NimcyLuv
by @halimahz
Nimcyluv budurwa mai shekaru 26, marubuciya me aji da aiki tuƙuru.
TAMBAYA: Da farko mene cikakken sunanki da kuma taƙaitaccen tarihin rayuwarki?
AMSA: Sunana Na'ima Sulaiman Sarauta. ina zaune a ƙasar Nigeria, garin Kano, a local government ta kumbotso, Zoo road/Sheka. Na yi karatu both Arabic da boko ina matakin aiki, yanzu kuma ina shirye shiryen ƙara komawa makaranta domin samu ilimin da baka da shi, ko burin da kake da shi na karatun ba zaka samu ka yi achieving ba dole sai da Wannan gurbin karatun.
TAMBAYA: ban sani ba ko ke kin sani, amma wasu daga cikin makaranta littafanki na ta so su san ta yanda akai sunan SARAUTA ya raɓu da sunanki, shin za ki iya ba su haske game da hakan?
AMSA: Daga ta ɓangarena da zuri'ata, dangi, sauran ƴan uwa abin a bayyane yake. Ga rayuwar social media wacce bata da tabbas rufaffan sirri ne ga rayuwar kowanne mutum (personal life). Abinda ka so mutum ya sani shi kawai zaka nuna masa a mu'amalarku. Kamar yadda sauran ƴan uwana ke amfani da sunan (Yarima, Prince, Magaji, Queen) ni ban taɓa alaƙanta kai na da hakan ba. Asalin sunan akwai wata Marubuciya mai suna “AUTAR MANYA” Idan muna chat komai ta faɗa na kan ce Uhm, ko dai magana a gajarce har ta ga ji ta auna mini zagi ta ce “Kina abu kamar wata Sarauta ko jinin mulki” Dariya na mata kawai don bana da abin faɗa, kawai ina mamakin yadda sometimes take fahimtata yadda ba kowa na bawa fuskar hakan ba, zan iya cewa ita ce dalili, kuma ta sanya ƙwarya a daidai gurbinta. Duk da sarautar bata ku je ku dawo ba ce🥰👐🏼
TAMBAYA: me yaja ra'ayinki ga fara rubutun littafai? kuma a wacce shekara kika fara? daga lokacin zuwa yanzu kin rubuta littafai mawa?
AMSA: Bani na ke da ra'ayin yin rubutu ba, rubutu ne ya ja ni zuwa cikinsa na yi tsundum. I didn't choose to be a writer, writing chose me to be a writer. Silar aikina na NGO ya sanya na fara rubutu, I can't remember what year I started writing, sbd sanda na rubutu ba sannan na fara sakarwa jama'a ba. Na rubuta a ƙalla littafai wajan 16.
TAMBAYA: kin taka wani matakin nasara ne a sanadin rubutunki? ya batun ƙalubale fa?
AMSA: Uhm! Idan an ce nasara, sai na cewa wanda ya faɗa ƙara murya! Bani da bakin faɗar irin nasarar da na samu a harkar rubutu, ba na da shi da gaske nikam ba na da shi sai dai na ce Allhamdulillah! Akwai mutane da yawa nasara a jininsu take. Da yawa wanda suke ganin baka isa ba, yanzu su ne suke ƙoƙarin ganin sun raɓi inuwarka, ba na da ƙwarewa amma ina da yaƙini akan na Iya. Ƙalubale? Me zan ƙalla na kira ƙalubale har yanzu na kasa fahimtar ƙalubalen da Marubuta su ke cewa sun samu, idan zan kira ƙalubalen da nake fuskanta da babban ƙalubale, bai shige ƙalubalantata da marubuta su ke akan shariya ba. Duk wani sauran abu da zan faɗa shirme ne, da gaske shirme ne don ban sa su aka ba balle har ya zame mini tashin hankali, duk da har group marubuta sun buɗe saboda da Nimcyluv sarauta👐🏼👸🏻 har sharrin da banji ba ban gani ba an yi mini wai na taɓa aure har biyu hadda yara ma🤣sai na yiwa wacce ta faɗa uzuri, mai hankali da lissafi shi ake tankawa ni kuma idan baka gabana baka birgeni ko inuwarka bata da daraja waje na.
TAMBAYA: kina rubutu da wacca manufa?
AMSA: Duniya, Al'umma, Gobena. Ba na rubutu don samun ɗaukaka, domin ita ɗin rigar aro ce, ba na rubutu don neman kuɗi, Sbd shi rubutu lokaci ne.
TAMBAYA: makaranta littafai da yawa na ƙorafi dangane da halayyar wasu marubutan na rashin amsa saƙonninsu, rashin son yin mu'amala da su da kuma nuna musu ɗagawa ganin cewa fa kamar sun fi su ne. ya kike ganin wannan lamarin? kuma ya mu'amalarki da na ki masoyan yake?
AMSA: Haka ne ba haka ba. Kafin sakin jiki da mutum ina fahimtar shi tukun. Ina son masoyana fiye da yadda na ke son Marubuta🫥🤏🏼 , masoya suna ƙashin bayana masu son cigabana a kullum.
Shariya kuma ni kaina ina da wannan, da farko ba na son raini duk abinda zai ja mini raini bamu haɗa hanya da shi ba. Kuma bani da surutu da yawa sun fahimce ni kuma a haka mu ke rayuwa suna sona ina son su. Sai kuma yanayin aiki.
TAMBAYA: A littafanki wanne ya baki wuyar rubutawa? me yasa?...wanne labarin ne kike jinsa har ƙashin ranki a cikin littafanki?
AMSA: Littafai uku suka bani wahala. amma zan iya ba da guda ɗaya MOON; abinda ya sanya ya bani wahala jigon shi; magana ce ta safarar mata dole a samu kuskure idan har rubutun za ka yi da gaske, domin akan rubutun na je har Bampai, na sha wahala sosai ta ɓangaren bincike yadda su ka sauya salo wajan safarar, da ƙasashen da suke kai mata duba da cewa ba ko wacce ƙasa ke lamunta ba, da yadda Deen ya raini Moon da hannayensa tun ƙuruciya har girma, na sha surutu ƙwarai littafin ya je (Viral, ya yi trending a Whasap ƙwarai).
TAMBAYA: A cewar wasu mutanen karatun littafi na ɓata tunani da tarbiyya. shin kina ganin hakan ne?. wanne tsokaci kike da ahi akan wanga batu?. akwai shawara da za ki bayar ga masu karatun littafi akan karatun?
AMSA: Fahimta fuska, manufar mutum zuciyarsa. Marubuta kalma ɗaya ce! Amma tana da faɗi da rabe-rabe, wasu na rubutu don ra'ayi da son ran su, ba tare da suna da ilimin yin hakan ba, wasu kuma don ɗaukaka, masu muhimmancin sune wanda suke domin al'umma da kuma yi da ilimin su. Ina nufin; A da gaske rubutu na ɓata tarbiyya, amma ba kowanne ba, marubutan da suke rubutun da ke ɓata tarbiyya ɗin da basan duniyar marubuta ta halicce su, da wanda ya karanta da wanda ya rubutu zunubin ɗaya ne, za kuma su iske shi. Duk wanda ya yi karatun da zai ɓata masa tarbiyya to son zuciya da umarninta ya bi, ai mutum na da hankalina duk wanda zai karatu yana da hankali, domin abinda zuciya ta yi umarnin mai ita ta bi, akwai littafin da tun a sama za ace na Adult ne idan baka kai 20 ko 18 ya zama haramun gare ka. Me zai sanya ka karanta?
Marubuta kuma su sani zasu girbe abinda suka shuka ne, za su karɓi littafinsu da hannayensu, at this point kowa ya iya allon shi ya wanke.
TAMBAYA: tsakanin rubutun online da bugaggun littafai, wanne yafi ma'ana da tsari? Kuma ke wanne ɓangare ra'ayinki yafi karkata akai?
AMSA: Ko wanne yana da fa'ida Sosai.
BUGAGGE manya sun fi karantawa da kuma maza masu nazari akan abu, kuma yana shiga kasuwanni akwai wanda still basu ɗauki waya da muhimmaci ba.
ONLINE Rubutun online shi ne na zamani, shi ne yake bawa kowa damar karatu, a irin su, Facebook, WhatsApp, Telegram, Arewabooks, Okadabooks, Ebook, Bakandamiyya e.t.c
Ni kam ina yin ko wanne daga na Online har Bugagge
TAMBAYA: akwai wacca kike kallo matsayin madubi ko uwar ɗaki a cikin ƴan uwanki marubuta?
AMSA: Babu! Sbd ni ba komai ke birgeni game da mutum ba, kamar yadda na faɗa miki rubutu ya zaɓe ni, ni kuma na yi masa halacci. Bana karatun da zan ji mutum ya kwanta mini har ya zama madubina. Ina da ra'ayin kai na, my own style. Duk duniyar marubuta mace ɗaya ce ke birgeni itama ba wai madubina ba ce.
TAMBAYA: cikin littafanki wanne ya sanya sunanki ɗagawa?. da wanne Mutane su ka fi saninki?
AMSA: Tirƙashi gobara a gemu🤭 ni da kai na ban sani ba, amma ko wanne littafi yana zuwan da kalar nashi masoyan kuma a kullum masoya ƙaruwa suke, kamar yadda na ke mamakin yawan marubutan da suke mini magana a taƙaice zan iya cewa MOON da UNCLE NE da MIJIN MALAMA.
TAMBAYA: Na'ima akwai wata kalma a fagen masoya da ake kira da SOYAYYAR SHAN MINTI. a matsayinki na marubuciya me hange da nazari da yin duba kan abu kafin ki haskawa masu hankali madubi, ki yi mana fashin baƙi akan kalmar ta SOYAYYAR SHAN MINTI, illolinta da hanyar da kike ganin za'a iya bi don ƙaurace mata?
AMSA: ZAMANI, LOKACI WA'ADi. Su ne suka samar da Soyayyar minti ɗin wacce kuma a yanzu tafi ƙarfi fiye da kima. Dole sai bango ya tsage ƙadangare yake samun wajan shiga, duk abinda aka kira da zamani sai dai a ce; Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Wato soyayya ce wai in jisu idan baka iya ba to baka zama wayayye ba, akwai gaɓar da ake cewa kai budurcinta gidan miji ƙauyanci ne🤓To kai bawa me zaka ce? Duk masu faɗar hakan sai dai ka bisu da addu'a.
Shi namiji yana iya yin sex da mace 100 amma babu wacce yake jin motsin son ta a zuciya, wacce bai taɓa riƙe hannunta ba kuma zai iya bada rayuwarsa sbd ita. Yadda zamani ya jasu zuwa tubalin wahala,haka zai ƙara jan su zuwa tubalin nadama da na shiga uku tabon da ba zai taɓa gogewa daga zuƙantansu ba.
TAMBAYA: matsayinki na ma'aikaciya da wanne lokaci kike samun damar yin rubutu? hakan bai takura rayuwarki? ba ya taɓa lafiyarki?
AMSA: Ina son yin rubutu da daddare, gari yayi shiru na ajjiye kayan ciye-ciyena a gefe. Sbd ko magana ake ina rubuta abinda mutum ya ce, daman kuma bana ƙaunar surutu da ihu a saman ka.
Yana taɓawa, ina yawan fama da ciwon kai amma komai lokaci ne tunda rubutu ciwo ne a zuciya, baka da sauƙi sai ka fitar kamar yadda ba zamu dauwama muna yinsa ba.
TAMBAYA: ban da ahalinki. mutane biyu da ku ka haɗu ta wata silar kike jinsu a tsagi na jikinki?
AMSA: Mutum uku dai😬
A'isha Adam(Ayushercool) Zainab Shehu(Zee kumurya), Nazeefah sabo Nashe.
TAMBAYA: wanne kafafen yanar gizo kika fi amfani da su wanda zai zama sauƙaƙar hanya da masoyinki zai sadu gare ki?
AMSA: Idan ɓangaren gaisawa ne kana iya yi mini Dm a Instagram ko WhatsApp. Idan batun karatun littafi ne kai tsaye zaka saman a arewabooks, da Okadabooks sai facebook.
TAMBAYA: A rayuwa me ke faranta ranki? me ke ɓata miki? me kika fi so a ba ki matsayin kyauta?
AMSA: Abinda ke faranta mini rai bai shige naga farin ciki akan fuskar iyayena ba, kuma ya samu ne ta dalilina. Abu na gaba mutum ya nemi taimako kuma na yi masa inma da kuɗi ko wani abu, ina jin farin ciki sosai.
Bana ƙaunar ban ce abu ba ace na ce, bana ƙaunar takura ko kaɗan, munafurci bai daman ba duk wanda yake yi yaga zai iya, bana son aci zarafina shi yasa bada kowa nake mu'mala ba.
Ina son ayi mini kyauta da turare da kuma chocolate. Ko Abaya ko shoe ko bag, i like fashion.
TAMBAYA: me za ki iya cewa daga ƙarshe?
AMSA: 😬me zan ce ni!
TAMBAYA: Babu fa yi shiru kawai abinki...Wanne fata za kiyi ga wadda ta jagoranci wannan shiri?
AMSA: Fatan alheri a duk inda take, fatan samun rayuwa mai inganci da kwanciyar hankali.
_____________________________
Alhamdulillah! Ƙarshen Interview ɗinmu kenan da Na'ima Sulaiman wadda aka fi sani da NimcyLuv. fatan kun ji daɗin tattaunawar tamu. kuna iya ajiye saƙon ra'ayoyinku a comment section ko kuma ta DM ***, dangane da tattaunawar da muka yi da ita marubuciyar, tambaya a game da ita, tsokaci akan shirin, ƙarin haske dangane da abin da ya shige muku duhu. ku ci gaba da kasancewa tare da ni Halimahz a shafin ArewaBooks domin katari da muhimman abubuwa, ku yi following domin ta hakanne shirye shiryen da zan ke gabatarwa zai riskarku akan lokaci.
FATAN ALKHAIRI...