗin.


“Nagode Allah ƙara buɗi....” Cewar Hajja cikin sanyin murya. 


“Ameen Mrs Areefullah It’s my pleasure and Ina rokonki da kada ki sanarwa su Ummah wannan zancen, please kinga sun manyanta be kamata ace kullum zuciyoyin su cikin damuwa suke ba. Sai dai zaki iya gayawa su Yaya Mubarak idan har damuwar ta maki yawa..”


Nodding kawai tayi sukai sallama dama Hajja daurewa kawai takeyi dan kada ta nuna masa damuwarta akan hakan. Daga haka ta shiga cikin gidah shi kuma yaja motarsa ya tafi. Kamar yadda ta ɗauki alkawari bata faɗawa su Umman ba wanda a nan ne ta yadda cewa tana san Areef. Tsakanin UWA DA ƳA sai Allah. Ganin yanayin da Hajjan ke ciki sai da Ummah ta tambayeta ya taga yanayinta ahaka? Hajjan tace bata jin daɗi ne saboda karatun da sukai na project defense. Umma tai mata faɗa akan ta dena damun kanta karta janyowa jikinta matsala. 


*****

Tunda akai wanann abun Hajja ta daina zuwa duk wani wuri da ta san Lionman zeje, dama Atika ce a wancan layin kuma yanzu tayi aure dan haka kullum yanzu Hajja na gidah ta kwantar da hankalinta bata da wata damuwa. Successfully suka gama defending project nasu sai awaiting of result kuma. Akai-akai Areef yake zuwa zance wajenta duk yabi ya ƙudindine Hajja da duk kan soyayyarsa. Sosai yayi nasarar cinye duka zuciyarta da daddaɗar soyayyarsa wacce sam yanzun damuwarta ƙalilan ce. Month's passed result ya fito Hajja ta fita da first class honor (4:78) tana ɗaya daga cikin waɗanda aka bawa scholarships saboda ƙwazon su. Acikin satin ne kuma aka umarce su da su ciro jamb slip nasu dan jamb tai authenticating nasu a matriculation list na ƴan NYSC. Yanzun har tahfiz Hajja ta fara zuwa a bayan gidansu da wani ustaz ke koya masu ciki harda littattafai na addini, abindai sai sambarka. A satin ne kuma Call Off letter nasu yafi to aka tura ta jihar Lagos ikoyi camp. Sucessfully sukai serving ɗinsu na tsawon sati uku suka dawo gida. Ba ƙaramin daɗi Hajja taji ba don dama tayi relocating zuwa Kano state, Freedom radio suka nemeta ta accepting Letter ɗinsu kuma Alhamdulillah ta samu anan zatai serving for a year kuma dama sun bata gurbi awajen permanently zata fara shirye-shrye guda biyu shirin *Duniyar mu a yau* da kuma d'ayan shirin da zasuyi da abokiyar aikinta me taken *Greatness of youths(Future Leader's)*


****

Kwance Lionman yake akan royal bed ɗinsa ya bararraje sanyin a.c yana ta shiga cikin jikinsa, lokaci zuwa lokaci kuma yana zuƙar tabarsa hannunsa ɗaya kuma riƙe yake da robar Coca-Cola, kallo ɗaya zakaiwa robar kasan ba lemo ne kadai ba akwai wasu abubuwan aciki. idanunsa sun kaɗa sunyi jawur dasu, hannu ɗaya yana zukar sigari ɗayan kuma yana ɗaga robar coke yana sha, ahaka Hanan ƴarsa ta shigo ta sameshi, ai kuwa da gudu ta juya ta koma wajen Mommynta don tasan halinsa idan yana cikin irin wannan halin taje masa toh faɗan da take sha sai ansamu masu tsawatar masa tukun yake Kyaleta..


“Ya kika dawo kima??” Cewar Raudah mahaifiyarta..


“Mommy Daddy ne..”


“Me Daddyn yayi?!” Ta tambaye ta cike da kiɗimewa,


“Kobah naganshi ba yana smoking cigarette, kuma Mommy faɗa zemin idan na tsaya shi yasa.”


“Oh ya Rabbi..” Cewar Raudah ranta a mugun ɓace. Dakyar ta miƙe saboda takaicin Lionman kiri-kiri yake neman lalata ƴarsa don base a tv take ganin ana shaye-shaye ba ra’ayil ayini yakeyi agaban kowa kuma babu abunda aka isa ayi masa. Banging ƙofar tai ta shiga da sallama be amsa ba da alama ya lula duniyar sama ta ƴan shaye-shaye.


“Aliyu we need to talk please..”


Beyi magana ba sai miƙewa dayai yana tangaɗi ya na neman rarumota ta gudu a saba'in zuwa ɗakin Areef ta sanar dashi halin da ake ciki kan ya tsawatar masa idan ma shaye-shayensa zeyi to yayi awaje ba’a cikin gidah ba ƴarsa tana gani. A kafule Areef ya shiga ɗakin Lionman dake tashin weeds da tsamin wine ga kararen tabar nan a zube tsakiyar ɗakin abin sai fatan shiriya kawai. Cin kwalarsa Areef yai dan Lionman ɗin ya kaishi ƙarshen bango. 


“Haba wai lionman fisabilillahi karasa inda zaka dinga shaye-shayenka sai a cikin gidah? cikin gidan ma gaban kowa ciki harda ƴarka? wannan wacce irin musiba ce ka ɗorawa kanka? kai Allah wadaran hali irin naka ma wallahi..” Tuntsirewa da dariya Lionman yayi yana faman layi kai daka ganshi kaga bugagge first class. Cikin maganar ƴan ƙwaya ya fara magana yana ɗaga robar Guinness ɗin hannunsa da alama yagama da coke ɗin yake cewa. 


“Wannan ha..ha...ɗin yafi karfin one gigabits, ina gaya maka 10gig ne akwai weed a ciki sannan akwai loracus, akwai marijuana ga kuma TomTom sannan akwai ku....” Be ƙarasa ba Areef ya rufe mai bakin yana faman dalla masa harara. 


“Dalah yi min shiru, kana zayyano shirmen abubuwanka kamar wani babban abu, kai ba abun kunya ban..” Lionman ne ya katseshi yana faman tangaɗi haɗe da ɗakko hannunsa ɗaya yana pointing kwalbar hannunsa yake cewa. 


“Yeah... yeah... harda kunya duk na... na.. Nasa aciki na wajena..” Ya faɗa sai faman tangaɗi yake yi. Dogon tsaki Areef ya sake saki a karo na babu adadi sannan ya sake shi tare da tura shi ya bugu da gado, cike da takaici ya dallamai harara ya fita. Dariya Lionman ya saki yana sake tuttulawa cikinsa giyarsa kafin ya daki gefan gadon yana cewa. 


“Crazy bitch..” Sai kuma ya hau ɓabɓaka dariya kamar wani sabon mahaukaci.


*Freedom Radio..*


Zaune su Hajja suke ita da abokiyar aikin su kowanne ya fara introducing kansa akan shirin da zasu fara mai taken *DUNIYAR MU A YAU*......!





*HAJJA CE*👈