5
by @mmnashfaq
Nabeeha Aminu ( Mmn Ashfaq )
9/10
Har ya shiga ɗaki wannan kalman tana mishi kuuwa a kunnen shi, yau ko sallaman da yakeyi bai samu daman yiba, yana shiga ya nemi gefen katifan su ya zauna, tare dayin tagumi da dukkan hannun shi biyu, damuwowi sun haɗu sun mishi yawa a kwakwalwar shi, ya rasa ta ina zai fara.
Yafendo ba tare data lura da yanayin shi ba ko kuma mishi sannu da dawowa ta fara mita haɗi da masifa kaman yadda ta saba kullun akan Akmal tace "Dattijo gaskiya nagaji da rayuwa da mara hankalin ɗanka a gidan nan, idan baso kake ya kashe ni ba, to ka nema mishi wajen zama, koni na futa nabar muku gidan kuyi rayuwar ku, ku biyu, yaro kwata kwata bayi da imani da tausayi, kullun da irin salon da yake futar mun a cikin gidan nan, ko albarkacin uwa bayasa ya girmama ni koya raga mun akan banzayen halayyar shi, yanzu a dalilin shi yau kowa da yunwa zai kwana a gidan nan, ɗazu ya fara haukan shi na banza, a garin tambayan shi yasa talge na da garin suka kife, dole sai garin kwaki na nemo nayi gada mirki naci, shi kuma yaci tsiyar shi dan na daina ciyar da ƙaton banza a gidan nan, idan yaga dama yaje yayi aikin ƙarfi ya ciyar da kan shi, idan kuma yaso ya zauna yunwa ya kashe shi, nida zai mutum ma wallahi danafi kowa farin ciki da wannan banzan rayuwar tashi tunda bayi da wani amfani a gare n..."
Wani irin gigitaccen mari ne ya yanke Mata maganan da takeyi ba tare data ƙarasa ba, bai bata daman yin tunanin daga ina marin ya futo ba ya sake wanketa da wasu kwarara guda uku, yana huci yace "tir da kasancewar ki uwa ga ɗana, Allah ma yasan baki da kyakkyawar zuciya shiyasa bai azurtaki da ƴaƴa da yawa ba, nayi dana sanin, sanin ki a duniya ta Yafendo, wallahi akan Akmal ba abun da bazanyi ba, idan kikace zaki taɓa yaron nan, tamkar daidai yake da taɓa auran ki, daga yau naja layi a tsakanin ki da ɗana, tunda ke baki san yadda uwa take lallaɓa ɗanta ba, kije can ki ƙarata da baƙin halin ki"
Yafendo ji takeyi kaman a mafarki take, wai yau itace Dattijo ya mare ta akan ɗanta, wannan wani irin masifa ne yake shirin faruwa da ita, wani irin tashin hankali ne yayi sallama a rayuwar auran ta, tunda take da Dattijo bai taɓa ɗaga Mata murya ba, amma yau shine harda mari da faɗan maganganu marasa daɗi akan ta, zaman ƴan bori tayi ta faɗa duniyar tunanin me takema Akmal na rashin so da har Dattijo yake ganin bata cancanci zama uwa ba, tabbas ya kamata tayi saurin ɗaukan mataki akai tun kafin wannan abun data raina ya ruguza Mata rayuwar farin cikin da take ciki."
Dattijo cikin ɓacin rai ya futa a gidan, tsayawa yayi a ƙofan gida yana tunanin me Akmal yafi so a abinci ya siyo masa, tunawa da yadda Akmal yake son kaza yasa ya nufi tukuban mai gashin kaji.
Tunda ta kwanta bata tashi ba sai ƙarfe ɗayan dare , idon tane taji ya Mata nauyi, kanta yana wani irin sarawa, a hankali ta fara buɗe idon ta harta buɗe gaba ɗaya, zare ido tayi a cikin duhun da take da sauri ta tashi ta zauna, a hankali tace idan ba idona ne ya daina gani ba kaman dare yayi sosai, hannu ta, ta ɗaga sama ta jawo wani igiya wanda makunnin wuta yake jiki, ta kunna a take haske ya mamaye ɗakin, Idon ta takai kan agogon da yake manne a ɗakin ta, taga ƙarfe ɗaya da minti ishiri na dare, dafe kanta tayi tana furta ya Salam, wanna wani irin bacci nayi mara daɗi, ya akayi Mama bata tashe ni nayi salloli ba, wayyo Allah na ya Ubangiji ka shiga lamari na ka mallaka mun wannan bawan naka a matsayin mijin aure na, ina son shi, soyayyar shi ta kamani da ƙarfi, ya shiga zuciyata shiga irin wanda bazan iya futar dashi ba, yama zuciya ta mungun kamu mai tsanani, sha'awar shi ta shigeni da yawa, matse cinyan ta tayi tare da sake wani irin kuka da ƙarfi tace wayyo Allah na, ana mun tsaki a ƙasa ta, wai meyasa duk lokacin dana tuna ka saina shiga mawuyacin hali ne?" Tashi tayi tanajan ƙafa tare da matse cinyan ta, ta nufi bayan gida, tana shiga ta tara ruwa mai zafi ta fara watsawa kanta, ji tayi kaman ana ƙara Mata sha'awar shi, da sauri ta ibo ruwa mai sanyi ta fara tsarki dashi, cikin ƙanƙanin lokaci taji abun da takeji a ƙasan ta ya fara raguwa, ajiyan zuciya ta fara sauƙe wa tana tambayan kanta "dama haka soyayya take? Ko nata ne yazo da haka?"
Wankan soso da sabulu tayi, kafin tayi na tsarki ta futo, bata tsaya goge jiki ba, ta saka ƙatan hijabin ta, ta tada salla, bayan ta idar da sallolin da ake binta, tayi nafila raka'a biyu takaiwa Allah kukanta, ta jima tana addu'a kafin ta tashi taje ta kwantaz ta lunshe idon ta, tana ta ayyana irin rayuwar da zasuyi idan sunyi aure, kafin ta fara tuna rayuwar ta da dalilin zaman su a ƙauyen.
Sunan ta Aishatu Muhammad Nasir Dala, haifaffiyar garin Kaduna ce, iyaye da kakanun ta duka ƴaƴan Kaduna ne, suna da zama a Dokto kwatas, mahaifin ta Shahararen mai kuɗi ne wanda duniyar mu take damawa dashi a yanzu, saidai duk tarin dukiyar shi ƴ......
Contact or chat me👇🏻
***
BA LAIFINA BA NE na kuɗi ne, domin samun karanta shi duka zaku tura 400 ta wannan asusun bankin 0148811051 Nabiyyah Aminu GTbank ko katin MTN ta wannan number ***.
Mmn Ashfaq