ZAMAN GIDAMMU(Mai cike da kunci)
Chapter 02
*ZAMAN GIDANMU*
_(Mai cike da kunci)_
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*
MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT ***
*B.CLEAR*
Matso kusa kuji amfanonin b clear kamar Haka.....🔥🔥🔥🔥
🌹 Koh kunsan b clear Yana maganin cututtaka da ake kwasa lokacin saduwa???
🌹Ina maza da Mata masu matsalar viginal infection Wanda yake sa kankancewar alaura ga namiji mace Kuma jin zafin saduwa?? Kuzo ga b clear
🌹Ina masu fidda ruwa Mai wari Koh Kuma masu fama da manya manyan marurai b clear na magani da yardar Allah
🌹B clear na taimakawa both mace da namiji masu fama da infertility
🌹 Ina masu fama da matsalar cikin jini b clear na wanko duk wani matsala ta jini da yardar Allah
🌹B clear na gyara fatar jiki tayi kyau sosai...
🌹Ina Wanda suka kone da wuta Koh ruwan zafi? B clear na taimakawa wurin kamar da wuta maana yayi saurin healing
🌹B clear na ba jikinki kariya daga kamuwa daga duk wani infection da zai shiga jikin Dan adam (immune booster)
🌹B clear na maganin yeast infection
🌹B clear na maganin hatsabibin basir
🌹Ina masu fama da kyankyamin damina kuga jikin mutum Yana kuraje kala kala toh b clear na maganin kuraje price__18,500
Muna Bada rabi ku kwata
Mmn MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT ***
*🅿️02*
*Area-Rumoula*
Hon Emeka ya zuba abakin Wani d'an karamin get dan Madaidaici. Wani inyamuri ne yazo Ya bude get di'n yana Faman kai gaisuwa ga oga cikin Harshen Turanci.
Tana Tsaye Aharaban gidan Sanye da Wani karamin wando Wanda ko Cinyoyinta bai Rufe ba, sai wata karamar Riga mai hannu D'aya wanda ta bayyanar Da duka Tsiraicinta waje,wanda ko Ramin Cibiyarta yana Waje,Kanta kuwa dauke da gashin Attachement Brown ta Zubosu har gadon baya. Wuyanta dauke da Wata sarka ta alamun Cross , kafarta na Sanye cikin wani Takalmi mai Tsinin bala'i Idanuwanta ta kara musu gashin ido sunyi Zaro zaro,hakama Kumbunan Hannunta suke zako zako Sunsha penti. Fara ce Doguwa Duk da tana karawa Dana kanti ammh babu Laifi tana da kyanta Daidai gwargwardo.
*POLINA JOSAYA* Kenan Arniya ce Kuma tangararriyar karuwa wacce taga Duniya kala kala. Abokiyar Holewar M.A ne Suna Tare Tun Shekaru Uku da Suka Wuce,kuma yakasa Rabuwa da ita,Tun kafin motar ta gama parking ta Nufeshi cikin yanga da kwakwarsa Ita ta budemai Murfin Mota ya sawo kanshi waje. Tunkafin Yagama Daidaita Tsayuwarshi Ta cakumoshi Zuwa Jikinta Cikin Wata murya mai Cike da Shagwaba tace"U know i miss u so much *MY SUGAR*.?
Tafad'a tana Fito da Harshenta tana lasan Gefen Wuyanshi kamar Wata mayya.
Rumgumota yayi Sosai yana kissing gefen Wuyanta Suka Fara Tafiya Zuwa cikin gidan Yake Fadin"I know Babe buh Stop give me a call. juzt text me kin riga kin sani, duk Ranar da My Noory ta ganoki Both of us We got into Trouble.."Batama Saurareshi ba Bakinta ta Had'a Danashi lokaci Daya Tana Shafa Sassan jikinsa,shikuma cikin kwarewa ya cakumi kirjinta Ahaka suka Shiga Falon gidan Suna Tsotsen Bakin Juna kamar Wasu mayunwata. Dakyar Polina ta bari suka Shiga bedroom Saboda yadda idonta ya Rufe Ta kosa taji ji sa a jikinta.
Cikin besdroom din Suka Shiga chan Suka Cigaba da lalacewarsu.
******
BAUCHI
*Area-Federal lowcost*
Zaune Suke Dukkansu a kayatattacen Falon na Hajiya. wacce ke Zaune kan lallausan Cafet din daya Malale dakin,Ta jingina da kujera gefenta an saka mata kananan Filulluka Guda biyu,Daga yadda take Yamutsa fuska Daga gani Bata da lafiya ne.
Ya'yan na ta Guda biyu mata Wato *ANTY NAFISA* da kuma *ANTY SAFINA* Sune Suka Tasata agaba Suna Faman mata Sannu. kai kad'ai ta ke d'aga musu Ta maida kanta ta Jingina da kujera tana Runtse ido, Anty Nafisa ce Ta kalli Hajiya ta Girgiza kai kafin ta Maida kallonta kan Anty Safina tana Fadin"Wai ni kan Anty Safina ba Wanda zai iya zuwa gidan Ya Baffan ya gano ko lafiyanshi kalau..? Wlh kina ganin Duk wannan Tashin Ciwon Na Hajiya Tunaninshi Ta Daurama kanta."
Anty Safina dake Ba ma karamar Diyarta Nono tace"Wazai je Nafisa, kema kinsan banda YA YUSUF ba wanda yasan Address din gidan ya baffa. to koma mun sani kinsan ko giyan wake muka sha Mallam bazai barmu muje ba,sanin Halin wannan Tsinanniyar Matar nashi wacce bata ganin kowa da gashi.
karshenta ta Wulakantamu Ta hanamu Shiga.."Ta fad'a Tana kwafa da alamun Abun na Cimata Tuwo kwarya.
Hajiya Datayi Shuru kamar batajin Me Suke Fad'a,tana jin Duk Abunda Suke Fadi,mirmishin gefen baki tayi batare ta ce komai ba. Anty Nafisa ko da Anty Safina suka cigaba ta tattaunawa har MAMAN FATI tayi sallama ta Shigo dakin. nan dukkansu suka gaisheta ta amsa cikin sakin Fuska tana Fadin"Ina wanka naji Shigowarku,Kunzo duba Hajiya ne..?
Anty Nafisa ce tace"Eh Maman Fati, Hajiya dai jiki yaki Dad'i,wai anya Mama Fati baza'a yi Wani abu akan Abunda ke Damun Hajiya ba.?
Wacce aka kira da Maman Fati ta Nemi gefen Hajiya ta Zauna tana Fadin"Toh Nafisa me za'ayi?,damuwarta bai Wuce Baffa ba. kuma Mallam yahana kowa mganarsa agidan nan nikaina Abun na damuna, ace ka Rataye iyayenka Fiye da Shekara daya,ammh ko waiwaiyansu bakayi ba,Anya Ba lauje cikin Nad'i acikin wannan al'amarin kuwa?
Anty Safina tace"Wlh Maman Fati matarnan ta Asirce Ya Baffa. kiga fa ko su Hajiya baya gani da gashi daga ita sai yan'uwanta Sune Mutane awajensu. mu yanzu haka ya Rataye Nombobinmu ko ka kirashi baka samunshi.."
Anty Nafisa zatayi mgana kenan Sukaji gyaran Muryan Prof.Abdallah Mahmud Azare. Mahaifinsu wanda kowa yake kiranshi da Mallam,da Sallama ya Shigo Falon na Hajiya Bayansa Dr Nura ne Likitansu ne.
shike Zuwa Dubasu in wani matsala tataso,dukkansu suka Shiga gaisheshi ya amsa cikin sakin Fuska,Tsohon Dattijo ne mai Haiba da kwarjini. Akallah ashekaru zai kai 70 aduniya, Dogo ne Fari ammh Farin gashi ya baibaye kanshi Da kuma Farin gemunshi. kallon Farko zaka masa ka Fahimci ilimin addini dana boko ya Ratsashi Duba da yarda Fuskarsa ke sanye da Wani Farin gilashi mai kara karfin gani. Akallon Farko in ka yi masa. Zaka Fahinci Tsantsan Kama da Suke yi da Abdallah,domin Hatta dogon Karan Hancinsu iri d'aya ne.
Mutun ne wanda yasan kimar D'an Adam da kuma sanin yakamata ba kowa ke Fahintar damuwar Mallam. bai cika bama Fuskarsa damar bayyanar Abunda ke Cikin Ransa ba, yana da kyakyawan alaqa da mutane,uwa uba Matansa da ya'yansa wand'anda suke Tamkar wasu Bangare na jinin jikinsa.
Maida gaisuwansu sukayi kan Mallam. Amal yar wajen Nafisa ya dauka yana Fadin"Saukar yaushe ya'yan Hajiya..?Anty Safina na Dariya tace"Bamu Dad'e da Zuwa ba Mallam.."
Yana kallon Hajiya tace"Kunzo Duba Mamarku ce. Kurika yi mata Fad'a ta cire Tunani acikin Ranta saboda jninta yahau sosai yanzuma mganar da Muke da Dr.Nura kenan."
Anty Nafi ce tace"Mganar da mukeyi kenan Fa,Hajiya bazata daina Tunanin ya Baffa ba mallam me zai hana ayi masa waya asanar dashi batajin dad'i kila in Matartasa taga dama ta barshi yazo ko ta ganshi taji Dadi.."
Mallam bai yi mgana ba,illah mirmishi kad'ai dayayi yana Kallon Dr Nura wanda ke gwada Bp Din Hajiya. sai da yagama Dubata kana ya kalleta yana Fadin"Hajiya gaskiya jininki ya ki daidaita. bakya Taimakonmu wajen Ragema kanki damuwa,Ga kuma Shekaru Don Allah Hajiya ki Rage zama Shuru da kuma Shiga Tunani mai yawa"Shuru tayi batayi mgana ba sai chan tace"Insha Allahu Dr za'a rage.."Tafad'a cikin muryan Ciwo. Gyada kai yayi kafin yace"Yauwa hajiya naji dad'i yanzu zan Wuce asibiti sai zuwa anjuma in nadawo zan biyo na kawo miki sauran mgungunarki.Allah yakara lafiya.."
Gabadaya Dakin suka amsa da Ameen.
mikewa Dr Nura yayi bayan ya Ramkwafa Yana ma Mallam sallama,Hannu Mallam din ya mika masa hannu sukayi masabaha kafin yayi sallama dasu ya Fita Mallam yabu bayanshi.
Bai dad'e ba ya Dawo dakin ya mika ma Anty Nafi Amal yana kallon Hajiya kai Tsaye yace"Hajara kinji dai ji Abunda Dr Nura yace Ko..? Bata dago ba ta gyad'a kai Gyara tsayuwa yayi yana Fadin"Toh ya rage Naki ki Rage ma kanki saka Tunani da damuwa kan yaron da baisan kinayi ba. saunawa zan gayamiki Hajara Baffa ba damuwarki yakeso ba addu'anki yake Bukata. Mu ma fa ba bamu sonshi bane,da kika ga Bamu Nuna damuwa akan Halin daya ke ciki ba. Wlh munfi ki damuwa Hajara kawai muna boyewa ne saboda kada muba damuwa dama tazo tayima illah.
Don Allah Hajara kicire Komai aranki Mu dage da yima Baffan addu'an Allah ya warware masa Duk Abunda ya Shige masa Duhu.."
Hajiya tayi Shuru tana Share Siririyar kwallar Data Zubomata Cikin sanyin Murya tace"Haba Mallam mganar Na dai damuwa fa Duk bata taso ba. kaduba ka gani Yaushe Rabon Baffa da garin nan Har Ciwo nayi na kwanta asibiti ba sau daya ba,bai zo biyu ba. Kanwarsa Tazo ta Rasu wajen Haihuwa Shima bai zo ba,Kuma yusuf ya sanar dani da bakinsa ya Fad'amai ammh bai zo ba. kuma bai kira waya ba,Tun ina kiran wayarshi baya dauka Karahema na daina samunshi. haka zamu Zurama Baffa ido ya lalace a gindin wannan Tambadad'diyar matar tashi da yan"uwanta"
Tafad'a Hawaye suna Zubomata Cikin tsausayi Maman Fati da Dafa kafad'anta tana bata baki
Mirmishin yake Mallam yayi kafin yace"Hajara kenan.! Ai shi yana ganin Duk Abunda yayi Daidai ne kuma da kike kiran matarshi Tabadad'diya toh ai gashi ya zabeta fiye dake. shiyasa nake kara Sanar dake mu dage da addu'a ammh babban Abun Takaichn Shine Baffa bashi da kokarin ibada balle addu'an tsari. shiyasa koma miye za'ayi mai bazai yi Wahalan kamashi. Bance karki damu ba,ammh ki Rage ko don samuwar Lafiyanki Don Allah Hajara."
Jin Haka yasa ta gyad'a kai Tana Fadin"Naji zan kiyaye insha Allahu."Yaji Dadin Haka kai tsaye yace"Alhamdullilah Allah ya kara lafiya. shikuma Allah ya warwarwaremai Abunda ke damunshi"
Gabadayansu suka amsa da Ameen kafin ya Fice Daga dakin. bayan Fitan nashi maa Su Anty Nafi hirarsu suka Dasa,da hajiya ta gaji daji tashi tayi ta Shige cikin bedroom dinta cike da damuwa ya'yan nata Suka bita da kallo. Sunfi kowa sanin yadda Yaya Baffa yake awajen Hajiya bata iya Hadasa da kowa duk acikinsu tafi sonshi Don ma tana mai kawaichin dan Fari ne. Kuma dama Hausawa sunce Duk d'an kafi so. shike Wahalar dakai.
Haka dai Suka cigaba Da tattauna Mtsalan yaya Baffa. har zuwa lokacin da aka kira sallar la'asar,suka mike suka gabatar da sallah. suka Fita waje Suka taya Maman Fati hada had'ar Dora abincin Dare,suna gidan kananan kanensu suka dawo daga mkrantan Boko. Fati da Mahmud,da Suka kuma yi Shirin Zuwa islamiya. Mallam ko yana Cikin dakinsa bai kara lekowa ba, shima ko bai Fada ba Mtsalan ta Baffa tana damunshi bayason Nunawa ne. Saboda kada ya karama Hajiya Wata damuwa, ammh ko su da suke kannenshi suna cikin damuwa da Wannan Halin da Yaya Baffa ke ciki, ammh gaskiyan Mallam ne,babu Abunda yake Bukata sai addu'a Tunda Allah ya Hadashi da Shedaniyar Mata mara Tsoron Allah.
Tare sukayi girkin Dare Su da Maman Fati suna yi suna Hirar Duniya babu Ruwansu in ka gansu bazaka ce Maman Fati abokiyar Zaman Hajiya Bace. saboda yadda take Tafiyar dasu kamar yaran data Haifa da cikinta,Sai Wajen 8 na dare kowacce Mijinta yazo ya Dauketa suka Nufi gida,dayake Duk anan garin Bauchin suke aure,ammh sai da suka Shiga wajen Hajiya suna kara Rokonta ta Cire Dukkan Wani Tunani aranta in har Takamar Wasila boka da Mallam. su kuma zasu Nuna mata Babu Abunda yafi karfin Allah. Hajiya taji dadin mganarsu Tayi ta saka musu albarka dama ita Abunda bataso Su Rika ganin laifin Baffa,wanda tasan da gangan Baffa bazai ki Zuwa wajensu ba,sai dai in da wani Dalili mai girma.
****
Tana Shirin Baro Wajen aikinta Suna Baban Falo ita da Sister bahijja bayan Sungama Round din ba da mganin karfe 6 na yammah. suna Zaune bisa wasu Fararen Kujeru suna hira ita da Sister bahijja,taji wayarta dake cikin karamar jakarta dake kan Teburin dake wajen ta dau Tsuwa,Ringing Tone din Dataji ne yasa ta saki mirmishin Mai kayatarwa sanin kowaye ke kiranta.
Cikin Azama ta jawo jakarta ta ciro wayarta inda taga Sunan mai kira Baro baro kamar Haka *RABIN RAINA* Cikin Doki ta daga kiran Tana Fadin"Rabin Raina kina Lafiya..? .Dagachan bangaren Aisha tace"Ina fa lafiya Rabin Raina,kwana nawa ban ganki ba na zata zaki zo cikin weekend din nan ammh naji ki Shuru"Tafad'a cike da Shagwaba.
Dariya Asma'u tayi kafin tace"yi hakuri Rabin Raina kinsan dai Halin da'ake ciki in ba Ranar aiki ba bana samun Fita. ki bari gobe in na Fito sai na biyo kafin nazo asibiti.."Tura baki Aisha tayi tana Fadin"wlh ban yarda ba. Nidai kizo yanzu in kintashi aiki gama D'anki nan yana ta Fama da zazzabi.."Zaro ido Asma'u tayi tana Fadin"Na Shiga uku meya Faru dashi Rabin Raina..? .
Aisha na gintse dariyarta tace"Zazzabi ne ke damunsa ,ammh na bashi mgani.."Asma"u najin haka tayi Tsaki tana Fadin"Baki kaishi asibiti ba? Gaskiya kina da sakaci Rabin Raina yaro baida lafiya ku barshi agida kuna Zencen wai kin bashi mgani,Allah daga ke Har Fahad din sai ahankali zan biyo yanzu in natashi Daga wajen aiki.."..
Tana Fad'ar haka ta yanke kiran. Aisha dake kusa da Fahad ta saki Dariyar Jin dadi tana Fad'amai Bisa kafad'a take Fadin"Allah sarki Rabin Raina. Bata wasa da Abunda ya Shafi Amir dinta,kaga yadda ta fara fad'anta na Fama gatanan zuwa yanzu.."Kanta ya Shafa yana Fadin"Baki da dama yanzu zaki sa in tazo taga karyane ta had'ani dani dake tayi ta Mana Fad'a ko.?
Dariya Aisha ta saki batare datayi mgana ba. Ranta yayi mata Dadi Jin Rabin Ranta zata Zo yanzu.
Itako hankalinta Duk ya tashi,Karfe 6:30pm suka tashi daga aiki Ko tsayawa Signing din Tashi batayi ba Sister Bahijja ta barmawa ta Fito da Sauri rataye da jakarta.
Adaidaita ta tara ta ce ya kaita G9,Bai Direta ako'ina ba sai akofar wani dan Madaidaicin gida,Kudinshi ta bashi kafin ta karisa bakin Get din ta Shiga kwankwasawa.
Aisha dake Jikin Fahad ta Saki dariya kafin ta kwalama Amir kira dake Haraban gidan yana Buga kwallo,Cikin daga murya tace"MAza Son Ruga ka bud'ema Mom dinka get.."
Yana jin tace Mom dinshi ya Kwashi Gudu yaje ya Bude mata sakatar get din,dayake Wajen sakatar bata da Tsawo yana dage zai kamota,Yana bude mata ya Tafi ya Fad:a jikinta yana Fadin"oyoyo Momy na,Sannu da Zuwa.."Cike da mamaki ta Hau Shafa kanshi bayan ta Rikoshi sun Shigo gidan Cikin Mamaki take Fadin"My Son ya jikinka. naji dadin ganinka kaji Sauki yarona.."..
Yana Rike da Hannunta yace"Ni lafiyata lau Momy. yanzu na dawo Daga islamiya ma Mommy.."Kura mai ido tayi tana kallonsa aranta tana Fatan Allah ya Shirya Aisha,hannunsa taja suka Fad'a Falon da sallama,da gudu Aisha ta bar jikin Fahad ta isa ga Asma'u ta Fad'a jikinta suka kamkame Juna.
Rumgumeta Asma'u tayi Tana Fadin"Uwar banza,mai Sama D'anta ciwo ko.?
Dariya ta kama Aisha ta saketa tana Fadin"Nasan in ba haka nace miki ba bazaki zo ba,gashi ni kuma nayi missing dinki over Rabin Raina.."Tafada tana Wani Shagwabe Fuska.
Tsaki Asma'u taja kafin tace"Allah ya Shiryeki bansan yaushe zaki Girma ba."
Tafad'a suna karisawa cikin Falon sai lokacin taga Fahad yana zaune kan Kujera yana musu Dariya,baki Asma'u ta Rike tana Fadin"Au kaima kana nan daman. Wlh wani Abun kai kake biye ma Rabin Rai tana Abunda taga dama,Allah ya Shiryeku.."Atare suka amsa da Ameen suna mata dariya.
A tsaye Suka gaisa da Fahad. ita kuma Aisha taje kichen kawo mata Ruwa,Amir ko na wajenta ta fiddomai Tsarabarsa data Siyamai akofar asibtin. Dakyar ta tsaya tasha Ruwa kafin tayi musu sallama ta Wuce basu barta hakaba Sai da Fahad ya matsa zai kaita gida data Nuna bataso. sai Aisha taji Haushi Dole ta amince. ya Fito da motarsa kirar 306 Aisha da Amir na daga musu hannu suka bar Haraban gidan.
*Janafty*