ZAMAN GIDAMMU(Mai cike da kunci)

Chapter 01

by @jamilaumarjanafty

*ZAMAN GIDANMU*

_(Mai cike da kunci)_


*Wattpad:JamilaUmar315*

*Mallakar:Janafty*

*Arewabook:Jamilaumarjanafty*


*Na Sadaukar da labarin Zaman gidanmu a karo na biyu, zuwa ga My Anty(Auntysis) tare da ke My best Halima yusuf gwarzo, da jajircewan ku Zaman gidammu ya sake zuwa ma su karatu a karo na biyu. Nagode sosai Ubangiji ya sake cika zuciyoyin ku da Alherai masu yawa Ameen*


_Ina gaida Nazifi yarima. Shima sosai ya ba da gudummuwarsa wajen sake zuwan wannan labarin a wannan karon, Janafty tace Madallah da Nazifi Allah ya yi ma rayuwa albarka Ameen._


MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT ***


*B.CLEAR*


Matso kusa kuji amfanonin b clear kamar Haka.....🔥🔥🔥🔥


🌹 Koh kunsan b clear Yana maganin cututtaka da ake kwasa lokacin saduwa???


🌹Ina maza da Mata masu matsalar viginal infection Wanda yake sa kankancewar alaura ga namiji mace Kuma jin zafin saduwa?? Kuzo ga b clear


🌹Ina masu fidda ruwa Mai wari Koh Kuma masu fama da manya manyan marurai b clear na magani da yardar Allah


🌹B clear na taimakawa both mace da namiji masu fama da infertility 


🌹 Ina masu fama da matsalar cikin jini b clear na wanko duk wani matsala ta jini da yardar Allah


🌹B clear na gyara fatar jiki tayi kyau sosai...


🌹Ina Wanda suka kone da wuta Koh ruwan zafi? B clear na taimakawa wurin kamar da wuta maana yayi saurin healing


🌹B clear na ba jikinki kariya daga kamuwa daga duk wani infection da zai shiga jikin Dan adam (immune booster)


🌹B clear na maganin yeast infection

🌹B clear na maganin hatsabibin basir

🌹Ina masu fama da kyankyamin damina kuga jikin mutum Yana kuraje kala kala toh b clear na maganin kuraje price__18,500

Muna Bada rabi ku kwata


Mmn MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT ***


       *🅿️01*


*SHIMFID'A*

*JIGAWA_Dutse.*


Misalin Karfe 2:30pm Na daren Ranar Monday. Litini kenan acikin anguwar Gida Sittin, Sautin karan Alamar din data Saitashi acikin wayarta Wanda ke Tashinta Duk Dare. shine yafara Bugawa Ajikin wayarta Dake Kan wata karamar Dirowa dake Gefen Katifarta

Cikin Natsuwa ta Farka Tare da mika,kafin Ta Zuro da duka kafafunta Waje. Wayar ta Fara Dauka ta kashe alarm di'n kafin tayi amfani da wayar wajen Haska dakin Sakamakon ko'ina ya d'au Duhu Dumdi'm. Nepa sun Dauke Wuta Tun kafin ta kwanta, gen kuma tana Tunanin Mai ya kare ya kashe kanshi,da Hasken Fitilan wayarta tayi amfani ta haska har ta Dangana da Tiolet di'n dake Dakin Tsrki ta Farayi kafin ta Dauro alwala ta Fito tana Tsane Ruwan Fuskarta da hannunta. Kai tsaye Dirowan dake Manne da Katifarta ta Nufa inda ta Dauki Dardumanta ta Shmfid'ata agabas,hijabinta Shima dake Ninke awajen ta Dauka ta Saka Wanda yakai mata har kasa,daga gani ta ijiyeshi ne Domin ibadarta,wayar Hannunta ta ijiye a gefenta, Gabas ta kallah kafin Ta daidaita Natsuwarta Ta Tada Sallah.

Sai tayi Raka'a Goma,sai kuma tayi Shafa"i da Wuturi Raka'a Uku kafin ta Sallame, Cikin Natsuwa ta kalmashe kafarta Ta sanya yatsun Hannunta tana kirga da shi. Ba'a ganin Fuskarta Saboda Dakin yana Da Duhu sai dai ana iya ganin Inuwarta, Cikin hakane Ta Daga Hannayenta Sama tana Kwararoma Allah kirari 


Ya Allah Don Girmanka da Isarka Don Mulkinka. Ya Allah Don Gudurinka Ya Mahaliccin Samai da kasa, Kaine kake Umartan Abu yafaru kuma ya Faru Nan take,Ya Allah kaine Gatan kowani Bawa kai ka Umarci kifi daya Had'iye Annabi Yunusa, kai kuma ka Umarci Wuta Data zama Salama ga Annabi Ibarahimu. Kai ne Shugaban Halittun Duniya,kai ne Ubangijin Annabinmu Muhammad Salallahu alaihi Wasallam, Yakai mai Sunaye Guda 99 Da Tara Nayi Tawasalli dasu ya Allah na sani kana sane dani baka kuma Manta dani ba. Kai ne kake bawa Wanda kaso arziki ko wani k'awan Duniya ka kuma hana Wanda kaso ba don baka son Shi Ba sai don Jaraba imaninsa, Kai kuma ke Aurar da wanda kaso,ka hana wanda kaso,ka azurta wanda kaso ka Hana wanda kaso. Ya Allah na karbi Kadarrata hannu bibbiyu Allah ina Rokon ka Sanya Jinkirina ya Zama alheri, Allah ka Bani Miji na gari wanda Zai Soni Tsakani ga Allah,wanda zai ji kaina ya Mutumtani dani da iyayena Gabadaya..Ya..Allah...Ya.Allah.."


Take Fad'a kuka na cinta kafin Ta kife Fuskarta da Duka Hannayenta tana Sakin Shesshekan kuka mai Cin rai,sai da tayi ya Isheta kafin ta Dago Fuskarta Bayan ta Share Hawayenta,Wayarta ta Dauka ta Duba taga 5 Saura na asuba da Hanzari ta Mike Ta Cire Hijabin jikinta ta Ninkeshi tare da Sallayan ta Maidashi inda ta Daukoshi Tana Kokarin Fitowa Daga Dakin, Sai ga Nepa sun Dawo da Wuta kau kamar Rana,ajiyar Zuciya ta Sauke sai alokacin na d'ago ina kallonta Yar Matashiyar Budurwa ce Wacce akallah zata kai Shekara 26 aduniya Fara ce Doguwa,mai Dauke da Dogon Hanci tana da Fad'in Fuska ammh ba Sosai sai bakinta daya kasance yana da Fadi kada'n, daga gefe da gefe kuma ya Tsuke kanshi. Avkallon Farko in kayi mata zaka Fahimci ta na dakyau daidai misali kayan Barcin dake Jikinta Riga da Wando ne. Kanta na Sanye cikin Wata Hula mai Raga raga kamar ta Sakan Zare, wanda Har ana Iya Hango Kitson kalaban data Hade'su Waje D'aya ta Dauresu da Band,Yanayin yadda kan nata yayi ne zai sa ka Fahimci tana da Yalwar Sumar gashin kai.

ASMA'U LADAN SHARIFF Kenan Tana daga cikin Jerin ya'ya na Uku acikin Jerin ya'ya goma da Allah yabama Alhaji Ladan. ma'akaciyar asibiti ce waccce ke aiki ababban asibitin Jahar Dutse

Cikin Hanzari Ta koma cikin karamin Tiolet din dake Cikin d'akin Ta Jona Kettle dinta bayan ta Cikashi da Ruwa,cikin d'aki ta Dawo ta Bude wani karamin Wardrope d'inta mai kofa Biyu ta Dauki Wani Hijabi Fari mai Kwalliyan Leshi Daga kasa wanda ake Kira Breziya Hijab, Ta sanya shi Saman kayan Barcin ta,batare data Tsaya komai ba ta Isa ga kofar Dakinta ta Zare sakata bayan ta Zura wani Takalminta mai soso ammh yana da Tudu kadan.

Koda ta Fito Tsakar gidan nasu yana da Duhu ita ta saka Hannu ta kunna makunnin Wutan Sai ga Haske ya gauraye Wajen, Bin katon Tsakar Gidan Nake da kallo Wanda yaji interlock ta ko' ina,Daga barayin Inda Jerin Dakinta yake Wasu Kofofine Guda uku wadand'a Ke Jere da Juna. Na farkon Dakin Uwargida ce Wato Ummah,sai na biyun Dakin Mai bi mata Wato Mama sai na Ukun Dakin Ta karshe ce Wacce Suke Kira Anty Amarya,Dukkansu kowacce tana da Makeken Falo ne da kuma 2 bedroom aciki bayan kowanne na Dauke da bayinsa, sai daga gabas kuma Wani Shashe mai girma Wanda nan ne Shashen Abba,sai daga Nesa yammah Shima wani daki ne Wanda nan ne Dakin Hajiya Iya kakarsu kenan,sai daga chan Nesa kuma Wani katon madafi ne ma'ana kitchen, wanda kusa dashi Dakin masu aikinsu ne,Sai Kuma wani korido wanda zai Sada ka da Shashen Rijiya Daga baya kuma inda Bayinsu na waje yake,in kuma ka Mike zaka Fita ne Haraban Gidan inda yake kawace da Filawoyi masu ban Sha'awa Gefe kuma Parking Space ne inda ake Adana Motoci,gasunan ma Guda Uku suna Fake awajen, sai Daga chan kofar Wajen karamin Dakin Megadi ne da kuma katon Get din dayayi ma Gidansu Katanga

Daga Kallon Farko in kayi ma Gidan nasu Sai ka Rainasa kace bai da girma sai ka Shiga cikin Gidan zaka san Gidan yana da Girma Sosai.

Kai Tsaye Madafi Ta nufa kan Windon Wajen ta Ciro key din Ta bude Kofar kitchen din kafin Ta kunna Wutar Kitchen d'in Wanda ya Taimakamata Wajen bayyana Hasken Wajen,:Madafin yana da girma mai Dauke da ciki da Falo wanda da alamun cikin Wajen ijiye kayan abinci ne. shi kuma wajen Inda suke girki ne domin ga gas nan Ajera da Kuma jerin Abubuwan amfani batare da bata lokaci ba ta kunna babban Gas dinsu Mai Hudu kowanne ta aza Tukunya asama Citta ta Dauko ta Daka cikin Wani karamin Turmi ta watsa atukunyar Farko, kafin ta saka kafa ta Bude Wata Dirowa Doya naga ta jawo da Dankalin Turawa,Ta zubesu nan Tsakar kitchen din,Wata yar Kujera ta Hau kafin tsawonta yakai Saman inda Wasu jerin Dirowowi suke nan ta Bude ta Dauko wasu Robobi da Wuka ta Sauko ta tara Kenan Jikin Famfon Dake Sink din kitchen d'in tana Diban Ruwa, dayake daga Wajen Rijiyansu suna jawo Ruwa ta Tankinsu.

Motsin Shigowa taji tayi Saurin waigowa ganin Dattajiwan mai aikinsu Baba Lami yasa ta saki ajiyar Zuciya,Tana Fadin"Ina kwana Baba lami."

Wacce aka kira da Baba Lami ta amsa tana karisowa ciki kitchen din ta ke fad'in"Lafiya lau Asma'ul Husna mai Tagwayen suna, sarkin Tsoro yanzu sai kice na baki Tsoro ko.? Ta fad'a cike da Tsokana,Dan mirmishi tayi kafin tace"Eh mana, Allah bakiji yadda gabana ya Fad'i ba,na zata Shigen beran nan ne dake Shigomana ta Rariya."

Dariya Baba Lami ta Saki kafin tace"Wai naga Tsiya wai Ma'u da Tsoron Bera, anya ke akwai Abunda zai baki Tsoro..? Ahaka dai kamar Jaruma,kullum fa kece mai tashinmu da asuba da Aikinki wanda bakya gajiya."

Mirmishi ta Saki tana Fara Fera doyan da ke hannunra tace"Kai kai Baba Wlh don nasan akwai Mutane ne,da ba kowa yaushe zan Fito wlh Tsoro nake ji.."Tafad'a ashagwabe.

Kusa da ita Baba Lami ta kariso kafin tace"Nasani ai ke sarkin Tsoro ce, ko Farar kura ya Shafa miki lafiya kinga bani Wukar na cigaba da Firan Doyan. maza je ki Shirya yau ba kina da Zuwa asibiti ba.."?

Hanata Wukar tayi tana Fadin"Zanje Mana. Ki barshi zan karisa kinga fa ko sallah ba'ayi ba kiran Sallar farko kad'ai akayi ina Da Sauran lokaci.."Ganin ta Hanata yasa ta Kyaleta sai ta Bude Dirowan kasa ta dauko Wata wukar taja kujera ta Zauna suna Ferewan Tare suna Hiransu ahaka Sauran masu aikin suka Fito suka Samesu,Dama su uku ne Baba Lami,Hassatu,da Zulai,wanda su Ba tsoffafi bane kamar Baba lami,Su suka mata chaa,sai da suka karbi wukar Hannunta.

Itama tana Shirin atashi ne domin taji an Fara kiran Sallah na Biyu Fitowa tayi daga kichen din ta barsu Suna Had'a had'an Faran Soyan Doya da Dankwalin Domin Duk Ranar Duniya Mutan gidan suna da List din Abunda zasu yi breakfast dashi da wanda zasuyi lunch da kuma Wanda zasuyi Dinner.wanann Duk Tsarin Umma ne.

Dakinta ta koma ta Fad'a Cikin Tiolet dinta Huncewa tayi,Kafin ta juye Ruwan Data sanya acikin kittle Tayi wanka dashi bata Fito ba sai da ta Dauro alwala,koda ta Fito har Wasu masallatai Sun Tada Sallah,saboda Saurin kada Lokacin sallah ya Wuce ta ko mai bata Shafa ba. ta Zura wata Doguwar Rigarta baka tana kokarin Shimfid'a sallaya ne taji Fitowar Abbansu yana bugama Anty Amarya kofa Ita da Mama Yana kiran su Walid kan Su Fito su Tafi masallaci.

Raka'atanul Fijir ta farayi kafin tayi Sallar Asuba sai da ta zauna ta gabatar da azkar din Safen daya Riga ya zaman mata jiki. Lokacin data gama Karfe 7 Saura da hanzari Ta mike ta Kwabe Hijabin jikinta,sai da tasha fa Man Shafawarta na OLIVE kana ta Cire Rigar Jikinta cikin Wardrope dinta ta Bude ta Dauko goggun Fararen kayanta Ta saka Riga da wando. wanda Rigar ta kawo mata Gwiwa,Kalaban dake kanta ta Fara tattarata waje d'aya ta saka Band ta Had'eta waje Daya,Farin dankwalinta ta Daura kafin ta Zura wani karamin Farin Hijab dinta,Wajen ma'adanan Takalmanta ta Nufa ta Ciro wani Toms,baki mai Wani kwalliya asama tana gogeshi da wani kyalle. ta dauko kenan Ta zauna Gefen katifarta tana kokarin Sanya Farar Safarta taji sallaman Hassatu amsa mata tayi tana Cigaba da Abunda takeyi don bata son ta makara ko Kadan.

Hassatu ta Shigo Dauke da Wani karamin Faranti mai Dauke da Wani karamin Fulas,da Kula wanda Soyayyen Dankali da kwai ke ciki sai Kofuna Guda biyu,Saurin tashi tayi ta karb'eta tana Fadin"Sannu Hassatu. Da kin barshi ma nazo kitchen na ci kafin na Wuce."

Hassatu na Dariya tana Fadin"Baba Lami ce ta matsa akawo miki batasan kina karin nan naki atsaye tasanki sarkin ujila ce.."Yar Dariya Asma'u tayi tana Saka takalminta take Fad'in"Allah Sarki Baba lami. Toh na gode Hassatu."itama mirmishin Tayi mata kafin Ta Fice tana Fadin"Afito lafiya.."


Adakin ma atsaye tasha Ruwan Tea din Kwan kadai taci kad'an don tana Son Soyayyen kwai sosai, Koda ta Duba karamin agogon Fatan dake Daure atsitsiyan hannunta Karfe 7:20am Daidai Da Sauri ta Zari Wani Blue d'in hijabin data Fito dashi ta Zura asaman Uniform dinta wanda yakai mata Gwiwa karamar bakar Jakarta ta baya. wanda yan matan yanzu ke yayi ta Dauka ta Rataya kafin ta Suri wayarta ta Tura cikin aljihun wandonta Tiren kayan karyawanta ta Dauka ta Fito da Hanzari saboda ta Makara.

Kitchen ta Shiga ta Mikama Hassatu tana Fad'in"Bari na leka na gaida Su Abba yau na makara.."Bata jira Cewarsu ba ta Fad'a dakin Abbanta inda taji hayaniyar su Walid, yana kan kujera acikin kayataccen Falonsa gefensa kuma Uwargida ce Umma ta hakimce,sai Su Walid da ke Tsalle tsalle atsakar dakin,daga chan gefe ta Duke tana Fadin"Ina kwana Abba,Ina kwana Ummi.."Abba ne ya amsa Cikin sakin Fuska yayinda Umma ta amsa cikin Wani yanayi Fuskarta ba Annuri,Tashi Asma'u tayi tana Fadin"Zan tafi wajen aiki Abba,sai yammah zan dawo.."Gyad'a kai yayi kafin yayi Mgana Umma ta rigashi ta tabe baki tana Fadin"UmH...Aikin kenan Yawon zuwa asibiti da sunan aiki. ana Bigewa da gantali wlh Abban Walid kai ne ka zura mata ido Dole sai ka Tsaya ta kawo maka wanda takeso ai kowaye ka samu ka Had'ata dashi, da dai wannan Yawon kan ta zubar din Datakeyi agari ana yi Dakai ."

Tafad'a tana Hararan Asma'u wacce ta sadda kai kasa,Hawaye sun cika mata ido,ammh inda ana Sabo da mgana yaci ace ta saba da Mganganun da Umma take jifanta dashi akullum.


Abba bai Tanka mata ba illah Dagama Asma'u Hannu da yayi yana Fadin"Sai kin dawo yau abini bashin kudin Mota. sai kin dawo zan baki yau ban kwana da kudi ba *MA'U*.." Tana jin haka tayi Saurin Cewa"Bakomai Abba ina da kudi atare dani Allah yakara girma da tsawon kwana.."Da Ameen ya amsa kafin ta Fice da Sauri tana jin Sadda Umma ta rakata da wani uban Dogon Tsaki.

Dakin Hajiya iya ta Shiga inda ta isketa zaune Baje akan Cafet tana Karyawa gefe D'aya kuma cinyar kaza ne ahannunta tana yaga tana korawa da Ruwan Shayin dake hannunta,Hajiya iya kenan Tsohuwa mai Ran karfe,Abba na bala'in sonta da ji da ita,Bata wani Tsufa ba. saboda tana Samun jin dadi,don a akidar karinta bata karyawa da Safe sai da kaza,Komai nata classic ne kamar wata yar Boko nan ko,ko kofar aji bata taba Zuwa ba.

Daga gefenta ta Tsugguna tana Fadin"Ina kwana iya.."Banza da ita tayi har ma ta cire rai da zata amsa,tana Shirin mikewa taji ta tana Fadin"Lafiya.."Daga haka ta Maida kanta ta cigaba da karyawanta Asma'u bata damu ba,illah d'an murmusawan datayi tana Shirin Fita iya ta dago tana Fadin"Hmmm,lalle Aikin kenan Kullum da Safe ashirya afita aiki. ba'a da Burin Aure kwata kwata Allah dai ya sauwake.."Tafada cike da jin Haushi,Wani kallo Asma'u ta makama iya Kafin tace"Ikon Allah Wai ni Iya Don Allah in Tambayeki shin Mijin nan Ana siyoshi akasuwa ne..? Haba kin dameni da mgana D'aya wlh da ana Saida Miji a kasuwa na Tabbata da Uwata ta Siyan min koda mafi Kaskascin daraja ne kodon na Wuce gori da Takaichin da Ake kunsamin acikin gidanan Musamman ma ke.."

Ta Fad'a cike da jin Zafin Abun lokaci Daya idanuwanta suna kawo Ruwa,Tana gama Fadin haka ta Fito afusace tana jin Iya na Zaginta tana Hada'wa da uwarta tana Fadin duk ita da Daure mata gindi to bazata sabu ba,Tana jinta ammh ta mata banza kofar Dakinta ta jawo ta Rufe da makulli saboda bacin rai ko Baba lami bata leka tama sallama ba,balle ta leka dakin Anty Amarya wanda ya zaman mata jiki Duk safe sai ta Shiga sun gaisa kafin ta Fita zuwa wajen aiki.

Ko Baba megadi sama sama suka gaisa ta Fito tana Sauri domin takwas ta kusa kuma 7:30 Masu call ke tafiya bayan sun ma masu aikin safe Handing over, Tafiya kad'an tayi ta isa bakin Titi,tana zuwa ta samu mai adaidaita ta Shiga tana fad'amai inda zai kaita GENERAL HOSPITAL DUTSE.Sun kusa isane taji wayarta na Neman dauki tana Fiddota taga Sister Bahijjja ce ke kiranta bata Daga ba,Saboda sun kusa kawowa babban Get din asibitin.


******

Portharcourt

Eleme


Kokarin Daura nektie d'insa yake agaban Makeken Dressing mirror din dake cikin Bedroom din. Inda yake Sanye cikin American Suit Ruwan Toka.

Na Samfarin DKNY. kafarsa sanye cikin Rufaffen Takalmi na Fatar damisa,hakama hanunsa yana Daure da agogon Fata na Kamfanin Rado,gabadaya dakin ya Bude da kamshin Turaren sa mai kamshi.


Yana juyowa nace Woww,Masha Allah Saboda yadda kyau Tare da Zati suka Dakeni lokaci d'aya. Dogon Namiji ne kakkarfa mai cikar Zati da Haiba Ba Fari bane,baki ne ammh yanayin Fatarsa ta samu Hutu da jin Dadi. Shiyasa Fatanshi ta Murje ta bada Wani Hot colour mai ban Sha'awa,doguwar Fuskarsa ita ke Rud'an Mutane dashi.

saboda yadda Dogon Hancin sa d'an Madaidaicin Hancinsa ya Dace da Dan karamin bakinsa wanda Wani Siririn bakin Saje yayi ma kwanya,Daga kasa kuma wajen gemunsa yana Tsire da wasu munafukan gemu,wanda daga gani zaka Fahimci Gemun na gayu ne. Sai Idanuwansa,Wadanda suke Matsaikata,Gasu Farare masu Dauke da Wani Sirri Wanda ke Rikita duk wata D'iya macen daya sakarmata su. Gashin idonsa zara zara ne,sai Gashin giransa mai cika da baki,haka gashin kansa yake baki Sidif a nannade kamar na Fulani yasha gyara da mayuka masu Tsada yana walkiya,Yana da Fadi daga samansa,Bashi da kiban jiki sai dai Ta murjewa da Hutu.


DEPUTY CONTROLLER GENERAL Kenan Wato DCG ABDALLAH MAHMUD ABDALLAH AZARE kenan Wanda Mutane Dadama Suka Fi sanin sa da M.A Azare. Matashi ne Dan kimanin Shekara 32 da Haihuwa ma'aikacin Costume ne,wanda ke aiki a affice dinsu dake Portharcourt,Onne port Federal Lighter Terminal.

Matashi mai ji da Kudi da aji da Takama Wanda Allah yabama Sirrin kyau da zati Hade da Kwarjini mai cike da Haiba. Burin kowacce ya mace ne Taga ta mallakeshi amtsayin Saurayinta ko Mijinta,Duk ko takamar mace da ajinta komin Mulkinta da ji da kudinta in ta Kalleshi sai taji ta Raina kanta da Duk Abunda ta mallaka.


D'ane ga prof Mahmud Abdallah Azare wanda Babban proffessor ne a jami'ar Abubakar Tafawa balewa Federal University Bauchi.

Wanda ke Zaune da Iyalansa Garin Bauchi.

ba iya Mtsayin Malamin Jami'a ya tsaya ba Malami ne daya Shahara abangaren ilimin Addini da sanin Littafai Dadama,Mutum ne mai dattako da Girma a idon Wanda ya sanshi Da wanda bai taba ganinshi ba ma. da Wanda kuma iya lbrinshi ya Tsira dashi sai yaji Sha'awar samun koda kwatankwacin Hallaya da ilimi irinta Prof Mahamud Abdallah Azare ne.


Agogon Hannunsa ya Duba yaga Har pass 8 Kada k'ai yayi ya Nufi bakin Wani Makeken Royal bed,Wanda yake awani Dunkule kamar alkaki. gefen gadon ya zauna tare da jan Wani makeken bargo mai Taushi,yana Fadin "My NOORY plz wake up hakanan kinsa fa yanzu pass 8 kuma ko sallar Asuba bakiyi ba.."Yafad'a yana Yaye mata bargon data Dunkule aciki kamar ma Mutum bai Shiga ba Saboda Girma da Fadinsa.


Mika ta farayi tana Mutseke ido take Fadin"Plz My DEE Bari na koma After 9 Zan tashi nayi sallar, Allah yanzu barci ne a idona."

Tafad'a ta na mai Kura mai kananun idanuwanta Wad'anda suka kara Shigewa saboda barci,Kallonta yayi kai Tsaye kafin yace"No ki tashi kiyi yanzu. Rana fa ta Fito,ba kyau wasa da Sallah my Wasi ina miki Fad'a Kullum."Dan Mirmishin Makirci tayi kafin ta Mike tana Fadin"Yes my Dee"

Ta fad'a tana Riko hannunsa,Shi kuma yayi Saurin Mikewa yana Dora duka hannuwansa bisa Kafadunta,Da kallo na bita ganin yadda Saboda Rashin Tsawo Bata ma kai ga Kafad'arsa ba,tana da kiba kadan. sannan kuma Farinta na kanti ne,Domin Faffadadiyar Fuskarta ta yii Dodar da ita,kanta kuma yana Daure da kitson Attachement,wanda akayi Shi kanana ya zubo mata har gadon baya duka kumbunan hannayenta Suna Sanye da Karin Kumbuna ba kyan gani. Mummuna ce ta karshe Kawai Kwalliya ce da Shafe Shafe ya maidata haka, girarta bata da gashi Sosai,kamar yadda gashin kanta yake,Hancinta sanye da Hudin hancin,Wanda yakara Fad'ad'a kofar Hancinta,tana Sanye da Wata Karamar Rigar barci pick colour Wacce Ta bayyana Duka Suran jikinta,domin Rigan Shara Shara ne bata Rufe komai ba.

Kiss ya sakarmata A tsakiyar kanta yana Fadin"Zan Fita my Noory.."Lum Tayi da ido kafin tace"Kayi breakfast kuwa...?"Girgiza mata kai yayi yana Fadin!"Zan karya office.."Kai ta gyad'a mai kafin ta sakeshi shikuma ya Fice da Sassarfa yana Kokarin Fiddo wayarsa dake Ruri acikin aljihun wandonsa yana kallon mai kiran sa.

Sunan dake yawo a sreen d'in wayarsa Wato POL1 da Saurin latsa mata Line busy ,yana Saukowa daga Saman Steps din cikin Sassarfa yake Rubuta mata Text.


Meet me in my Guess House Now..,!


Da hanzari ya Tura mata kafin ya Maida wayar aljihun wandonsa. Josepen dake ta kokarin Jera breakfaat a kan Dining table ya Duka yana Fadin"Gud mrning Sir."

Hannu kad'ai ya daga mishi kafin ya karisa tsakiyar Falon inda yaci karo da Kannen Matarsa Wasila. Wato Jamila da Hafsa wadanda Suke Sanye dakkansu da mai bin jiki da kuma wasu kananann Riguna wad'anda suka Fitar Musu da Duka Tsiraicinsu. Kowacce ta baje kan Kujera suna ta Latse latsen waya. Kallo d'aya yayi musu ya kauda kai, suma cikin Yanga suka gaisheshi ya amsa Sama sama kafin ya Fice da Hanzari koda ya isa haraban gidan Direbansa Emeka dake jiransa yayi Saurin Bud'e mai Bayan Motarsa prado ya Shiga da hanzari ya zagaya ya Shiga bangaren Direba yaja da Karfi suka Fice daga gidan Bayan Megadi yabude musu get.










*Janafty*

*19/09/2023*

*Reposting on 20/10/2023*

*Wattpad*

*Arewabook*

*WhatsApp*